← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 106

Sashe 75

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Toh naji idan muka koma zan faɗawa Mama saita samu Baba Amma kisani ba lallai ayarda da yiwa Yaya habibu aure kai tsaye bayan ƙarancin shekaru ga rashin aikin yi, shi kansa yasan da hakan shiyasa bai yarda yaje yasamu wani da zancen ba" tayi hugging ɗina tana faɗin.

"Ni in hardai zakije toh babu damuwa dan nasan Mama bazata ƙiba tana sona sosai"

"Allah yasa shine kawai abunda nafaɗa". Sai wajan 10 kafin yafita a ɗakin. Washe gari sassafe aka sallamemu shi yazo yakaimu gida dan jikin nata babu ƙwari sai Ummi tace yawuce da ita gida kawai.

Su Mama dama hakan sukaso dan jikin nata babu ƙwari amma bazasu iya tambaya ba sai sukayi shiru gashi kuma An kawota gida.

Harna manta da zancen da Maryam tayimin sai bayan ƙwana biyu kafin nasamu Mama nayi mata magana. Batacemin komai ba dan haka bansan abunda take nufi ba ban bawa maryam wani feedback ba sai bayan ƙwana uku naga Ansiyo goro Ashe da Mama tasamu Baba da zancen yace Yaya za'ayi yayiwa Habibu sure a yanzu? Bayan ƙarancin shekaru ai baida aikin yi. Amma zaiyiwa aikawa Alhaji habibu Magana. Da Alhaji habibu yaji abunda Baba yaje masa dashi sai yace. Babu komai tunda yagama karatunsa zai sama masa aiki kafin lokacin aure idan aiki bai samuba zai bashi jari mai ƙarfi yanda zai kama ƙasa dan haka yanzu babu damuwa akai tambayar kawai tunda tambaya ai ba itace aure ba daga baya sai ayi maganar aure. Baba ya anince da shawarar Alhaji habibu san haka cikin 3days ɗin aka siyo goro. Tunda nakira maryam na faɗa mata za'a kawo take ihun murna godiya kawai take surfamin. ankai tambaya. Ranar Maryam murna kamar zata goyani shi kansa Yaya habibu saida yayimin godiya.

Saida Aysha tayi sati ɗaya agida sannan yazo tafiya da ita har shiɗewa takeyi tsabar kuka sanna tace babu yanda zataje babu irin rarrashin da Ba'ayi mata ba amma tace bazataje ba magana har gaban Baba. Baba ya roƙi yabarta ta sake sati guda hakan akayi nanma da akazo tafiya da ita tace bazata jeba har faɗa Baba yayi mata tace batta zuwa ko'ina saida ran kowa ya ɓaci agidan. Baba ne yace su Mama su zauna da ita suji matsalarta. Daƙayr suka sanya tafaɗa musu abunda yake damunta. Mama tasamu Baba tayi masa bayani. Gabaki ɗaya sun rasa yanda zasu ɓullowa lamarin daga ƙarshe hakuri da Lallashi kawai akayita mata takoma sannan suka bata shawarwarin daya kamata ace sun bata mukanmu tausayi take bamu yanzu dan abun yana damunta kuma tasakashi aranta hakan yasa sai ramewa kawai takeyi.

Hammaood baizo Bayan mungama exam ba sai bayan Babbar sallah harda wata guda sannan ya turamun message akan akowani lokaci zan iya ganinsa babu wanda na sanarwa sai zallan damuwa dana sakawa raina bansaniba ashe ya rigada ya sanarwa Ya Ahmad da Baban shi kansa.

Ko Baba saida walwalarsa ta canja sannan sun shirya akan idan tafiyar tazo zamu tafi tare da Mummy da Anty fadeelah da Yaya Habibu zasu ƙwana biyu acan suga yanayin yanda wajan yake sannan kafin su dawo Ya Ahmad zaije ko bayan sun dawo dan Baba yadamu sosai yace bazai iya badani ni kaɗai mutafi ba. Dama kafin lokacin already angama min duk wani abunda za'a buƙata na tafiya Yaya Ahmad ya tsaya akan komai akayi cikin lokacin daya dace. Sai Anty fadeelah tare aka haɗa akayi mana yaya Habibu kam dayake shi dama bai daɗe da dawowa ƙasar ba yanada duk wani abun buƙata sai Mummy itama haka.

Bayan na idarda sallah Ina zaune nayi tagumi Mama tashigo ta sameni ina Jin shigowarta na sauƙe tagumin da sauri tun kafin na sauƙe ta kalla dan haka takeni waje tazauna.

"Marmeeyy akwai wata matsala ce?" Dasauri na jijjiga kai. Murmushi tayi.

"Idan kinada wata matsala gara ki faɗamin tunda kinga nisa zamuyi nanda wani lokaci zaki ƙwana biyu baki ganni ba zakiso ace ina kusa ki faɗamin abunda kikeson faɗamin amma bazaki samu daman hakanba yanzune damarki da zaki samu zantawa dani fuska da fuska" hawaye yafara gangara a fuskata inajin gabaki ɗaya kamar rayuwata ne take shirin zuwa ƙarshe.

"Mama tayaya za'ayi na iya rayuwa ni kaɗai acan wata ƙasa wajanda babu ke babu Baba babu wasu ƴan uwana? Tayaya za'ayi rayuwa tayimin daɗi har yanzu nakasa tunanin yanda rayuwa zata kasancemin shin rayuwa zata tafi ko kuma tsayawa zatayi?"

"Tabbas rayuwa zata tafi Marmeeyy babu abunda zai tsaya kuma zaki rayu kamar yanda kowace mace take rayuwa agidan mijinta sai dai zaki rayu da kaɗaici zuwa na wani lokaci da zarar kin fara tara yara zasu ɗebe miki kaɗaicinki. Kisani bakece mace tafarko data fara barin garinsu ko ƙasarsu zuwa wata ƙasa da sunan aure ba dubu sunyi kuma sun zauna lafiya cikin farin ciki sun bawa abokan zamansuma farin ciki yanda zaki tafi yanzu sune zasu kasance danginki na har abada kamar yanda muke fata" Hawaye yakasa barin tsiyaya a fuskata ina shirin fashewa da kuka nake magana"

"Mama bakijin zafin tafiyar da zanyi ne? Inaga kaman baki fahimci yanda nakeji ba kowa nawa fa zan bari natafi can wani waje danyin rayuwa" saida tayi murmushi mai cike da ciwo sannan tace.

"Nasan yanda kikeji mana Marmeeyy tunda ina tunanin inajin fiye da hakan ko kwtaankwacin hakan nifa uwace tunda na haifeki baki taɓa tafiya mai nisa kinbarni ba sai yanzu zakiyi kuma tafiya wanda muke saka ran idan anyita anyine ta har abada sai dai kizo mana ziyara, ke kaɗai Allah yabani ƴa mace duka sauran mazane tayaya zakice bazanji ciwo ba? Ko naji ciwo yaya zanyi tunda ai ba'a kanki aka fara barin iyaye da gida ko gari ko ƙasa da sunan aure ba ba'a kanki aka fara irin wannan aurenba to yazama dole gabaki ɗaya mu sakawa ranmu haƙuri dan kisanu kije kiyi zaman aure kiyi ibada yanda ya kamata" Mama tayi tamin nasiha.

"Duk wnai abunda ya kamata na koya miki wanda idan kinyi aure zaki rayu a gidan mijinki na koya miki tub daga tasowarki ban bari sajda kika girma ko sai kinyi aure kinzo barin gida kafin nafara miki nasiha ba inada tabbacin duk suna ƙwaƙwalwrki abubuwanda zan ƙara miki bazasuyi yawa ba" tayi tamin nasiha da saida nayi kuka mai isata" dakyar na haɗiye kukana kawai Mama tamiƙe tanajin zafi aranta amma yaya zatayi? Dole ta ƙwantarwa Marmeeyy hankali ta nuna mata komai ba komai ba har ta ƙwantarda hankalinta.

"Mama fita zakiyi? Har yaufa baki taɓa tambayata ina sonsa ko bana sonsa ba" Tajuyo tayi murmushi.

"Kina sonsa mana Marmeeyy"

"Meyasa kikace haka bayan baki taɓa tambayata ba"

"Marmeeyy nifa mahaifiyarki ce lokuta dadama bakya buƙatar saikin furta kafin na gane abunda kike nufi"

"Mama zata iya yiwuwa biyyay kawai nake yiwa Baba ga zaɓinsa gareni shiyasa kike ganin kamar ina sonsa" na faɗawa Mama hakane saboda inaso ta bani wani dalili guda ɗaya wanda ni kaina zai gamsar dani cewa inason Hammood dan ina kokonton son danake masa. Alokacin ina tare da Hamma idan bai kirani na nakan damu na kirashi Amma hammood bakan iya cireshi araina daya kira badai kiraba ban damu ba"

"Banace A'a ba marmeeyy ta iya yiwuwa biyayyar ce tasanya soyayyar tashiga ranki abu guda dana sani shine kina sonsa, bari naje na dafawa babanku ruwan shayi dasauri na miƙe.

"Mama bari zan haɗa masa" toh kawai tace nafice zuwa kitchen na haɗa kayan shayin na ɗaura a wuta inajin shigowarsa na juye nakai masa. A palour na sameshi yana zaune nashiga da sallama bayan nayi masa sannu na zuba masa ruwan shyin na miƙa masa. Shi kansa ya lurada yanda jikina yadawo sanyi-sanyi. Daurewa yayi yayimun nasiha sannan yacemin Zanje gidan Hajiyarsa na ƙwana biyu."

"Washe gari Sassafe Natafi gidanta naji daÉ—in zaman danayi a gidanta danna koyi wasu abubuwa da bansamu na koya a shekarata sha tara ina neman ta ashirin a duniya ba. Kuma hajiya batajin kunya duk wani abunda yakamata ta koyamin tana koyamun shi har wasu daga cikin al'adu na zamantakewa da larabawa wanda bansan a yanda ta koyi hakanba.

Mummy kuwa anata wajen sayyaya kawai takemin tana kashe kuɗi wanda ita kanta batasan yawansu data kashe ba duk wani abunda tasan idan naje can zan buƙata ta siyamin maimakon ƙwana biyu saida nayi 5days a wajan Hajiya sannan nadawo.

Nasamu Baba da maganar Exam ɗita guda ɗaya wacve take kaina tubda dama ya riga yamin register bandai taɓa zuwa ko lactures bane nasiya material da zummar zanyi karatu kawai idan takama za'ayi practical ko wani abun sai naje. baba yace shi yanzu baisan yanda za'ayi ba tunda yasan tafiyarmu wannan satin ce gashi kuma exam ɗin gabaki ɗaya bazata wuce 7 weeks ba kuma baza'a fasa tafiya saboda exam ba abunda za'ayi shine udan naje nayiwa Hammood maganar jarabawar duk da yasan bazai rasa masaniya akanta ba.

A daren ranar jirginsu Hammood ya sauƙa a abuja ƙwana ɗaya yayi a abuja ya iso bauchi. Adaren ranar kuma Yazo gida saida suka gaisa dasu Mama sannan nashiga wajansa. Kallo ɗaya yayimin yasan ina cikin damuwa nikam nakasa kallonsa gabaki ɗaya ma. Hira sai jifa-jifa mukeyi san dama kwana biyu gabaki ɗaya banida walwala tunda nasan ya iso Abuja sai rashin walwalar ta ƙaru bare yanzu danake ganin baifi ƙwana biyi nabar gida ba. Hammood cikin kulawa yakira sunana.

"Zaynab" na ɗago na kalleshi tunda bashiga sai alokacin na kalleshi idanuwanmu suka haɗe waje ɗaya gabana yahau faɗuwa dasauri na kawarda idona. Ajiyar zuciya ya sauƙe sannan ya jefomin tambaya.

"لا تريد الذهاب معي"
(Bakison tafiya ne dani)?" Dasauri na gyÉ—a kaina alamun eh. Yayi murmushi yasan za'a rina."

PAID BOOK

Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab  m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance  zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."
Chapter 75 · 0% Book details