← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 106

Sashe 47

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ciro zoben ki bani babu musu na cire ma mika mata. Zanyi magana da Babanku amma sai bayan iyayen su Hamma sunzo dan yanda mukayi magana da ita tacemin cikin wanan satin kafinnan banaso adago komai har bayan sunzo anyi magana. Hamma ya kwantamin arai sosai kuma naji dadi daya kasance shine wanda kik zab daga yanyinsa yanada nutsuwa sosai Allah ya sanya alkhairi a lamarin. Na sunkuita kaina kasa ina murmushin jin dadi.

"Sannan zanbawa Habibu zoben nan yaje yaji kudinsa dan tun lokacin dana gani jikina yabani ba karamin zobe bane sai dai sanin babu yanda zaki samu diamond ring yasa nayi tunanin imitation ne kawai kika saya" tana gama magana ta ta dauki wayarta ta danna numbern Yaya Habibu minti biyar ya shigo ta mika masa zoben tace yaje yaji kudinsa."

Har Bayan magrib Yaya habibu bai dawoba sai can ya dawo a gajiya kai tsaye dakin Mama yashige muna ganin Haka muka bishi.

"Mama a'ina kuka samu zobenann anya bana sata bane?" Zaro ido dukanmu mukayi araina in fadin nashiga uku. Wata zuciyar tana fadin maganina kenan da aka kawomin abu babu bincikr nakama nasaka a Hannuna"

"Kai yimin bayani mana menene yafarau?"

"Kinga mama Wallh kaff garinnan yanda nasan ana saida zinare saida naje wasu wajan kanma ce suke cewa basuda na'urar da zata iya gane mai kyau ne ko fake daga karshe wani yabani shawara akan na aika abuja anan zasu iya ganewa shime naduki pics dins na turawa frnd dina dayake can yaje wajan da kansa ya hadani da branch dinsu nanan bincike yayi bincike hr wajan Police yanzu haka sun rike zoben sai anyi bincike akansa campanyn dake abuja zasu tuarawa dubai companyn da suka kera zoben asamu bayani akansa. ko harma sun turane oho su ayanda can Abuja suke bayani wai suna tunani a kasarnan abune mawuyaci asamu wanda zai iya affording zoben bawai dan babu masu kudinda zasu saya ba sai dan babu wanda zai iya kashe mukudan kudaden nan kawai akan zobe" Yanzu sun karbi details dina da komai nanda 3days zamuji bayani dan zasu aika dashi abuja idn bayani yafito idanma ma kamawane zasuzo su tafi dani ya wurgamin Harara bayan karasa maganar.

"A hannun wannan ja'irar nake ganin zoben zakiyi bayanin yanda kika samu idanna kamaki na kalada miki duka" dagani har Mama bmuce komaiba.
24hours kawai zoben yayi a wajansu yaya Habibu yasamu kira daga wajan police da campanyn da suka karbi zoben. Hakuri sosai suke bashi. Babban police dayake kan case din yafara magana.

"An tura dashi can abuja daganan suka tuntubi campanyn da suka kerashi sun tabbatar musu da guda biyu kawai suka kera kuma maishi yayi musu biya ya bukaci kar asake kera makamancinsu couples ring ne na mata da miji wannan shine na matar. Sun tuntubi wanda yasaka aka kera masa zobinan ya tabbatarda ba sacewa akayi ba zoben yana muhallinsa ne. Mun bukaci address da komai saboda binciike company sun bamu da yardar wanda yasa aka kera masa zoben. Address dai-dai yake da naka wanda kabamu sannan sunama surname yazo daya da naka Zainab Muhammad Dani. Kaga kenan bamuda wani dalili face mubaka kaynka amma a shawarce kusan yanda zaku killace zoben. Idan ku yan siyasa ne zaija muku Babbar matsala zai bata muku carrier naku sboda babu wanda zai yarda bada kudin government kukayi amfani wajan sayan zoben ya zame muku babbar kadara ba daganan jami'an tsoro na fanni daban-daban zasu shiga zancem daga karshema government zata karbi zoben. Abuna biyu idanku ba yan siyasa bane duk dai ido yahau kan zoben ba',asan abunda zai jawo ba dan mutane dayawa sunsan dazamansa mukanmu cikinmu bamusan ko akwai masu boyeyyen nufi da zasu iya neman mallakarsa ba. Abu mafi alkhairi shine kusan yanda zaku adana shi" Godiya sosai yayi masa sannan ya amshi zoben ya tafi.

Yadawo yayiwa Mama bayanin duk yanda sukayi.

"Mama dan Allah ki fadamin abunda yake faruwa har yanzu fa bakimin bayanin komaiba" cewar Yaya Habibu. Mama tayi masa bayani jikinsa yayi sanyi haka itama Jikinta yayi sanyi sosai dole Baba yashiga mganar amma sai zuwa jibi tunda gobe Maryam ta fadawa Marmeeyy akan taji iyayensu suna cewa zasuzo. Kuma har Mama ta sanar dashi amma cemasa kawai tayi zaiyi baki iyayen Maryam zasuzo. Shikanma yadauka cewa zasuzo ne suyi musu godiyar zaman Maryam kamar yanda Mama ta fada masa dawowarta tace sunata godiya sunce ma zasuzo suyi masa godiya."

ZAINAB ALABURA

Wannan Littafin na kudine kibiya 300Naira ta asuusn bankina domin samun damar yin karatu cikin kwanciyar hankali. 0003075326 JAIZ BANK ZAINAB M BAWA

Ranar aka sake mana result yayi kyau amma banci jarabawata guda daya danayi ta karshe ba lokacin da wannan abunn yafaru tsakanina da Hamma. Hamma gabaki daya ya dauki laifin ya alakantashi da kansa hakuri kawai yake bani. Banji dadin rashin cin jarabawarba amma haka na daure na nun babu wani abun kodan shima Hamma ya kwantarda hankalinsa. Har alkawarin fitar dani kasar waje karatu yayi saboda yayi silar faduwata a jarabawa yayi alkawarin rike hannuna zuwaga samun cikagaba yayi alkawarin sanyani a hanya har sai nacika mafarkina. Nidai kawai dariya nakeyi wannan abun kadai yasa naji zafin faduwa jarabawata ya ragu araina.

______________________

Mama batayi wani aiki ba kawai order snacks tayiwa masu zuwa dakin Baba kuma tasan akwai cartons na drinks da ruwa tun auren Ya Ahmad da sukaje aka cika musu butt din mota dashi Alhaji Habibu mahaifin Mama kawai iya wand . zaiyiwa iyalnsa tsaraba ya deba dake yanada ciwon sugar bayashan carbonated drinks sauran duka Baba yadawo dasu ya bawa matan ya ajiye saurn dake shima ba gwanin shan zaki bane.

Baba yana zaune Mama tashiga wajansa da mamaki take kallonsa yaya Baka shirya ba? Ya kalleta.

"Oh wai dawuri zasuzo?" Haka nake tunani dan Umminsu ta kirani ina tunanin tafiya biyu zasuso da neman iri" saida gaban Baba yafadi dan yanajin haka yasan Zaiyi wuya idanba Marmeeyy bace. Yadaure yace.

"Tofa wace kenan cikin yaran?" Sai sunzo dai maji dannima haka aka sanar dani" hmy

"Toh Allah yakawosu barina kira Baba (Alhaji Habibu) na sanar dashi bai kyautu suzo su sanemi ni kadai ba.

" Eh hakanma yayi Allah ya taimaka ya amsa da amin"
Alokacin yakira Alhaji Habibu ya sanar dashi. Yanata Allah-Allah Alhaji Habibu ya iso kafin isowarsu saboda idan ya kasance Auren Marmeeyy akazo nema zaifi kyau ace yana kusa danshi zaifi yimusu bayani yanda zasu fahimta sosai.

Kafin Alhaji Habibu ya iso su Abban Hamma da mahaifinsu dawasu daga cikin yan uwan Abbansu sun iso. Ana gaggaisawa Alhaji Habibu ya iso shima. Batareda bata lokaci b suka sanarda abunda yakawosu. Bayan shaida musu da akayi yara sunason junansu. Baba yaji Babu dadi matuka dayasan akwai wanda Marmeeyy takeso da bazai taba aurarada itaba shiru yayi yakasa magana.
Alhaji Habibu ne yayi musu bayani hadeda basu hakuri bai fito kai tsaye ya fada musu anyi mata aure ba amma ya fada musu da sadakin wani akanta ita kanta yarinyar bata saniba yakara basu Hakuri. Mahaifin Abbansu ne yafara magana.

"Babu damuwa Allah yasa hakan shine mafi alkhairi Amma kaya kam munzo dasu bazamu koma dasu ba mu a al'adarmu ba'a fita da kayan aure adawo dasu. Dan hakw idn kanada wata yarinya koda kanwarta ce sai abashi mu mika sadaki kamar yanda mukazo da niyya anyi niyyr kulla zumunci Allah har indai akwai yanda za'ayi toh kar afasa"

"Amma baka ganin su yaran bazasu so hakanba?" Cewar Alhaji Habibu.

" Ai tunda itama wannan an karbi sadakin ta batareda saninta b suma hakan za'ayi inada tabbacin yakini da kuke dashi akanta shiyasa suka yanke hukunci bada saninta ba. Suma wadannan ku sanya wannan yakinin akansu ina fata bazasu bamu kunya ba dan sun samu tarbiya. Inbanda yanzu zamani ma da yara suka kwallafa rai a soyayya ba dacan ina akasan wata soyayya aure akeyi batareda Sanin junaba kuma muyi hakuri mu zauna"Kowa a wajan ya aminta da shawarar da mahaifinsu Abba ya bayar na hada auren Hamma da Aysha Baba shikansa yaji dadin hakan amma jin dadinsa yana yankewa kasancewar baisan yanda yaran zasu dauki zancen ba." Dake Bbbane sosai dan har Alhaji Habibu ya girma ya sanya babu gardama duka mutanen wajan suka amince aka karbi sadaki na Aysha da Hamma. Dake azumi saura 2weeks hakan yasa aka saka auren sallah da sati biyu. Duk wani abun al'ada alokacin sukazo dashi. Dama sun gama shrinsu na komai dan haka aka saka rana bayan Sallah da sati biyu. Yara kuma zasuzo suga juna."

Anrabu cikin aminci da mutunta juna basu wuce gidansu Hamma ba gidan Mahaifinsu Abba suka wuce zasu tattauna. Mahaifinsu yaja musu kunne barinma Abba akan kar wanda yasake yafadawa iyalansa dalilin fasa auren har Ummi dashi kansa Hamman dan yasan iyayenta bazasu yanke hukunci su karbi kudin aurenta batareda saninta ba babu wani kwakwaran dalili. Dan haka kada ayi musu katsalandan abarsu su sanarda ita da kansu. Kowanne a cikinsu ya aminta da hakan.

Ummi kuwa batasan yanda abun ya kaya ba kawai wucowa tayi gidanmu.

Tunda naji muryarta na kule adaki dama tunda bakin suka iso ban fitaba. tareda Maryam sukazo ina jiyota tana tambayar Mama wajena Mama tace mata ina ciki. Tashigo tasanemi zaune akan gado ta dan maki kafadana hadeda fadin.

"Amaryar Hamma yane? Yaya da zaman tunani karki damu lokacin zaizo dawuri. Nayi yake kawai dan na lura Maryam batasan Yaya akeji ba idan akace anzo maganar aurenka baza iya biyeta muyi shirmen ba dan haka na koma na kwanta. Sai tsokanata takeyi amma ban kulata ba saida taga banda niyyar yimata magana saita mike tace.
Chapter 47 · 0% Book details