← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 106

Sashe 40

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Shikenan yawuce Allah yayafe mana baki É—aya" ya amsa da amin.

"kin yarda zaki koma ɗakinki kenan?" ta gyada masa kai a fili yace Alhamdulillhi a zuciyarsa kuma yana tunanin lallai Mummy ta canja danta bashi mamaki da tayi saurin saƙƙowa bai zaci samun hakan da wuri ba amma kamar yanda tafaɗa shekara sha ɗaya ha ƙwana sha ɗaya bane.

Alokacin ta aika akawo masa abun taɓawa dan dama kafin tafita saida tabi kitchen tabada saƙon abunda za'a kawo. Aciki harda ruwan shayi da tuwo miyar kuɓaiwa yaji manshanu datasa akayi masa sanin cewa yafi sonsa akan kowani irin abinci. Dama already akwai tuwo da miyar stew da akayi. Tana basu umarni suka kaɗa zallan kuɓaiwa aka haɗo da Non sugary natural made drinks Suka kawo.

Aƙasa suka zauna aka baje abincin sunaci suna hira dariyarsu kawai ake jiyowa. Sannan Mummy ta roƙi Baba akan kar yafaɗawa yaransa cewa ta yarda zata koma dan ta lura cikinsu Marmeyy kaɗai keson takoma. Baba ya yarda cewa canjawar Mummy harda aikin marmeeyy ajiki. Ƙaramar yarinyace amma akwaita ta iya tsara zance na hikima har indai kalamine kam Allah yabata.

Alhaji habibu acan haƙuri yabawa mahaifin Mummy sannan yace ayi haƙuri takoma ɗakinta.
Ga mamakinsa shima mahaifin mummyn haƙuri yake basu sannan yace har indai ta amince takoma kawai.

Yayanta dayake zaune yace.
"Ai bawai sai anjira ta amince ba kabata umarni kawai takoma É—akinta sufa yanzu ba yara bane abun kunya suke yiwa yaransu. Yanzu idan Æ´arsu ta tattaro tadawo gida bayan an aurarda ita sai suce zasu mata faÉ—a?

Jikin mahaifin Mummy yayi sanyi danshi kansa abunda yayi kenan tunda Mummy tazo gida ko sau ɗaya bai taɓa mata faɗa ba. Shima fushin yayi kamar yanda tayi sai daga baya daya lura cewa abun bana ƙarewa bane shine ya sauƙo. Dafarko yayita neman hanyarda zaiyiwa Baba magana yazo yatafi da matarsa amma baiyi hakanba saboda yanaso yayi yanda bazata ganeba dan yasan idanta gane tabbas zatayi fushi shikuma bayason fushinta kasancewar ita kaɗai Allah yabashi mace sai maza guda biyu.
Alhaji Habibu yace.

"Abi komai a hankali kasancewar su yanzu ba yara bane yakamata abarsu su ƙara tunani tunda yanzu hakama natafi nabarsu ita da shiɗin nasan zasu sasanta kansu" yayan Mummy yace.

"Tunani a tsawon shekarunnana kowani irine ai sun ƙareshi dan dai nasan ku kanku sun gaji da zamanta ahaka itama idan dai bawai zuciyar ƙashi takedashi ba nasan yanzu ta sauƙo" mahaifin Mummy yace.

"Kamar dai yanda yace abi komai a hankali toh abishi a hankalin idan abun ya gagara sai mushiga ciki barema nasan bazai gagara ɗinba" Ahaka suka tsayarda maganar Bayan Baba yagama dakanta ta rakoshi ya gaida mahaifinta hakan ya tabbatar musu da babu wata matsala komai ya dai-dai ta. A wajan shima Alhaji habibu yaci abinci tareda mahaifin Mummy sannan sukayi sallar la'asar aka kiramu mukayi sallama ana ganin Babanmu za'a fahimci yana cikin walwala itama mummy haka farin ciki yagaza ɓoyuwa a fuskarta. Bayan mungama sallama suka kama hanya. Bayan Mummy tasaka ancika musu boot da tsaraba na mama dana Hajiya saina Alhaji habibu ma nasa daban. Bata bada na anty ba baisan ko har yanzu fushi takeyi da ita ba.

Suna tafiya mukayi shiri muka tafi walima. Bayan angama walima aka É—auko amarya. A wajan Ya Ahmad aka ajiyeta dayake yanada girma.

Da dare za'ayi dinner munata shiri danso mukeyi mufi kowane lokaci É—aukan wanka wannan dinner ta dabance har Mummy zata halarta.

Dake da dare za'a tafi mai makeup dakanta zatazo tayi mana. Ana sallar isha'i muka fara shiryawa dama su Anty fadeelah kam ta rigada tafara shiri har anyi mata kwalliya dake ita ba sallah zatayi ba."

"Hammood

ZAYNAB ALABURA

Assalamu alaikum barkanmu da sallah fatan munyi sallah lpy Allah ya karɓi ibada ya amsa mana addu'oinmu. Mun dawo hutun sallah in in sha Allahu zamu daura daga yanda muka tsaya.

Wannan littafin na kuɗine kibiya  ₦300 ta asusun  bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya

Gabaki ɗaya ma'aikatansa saida suka fahimci irin yanayi najin daɗi dakuma farin ciki da Hammood yake ciki basu taɓa ganinsa a yanayi makamancin wannan ba lokaci-lokaci yake sakin murmushi mai sauti akasin yanayinsa da abune mawuyaci kaji saurin murmushinsa koda yayi sai dai kawai ya motsa lips ɗinsa idan zaiyi murmushin. P.A wanda shi kaɗai yasan abinda ya faru yana sakin murmushi shima yake tayashi yasaki nasa murmushin.

Yau yashirya zuwa yaganta daga nan kuma zaibar ƙasar wayewar asubahin washe garin ranar dayake yanada abubuwan da zaiyi a satin dayawa.

Idan yatuna zai ganta sai ya tsinci kansa yanayin daɗi dakuma fargaba aduk lokacinda zai haɗu da ita irin yanayinda yake tsintar kansa ciki kenan. Shi kaɗaine zaune a ɗakin yayi nisa cikin tunani ƙarar wayarsa tadawo dashi daga duniyar tunanin daya lula. Ya furzarda iska sannan yadubi wayar Sunan mahaifiyarsa ya bayyana akan wayar. Har tayi tagama bai amsa ba tun jiya daga ita har nawrah babu abunda sukeyi sai aikin kiransa shikuma yaƙi picking idan suka gaji da kira bai ɗaga ba daganan sai su fara kiran P.A Babu yanda basuyi ba amma P.A yaƙi basu cikekkiyar ko gamshesshiyar amsar tambayarsu. Shima kansa yagaji da amsa kiransu da yanada yanda zaiyi bazai amsa ba amma babu halin yaƙi ɗaga wayar kamar yanda Mood yakeyi sai dai koda ya amsa babu wani bayaninda suke samu.

Bayan wayar tagama ringing dakamar 9minute P.A yayi knocking a hankali. Ogannasa yabashi umarnin shigowa. Sai da ya saka katinsa ƙofar ta buɗe sannna ya murɗa yashiga. Ya ƙarasa har yanda Mood yake sannan ya tsaya. Mood ya ɗago ya kalleshi dan yasan magana zaiyi. Ganin haka yasa P.A yafara magana cikin harshen larabci.

"Mood sir baka ganin yakamata a sanarwa Mummynka da ƴar uwarka wannan maganar? Sun damu sunataso susan gaskiyar lamarin akan abunda yaketa yawo" Mood ya miƙe tsaye yafara tafiya sannan yayi magana.

"idan ina buƙatar sanar dasu zan faɗa musu da kaina yanzu get ready it's almost time for isha'i" P.A yagane abunda yake nufi dan haka yayi masa sallama yafita shikuma ya nufi toilet yadaɗe sosai a ciki kamar yanda yasaba sai da aka fara kirayen kirayen sallar isha'i sannan yafito ya shirya sannan ya tara gabaki ɗaya ma'aikatansa sukayi sallah sannan suka zauna dinner bai wani ci abincin sosai ba dan zumuɗi dayakeji tun jiya bai samu yaci abinci sosai kamar yanda yasaba ba saiya zauna sai yaji gabaki ɗaya murna da farin ciki sun cika masa ciki. Zama yayi wani ɗan lokaci baya jimawa yake duba agogo yagani ko time yayi. gani yakeyi kamar lokacinma yaƙi tafiya. Idan yaɗan duba time saiya saki ajiyar zuciya yana ɗan jijjiga ƙafa."

-------

Sai wajan 9:00pm muka gama shiryawa lokacin har anfara tafiya Amarya da angone kawai basu tafiba Munyi kyau sosai. cikin laces mai É—an karan tsada da Mummy tasaka aka É—inka mana mu mukayi anko.

Alokacinda muka fito lokacin angama yiwa amarya tata kwalliyar itama tayi kyau sosai an jejjera motoci ana jiran fitowar sauran masu tafiya.

A harabar gidan muka samu su Yah Ahmad yasha babbar riga yayi kyau sosai sunyi anko da amaryarsa. Muna isa dai-dai wajansu abokinsa yana ƙarasowa ya dubi Ya Ahmad yace.

"ku hanzarta mana lokaci fa yana wucewa ga motoci duka sun taru ku kawai ake jiran"

"Okay toh muje koh?" shine abunda Ya Ahamd yafaÉ—i. Yafara tafiya zuwa wajan motarda zasu shiga. Abokinsa yace.

"Ba wancan motar bace taku?" yafaɗa haɗeda yin pointing wata mota datake ɗan gefe kaɗan. Gabaki ɗaya motocin wajan masu tsada ne wanda ake yayinsu amma wancan dabance duk ciki babu wacce takamo ƙafarta. Ya Ahmad yaɗan dakata sannan yace.

"Au kaga na manta" sai yajuyo yakallemu yace"

"Marmeeyy kushiga wancan motar kutafi yafaÉ—a yana nuna mana motar dake can gefe. abokinsa yace.

"Dakata mana malam. Kamar bakasan yanda tsarinmu yakeba? Aƙa'ida amarya da ango suke shiga motarda tafi kowacce ko kamanta ne?" Ya Ahamd yayi murmushi sannan yace.

"Mutumina kar kaja magana kaga lokaci na tafiya." sannan yajiyo ya kallemu yace.

"Kuwuce kutafi"kamar wanda yatuna wani abun yayi saurin faɗin marmeeyy dawonan dasauri najiyo ya ɓata fuska yafara faɗin.

"Wato ke bakyajin magana koh? Wuce ki É—auko mayafinki. Nayi narai-narai zanyi kuka yace.

"Wallh koki wuce koki fasa zuwa" na juya nadubesu dukansu babu mai gyale har amaryarsa bata saka gyale ba sai dai kawai yanayin É—inkinta na amare ne amma ai itama da saiyace tasaka gyalen. Abokinsa yace.

"Haba mutumina na yau kaÉ—ai dai kabar yarinyar nan na sake kana takurata wallh"
tsaki yaja nikuma ban kula ba na juya nafara tafiya idona tacika tamm da hawaye kaɗan nake jira na fashe da kuka. ina shiga na nemi waje na zauna banason hawayen ya sauƙo dan karya ɓatamin kwalliyata dan haka na riƙe hawayena na zauna kawai inaji kamar nafasa zuwa event ɗin gabaki ɗaya.

Ganin natafi naƙi dawowa ya sanya Maryam tabiyo bayana. Bayan tabar wajan Aysha ta dubi Ya Ahmad tace.

"Ya Ahamd ko a fili baka iya ɓoye bambamcin da kake nunawa tsakaninmu da Marmeeyy mune muka fito ciki ɗaya dakai amma kafi nuna kulawa akanta. Mu koyaya zamu fita baka damuba amma ita bazata fita ko yaya ba dan ita ta musammance kowa yafi sonta. Koda yake ba abun Mamaki bane tunda mummynmu uwarda ta haifemu tafi nuna mata kualawa dan kai kayi haka bai kamata muyi mamaki ba." Anty fadeelah tana ƙwabarta amma saida ta ƙarasa abunda take faɗa tana gamawa tabar wajan fuuu. Murmushi kawai ya Ahmad yayi. Anty fadeelah tace.

ZAYNAB ALABURA

Wannan littafin na kuɗine kibiya  ₦300 ta asusun  bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya

Bafa murmushi zakayi ba kana gani yanda ranta ya ɓaci.

"ita waccar nayi mata faɗa akan mayafi ranta yaɓaci tana ganin kamar na takurata bana sonta ita kuma wannan banyi mata faɗaba tana ganin kamar ban damu da itaba me zanyi idanba murmushin fadeela?" anty fadeelah tace.
Chapter 40 · 0% Book details