← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 106

Sashe 13

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

  "wallh kuma sonsa nakeyi kamar hauka"

"iyyeh ko kunyar idona bakyaji?" Hararta nayi nace.

"ke Ummi ce da zanji kunyarki?"

"Anzaga ɓoyeyyen masoyi ta bayan fage" cewar maryam. Na taɓe baki nace.

  "anata Hamma wa yake tawani can kecema naga dama kin damu dashi" tayi saurin girgiza kai tace.

"ke rabani gida bai ƙoshi ba ina za'akai wani waje?"
Na tuntsire da dariya nace.

  " kin dawo saiti Yarinya" alokacin na roƙeta akan kada ta faɗawa Ummi dafarko taƙi dan cewa tayi Ummi zatafi kowa farin ciki amma daga Baya ta yarda tunda itama firr taƙi saurayinta ya tura saboda tanaso saita gama karatu."

     Ma'akatan cafeteria naga sun nufo wajanmu hannunsu ɗauke da box suna zuwa suka ajiye a table ɗinmu haɗeda faɗin saƙonmu, mukace musu mu bamuyi saƙoba sukace tabbas munyi dan har anyi making payment, zanyi magana maryam ta girgizamin kai sai nabari tace musu mungode sannan suka juya. Saida suka tafi ta kalleni tace.

"Ba shakka Kinsan mai wanna aikin mutumin da zai iya sakawa ayi deleting pictures ɗinmu akafar sada zumunta ta instagram kinsan zaiyi fiyeda haka. Yanzu abunda nakeso dake idan kinaso alaƙarku da Hamma tayi nisa to ki koyi ɓoye al'amura sannan kibi da wannan Ɓoyeyyen mutum a yanda yakeso ina nufin babu gardama kamar yanzu da suka kawo idan kullum zasu kawo babu jan lokaci kikarɓa, sannan Sai yanxu nayi tunanin kinyi hikima da kika hana Hamma zuwa zance dan tabbas BIBIYARKI wannan mutumin yakeyi sannan kuma bamusan WAYE SHI? ba komai zai iya aikatawa idanya ganku tare ki koyi gudun duk wata mu'amala da zata haɗaku awaje  har abun ya tabbata sannan karki yarda koda sau ɗaya kuyi waya ko chat da ainihin layinki wannan ƙaramar wayar daya baki komai tanayi dan haka ki buɗe whatsapp da layin daya baki da ita sannan kar Hamma yasan wannan lamari har muga ƙarshensa" tana bayani ina murmushi dan tabbas ta samomin mafita."

Ganin lokaci yana tafiya ya sanya muka É—auki box É—in da bags É—inmu muka fice saida mukaje class sannan mukayi kyauta da snacks É—in. Sai six muka gama lactures kafin mufito Hamma yazo É—aukanmu muna fitowa muka taras dashi yafara kaini gida sannan suka wuce."

  Duk sanda mukaje wajan wani cin abinci ko wani wajan sayayya kafin na biya zan samu anbiya wasu lokutan ƙin karɓa nakeyi nafice awajan soyayyata da Hamma kuwa tananan kullum ƙaruwa takeyi.

Yau nadawo a school dake yauma nayi Yamma gabaki ɗaya yanayin Anty fadeelah da Aysha ya canjamin saida nakada haƙuri na tambayesu, Anty fadeela ne yake shaidamin Mummynsu ta kafa musu ƙahon zuƙa sai dai su tattaro su dawo, Su fasa karatun kuma su  ahalin yanzu basason tafiya,
Jin wannan zancen nasu saida ya sakani a damuwa Domin nasan ba ƙaramin tashin hankali Baba zai shigaba idan suka tafi  dan yayi murna da zuwansu sosai a kullum burinsa gidansa su dawo su haɗe yana murma sun fara haɗuwa yanzu yaya zaiji aransa idan akace sun sake tafiya?.

   Kwana biyu kenan dagani harsu bbau wnada ya samu kwanciyar hankali sannan bamu iya faɗawa kowa ba, yauma Nadawo daga makatanta na samesu cikin tashin hankali sai kuka anty fadeelah takeyi, dafata nayi nace.

Haba anty fadeela dan Allah kidain wannan kukan in sha Allahu babu wani abunda zai faru bazaku koma ba Baba ma nasan bazai bariba" girgiza kanta tayi tace.

"ke bakisan mummynmu bane ayanda mukaji labari shi Kansa baban shakkarta yakeji kuma idan tace zatayi abu saita aikata, Marmee bazaki fahimci halinda muke cikiba kinsan yanda mukeji kuwa? Kinsa  raɗaɗin tashi ba agidan mahaifi ba kuwa? Mahaifinmu ba yana raye amma muna rayuwa kamar marayu shikenan komai zai ƙara tarwatsewa akaro na biyu dukda cewa bawai ya gyaru bane amma zamanmu anan yafi mana kwanciyar hankali"
Ciked kufula Aysha tace.

"ko menene na fitowa kiyita faɗar wannan maganar?  akwai wani abunda maganarki zata canja ne? Kitashi ki haɗe kayanki nasan nanda ƙwana biyu dole zatasan yanda zamuyi mukoma koda bamu koma ta daɗin raiba" cikeda tausayi na dafa Anty fadeela nace.

"nima kubani  kwana biyu zanyi duk yanda zanyi na tabbatar baku koma ba in sha Allahu" aysha ta taɓe baki tace.

"Kina faÉ—in haka saboda bakisan Mummy ba" Anty fadeela kuma tace.

  "kinyi Alƙawari?" nace.

"in sha Allahu" da sauri tayi hugging ɗina tana murna cikeda tausayinta nima naji idona yanason kawo ruwa." 

  Ƙarfe sha biyun dare ina cikin bacci naji wayata tayi ƙara. Sautin ƙarar yasa bazan iya haƙuri batareda na dubaba aduk lokacin danaji ƙarar saƙon hankalina yakan kiɗima har sai naga da wani irin al'amari saƙon yazo, ban kaiga buɗe idanuwa na ba Ƙarar wani saƙon ya ƙara shigowa hakan yasa natashi na zauna ya ɗauki wayar nashiga saƙon.  Saƙon farko kamar Haka. 

عيد مولد سعيد  قلبي
أتمنى أن يملأ عيد ميلادك بلحظات ❤️

Abunda wannan saƙon yake nufi shine (Barka da zagayowar ranar haihuwa my heart May your birthday be filled with joyful moment❤️)

Sai na biyun kuma

حان الوقت

Hakan yana nufin(It's time) toh lokacin menene yayi kenan? Ganin saƙon saida ya sanya gaban yafaɗi.
Inata tunani cikin raina ko lokacin menene yayi. he's definitely up-to something.

 
   Kamar nakira Hamma na naji ko ya isa saina haƙura. yayi tafiya zuwa Abuja gabaki ɗaya hankalina yakasa kwanciya inason naji halinda yake ciki haka na haƙura na kwanta washe gari ina tashi d asubahi naji karo da saƙonsa da yayimin nayi murmushi, sai bayan natshi da safe na kirashi harya fita wajan aiki dama yacemin yana isa sassafe zai fice saboda yagama abunda yakaishi, Kusan 1hour kenan daya cemin yana tsaye a titi motarsa ko gotawa batayi tsabar cinkoson ababen hawa, yana zaune a mota nikuma ina tayashi hira."

"Hammana" nakira sunansa yace.
"Na'am babyna" wai meyake faruwa agarinne cinkoso yayi yawa haka?" Na tambayeshi.

"Ɗan wasan kwallon ƙafane zaizo shine gabaki ɗaya garin ya rikice tako'inafa jami'an tsarone ko shugaban ƙasa bana tunanin za'ayi masa wannna tsaron" ya bani amsa.

"Oh tabbs kuwa nasanda zancen zuwannasa dan anata sanarwa a kafafen sada zumunta mutane kamar zasuyi Hauka nima naso naganshi i am his big fan" Dariya Hamma yayi yace.

"kima haƙura dan wannan a manya manyan ƙasarma ba kowa bane zai samu ganinsa ai ba ƙasarmu ba kawai duk ƙasar dayaje saiya rikita ƙasar tunda anyi ittifaƙin babu wanda yataɓa kafa record ɗinsa a yanzu fa shine matshin dayafi kowanne sanuwa a duniya ni bansanma  abunda zai kawoshi ƙasarnan ba"

"May be personal issue ne shiyasa ba'a buga dalilin zuwannasa ba" nabashi amsa.

"Eh toh amma inagako shugaban ƙasa yakeda issue dashi zai iya binsa har ƙasarda yake ammma bansaniba basu sanar a media ba" canja zancen mukayi da wani zance daban."

***********

  Wani katafaren gini ne mai Hawa biyu kusan gabaki ɗaya ginin da glass  akayishi, gini  yayi masifar haɗuwa gabaki ɗaya shape ɗin gidan curve yabada daga nesa kyallinsa kawai ake kallo, cikin katafariyar harabar gidan ansake wani katafaren ginin wanda yake kamada ma'aikata sai gefe filin kwallo ne wanda shima aka tsarashi, cikin wannan gini Kama da ma'aikata akwai wani Babban office aciki mai girman gaske yana ɗauke da set ɗin kujeru har guda biyu. Cikekken Balarabe ne matashi  kyakkyawan gaske yanada  tsayi sannan kuma baida jiki sai dai yanada murɗaɗɗan jiki bazai wuce 30years ba kansa cike take da kwancecciyar suma baƙiƙirin tayi luff yanada dara-daran idanuwa ƙwayar idanuwansa fararene tass yayinda tsakiyan  eyeball ɗin yaci baƙi sosai fatarshi har wani tarr takeyi yanada haske sosai cikin larabawanma shi mai haskene, zaune yake a ɗaya daga cikin kujerun yana duba wasu takardu yagama sanya hannu ya miƙawa mutumin dake zaune a kujerarda take facing ɗinsa ya amsa sannan cikin harshen larabci yadubi wannann mutumin Personal Assistant nasa yace.

"Idan mungama zamu iya tafiya" Mutumin yayi murmushi cikin harshen larabcin yace.

"mood sir kanada tabbacin samun abunda zakaje nema? Kamar yanda kafaɗa bazaka taɓa dawowa batareda cika burinka ba, sanya ran cikar burinka yasa kaja tsawon wannan lokacin ka daidaici lokacin daya dace dan aiwatarda ƙudirinka, ina fata Allah yacika maka ƙudirinka duk da abune mawuyaci ace kamar yanda kake wannan ƙudirin yakasa cika" Murmushi yayi saida gefen kumatunsa suka lotsa Ya furzar da iska mai zafi a bakinsa ya ɗauki ƙafarsa ɗaya ya ɗaura kan ɗaya ya jingina ya lumshe idanuwansa ya buɗe  hannaye akan saman kujerar yasake furzarda iska mai zafi, mutumin nan cikin harshen turanci yasake cewa.

"are you nervous? jijjiga masa kai kawai yayi alamun eh. Mutumin yace.

"don't be sannnan ya canja harshe zuwa larabci yana faÉ—in.

    bana tunanin a duniya akwai wani wanda zasu ƙi baka aure bana tunanin a duniya  akwai macen da zataƙi aurenka, kanada kuɗi kyau suna da komai na maore rayuwa meyasa bazata soka ba?" sai alokacin ya ɗago ya gyara zamansa yace.

Idan har zata soni saboda wannan qualities ɗin menene bambamcinta da sauran matan? Kamar yanda soyayyarda  nake mata ta kasance ta daban inaso itama ta kasance ta daban"  Ya miƙe yace.

" Zamu iya tafiya yafaÉ—i haÉ—eda fara yin gaba wannan P.A nasa yabishi abaya dama an rigada anshirya masa motaci guards É—insa suka suka buÉ—e yashiga sannan suka rufe suma suka shiga dasu aa tada motocin sai airport. Dama da Jirginsa na musamman hakan yasa da gabaki É—aya guards É—insa duka suka tafi."

PAID BOOK

Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."

✔️Ote
Comment
Follow
share

To be cintinued

Zaynab Alabura
*BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI)*

Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.

PAGE 11
Chapter 13 · 0% Book details