← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 106

Sashe 57

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Haba Baba dan Allah kabari kana sani jin wani iri karka sanya nadawo ƴarda bata gari ba wanda bazata iya farantawa iyayenta ba karka sanya najibkamar ban cancanci zama ƴarku ba har indai zaka tsaya bani haƙuri akan wannan lamarin. Shin wai Baba bankai ka yanke duk hukuncin da kaga dana akaina bane? Nifa da bakina na faɗa maka duk wani hukunci dakaji yayi dai-dai dani a rayuwa ka yankeshi kai tsaye. Bazan taɓa bijierewa umarninka ba kuma zan amshi kowani irin hukunci daka yanke akaina hannu bibbiyu kainefa ka haifeni Bani haƙurinda kakeyi zaisa naji kamar bibiyar danake maka takasa wacce yasa kaji idan ka yanke abu akaina yakamata kabani haƙuri banga abunda bazan iya sadaukar dashi akanku ko wani ɗan uwana ba.

"Shikenan Allah yayi miki albarka" shine kawai abunda yasake faɗa dan yanajin bayida wata kalma da zata nuna irin farin cikin dayake ciki face yayi mata albarka sannan idan yazo sallah yayi addu'a ya roƙi Allah ya kareta sannan yayi masa godiya da azurtashi da ƴa kamar Marmeeyy" Muda Ya Ahmad duka muka amsa da Amin. Jin shiru ya tabbatarmin da Baba yagama maganganunsa. Nadubi Ya Ahmad.

"Muje koh? Yanzu kusan huÉ—u da rabi lokaci yaja"

"Oh kin shirya kenan? Eh nashirya kai kawai name jira"

"Anya kuwa tafiyarnan matafi da wannna shiga Marmeeyy?" nadubi kayan jikina dakyau sannan na É—ago na kalleshi batareda nace komaiba.

"Kije ki canja kaya ya" na miƙe dasauri nayi ɗakin Mama 5minute nadawo na canja a palour na sameshi harda Mummy su Anty fadeelah gabaki ɗaya sun shirya.

"Au wai kin shirya kenan Marmeeyy? A'a jeki canja kaya" na kalleta kamar zanyi magana sai kuma na juya saida na canja kaya say uku na huÉ—unne nasaka wani riga da skirta wanda ya kamani sosai wanda ya Ahmad ya hanani sakawa a bikinsa nasaka hijab akai dannasan zaiyi magama idanna saka gyale.

"kayan yayi amma jeki saka gyale" mummy ta umurta na kalli ya Ahmad yabani yamin alamu da kayi nakoma ɗauko gyalen nasamu Mama tana fitowa miƙamin zobena tayi wanda tunda ta amsheshi bata sake baniba yanzu kam ta fahimci daga yanda zoben ya fito dan fitata nazari take tayi tasan dole shi kaɗai yakeda wannan ikoj yin hakaa akan zobe zallah. Na amsa batareda musu ko tambaya ba nasaka Nawuce na ɗauko gyalena turare Mummy tabini dashi kamar wanda zatayimin wanka har saida naji yahaumin kai duk sanyin ƙamshinsa.

waje dukanmu mukayi anan naga ƙawayen aysha cousin sis ɗinta suna shiga mota tareda Yaya habeeb dama tunda aka fara biki Baba yabawa Yaya habibu mota a hannunsa. Wannan uwar rawan kai itace ya shiga gaba a lokacin a abuja ta nuna tana sonsa har mun taɓa jiyota tana faɗawa aysha.

Na taɓe bakina na buɗe baya na zauna dake harda matarsa zamu tafi Anty fadeelah ma tashigo baya haɗeda wasu cousin sis ɗinsu. Matar Ya Ahamd tashiga gaba suma suka cika wancan motar muduka muka nufi gidan Aysha."

ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya

Assalamu alaikum yan'uwa da abokan arziki🤝🤝🤝
Ina mata masu fama da wadannan matsalolin

Matsalar haihuwa
rikicewar al'ada
ciwon mara yayi period
Fesowar kuraje ga gaba
Ganin farin ruwa mai wari yana fito maki
Kurajan gaba
Kaikayin gaba

Da dai Sauran wasu alamomi to yar uwa kinsan ko miye to ba wani abu bane face sanyi ne ya taro yayi maki yawa 😔😔😔

Toh masha Allah sha kuruminki Allah ya kawo maki sauki ga wannan addababai ciwo

Maganin da zaki sha kiyi garau da yarda Allah 🙌👍

Toh ga dama ta samu maza ki kira aunty zee mom mujahid Katsina akan wannan lambar wayar ki ce mata MAIJIDDA MUSAWA ce taba ki wannan number
ki na son sanyan magani
08162859027🤝
-------

Acan muka samu Maryam dan tunda naga ya Habibu zai tafi na tabbata saiya sanarda ita taje.

Da alamu itama zuwanta kenan bata daɗeba muka iso. Da sallama muka shiga ciki Aysha taba zaune akan kujera jikinta da sauƙi sosai dan ahaka bama za'ace akwai abunda yake damunta ba. Ya Ahmad da Ya habibu basu shigoba suna daga waje muma muka ƙarasa ciki muka zaune. Aysha batayi tsammanin ganina a gidanba dan naga hakan daga fuskarta data ganni kuma sakta yatsine fuska. Murmushi nayi Aysha kenan adakeni a hanani kuka ni itace ke kishi dani bayan masoyin nawane bata iya ɓoye haushin da takeji aranta ako'ina nunashi takeyi. Bayan nayi mata yaya jiki bansake bin takanta ba. Dan naga daƙyar ta amsa. Ƙawayen suka fara zolayarta ta yatsibe fuska tana faɗin.

"uhmm kedai bari aini naji jiki banɗauka haka yakeba mutum ace babu haƙuri" kallonta nake da mamaki yanda take ƙoƙarin fitarda sirrinsu itada mijinta ko tanayin hakanne danta bani haushi?" toh idanma hakanne batayiwa kanta dabara ba. ga anty fadeelah ka matar ya Ahamda sannan ga maryam awajen kota manta maryam ƙanwarsa ce oho ayi mutum sam babu wayo ƙannen bayansa Sun fita gane dai-dai da rashinsa. Namiƙe ina faɗin.

"Toh Allah yaƙara sauƙi bari natafi kema Maryam Yaya habibu yana jiranki fa" ta miƙe dasauri dan itama maganganun Aysha suna shirin ƙure mata tunani.

" sai kundawo cewar Anty fadeelah na amsa mata sannan nafice. Ita Aysha a tunaninta maganganunda tafara ne ya sanyani barin wajan. Muna fita harabar gidan motar Hamma ta danno kai ya tsaya yafito suna gaisawa da Ya Ahmad muka ƙaraso wajan tun daga nesa dana ganshi gabana yake faɗuwa amma haka a daure na ƙarasa dan ahalin yanzu inaso komai da komai da ƙarfi da arziki na yakiceshi araina. Muna ƙarasowa ya Ahmad yace.

"Kinfito"

"Eh"

"toh muje koh" na gaisheda Hamma ina kallon gefe saida ya kalleni na Æ´an wasu lokuta sannan ya sam muryarsa da sanyi sosai ban yarda mun haÉ—a idanuwa dashi ba na juya wajan Yaya habibu.

"Yawwa kinga wannan yarinya wacce tayi zancensa a abuja har take cewa yayi mata abata lambar wayarsa? Wallh yau a gaban motarsa tazo sai hira yake mata ingaya mikk gara ki taka musu burki" maryam ta ɓata rai sosai ta kalli Yaya habibu. Yafara girgiza kai yakasa magana. Da dukkan alamu ta ƙulu sosai. Nacewa a ya Ahmad mutafi. Sai alokacin yayi magana.

"Kaji munafunci kaga yarinyarnan tazo zata haɗamin makirci tayi gaba abunta yanzu da kika haɗe bomb ɗin daɗi kikaji? Munafuka" Hamma harya buɗe baki zaiyi magana dan yaji ransa ya sosu sai yatuna yanzu ba daa bane kawai yayi shiru yayi musu sallama yabar wajan yanata kallona kozan kalleshi nayarda mu haɗa idanuwa naƙi ƙarshe. Ƙin kallonsa danayi yasanya yafara tunanin ko haushinsa nakeji akan abunda yafaru da zai iya dayayimin bayani cewa bada sonsa hakan tafaru ba amma menene amfanin yimin bayani? Ya nunamin bayason matarsa kenan? bayan kuma aure yanzu ya rigada ya haɗa. Da wannan tunanin yashiga ciki ganin mutane ya sanya ya shige ciki baiso yasamu mutane a cikin gidanba dan a hannu yadawo."

"Kai dai faɗi gaskiya nima na lurada kai da yarinyar nan tunda aka fara bikinanna" Ya Ahmad yafaɗa bada alamun wasa ba. Yana gama faɗama yashige mota. Yabar Yaya habibu yanata rantse-rantse. Nacewa maryam tajirani idan sun gama karta tafi saboda tanan zamu dawo. Nima nashiga motar muka tafi. Ina kallo saida yatura wani saƙo kafinnan ya ajiye wayarsa yafara tuƙi.

Kafin mu isa yanda zamuje anfara kiraye kirayen magrib kai tsaye naga sunbar Ya Ahmad yashige damu ciki tako'ina jami'an tsaro sunata shawagi ya Ahmad ya tsayardani a bakin reception na wajan yace na ƙarasa ciki zaije yayi sallah idan ya idar kuma batanan zai shigoba zai turo akaini wajanda zanga surprise ɗinda ya shiryamin. Wajan akwai tsaro sosai bansan kodan bantaɓa shiga bane nake ganin tsaron wajan na musamman ne tunda nashiga ko mutum ɗaya banganiba dan banma shiga wajan reception ɗinba daga yanda ya ajiyeni na hangi masallaci ma'aikatan wajan mata sunata shiga wajan. Nashiga nayi alwala nima na gabatarda sallar magrib dake hadari yahaɗi agarin ga iska mai daɗi yasa aka haɗa Sallah da isha'i. Bayan mun idar ina zaune naga duk ma'aikatan da suke wajan mata sunfita dasauri Da alamu anbasu time ɗinda akeson su hallara a yanda zasuje nayi tunanin hakanne ganin yanda suke sauri su dukansu. Ina zaune a cikin masallaci message na Ya Ahamd yashigo wayata wacce zata Ƙarasa dake ciki tana ƙofar masallaci tana jiranki. Nayi mamakin yanda akayi ya Ahamd yasan ina masallaci.

Na ɗaura ƙwalina nafita a wajen an taradda wasu mata guda biyu ina fita suka fara gaisheni cikin ladabi ɗaya christian ɗaya musulma dukda ƴan matane amma sun girmeni feww da aniya hakan yasa nakasa amsa gaisuwar suka fara yimin iso acan gefe da ainihin main ginin guest palace ɗin mukabi ahaɗe suke da main ginin amma shi a gefe aka haɗashi daban step muka fara hawa amma step ɗinda muka hau baifi 10 ba steps ba muka riski ƙofar wajan ta glass ce ana iya hango komai dake ciki daga wajan. Tun daga wajan suka barni suka juya na danna ƙofar ta buɗemin na shiga ciki saida nakusa tsayawa yin ƙauyanci domin an ƙayata wajan matuƙa dagaske wajene akayi decoration ɗinsa matuƙa yahaɗu kujeru ne a gefe guda biyu da table sunsha decoration da candles gabaki ɗaya wajannma haske candles ne ya haskeshi sai cups guda 2 da kwalbar wani abunda bantaɓa kallon irinsa ba can gefe da wajan kuma Unique lixury italian chairs ne wanda sukayiwa wajan yazaa kamar living room. Harda madaidaicin TB a gafen can ƙasan wajanma gabaki ɗaya carfet ne samansa kuma fayau ana iya kallon komai duk yanda zan tsaye faɗa muki kyau da tsaruwar wajan abun bazai misaltu ba."

Ya Ahmad yana tabbatarwa nabar na isa wajanda Hammood yake yajuya yatafi dan É—aukansu Anty fadeela suwce gida.

Tun safe Anty fadeelah bata kunna data ba tana kunnawa notification suka fara shigowa cikin notification ɗin harda wanda akace mata Hammood yayi following Marmeeyy gabaki ɗaya hankalinta bai kaiga marmeeyy ƙanwarta ba ita bama son ƙeallon kafa takeyi ba tun lokacin Marmeeyy batada waya tana afani da phone ɗinta wajan kalle kallen ƙwallo tayi mata following ɗinsu dayawa. Ta danna kan notification ɗin tashiga wajan tana faɗin.
Chapter 57 · 0% Book details