← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 106

Sashe 86

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan yaji dama-dama ya tashi daƙyar yake ɗaga ƙafafunsa har suka kaishi zuwa gadon. Kafeni da idanuwa yayi yaga yanda nake bacci cikin ƙwanciyar hankali shikuwa yasan baida wannan damar, ƙwanciya yayi gefensa na dama ya mirginoni nadawo jikinsa, Buɗe idanuwana nayi jin mutum ajikina dake baccin ne a idona na mayar na rufe riƙeni yayi gam a jikinsa kamar wanda za'a ƙwaceni, saida dare yaraba kafin bacci ya ɗaukeshi. Nikuwa tunda na koma bacci ko alamun farkawa ban sake yiba har asubahi. Saida ya shirya tafiya masallaci kafin ya tasheni yafice. natashi saida nayi wanka kafin nayi sallah. Na daɗe ina addu'a akan mahaifiyarsa naga alamun bazamu ƙwashe ta daɗi da itaba abune mai wuya ta amsheni batareda ansha wahala ba.

A kan sallaya yadawo ya sameni ina ganinsa na sunkuyar dakai dan danasan zai shigo dawuri dana ƙwanta kamar wacce nakoma bacci. Fuska babu walwala ya ƙarasa kusa dani nayi masa barka da safiya ya amsa yana kai hannusa kaina shafa kan yayi yana kallon fiskata nikuma naƙi ɗagowa muhaɗa idanuwa dashi saboda ina matuƙar jin nauyinsa. Muna zaune ahaka har yaga alamun bacci nakeji.

Miƙewa tsaye yayi ya nufi wani gefe a ɗakin ya buɗe closet wata ƴar ƙarama itama dai kamar duka closet na gidan baza'a taɓa ɗauka ma'ajiyar kaya bace sai dai ita bata kai girman Wall guda ba kayansa ya canja izuwa na ball ya sanya takalmi ya juyo gareni.

"Zanje training ki koma bacci idan na gama zan shigo karki buɗewa kowa ƙofa" kai kawai na gyaɗa masa ya fice yatafi.

Sassafe Mum tabar ƙasar batareda ta yarda sun haɗu da Hammood ba kodan tasan zatayi zaman jirane kawai batareda ta ganshi ba.

Lina kuwa tana tashi ta ɗauki wanka tasaka ɗan ƙaramin skirt da Half vest wacce ko chest ɗinta bata gama rufewa ba bare ayi maganar cibiya. Tambayan ma'aikatan gidan yanda Hammood yake tayi suka shaida mata yana filin wasa a filin ƙwallon taje tazauna tana kallonsa. Tunda ta isa wajan hankalinsa bai kai kanta ba gabaki ɗaya ya tattara hankalinsa a training ɗinda yakeyi saboda a lokacin ya fara tun fitowarsa yana Gym Ya ɗauki lokaci yanayi Sannnan Ya zauna zai huta ruwa taɗauka a water bottle ta nufeshi tana zuwa babu magana ta miƙa masa kallon ruwan yayi ya kalleta daga ƙasa har sama ta sakar masa murmushi ya amsa haɗeda yimita godiya ta zauna gefensa.

"Meyasa baki bi Mum ba?" ya jefa mata tambaya a yayinda ya buÉ—e bottle É—in ruwan.

"Saboda Ban aiwatarda abunda ya kawoni ba" Yakai bottle ɗin ruean bakinsa Saida yasha ruwan sosai ya kashe ishinsa sannan ya miƙa mata haɗeda sake godiya ya miƙe batareda yasake kulata ba yawuce cikin fili dama coach ɗinsa yana zaune a gefe yana jiran dawowarsa (wannan his personal coach ne bawai na team ba). Sai 10:00am kafin yagama Abunda zaiyi har alokacin tana zaman jiransa a gajiye ya nufi ciki tabishi tanason yin magana dashi.

"We'll talk later lina yanzu I'm tired idan nafito zan nemeki" oKay zan jiraka yanzu amma barina rakaka zuwa Sahshinka"

"is okay zan tafi dakaina" baijira cewarta ba yaƙara saurin tafiyarsa. Sai tara da mintuna kafin natashi kai tsaye wanka na shiga na daɗe sosai a ciki na haɗa ruwan wanka ina zaune ciki. Sai wajan 10:00am na fito daga ruwan na ɗauki towel gabaki ɗaya towel da suke wajan Medium ne basuda girman da zasu sauka har cinya idan suka rufemin sama bazasu rufe ƙasa mai kyauba idan suka rufe ƙas akuma sama bazai samu rufuwa dakyau ba babu yanda zanyi na ɗaura nafice zuwa cikin ɗakin a hankali nake tafiya saboda tsoron sincewar towel ɗin na isa gaban mirror mai nafara murzawa lallausan fatar jikina sannan na shafa duk wani abun ƙamshin da nafara amfani dasu zuwana nan na gyara kaina na shafa masa shima mayuka da Hair spray. Ina cikin shirys kaina yashigo baibi takaina ba yawuce toilet ajiyar zuciya na sauƙe ganin kamar bai lurada yanda nakeba. Closet na buɗe sai dai babu wani kayan arziki kusan kayan barcin da nasaka jiya yafisu mutumci. Duk wata riga da skirt Skirt ɗin Mini ne sai Bomb-short masu yawa babu dguwar riga ko guda ɗaya. Wancan ɗakinne yakeda dogayen kaya. Daƙayr na iya nemo shashin Riga da long trouser sai dai rigunan suma kaff ɗinsu half ne wasu sun kai kan cibi wasu basu kaiba.

Nacire wandon nasaka kamar wanda aka gwadashi da shape ɗin jikina yayi masifar kyau nasaka rigarma sai dai bazan iya zama da rigarda cibi yake wajeba. Dole zan tafi can ɗakin na nemi kayanda zasu suturtamin jiki. Ina fita nasamu yayi locking ko'ina Babu yanda za'ayi na iya buɗe ƙofar, shikuma bayaso lina ta biyoshi ne yasa yayi haka. Bazan iya buɗewa ba hakan yasa na zauna falo na takure kaina.

Bayan yafito a wanka sannan ya nemi wajan da nake bai ganni ba hakan yasa yafito palour dan yasan bazan iya fita ba dan bansan pin na ƙofar ba. A zaune ya sameni na takure jikina ya ƙaraso ya zauna cikeda kulawa ya jawoni jikinsa.

"Menene yafaru? Ya tambaya.

"Banason wannan kayan da yake jikina a dole nake sakasu ka buɗemin ƙofa naje na saka wasu kayan please" cikeda sigar lallashi da tarairaya kamar wanda yake magana da ƙaramar yarinya yafara magana.

"Bakison farantamin ne? Inason irin kayanda yake jikinki sosai shiyasa na zubasu a cikin wajan cikeda saka ran zaki sanya danki farantamin wajanki kaÉ—ai nakeda hurumin gani naji daÉ—i. kece halalliyata da kika halatta gareni, Amma har indai kinji zaki takura muje in rakaki ki canja" kalamansa masu cikeda da hikima da wayo sun karyar mun da zuciya na girgiza kai alamun nafasa canjawa.

"Okay toh tashi naga yanda kayan sukayi miki" na maƙe kafaɗa alamun A'a. Ya tattara hankalinsa gareni gabaki ɗaya ya sake matseni jikinsa ya saisaita murya.

"Kinga Lina yanzu muka rabu da ita ƙananun kayane jikinta banson ganinta yasa nataho ciki danna ganki" ɓacin rai ya ziyarci zuciyata na haɗe raina sosai ido sukayi narai-narai.

"Ni banason zamanka da ita kaga fa irin shigar da takeyi baka hanata ba bayan kasan Babu kyau kuma ranar a idona ba kunya ba tsoron Allah ta rumgumeka gaskiya ni kace mata tatafi" saida yayi Æ´ar dariya sannan ya amshe.

"Yaya zanyi toh kinga ita addininsu baice mata dole saita rufe jikinta ba idan tasaka Kawai hanya guda ɗaya da nake dashi na kalla a jikinki, ana gama worldcup zata tafi she's my cousin yarinyar sistern Mum ce and kuma ranar tayimin unexpected hug ne bansan zatayi ba da zan kaucewa faruwar hakan ranki ya ɓaci ne? Idan kinji babu daɗi I'm sorry.

"Yarinyar sistern Mum ce kuma ba addininku É—aya ba? Kuma kasan dole zanji babu daÉ—i tunda dai niba dutsi bace da wata zata rumguni mijina a gabana batareda naji wani iri ba, wata frdn É—ina Umm najma dana faÉ—a mata cewa tayi da itace saita bata Blow a baki" dariya sosai Yayi.

"Rouhii kodai kece kikaji kamar kibata blow?" no bani bace Umm najma ce tafaÉ—a data faÉ—awa Ameerah tayita zaginta itama harda cewa Allah yasa karta É—auki hankalinka."

"Ni bazata É—auki hankalina ba koda wasa, amma wai cikin Frnd É—innaki babu wacce take bki shawarar yanda zaki kula da miji? Kunyarki tayi yawa"

"Akwai dayawansu ma irinsu Aisha É—alhatu da meelarh gumel kullum zancen kenan"

"Okay idan kin ɗauki shawarasu Show me tashi ki nunamin kayan jikinki" A matuƙar kunyace na miƙe ina sunna kaina. Ciff-Cff kayan yayimin kamar wanda aka aunashi a jikina na sanya hannu ina kare cibiya na. Saida yaji tsikar jikinsa ta zuba saboda yanda kayan yayimin kyau ajikina dama kuma sam banda tumbi sai yayi kamar wanda aka zana ƙirar. Hannunsa ya ɗaura akan hips ɗina ya matsa saida na runtse idanuwa. Kyawawan idanuwansa nan da nan suka fara canja launi izuwa kalar namijin dayake cikin buƙata. Jawoni yayi nafaɗa jikinsa ya ƙwantar dani ya yabi yamun rumfa. Cikin sarƙaƙƙiyar murya yafara magana yanaji yanashan iska.

"Babe i need you please please kibari nasamu nutsuwa daga gareki, karki yimin kuka domin duk buƙatuwar danake ciki bazan iya jure kukanki ba" yafaɗa har maganar tana ƙaƙarewa. Dasauri na girgiza kaina. Ya rintse ido yanajin wani yanayi a cikin jikinsa"

"Why? Meyasa kikaƙi amincewa dani har yanzu? Bakya sona koh?"

"No bahaka bane Ina tsorone?" shiru yayi yana auna maganata daga yanda yaga jikina yake rawa ya fahinci a halin yanzu bazai taɓa samun abunda yakeso daga gareni ba, tun baiyi komaiba nafara shirin kuka. Zaiyi haƙuri yajira har ya daidaici lokacin daya dace Kuma yanzuma ko yayane yana buƙatar rage zafi"

"Is Okay naji bazan kusnceki yanzu ba amma sai yaushe? When zaki bari musamu farin ciki daga junanmu?" Nayi shiru naƙi bashi amsa saboda bansan yaushe zance masaba.

"Idan kin amince nasamu sauƙi daga gareki bawai ina nufin na kusanceki ba, gangar jikinki nakeso ki aramin nasamu nutsuwa batareda na shigarda kaina izuwa jikinki ba" kai kawai na gyaɗa masa. Lokaci guda yafara kissing ɗina jikinsa har rawa yakeyi. Tsayawa yayi cakk yana kallon fuskata da na rufe ko motsi banayi.

"Bazaki tayani samun nutsuwar ba?" Idona yana rufe na tura baki.

"Kai kace na ara maka gangar jikina" murmushi yayi ya yi kissing kan hancina wasa gaske ya lura wata irin rigima nake dashi.

"Toh drama Queen ataimaka a tayani samun nutsuwa" na maƙe kafaɗa yayi murmushi kawai ya tashi ya ɗaukeni cakk izuwa ɗaki dan budirin dayakesonyi kujera tayi masa kaɗan. Mamakin yabda ya ɗagani nake danni kaina nasan zanyi nauyi amma shi kamar bai ɗauki wani abu mai nauyi ba.
Chapter 86 · 0% Book details