Sashe 35
Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washe gari tunda mukayi sallar asubahi bamu koma bacci ba. da sassafe muka shirya tafiya har Baba ya rakomu har mota da Mama anty kam bata fitoba dan ita wajanda Ya Ahmad yake bata zama dan bayajin tsoron disgracing É—inta gaban kowa. harda Yaya habibu a tafiyar. Mu bamusanma dashi za'a tafi ba sai ganinsa mukayi ya shirya ya fito. Muka shiga motar dukanmu muna baya sai Yaya habibu yana zaune agaba.
Addu'a Baba yasanya mukayi sannan yayi mana sallama nan da nan naji idanuwana sun fara cikowa da hawaye dan tunda nake bantaɓa tafiya nabarsu ba koda sau ɗaya ne kullum inanan ina naniƙe da iyayena. Idona taciko taff na runtsesu inajin wani iri acikin zuciyata kamar wacce zantafi nabardu gabaki ɗaya. Har muka ɗauki hanya addu'a nakeyi acikin raina idona suna lumshe ban buɗesu ba. Ina jiyosu har suka fara hira. ban buɗe idanuwana na ba har saida naji ƙarar wayata ina dubawa naga Hamma batareda na amsa ba najira ta katse na sanyata a silent na maida jaka. Anata hira bansaka baki ba sai can yaa Ahmad yace.
"Wai ina marmeeyy ce ko bacci tayine?"
"Ganinnan" nabashi amsa.
"Naji bakinne ya mutu muÉ—us. Kardai duk san tafiyar abakine?"
"A'a Yaya kasan nifa bantaɓa tafiya ba"
"Tooh kar amin amai amota" yafaɗa hankalinsa yana kan tuƙinsa. Tunda muka fara nisa ya lura da wata mota a gabanmu ɓaka siɗik wanda taɗan bamu tazara kaɗan. Bayan kusan 30minute ya gano wata a bayanmu motocin ba iri ɗaya bane amma jikinsa yabashi tafiyarsu ɗaya kokuma yace tafiyarmu ɗaya atakaice. Ta bayanmu bata zo ta wuce ba dukda bawani gudu muke ba, ƴat tazara tabada a tsakaninmu. ta saita speed ɗinta dai-dai da namu namu yanda tazarar bazatayi yawa ba sannan kuma kusancin bazaiyi yawa ba. Ta gabanmu kuma batayi nisa damu sosai ba. sunyi abun atsari yanda baza'a fahimci komai ba amma Yaa Ahmad dake yasan komai dole zai fahimci wani abun.
Murmushi kawai yayi dan ya tabba wannan motar tare muke tafiya dasu. Yayi tsammanin hakan sai yaji abun ya matuƙar birgeshi dan koshine a matsayin Hammood zai bawa abunda yakeso tsaro na mamaki wanda idanba ikon Allah
ba babu wani abunda zai iya tunkarar abunda yakeso. Hankalinsa ƙwance yake tuƙinsa har muka kusa isa Abuja."
__________
Ƙarfe uku na dare jirginsu ya sauƙa a Abuja cikin sirri dan babu wanda yasanda hakan. Ko ma'aikatan filin jirgin manyan kawai sukasan da sauƙar kuma angargaɗesu da kar kowa yasani dan haka bbau wani yasani daga ƙofar filin jirgin motaci sukazo taryansu aka wuce dasu masauƙinsu.
Yariga mahaifinsa sauƙa danshi sai awajan asubahi ya sauƙa dama shi yake jira tafiyarsu da bambanci.shi daga Abu dhabi yazo mahaifinsa daga kuwait kuma lokacin tashinsu ba ɗaya ba so dole aka samu bambamcin lokaci dama shi isowar mahaifinsa yake jira so yana isowa jirginsu yatashi zuwa bauchi Acan sukayi sallar Asubahi.
Abhie yana sanardashi cewa Nawrah ta matsa sai yazo da ita. Baizo da itaba saboda bai fahimci amfanin zuwannta a yanzu ba yayi mata alƙawarin next zuwa da ita zaizo amma yanzuma yasan halinta da taurin kai ba lallai idan ya amince ta zauna ɗinba. Murmushi kawai moood yayi sanin cewa sassafe Marmeeyy zatabar garin koda tayi gigin zuwa bazata haɗuda itaba dan yasan damuwarta ta ganta ne kawai, shikuma ba yanzu yayi niyyar nunawa duniya itaba yasan wacece Nawrah da zarar da santa ta kowa ya santa. Yasan yanda rayuwarsa take akan idon mutane ko kaya yasaka sai an faɗi kuɗinsa har turarenda yake shafawa mutane sunsan kuɗinsa. Amma wannan karon lamarin ysha bambam. Ya barwa mutane abunda yaga damar su sani amma banda wannan itaɗin sirrinsa.
ZAYNAB BAWA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya
A lokutan baya aryuwarsa baiyi tunanin akwai abubuwa masu muhimminanci wanda muhimmancinsu har yakai bazai iya fitowa duniya ya nuna musu ba sai yanzu daya kamuda soyayya a cikin zuciyarsa. Yana Masifar sonta da kishinta wanda yasa bazai iya jurar ganin ta ɗaura pics ɗinta a social media ba. Aranarda taɗaura pics ɗinta batareda niqab da Hijab ba ji yayi kamar zaibar duniya dan baƙin ciki. Yanzu yasan yanda ake tallali da ɓoyen abunda akeso. Kuma shi koda nan gaba bayida ra'ayin fitowa ya nunawa duniya suffar rayuwarsa da matarsa wato yana nufin kamar yanda celebraties suke ɗaura matansu da rayuwarsu su nunawa duniua shi bazai iya ɗaura musu ita su gani ba. Marmeeyy tasa ce shi kaɗai batareda fans ɗinsa da sauran mutanen duniya ba. Zai killace abarsa ya bata kulawa. Amma yanzu lokaci baiyi ba da zai sanarwa da duniya da zamanta alokacinda zai yi hakan toh yanada tabbacin yanada ikon da zai iya kareta kota wace hanyace yana nufin alokacinda tadawo ƙarƙashinsa yana kallonta kusa dashi.
  ƙarfe 12:00pm tayi musu a cikin gidan Baba dayake dama Baba yasan da zuwannasu dan haka yayiwa Alhaji Habibu magana. Mahaifin Mama kenan shi kaɗai suka taryesu.
A wancan lokacin da Mood yazo wajan Baba yaɗauki week guda yana jigila amma Baba yaƙi yarda ya amince masa da bashi auren Marmeeyy. Baba kuwa yayi hakane bawai dan bai yarda da Halayansa da soyayyarsa ba. Celebraties gabaki ɗaya rayuwarsu a fili take. Barinma footballers ko shaye-shaye player yakeyida neman mata ansani saboda su kansu ƙungiyar ƙwallon sunada nasu ƙa'idojin. Duk wannan shirmen basa ɗaukarsa. Soyayya kuma har indai zai tsalleke kaff matanda suke gabansa celebreaties da masu faɗa aji a duniyar baki ɗayanta yazo neman auren Marmeeyy wacce a anguwarsu ma ba wanda ya santa sai ƴan tsirarrun mutane toh lallai soyayya takai a kirata soyayya. Tun zuwansa na farko ya yanke shawarar bashi auren Marmeeyy amma dole saiya gwada masa muhimmancinsa ƴarsa. Yasan komai ya nema a rayuwarsa yana samunsa cikin sauƙi amma yanaso ya gwada masa banda ƴarsa dole saiyasan darajarta kafin yabashi aurenta.
Saida yayi shawara da Yaa Ahmad. Dafarko ya Ahmada kamar almara yaɗauki abun dukda yasan Baba bazaiyi masa wasa ba har saida yaga Mood da idanuwansa. Bayan sun haɗu Ya Ahamd yabashi goyon baya ɗari bisa ɗari yasake ƙarfafa masa guiwa akan hukuncinda ya yanke.
 Daga nan Baba ya yankewa zuciyarsa da zai bashi aurenta tunda ya fahimci abune mawyyaci yasamu wanda yake sonta kuma zai kulada ita kamarsa. Tun aranar farko ya fahimci hakan. Shiyasa tin ranar Ya roƙi alfarma a wajanta saboda zai yanke hukunci akanta. Alokacin zuciyarsama bata gama tsayawa hukuncin daya yanke ba amma magana da Ya Ahmad yasa ya tsayarda zuciyarsa waje ɗaya. Yasan duk yanda akaje akazo zai amincewa aurenne. Tun alokacin wancan zuwan Baba ya amince masa yayi alƙawarin bashi aurenta shiyasa yakoma cikeda ƙwarin guiwa amma sai dai shima Baba ya nemi alfarmar karya nuna mata kansa kamar yanda bata sanshi ba suyita tafiya ahaka har sai lokacinda Baban da kansa ya bashi umarnin hakan. Mood Ya aminta da hakan ɗari bisa ɗari dan shima kansa yaga ƙarancin shekarunta sosai. Ko wannan zuwan kafin suzo saida suka sanarda Baba. Dan haka ya rigada ya shiryawa zuwan nasu. Suna zauna sun tattauna sosai akan maganar har suka kaiga matsaya a amma sai washe gari zasu gama yanke magana. Baba da Alhaji Habibu ganin abun sukeyi kamar amfarki kamar wani almara gani yakeyi kaman zai tashi a bacci yasamu mafarki yayi. Ace yau waɗannan mutane sune gidansa neman auren ɗiyarsa.
  5hours ta shigar damu garin abuja. Lokacin da muka isa rana tayi ana shirin kiran azahar. Muna shiga garin Abuja waɗannan motocin da suke biyedamu kowacce takama tata hanyar ba Hanya ɗaya sukabi Ba dan ɗaya ta riga ɗaya fara tafiya kuma sunyi hannu riga hakan yasa Ya Ahmad yafara kokonton ko dama tun can tafiyar ba ɗaya bace kawai shine yayi tunanin haka ganin yanda muke tafiya ƙafa da ƙafa.
 Gidansu Mummy dake maitama muka nufa. Gidane ƙayatacce nai kyawun gaske wanda zan iya cewa bantaɓa kallon gida mai kyawunsa ba. Gate uku ne kafin isa cikin gidan kuma kowanne sai anyi tafiya kafin aje ɗaya. Tsararren gidane sosai wani shashi muka nufa kusan duk sashin gidan iri ɗaya ne. Yana isa dai-dai parking lot dake jikin gidan yaja ya tsaya. Tun kafin mushigo Cikinsu Aysha da Anty fadeelah yagama ɗuran ruwa ana kallonsu za'a fahimci suna matuƙar tsorace. Saida Ya Ahmad yayi magana sannan naga sun fara ƙoƙarin buɗe ƙofar muka fita dukanmu. Muna fita wasu daga cikin ma'aikatan suka taho wajan motar aka buɗe musu boot suka fara shiga da kayan. Yaa Ahmad yaja hannun Yaya Habibu suka barmu a wajan.
Aysha ce tayi ƙarfin halin juyawa tabar wannan part ɗin ta nufi na gefensa ganin anty fadeelah ta rufa mata baya sai muma muka bita.
A palour muka samu wata dattijuwa a aƙalla zatakai 75years tana zaune a kan kujera da wasu wanda bazasu wuce sa'anni da itaba. Muka shiga da Sallama suka amsa.
Matan kana kallonsu zaka tabbatarda cewa manyan matane dan tsufarsu bata hanasu yin kwalliya da kayan alatu ba. Hannu da wuya duka sunsha zinari sai yalli sukeyi.
Muka isa ciki matar dana kallonsu da saki fara'a tana tarɓanmu. Muka zauna muna gaisheta ta ansa da sakin fuska gabaki ɗayanmu kamar tasanmu duka.
"Yaushe kuka sauƙa?" cewar wannan matar
"Yanzunan ma" Aysha tabata amsa.
"Baku shiga wajan Mummynku ba kenan?" ta tambaya. Anty fadeelah tace.
"bamuje ba ni wallh ma tsoro nakeji. Hajiya tana fushi damu koh?"
"Ni ina nasani ne? Kunyi mata laifine?" kunsan halin mumynkubai ba'a iya predicting yanayinta" .
"kutashi kushiga ciki ku huta sannan kuzo kuje wajanta koma fushin takeyi ai yanzu idanta ganku zata sauƙa" muka shige ciki ba mu muka fitoba sai ana daff da la'asar. Part ɗin Mummy muka wuce kai tsaye. Babu kowa a palour muka zaun anan bamu daɗe da zamaba mukaji footstep tana sauƙowa gabaki ɗayansu naga sun miƙe jikinsu har kyarma yakeyi tana sauƙowa idanuwanta suna kanmu.