← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 106

Sashe 51

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun da aka ɗauki azumi akayi sallah gabaki ɗaya hankalinsa ya karkarata yayi wajanta babu wani abu dayake muradi da burin gani daya wuceta. Yana mararin sanyata a idanuwansa yayi kewarta samada yanda baki zai iya faɗa. Ga abubuwa sunyi masa yawa kuma a wannan lokacin yana tunanin dole ya bayyana mata kansa a yayinda zaije gareta yagaji da ɓoye kansa wannan karon yana buƙatar shima tasanda zamansa matsayinsa na mijintabamma yaya zaiyi da alƙawarin da ya ɗaukawa Baba? Yazama dole yacigaba da ɓoye kansa har lokacin da Baba zai bashi izinin bayyana mata kansa. Wannan dalili ya tsareshi daga zuwa ganinta ya taushi kansa yabawa zuciyarsa haƙuri amma yaga zuciyarsa a wannan karon tana neman fin ƙarfinsa kodan ba wannan karon bane ta saba yimasa haka. Alokacinda ya fara sanin Marmeeeyy yaso ya danneta amma ta gwada masa bazata dannuba saboda taga abunda takeso haka taci galaba akansa ya biye mata wannan karonma hakan takeso tayi masa. Ziciyarsa ta azabtu da son ganinta ko jin muryarta. Ɗaya daga cikin wayarsa ya ɗauko. Yanata tunani yayi ko kar yayi bazai iya hana kansa ba A wannan lokacin abisa tilastawan da ziciyarsa tayi masa yayi dialing numbern marmeeyy.

Ina zaune abun duniya ya taru yayimin zafi narasa yanda zan saka kaina tunda naji labarin an ɗaura auren nakejin jiri-jiri harda zazzaɓi dan zuciyata sai tashi takeyi nakasa cin komai. Tun banaso kowa yagane har Mama tazo ga sameni a cikin wannan yanayin tashiga tashin hankali matuƙa zama tayi tanamin nasiha da kalamai masu ƙwantarda hankali da sanyaya zuciya.

"Marmeeyy kina jina? Ki ƙwantarda hankalinki kisan cewa kowani irin lamari rubutacce ne wajan ubangiji dama can Allah ya rubuta Hamman ba mijinki bane. Kuma bamu isa muja da hukuncin Allah ba. Alkhairi kawai muka roƙa a wajansa kuma inada yaƙinin alkhairin zai bamu. Karkiji komai karki riƙe komai a zuciyarki ki tashi ki fita cikin ƴan uwanki ko zakiji sanyi. Idanma bazaki iya hakanba ki zauna anan ki ɗauki ƙur'ani ki kiranta zakiji sanyi. Tayi tamun nasiha sosai ina jinta har tagama kuma Alhamdulillhi nasamu sauƙi. Na lumshe idona kamar mai bacci ganin haka yasa tafita. Ina zaune ƙwance wayata tafara ruri a hankali na jawota. Ina ganin lambar saida gabana yafaɗi amma na dake. Baitaɓa kirana ba tsawon shekara biyu anshiga da uku kullum saƙonnk kawai yake aikon dasu. Bansan dalilin kiranba yasa bazan iya ignoring ba amma kafin na ɗauka nayi saƙa da warwara sunfi goma. Ina pjcking na kara a kunnena nayi shiru. Ba'ace komai ba daga wayar nima bance ba. Na maida idanuwana na lumshe wayar tanakan kumatuna saitin kunnena a hankali nake sauƙe numfashi. Bansan me yasaba sai nakeji kamar mai kiran yana saurarona daga numfashin danake fitarwa.

Daga yanayin yanda numfashina yake sauƙa yagane cewa ina cikin damuwa gabaki ɗaya sai yajishi babu daɗi Marmeeyyn da yasani mak surutuce da fara'a amma yajita shiru gashi tana jan bumfashi tana sauƙar dashi cikeda damuwa bazai iya sauraran hakanba dan haka ya datse kiran. 15minute bayan datsewar kiran naji sallamar Yaya Ahmad. Har yanzu wayar nakan kumatuna yanda take ban sauƙetaba koda naji datsewa wayar. Sallama yayi nabashi izinin shigowa dan bazan iya tashi jafita palournba sam banason haɗuwa da mutane. Tubda Ya Ahmad yake inbanda yarinta bai taɓa shiga ɗakin mama ba sai yau. Yashigo yazauna akan comfy bedroom chair dake gefen gadon Mama. Na gaisheshi batareda na tashi ba.

"Marmeeyy tashi ki zauna zamuyi magana" batareda na amsa ba na nemi mike zaune.

"Kina sonsa da yawane har haka?" nayi ƙasa da kaina ya fahimci abinda nake nufi zuciyarsa tayi wani iri yakasa cewa komai. Bayan wasu mintuna kafin yacigaba da magana.

"Marmeeyy kisan cewa kuma na yarda cewa Allah bazai ƙwace wani abu atare dake batareda ya canja miki da ninkinsa sau babu adadi ba. Mijinda nake mikk buri da fata shine wanda zai soki ya ƙaunaceki ya riritaki yaga kimarki da darajarki ya zame miki gata kamar yanda kika zamewa gabaki ɗaya ahlinki gata. Ina miki fatan mijinda zai soki aduk yanda kike mijinda zai fahimci kina cikin damuwa daga zallan numfashinda kika sauƙar basai laɓɓanki sun furta ba wanda zai fahimci damuwa acikin ƙwayar idanuwanki batareda taimakon kalaman bakinki ba. Na tabbata bazaki daɗe cikin wannan damuwar ba dan ayau na tabbata cewa Allah ya amshi addu'armu.
Yanzu kitashi kiyi wanka idan kingama ki kirani zan fita dake may be zakiji sanyi aranki daganan zan wuce nasamu Baba zamuyi magana akwai wani suprise da zan miki amma sai kinmin alƙawarin sakin ranki nayi murmushi sannan nace.

"Ya Ahmad karka damu kanka da saika farantamin kar kaje ka takura kanka kaga ranar haka kacire maƙudan kuɗi ka siyamin wayarda tafi ƙarfina idan kanaso na saki raina zan saka kasan kawai zanji babu daɗine amma yanzu zan tashi nayi wanka ma" murmushi kawai yayi ya fice natashi daƙyar nashiga nayi wanka.

A ɗakin Baba Ya Ahmad ya shaidawa Baba abunda yake faruwa badan ya ɗaga masa hankali ba sai dan yanaso yaɗaga maganarsa akan cewa ba yanzu zai nunawa Marmeeyy akwai auren Hammood akanta ba shi aganinsa tunda marmeeyy nason Hammood koda da son bana aure bane bazatai masa uwar shawo kaiba. Sannan yana ganin Hammood kaɗai zai iya cireta a wannan damuwar da take cikk ya ƙwantar matada hankali. Bai bar ɗakin ba har saida ya sanya Baba ya amince da zai Kira Hammood da kansa dan yazo ya bayyanawa Marmeeyy kansa."

Bayan na fito a wanka wadrope na buɗe anan idanuwan suka sauƙa akan kayanda nasaka ranar diner ya Ahmad na cirosu ƙamshinsu yana dukan hancina har lokacin kayan ƙamshin turaren wannan mutumin sukeyi dukda sun ƙwana biyu a ajiye tun ranar dinner bansake sakasu ba bansan dalili ba amma naji daɗin ƙamshin danya sanyamun nutsuwa kuma dama tun abaya ƙamshine mai saka nutsuwa. Daga yanda nasaka kayan na gane naɗan faɗa ban shafa komaiba na ɗaura ɗanƙwali na yafe gyale tunanin Ya Ahmad zaiyi magana yasa na canja zuwa hijabi wanda zai shiga da kayan na saka plat shoe na fito a plaourn mama naga matar Ya Ahamd ni banmasan shigowarta ba na gaisheta sannan nafice fitata tayi dai-dai da fitowar ya Ahmad daga ɗakin baba. Ficewa mukayi sai bayan azahar sannan muka dawo."

Da Yamma na kira Maryam nace ta shirya zamuje diner datse kiran tayi bayan 40minute kawai sai najita a gidanmu.

"Babe wai kinyi haukane? Dagaske kike wai zuwa zakiyi? Toh me zakije kiyi? Dan Allah ki haƙura kiji da abu ɗaya haba"

"Zuwa zanyi mana kuma tare dake toh mema zai hanamu zuwa?"

"Babe please stop kina ɓatamun raina Allah na tuba mai Zai kaimu? Kinaso kisake tada ciwon da yake damunkine? Gashi duk kinbi kinyi wani ƙashi kin rame abu bakyan gani" cikeda jin haushi nakai mata duka"

"Ji banza wallh bansan wulaƙanci nice babu ƙyawun ganin?"

"Toh ƙarya nayi? Kije ki kalli mudubi shi zai baki amsa"

"Mtswww naja tsakk na ɗebeta na watsar" tayi magiya ta gaji nasake tabbatar mata da zamuje diner babu fashi duk yanda taso tayi convincing ɗina akan kar muje naƙi biyeta daga ƙarshe ficewa tayi tabarni.

Sai bayan magrib aka ɗauki amarya amma gidan iyayensa aka wuce da ita kamar yanda al'adan ƴan garin bauchi yake saisun ƙwana ɗaya gidan iyayen miji idan aka gama biki sai akai amarya ɗakinta.

Mama da anty suka raka amarya sai Ummi tana kallon harda Mama akazo ta jata ɗaki ta tambayeta yanda nake sannan tabata labarin irin halinda Hamma yashiga har yanzu ta sanar mata bai ƙwantarda zuciyarsa ba. Mama ta shaida mata nawa wajanma hakanne amma yaya zasuyi iyaye sun rigada sun zartar da hukunci. Ummi ta tambayi Mama akan dalilin canjuwar auren Mama ta nuna mata bata saniba. Basu daɗe a gidanba suka dawo akabar zallan amarya da ƙawayenta sai ƴan manya guda biyu.

Dare yayi anata shirin tafiya saida kowa ya watse sannan na shiga nasake wanka lace na ciro wanda aka ɗinka mana a sallah na sanyashi powder kawai da lipstick nasaka na ɗaura ƙwali yazauna akaina ni kaina nasan bawani kyau zanyiba tunda fusk duk bbu annuri amma yaya na iya? Dole zanje ko ban daɗeba na dawo. Sai bayan nagama shiri na fita naduba kowa yatafi dagani Sai Anty fadeela wautarmu nagani lo yanzu da muka bari kowa yatafi waye zai kaimu? ɗakin Mama muka dawo muka zauna bamu daɗe da zamaba wayata tafara ruri Ina duba naga Maryam dasauri mayi picking ina ɗauka tace.

"kifito ina waje tana faÉ—in haka da datse kiran nayiwa Anty fadeela magana muka fita. Waje yayi kyau ya tsaru anarya na tayi kyau sosai É—ass da ita Babu Mummy a wajan da alamu bata jeba. Saida mukayi kusan 30minute da zuwa kafin aka sanarda isowar ango saida gabana yafaÉ—i rasss."

ZAYNAB ALABURA💕
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya

Assalamu alaikum yan'uwa da abokan arziki🤝🤝🤝
Ina mata masu fama da wadannan matsalolin

Matsalar haihuwa
rikicewar al'ada
ciwon mara yayi period
Fesowar kuraje ga gaba
Ganin farin ruwa mai wari yana fito maki
Kurajan gaba
Kaikayin gaba

Da dai Sauran wasu alamomi to yar uwa kinsan ko miye to ba wani abu bane face sanyi ne ya taro yayi maki yawa 😔😔😔

Toh masha Allah sha kuruminki Allah ya kawo maki sauki ga wannan addababai ciwo

Maganin da zaki sha kiyi garau da yarda Allah 🙌👍

Toh ga dama ta samu maza ki kira aunty zee mom mujahid Katsina akan wannan lambar wayar ki ce mata MAIJIDDA MUSAWA ce taba ki wannan number
ki na son sanyan magani
08162859027🤝

------

Ango yayi kyau sosai sai dai ya rame dan sam baida walwala ana ganinsa za'a fahimci hakan. Aysha tana kallonsa tafara sakin murmushi alokaci ɗaya haƙwaranta suka fito waje sai buɗesu takeyi dan murna ya isa zuwa wajan babu wani annuri a fuskarsa yana isa akacigaba da gudanarda shagali. Ƴan uwansa ƴan tsirarrune sukaje wajan ana kallon amaryar da angon za'a fahimci babu wata shaƙuwa atattare dasu. Nidai ƙasa nayi dakaina ina danna wayata dan duk lokacinda na ɗaga idanuwana na dubesu sai naji gabana yafaɗi.
Chapter 51 · 0% Book details