Sashe 79
Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 7 min read
Katse shirun nayi da tamabayar yakiramin gida dan layikanmu gabaki ɗaya sun daina aiki. Babu ɓata lokaci ya danna wayar Baba yakira bugu biyu Baba ya amsa dasauri na amshe wayar banbari sun gaisa ba. Alokacin danaji muryar Baba fara'ata da faɗaɗa ayayinda shikuma ya dafa saman kujera yana kallona waya nake cike da kewar gida inayi ina murmushi daganan sai hawaye. Gabaki ɗaya mutanen gidan Saida muka gaisa banda Mama wai tana aiki a kitchen mun daɗe muna waya sannan Mama tashigo ta amshi wayar.
"Kuna lafiya Marmeeyy"
"Lafiya Kalau Mama ina kwana?"
"Kwana kuma Marmeeyy mukam yanzu ai nan ranace kinga yanzu Babankuma masallaci zai fita aja kiram Azahar" na É—aga wayar a kunnena na duba time sannan na maida.
"Mama mukam Nan ƙarfe goma ne da mintuna"
"Toh barka dama ai akwai bambamcin awanni tsakani inasu Mummynki?"
"Nima bangansu ba tunda natashi ko motsinsu banji ba sai dai na nemesu"
"Barsu idan kin sake kira ma gaisa amma yanzu Babanku zai tafi sallah zan bashi wayar sai anjima" bata jira abunda zance ba ta datse kiran. Na ɗaga wayar hawaye yanabin kuncina Naso muyi hira yafi haka da Mama amma bata tsaya ba hawaye wasu nabin wasu banaso nayi kuka mai shessheka. A hankali ya sanya tausasan hannuwansa ya sharemin hawayena na ɗago na kalleshi nima shi yake kallo. Na tsura masa idanuwa tunanuka dayawa cikin raina. Tunani nake me Mutum kamarsa yagani a wajena da har zai soni ya ɗaukoni ya rabani da ƴan uwana? Menene da yake nema wanda bazai sameshi a matan da suke kewaye dashi ha dahar saiya rabani da Ahalina? Tabbas Daba ace Hammood bane da sai naji haushinsa matuƙa amma tayaya za'ayi naji haushin Hammood? Na sauƙarda idona ƙasa haɗeda turo baki.
Allah yagani shi komai nakeyi burgeshi nakeyi yanzu haka mamaki yake yanda nake haɗa dariya da kuka lokaci guda. Yaga tsantsar farin ciki a fuskata da ina magana da dangina zaiso ace zai bani farin ciki kamar haka a gidansa amma yanzu ma zai ƙoƙarta. Ganin yana kallona yasa na sake shagwaɓe fuska wanda hakan akoda yaushe nayishi ni kaina nasan yana ƙaramin kyau bare kuma mai kallona. Yanzu nagama dariya amma inaso na ɓige da rigima.
Sauƙar hannunsa danaji akan shafeffen cikina a razane na ɗaga na kalleshi ɓata rai nayi sosai na sanya hannuwana biyu inaso na cire hannunsa daga cikina kasa cirewa nayi a lokaci ɗaya ya fara shafa cikin na runtse idona dan saida tsikar jikina ta zuba.
"هل أنت جائع"
(Kinajin yunwa) Dasauri na girgiza kai dan inaso ya cire hannunsa daga cikina.
"أعر٠أنك جائع"
(nasan kina jin yunwa) bai jira abunda zan sake cewa ba ya sauƙe hannunsa saida ja sauƙe ajiyar zuciya ya kamo hannuna .
هيا تعالي" Yanje hannuna nayi daga cikin nasa nafara binsa abaya. Saida muka fita gabaki ɗaya daga cikin wannan shashin wani waje daban muka nufi wata ƙofa da take buɗe. Ƙaton kitchen ne wanda shi kanshi mai gidan wannan ne shigarsa karo ta farko. Fridge ya isa ya buɗe na tsaya na jingunu jikin cabinet Fuska babu fara'a. Abubuwa ya dinga cirowa cikin fridge yana nunamin ina kauda kaina gefe idan nayi hakan yaga alamun banaso kenan ƙarshe sai ficewa mukayi cikin kitchen ɗin batareda nasamu abunda zanci ba bawai dan banga abunda nakeson bane kawai bazan iya amsa a hannunsa bane. Palourn da muka zauna ɗazu muka dawo yabarni a wajan ya fita bai daɗe da tafiya ba yadawo Muna zaune kusan 30minute muna zaman kurame sau dayawa nakan saci kallonsa muna haɗa ido saina haɗe rai har wata ma'aikaciya yazo tauwce dining ta jera abincin data kawo.
Cikin ladabi tazo ta tsaya daga gefe tace tagama abunda ya sakata. Bai amsa ba amma sanin yaji abunda tafaɗa sai tabar wajan. Miƙewa yayi ya isa wajan dakansa ya buɗe yagani sannan ya dawo wajena yatafi dani dining ɗin. Nigerian fried rice ce kamar yanda ya umarceta tayi haka tayi. Nazauna nafara ci babu laifi dai amma baiyi kamar yanda mu mukeyinsa ba. Naci iya dai-dai cikina natashi Kallona yakeyi yana ganin kamar inaƙin cin abincine saboda yana wajan baisan cewa ni dama bawai inadaci sosai bane kuma maganar gaskiya cinda Hammood yake dashi ba kowane zai iyaba.
A palourn muka sake wani zaman kuramen TV ya kunna amma hankalinsa sam baya jiki yanada abunda zaiyi amma bayaso yatafi yabarni ni ɗaya a gida dan yasan zaman kaɗaici zanyi sai su Mummy sun dawo zaifita. Ana kiran sallah ya miƙe yafita nikuma nakoma ɗakina anan nasake wanka dake August ne kuma a watan suna experiencing extreme hot waether dukda cewa gidan Babu zafi amma kuma babu sanyi sai sanyin AC wanda lokuta dayawa yakan dameni. Ba kayan ɗazu na mayar ba wasu kayan nasaka dolena na nemi marassa nauyi. Daganan na ƙwanta bacci. Shigowa ɗakin yayi yaga ina ƙwance ya ƙarasa ciki bayan ya tabbatar bacci nakeyi sai asannan yasamu damar fita dan aiwatarda abubuwan da suke gabansa. Sai Yamma su Mummy suka dawo ashe Hammood yasa aka fita dasu dan suga gari suyi shopping.
Haka rayuwa tacigaba da tafiya kullum a ɗakina nake ƙwana Mummy ke korani kamar mai kunnen ƙashi kullum sai naje zan ƙwana wajanta ta koroni. Kullum Mummy ke haɗamin ruwan wanka tana turarani da turaruka masu ƙamshi daga jiki har kaina sannan akwai wani abu guda tunda ta bani naji daɗinsa bokiti guda dakaina nake zuwa na dauka inaci. Zallan dabino da ƙwaƙwa da madara akayi sai sauran garirrika amma dabino da madara da Kwaƙwa sun kauda tastse na komai dake ciki Mummy har magana takemin akan cinsa danake kamar ba gobe amma banji ba idona yana kaiwa wajan ajiyar sai naci. Kum harga Allah har raina bansan amfaninsa ba nidai kawai inacine. Mummy suna fita zaga gari idan yau su basu fitaba fita ba washe gari zasu fita. inaso ina binsu Amma Mummy firr taƙi tace idanda yanada ra'ayin barin matarsa tafita toh da zai sanya dani cikin masu fita. Yanzu kullum zaman kaɗaici nakeyi dan wata rana saina wuni zubur ban ganshi ba. Ana saura 3days su Mummy sutafi ina ƙwance a ɗaki ga zullumin tafiyarsu dayake raina gakuma zaman kaɗaici. Hammood yashigo ɗakin na ɗaga idanuwana na kalleshi na maida na rufesu duk da abaya ba arufe ɗin suke ba. Hawa gadon yayi yana kallona shi kansa yana shiga damuwa da halin kaɗaicin danake ciki.
"Zaynab"
"Uhumm" na amsa batareda na kalleshi ba.
"Meke damunki?" na jijjiga kai alamun babu komai amma hawaye nabin fuskata daga ƙwancen danake. Ajiyar zuciya ya sauƙe ya ciro waya ya miƙamin dake idona a rufene banganiba har saida yayi magana na buɗe ido na amshi wayar sannan na kalleshi ina neman ƙarin bayani.
"Kiyi amfani da wannan wayar layinki na can bazaiyi amfani anan ba" ki kira gida a duk lokacin da kikaji kewarsu" nayi murna sosai nayita masa godiya dan wata kewarma harda rashin waya a hannuna.
Murmushi yayi haɗeda shafa kaina a hankali kamar wanda yake rarrashin wata ƙaramar yarinya naga alamun ɗaukar jaririya yake yimin yanda yake treating ɗina ya nuna hakan. Idan kuma ba haka ba toh akwai wani abun aransa dan ko sau ɗaya Hammood bai taɓa taɓani da niyyar wani abunba bansan ko yanajin bazai iya haɗa jikinsa dani bane kokuma bai shirya zamar dani cikekkiyar mace ba ko akwai lokacin dayake jira amma ni ayanda naji idan akayi aure tsakanin mace dana miji koda babu soyayya akan samu wasu abubuwan da zasu shiga tsakani ga Hamma da Aysha nan ba auren soyayya sukayi ba amma hamma ya kusanci Aysha ranarda aka kaita gidansa bawai ina tunanin hakan dan ina matse kona damu da inaso Hammood ya kusanceni ko yafara nunamin wani abunba a'a ayanda nakeji kuma nasan kaina zamu iya rayuwar shekaru ahaka batareda na damu a inbanda bambamcin yare da al'ada dake tsakaninmu ba ina tsoron kar Hammood yana ƙyanƙyamin hada jiki dani kasancewata baƙar fata ne. Abunda yake damuna kenan tunda koda bansaniba labari nakanji cewa maza sam basuda sauƙi har indai akan macece ko Yaya take kuwa. . Na zame kaina Murmushi yayi ganin na ƙwace kaina yasan rigimata bata wasa bace. Na danna wayar a yayinda nake shiga ciki numbernsa kaɗai aciki na ɗago na kalleshi.
"Meyasa kake amfani da layikanka a ko'ina kana kirana da layinka kananan ko can" Miƙewa yayi daga zaunnen dayake sannan yabani amsa.
"Saboda nine Hammood" Na jijjiga kaina dan gamsuwa da maganarsa tabbas dan shine hammood shiyasa zaiyi abunda yaso a yanda yakeso. Narai-narai nayi da fuska kamar zanyi kuka dan ganin shigowarsa naji daɗi har naɗan ware amma har ya miƙe zai fita. Kasa daurewa nayi na tambayeshi.
"Fita zakayi?"
"Yes ko bakyaso nafita?" dasauri na jijjiga kai. Ya miƙomin hannu.