← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 106

Sashe 26

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Babu wanda ya shiga dan likitoci sunce abarki kihuta" nayi shiru kawai amma tabbas nasan akwai wanda yashiga. Babu yanda batayi ba takira Hamma yakaini gida naƙi danni babu abunda nakeji bamu tafiba kuma har saida aka tashi. Datayi maza bayani cikeda damuwa yace.

"Baby anya bazamu haƙura da karatunnan ba? Muyi aurenmu kawai yafiye mana" Nayi murmushi nace.

"Hamma babu komai fa banajin komai yanzu haka"

"Ai wannan bashine karo na farko ba Hamma" ta taɓayi lokacin muna aji biyu" maryam ta tsomo bakinta cikin maganar.

"Harara nayi mata nace kekuma waya sakoki ciki?"

Har muka isa Hamma mita yakeyi dama mai neman kukane yayi tuntuɓe da ɓawon gyaɗa.

-----------

Duk wasu abubuwan da suke ɗakin angama tattarawa dake dama tunda aka tabbatarda yanda zai sauƙa aka fara bawa ɗakin special service saida akayi renovating ɗinsa aka canja komai tsarin wajan yadawo dai-dai da tsarinsa.

Shi da P.A sai zallan driver suka je makarantar. Mun kai 1hour da zamansu kafin muka shiga wajan.

Dama jiran shigowata yakeyi yaganni yau zai wuce ƙasarsa. Gabaki ɗaya yanajin babu daɗi tafiyarda zaiyi yabarni.

Na kallesu Yau tsawon 1week kenan killum sai sunzo wajan kuma yanzu jikina yana bani da wani dalilin suke zuwa. To kona tunkaresu ne naji dalilinsu na BIBIYATA? Toh amma idan masu cutarwa nefa?" da masu cutarwa ne da yanzu sun daɗe da cutar dake zuciyata ta bani amsa. Neman waje nayi na zauna. Amma wani abun mamaki bantaɓa kama wani acikinsu yana kallona ba ko wani dalilin yake kawosu?"

Jiki a saɓule natashi nayi wajansu yau ina buƙatar jin dalilin bibiyata da sukeyi."

ZAYNAB ALABURA
*BIBIYATA YAKEYI*
              *(WAYE SHI?)*

       Wannan littafin na kuɗine kibiya  ₦300 ta asusun  bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.

Dasauri na dakata saboda yanzu zuciyata take bugawa wata Zuciyar tacemin what if ba wajanki suke zuwa ba? Idan wata damuwarsu daban take kawosu fa? Toh idan taje ta tunkaresu ma me zata ce musu? Menene dalilin samun nasu da zatayi. Taji ƙamshin turarensa a gidansu. Anya wannan ta isa shaidar da zata tunkaresu kuwa?" canja akalar tafiyarta tajuya ta zuwa. Tana zaune maryam tazo ta sameta suka jira aka kawo musu abunda sukayi order.

P.A ya dubeshi cikeda tausayawa ya fahimci hakinda yake ciki tafiyar gabaki É—aya bata jikinsa. Dama mutumne shi mai sanyin rai amma na yau dabanne ya canja gabaki É—aya kuma yasan taraddadin rabuwa da Itane.

"Mood sir" ya É—ago ya kalleshi batareda yace komai ba yana kallonsa alamun yana jira yayi magana.

"Ko zamuyi É—aga tafiyar ne? Idan zai zama issue lets postponed it" saida yayi murmushi sannan nodding kansa.

"bazamu É—aga ba We're going. However i'm going to miss her" P.A yayi murmushi cikin lallashi yace.

يجب أن نعود قريبا"
"(we should come back soon) Thats my opinion" Saida murmushi ya kufce masa yace.

حسنًا ، لنفعل ذلك"
(okay lets do that). P.A yace .

"علينا أن نذهب الوقت يذهب"
(we have to go time is going).

لا دعها تذهب أولا
"(No let her go first). Suka zauna jiranta harta gama abunda takeyi tatafi tukunna suma suka miƙe suka tafi.

Tunda mukayi lectures na safiya bamuda wani lactures har sai 4dan haka muka wuce masallaci muka zauna dan munfi samun sakewa acan tunda maza basa shiga.

tunda nashiga muke waya da Hamma har kusan 1hour maryam harara kawai takeyimin tana faÉ—in.

"Kekam dai wallh bakiji daɗi ba. Kullum ananiƙe da waya idan kukayi aure babu mai zuwa gidanku saboda jaraba" tayi maganar ne yanda bazai jiba amma ya jiyota daga cikin wayar yace.

"Baby maryam ne take magana?" nayi saurin cewa.

"A'a ba ita bace kaji wani yayi magana ne" na tambaya.

"Ke dai karki kare ƙawarki naji ta kiramu da jarabbabu. Idan mukayi aure karma ta nemi hanyar gidanmu dan saina tabbatr mata abunda ta faɗa a idonta tagani" Nayi shiru dannasan halinsa yasamu shafi kenan yanzu kuma zai fara sakin layi. Ya narke murya yayi muryar tausayi yace.

"Baby" Saida tsikar jikin ata zuba nakasa amsawa yacigaba da faÉ—in.

"Baby bakyajin kamar a matsoda lokaci muyi aure mu kasance tare? Na matsun mu kasance atare baby i wish the clock will work faster dan normal. Am morethan earger babyyy". Saurin É—aga wayar nayi a kunnena dan ganin yanasan Jefani wani hali.ganin na É—aga wayar da sauri ya sanya maryam ta dubeni tace.

"Babe lpy" juya mata baya nayi na maids wayar kunnena cikin shagwaɓa nace.

"Hammana kabari"

"meyasa Baby? Bakison na faÉ—a miki yanda nakeji gameda kene? Baby inaso kisan yanda zaki kula danine bayan aure mijinki bakowani irin miji bane. Bakyaso kisan wani irin miji kike shirin aura?"
Shiru nayi yacigaba da magana.

" baby kina jina?"

"Uhm inaji"

"shine kikaƙi kulani? Baby Bakison magana danine?"
dasauri nace.

"A'a Hammana inason magana dakai sosai idan banso magana dakai ba dawa kakeso naso magana"

"okay tob idan kina sona kiso abunda nakeso. Akoda yaushe inaso ina expressing feeling É—ina idan ina tare dake saboda kece wacce zan zauna dake inaso ki fahimceni fiyeda kowa" Naturo baki nace.

"Nitoh menace Hamma? Nifa kawai bazan iya cewa komai bane yasa nayi shiru"

"Baby kunyarki tayi yawa kada kibari kinyarki tayi mana shamaki a jindaÉ—in rayuwarmu"

"toh" kawai na amsa masa. Yacigaba da maganarsa ina sauraransa har saida mukayi sallama lokacin ameera tacika tayi damm. Najuya ina mata magana ta shareni haka nayita lallashinta harta sauƙo.

"Babe kinsan meya faru?" na girgiza mata kai tace.

"Ummi da Abba sunaso sutafi Umra kuma wai gidan ƙanin Abba zasu barni wallh babu wanda nasaba dasu a gidan kuma nasan ba daga umarar zasu dawo ba dan Allah kiroƙamin Baba yayiwa abbanmu magana yabarni na zauna gidanku" na zaro ido nace.

"Yaushe abba zai bari ke dai ki zauna gidan ƙanin abba kawai" nafaɗa cikin wasa ta ɓata rai sosai tace.

"Wato inzauna abuna nagode babe tunda gidanmi ba gidanku bane" tunda tafaɗi haja taja tayi shiru tadaina kulani. Nayi mata magana naga ranta ya ɓaci sosai ban ɗauka haka zata ɗauki abunba har mukayi lactures muka fito bata kulani. Ganin abun nata na gaskene yasa nace.

" Babe wai meye hakanne daga wasa kinwanibi kin tanke fuska?"

"Au ashe wasa kikeyi tafaɗa adaƙile"

"idanba wasa ba menene zanƙi ki zauna gidanmu ne?" amma kina kallon Abba zai barki?"

"In Abbane baida matsala. Koni nafaÉ—a masa zai iya yarda amma nafiso Baba ya sanar dashi kansa shima kinga zaisanda zancen tun kafin lokacin"

"Toh shikenan idan hakane kibani lambar Abba zan bawa Baba zaiyi masa magana zai aminc. tayi hugging É—ina tana faÉ—in.

"thank you babe i love you. Wallh zanfi samun kwanciyar hankali agidanku kinga zanfiyin karatu hankalina ƙwance"

" shikenan. Amma ai fushi kikayi daniba haka zamuje kullum muna yiwa su mama faÉ—a da fushi?"

"Masu hali ai basa fasa halinsu toh hakama su mama zasuyi haƙuri su gansu su barmu"

"Gara kizauna agidanmu ma kinga zan samu ina kallon Hamma na alokacinda nakeso"

"Babe wai sai yaushe za'ayi maganarku da Hamma sai yaushe iyaye zasu shiga? Wallh gara kibashi dama ayi magana dan Hamma zai cinyeki É—anya"

"Bansan munafunci ke ina ruwanki ya cinyeni É—anye mana kinada matsala da hakanne?"

"Allah yabaki haƙuri amma gaskiya yakamata Azo ayi magana musha biki My babe zata auri Hammanna. Babe zamusha biki. Kullum agidanku Fadeelah ta ƙarasowarta wajan kenan tace.

"me nakeji? Zainab Dama soyayya kukeyi da Hamma?" Nayi farr da ido nace.

"yada cewarki?

"Amma wallh zainab kinci amanata ashe dama kema kina sonsa? Kema Maryam bakida kirki saboda kunfi kusanci da Zainab shine kika haÉ—ata da Hamma" Maryam tace.

" ni? Nina haÉ—asu?"

"Ke ni bbu wanda ya haÉ—ani da Hamma. Shiya ganni yace yanaso nima ina sonsa keni nama manta kina sonsa sai yanzu"

"Gara kiyi haƙuri dan Wallh kamar zasu cinye junansu suke" Alokacin Hamma ya sake kirana.

" kingani koh toh ki shafawa kanki lpy Hamma baya ganin kowawacce budurwa da gashin ido sai ita"

"Allah zainab kinmim shigan sauri wallh" Ko kulata banyiba natashi nabasu waje Batasan zancenda takeyi haushi ma take bani ba."

Bayan nakoma gida na tsinci wannan ƙamshin turaren ga dukkan alamu Yauma Baba yayi baƙi. Inaso na tambayi Baba baƙinda suke zuwa wajansa amma bazan iyaba saboda nasan banda hurumi a sanin wanda sukazo wajansa."

-----------------

Ƙarfe goma tara na dare jirginsu ya sauƙa a ƙasar UK. As usual motoci sukazo taryansu kamar yanda aka saba, kai tsaye wani gida suka nufa mai masifar kyau wanda yakeda girma sosai. Gidan akwai jami'an tsaro da ko'ina sai zagaye-zagaye sukeyi.

Har bakin mashigar gidan motocin suka kaishi sannan guards suka buÉ—e cikeda nustuwa yanufi ciki,
Kai tsaye cikin falon ya kutsa kai ya isa har zuwa É—aya daga cikin set É—in kujerun da suke falon ya zauna,

Jin ƙarar sauƙowa a step ya sanyashi miƙewa ta ƙaraso yanda yake tayi hugging ɗinsa shima yayi hugging ɗinta back sun ɗauki seconda ahaka tana shafa bayansa sannan ta sakeshi ta sumbaci gefen kumatunsa haɗeda faɗin.

"Welcome mood" ya sakar mata murmushi ya zauna gefe. Itama ta zauna a kujerarda yake zaune.

"Mood" takirashi ya jiyo ya kalleta ta jefo masa tambaya.

"Me kaje yi wancan ƙasar?" baka sanarda niba. Business trip? Ko ƴan jaridu basusan dalilin daya kaika ba" Ya miƙe batareda ya amsata ba yana faɗin.

" i'm hungry lets discuss latter. Yafaɗa alokacinda ya nufi dining tasan da zuwansa therefore yasan tashirya masa abinda zaici ya zauna masu aiki suka ƙaraso dama suna tsaye a wajan aka fara serving ɗinsa a nutsuwa ga dukkan alamu baya ɗaukan shirme dan duk wanda suke tattare dashi suna abu cikeda kulawa da nutsuwa. Aka gama serving yafara cin abincin cikin nutsuwa. Wannan matar tataso ta zauna gefensa tana faɗin.

"Mood am talking" Ya É—ago ya kalleta yace.

"Mum please" tayi shiru ta rabudashi harya gam.

Cikekkiyar baturiya ce wacce bazata wuce 55yrs ba.
Sai bayan yagama sannan ya dubeta yace.

"Naje neman Aurene" ta kalleshi da mamaki tace. You joking right? Bai amsa mataba ya kalleta kawai hakan ya tabbatar mata da gaskiya yakeyi.
Chapter 26 · 0% Book details