← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 106

Sashe 32

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Munafuka idan ke zaki mana auren saiki Hana. Kuma waLlh naji zancenann bakin wani saina takaki" wajan sai zafi yakemin ina sosawa Idona yacika da hawaye najuya nadubi maryam tataɓe baki haɗeda yatsina fuska. Ni harga Allah bnsan sunrigada sun ƙulla soyayyarsu ba na ɗauka suna shirin yine hakan yasaka nayi kasassaɓa. Amma Na ƙudirci rama abunda tayimina najuya nashige ciki.
Nashiga da Sallama nawuce ciki fuuu Mama tace.

"Yauma ansake wani rikicin kenan yara sai azabar rikici kamar masu ganin hanjin juna" anty tayi dariya tace.

"Nifa rikicin nasu ma dariya yake bani ba jimawa anyi faÉ—a ba jimawa an shirya" Ana haka Maryam tashigo itama a murtuke tayi musu sannu da aiki tawuce. Akwance nasamu anty fadeelah a cikin É—aki dake ita diploma tayi tagama aysha ce take degree yanzu take ajina biyi. Ganin yanda nashigo yasa tace.

"A'a marmeey jarabawarce duk haka? Na yi nodding kaina batareda nayi maganaba kawai na danna kiran Hamma" yana ɗauka nasaka kuka. Lokaci ɗaya ya rikice ya dibirbirce yana tambayana abunda yafaru daƙayr na tsagaidata cikeda shagwaɓa mai haɗe da taɓara na faɗa masa abunda yafaru. Tun daga can ina iya jiyo hucinsa ya katse kiran kawai. Yana datsewa yakira Maryam yayi mata tass-tass kuma yace karta yarda su haɗu ido biyu saiya wanke fuskarta da mari. Bayan ya kashe yakirani yayita lallashina har nayi shiru nasake mukaci gaba da Hira. Saida mukayi sallama sannan anty fadeelah ta dubeni tace.

"Lallai Marmeey kincika Æ´ar rainin hankali ke kina soyayya da yayanta ke kice bazatayi da naki ba? Wallhy Hamman nema dayake biye miki yabi ya sakaltaki da yawa ya fifitaki akan Æ´ar uwarsa. Saida naturo baki sannan nace.

"nima ai nawa ɗan uwan ya fifitata akaina ranƙwashinafa yayi harda cemin munafuka"

"Oh yanzu ranƙwashi kike yiwa wannan kukan taɓaran? Wani sai yace ai dorina yasaka ya zane miki jiki. Mijinki ya shiga magana da sakalci"

"Naga Hamma ne mijin? Kuma shine ya sakaltani koh? Babu damuwa ai" ta jijjiga kai haÉ—eda faÉ—in

"lallai Marmeey bakida kunya" muna cikin haka maryam tashigo ranta a ɓace sosai ta zauna gefe sannan ta dubeni kamar bazatayi magana ba sai kuma tace.

ZAYNAB ALABURA

Wannan littafin na kuɗine kibiya  ₦300 ta asusun  bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.

  "Wai haushi kikaji? Ashe babu daɗi zafi kikaji?  Kinmanta abunda  kike saka Hamma yakemin? Ai wallh tsaf zan rama  ɗaya bayan ɗaya saina rama abunda kikayimin da kin ɗauka ke  kaɗai kika iya soyayya koh? Toh nima na'iya kuma Yaya habibu yana sona bake kaɗai bane wacce akeyi miki soyayyar. yanzu zai ɓaɓɓalaki akaina. Wai har kinkira kin faɗawa Hamma har yana cewa zai maremim fuska a'ina zai ganni? Aiko yadawo bazan yarda mu haɗuba har sai su Ummi sun dawo. Itakuma bazata bari ya dakeni ba" naƙi na kulata dan haushinta nakeji sosai Anty fadeela da muke bata takaici da dariya tace.

"Wai shin maryam da Marmeey yaushe zakuyi hankali? Yarinta fa ke damunku kuna juya yayyyunku yanda ranku yakeso sukuma dake Allah yayi sokaye sunata biye muku kuna rashin hankali. Na turo baki ina ƙunƙuni nace.

"Anty fadeeala idanfa kin girmi Yaya habib baki girmi Hamma ba kidaina ce masa soko"

"Wai dama kingirmi Yaya Habib" cewar Maryam sai alokacin na tankata nace.

  "Sosai ma kuwa aiko aysha ta bashi watanni" na faɗa cikeda gatse. dasauri ta miƙe zata fita anty fadeelah tace.

"dawonan" sumu-sumu ta dawo ta zauna. Anty fadeelah tacigaba da faÉ—in.

"Ina zakije? Kuyiwa kanku faɗa kutsaya kuyi exam ɗinku cikkn lafiya kugama lafiya amma kunfi bawa soyayya muhimmanci fiyeda karatu banaji agida duka ansan abunda kuke shukawa ku faɗa musu subarku kuyi karatu idan bazaku iyaba ni saina kirasu dukansu nace su ƙyalesu kugama exam tukunna"
Dasauri nace.

"A'a ni wallh a'a Ina karatu karki kirashi bakiga yanzu ko waya bamayi da dare ba? Shi yacemin natsaya nayi karatu a nutse"

"Kefa" tafaÉ—a tana kallon maryam.

"Nima zanyi tabata amsa" toh gara ai tafaɗa sannan ta maida hankalinta kan wayarta. Ahaka Aysha tadawo daga school ta samemu muna zaune jefi-jefi muke harara juna. Idon Aysha na kanmu  ta ajiye jakarta tana faɗin.

"Ayagis yauma ansake wani rikicin kenan?"

"Keda kikasan halinsu cewar Anty fadeelah"  kafin mubar ɗakin saida muka shirya tukunna."

  Wasa gaske soyayya tanata ƙarfi tsakanin Yaya Habibu da Maryam. Da ɗai-ɗai da ɗai-ɗai saita mutanen gidan suka fara ganewa. Abun kamar wasa har barazana nayi mata nace saina faɗawa saurayinta. Tace.

"Kinga dakin hutasar dani dan inata masa kora da hali sai yanzu yafara ganewa kinga kina faɗa masa zai fita hanyata. Nasamu Yaya  habib maikuma zanyi dashi? Ko wayarsa bana ɗagawa sainaga dama amma haka zai nace saiya kirani. Ni karma wata rana yaje yakira gaban Yaya Habib yazo ya kashemin aure"
Sake baki nayi ina mamaki nace.

"Wai kekam nake ke cemin ba'a gwadawa namiji so ba? Koduk munafunci ne?" bata kulani ba dan tasan tafaÉ—a."

  Mama tana fahimta takirashi ta zaunar dashi. Dafarko tafara tambayarsa Habibu wai shin Soyayya kukeyi da maryam ne? Saida ya sunkuyarda kai sannan yace.

"Eh mama dama inataso na faɗa miki" ashe  kin sani"

"Wanann rawar kan badole kowa yasani ba Habibu? Amana  batace haka ba an bani amanarta bazan bar wannan abin yacigaba da faruwa ba yarda damu yasa iyayenta suka batta a wajanmu kubar wannan rashin hankalin dan Allah" yayi ƙasa dakai alokacin yayi dai-dai da shigowarmu daga makaranta kenan muka tsinki maganar. Dasauri mayam ta ƙarasa ciki sai ganinta kawai sukayi fim. Tazauna gaban mama sai haki take tafara faɗin.

"Mama bansam zancenda kukeyi ba amma kaman akanmu ne dan Allah mama karki rabamu wallh inasonsa nicema nafara sonsa kafin yafara sona" Daga yaya habib har mama baki buɗe suke kallonta shi kansa namiji bazai iya wannan kasassaɓar ba. Nikam bani na aikataba amma inaji mata nauyi dan haka naja ƙafata nayi ɗakinmu na daa. Babu kowa aciki nazauna gabana sai faɗuwa yakeyi sai inaji kamarn nice soyayyata ta bayyanawa duniya aka santa. Ko har indai zanji haka akan soyayyar aminiyata da Yayana. Yaya kenan aranarda aka gano nice mai soyayyar? Bazanma iya imagine ba dan haka na fiske. Banfito aɗakin ba saida naji fitowar Yaya Habibu sannan nashiga ɗakin Mama. Bansamu kowa a palour ba sumu-sumu kamar munafuka nawuce ɗakinmu dan banaso ma mama taji shigowata. Ina shiga na sameta ƙwance akan bed ta rufe har Kanta" zama nayi bakin bed ɗin na janye bargonda ta ruhu dasauri ta buɗe ido ganin nice ya sanya ta sauƙe ajiyar zuciya. Nace.

" me kikeyi anan?"

"Babe ki ƙyaleni bazan iya haɗa ido da mama ba kinsan kasarsaɓar danayi? Wallh tsorone ya kamani sai naji kamar wanda za'a rabamu shine fa nakasa controlling kaina" Tausayi tabani sosai cikin Sigar ƙwantarda hankali nace.

"Ki ƙwantarda hankalinki har indai mamanda nasani ne bazata rabaku ba sannan zata nuna miki kamar babu abunda yafaru. Mama nasonki dan haka zata asheki hanni bibbiyu"

"Allah babe?"

"Allah kuwa ke kinsan mama batada matsala ai"

"Nasani sosai amma nayi rashin kunya fa. Wallh saida nayi nace anya nice kuwa? Kamar ba bafulatana ba"

"Share kawai Babe kina dani ai babu wani abunda zai faru" tayi dariya tace.

"Nasamu gwarin guiwa."

Tunda tana raɓe-raɓe taga mama ko kaɗan bata canja ba saima wata kulawa data ƙara bata saita saki jikinta.

Ahaka muka kawo ƙarshen exam ɗinmu sauran guda ɗaya amma ita anbada interval atsakani. Yayinda auren ya Ahmad sai ƙaratowa yakeyi. Maryam ma tace itama zai taje bikin amma har lokacin bamu tambayi baba ba. Koda yaushe munada exam Hamma ke zuwa yakaimu amma bashi yake dawo damu ba. Yanzu bamucika samun lokaci tareda shi ba shidai haƙuri kawai yakeyi yana jiran agama wannan exam ɗin yasako mahaifa acikin lamarin.
Ana gobe Zamu rubuta exam ɗin ƙarshe Maryam tace na rakata gidansu ta ɗebo wasu kaya ta canja kayayyakinda tayi amfani dasu. Tunda immediately
ana gama exam zamu tafi bikin Yaa Ahmad.

Da rana muka shirya muka tafi munsamu ƙofarda zai kaimu cikin gidan a buɗe hakan ya nuna Hamma yana gida tunda dama tun kafin mu fito na kirashi na gaya masa.

   Har muka kusan gama abunda mukaje yi Hamma bai fitoba sai ga kiran wayarsa na ɗaga yacemin.

"Baby har yanzu baku iso bane?"

"Mun iso muna ɗakin Maryam"  nabashi amsa.

ZAYNAB ALABURA

Wannan littafin na kuɗine kibiya  ₦300 ta asusun  bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.

"Okay toh kizo É—akina ki sameni Ina jiranki yafaÉ—a sannan ya kashe wayar" maryam tace.

"Muje koh babe?" nace.

"Hamma nakirana bari nadawo saimu tafi"

"Ohh toh shikenwn jeki kinga shaff na manta ma ban ɗebi jewelries ɗina ba barina ɗeba you can go" saida na tsaya ganan madubi nadubi fuskata daƙyau sannan na fice nabarta tana ɗeban jewlries ɗin.
Saida na ratsa har nakai ƙofar palournda nataɓa samunsa aciki sannan nayi knocking dakansa yataso ya buɗemin ƙofar idanuwana suka sauƙa akan fuskarsa ya sakarmin murmushi nima na mayar masa sannan nayida kaina ƙasa. Ciki yayi nabishi a baya ya isa ya zauna akan kujera naje kujerarda take gefe ta zauna.

Nasake gaisheshi ya amsa sannan yace"

"Babyna kinyi kyau sosai. Nadaɗe banganki da kayanda ba uniform ba sai yau. Tunda nace ina sonki kika ƙauracewa gidannan" nayi murmushi kawai yacigaba da faɗin.

"finally gobe zaki gama exam kina gamawa Su Abba kawai zamu jira su dawo ayi magana. Amma inaso ki sanarwa mama kafin su dawo"Na zaro idanuwa nace.

"Hamma yaushe zan iya? Kabari kawai idan sun dawo ka faÉ—a musu" ya harereni yace"

"Wato ni maras kunya koh?" dasauri na girgiza kai nace.

"A'a Hamma ni bahaka nake nufi ba" Ya jijjiga kai alamun bai yarda ba nace.

"Allah kuwa Hamma" yayi murmushi sannan yace shikenan nayarda. Amma gaskiya kiyi yanda zakiyi mama tasani" na gyaÉ—a kai alamun nayarda amma bawai dan zan iya faÉ—a matan ba?. Najiyo muryarsa yana faÉ—in.

"Ina tunaninma Abba ya fahimci wani abun amma dai baice komaiba sai dai yanayinsa alokacinda muke tafiya abuja ya nunamin" nan da nan cikina ya É—urk ruwa jikina har wani É—an bari yakeyi kaÉ—an nace.
Chapter 32 · 0% Book details