Sashe 42
Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Idan bazakayi magana ba ni zan tafi" nafaɗa ina ƙoƙarin barin wajen. Dasauri yace.
"انتظر"
Kamar wanda ya tuno wani abun kuma sai yace.
"Ohhh please wait" alokacin daya ambaci kalmar na larabci na tsaya da saida gabana yafaɗi domin muryarsa batayi kamada wanda ya iya hausa ba. Tabbas wannan muryar ba tamu tanan bace kawai jikina yafara bani cewa shine wanda yake yimin text da kalmar larabci wani lokacin da turanci. Sai yanzu tunanina yake dawomin cewa wannan mutumin dayake zuwa makarantarmu ga dukkan alamu ba ɗan ƙasarnan bane. Idan kuma ɗan nan ne toh ruwa biyune dan abune mawuyaci acikinmu asamu mutum mai hasken fata kamar nasa. Nasauƙe ajiyar zuciya. Sannan a nima nace.
"Me zan tsaya namaka? Bazakayi maganaba? Bakuma zaka nunamin fuskarka ba. Inada abunda zanyi aciki" nafaɗa alokacinda nake ƙoƙarin sake barin waje. Bai hanani har saida nakusan barin wajan gabaki ɗaya zuciyata taƙi samun nutsuwa nasan idan natafi batareda wata ƙwaƙwaran bayani ba zanbar kaina cikin tunani. Iska ya furzar ya sunkuyarda kansa yanajin babu daɗi. Ko kalma ɗaya da zatazo bakinsa yayi mata magana ya nema yarasa.
Jin takun takalmina ya sanyashi ɗago kansa ya sauƙe ajiyar zuciya yana kallona na dawo na harɗe hannayena a ƙirji ina kallonsa dukda ba iya kallo fiskarsa nakeyi ba Cikin harshen turanci nace.
"Idan kanajina idan nayi magana respond idanba hakaba zanyi tafiyata"
"Okay" shine abunda yafaÉ—a.
"Sunanka" nafaÉ—a kai tsaye kamar mai bashi umarni. Ya nisa sannan Yace"
"You'll know soon" da hausa nace.
"bazaka faÉ—aba kenan?
"Mood" kawai ya yace dan yanda nayi maganar yagane cewa zan iya tafiya.
"Mood! Mood! Mood! Na nafaÉ—a inata nanatawa nakasa gane wane irin sunane wannan"
"Okay zan iya tafiya yanzu?" Kawai na tambaya. Da tambayoyi dayawa a raina amma banida lokacin yinsu dan bazanyita tsayuwa da mutuminda bansanshiba a wajanda babu kowa."
ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya
"No please stay" shine abunda yafaɗa naja numfashi  nasamu kaina dayin abunda yace na buɗe mota na zauna gabaki ɗayana a waje nake amma ina zaune a cikinta. Shirune yabiyo bayan Zaman na tsawon lokaci. Naja ɗan siririn tsakinda bazai iya jiyoni ba banga dalilin zamanba tunda babu wani abunda muke faɗa sai zallan kallona da yakeyi wanda banida tabbacin yana iya kallon nawama sosai sabida duhun dake wajan. Ina zauna inata tunanin dalilin da zaisa nabi son zuciyarsa na zauna sai asannan nagano dalilin zamana awajan shine dan banaso nayi masa gardama saboda dagani saishi a wajan kuma bansanshiba bansan kamanninsa ba. Bare idan wani abun yafaru na iya bayani. Gara nabishi ayanda yakeso tunda naga alamun idan nayi hakan zamu wanye lafiya. Amma raina yana faɗamin har indai shine yake zuwa wajan Baba na tabbata bazai yimin komai ba. Toh idan kuma bashine wanda yake zuwa wajan Baba bafa? Wata zuciyar ta jefomin tambaya Ajiyar zuciya na sauke alokacin da zuciyata ta gajida saƙawa da warwarewa amma nakasa samun nutsuwar zuci. Idan bawai nasamu amsa ba hankalina bazai kwanta ba kuma Tunda gani gashi babu wata hanya da zanbi nasan hakan face na tambayeshi nasake sauƙarda ajiyar zuciya a karona bbu adadi. Har alokacin idanuwansa suna kaina Fuskarsa tana kallon tawa muna facing junanmu alokacin wata iska tafara kaɗawa yayinda take busamin ƙamshin turarensa mai cikeda wani sihirtaccen daɗi mai sanyawa zuciya nutsuwa. Na shigarda Kaina cikin motar sannna na ƙwanta na lumshe idanuwa a hankali yanda zai iya jiyoni nace.
"Do You know My father?" na jefa masa tambaya.
"نعم"
"Ohhh sorry yes" iska na furzar sannan na É—an sake shige ciki na tayarda kaina sannan cikin harshen turanci nace.
"Sir nifa musulmace karkayi tunanin cewa ban iya larabci ba" saida yaÉ—an murmusa saboda maganar tabashi dariya baice komaiba. Asannna nasake jefo masa wata tambaya.
"هل قبلته؟"
"(Did you meet him)"
"who?"
"Baabna mana" yasan abinda Baba yake nufi akowani irin yare ana iya kiran mahaifi da Baba dan haka tsoron karna tafi nabarshi ya sanya yayi saurin faÉ—in.
"Yes" shiru kawai nayi ina mamakin daya haÉ—uda babana meya faÉ—a masa' wasa gaske duk wani zatona yanaso ya zamo gaskiya akan mutuminnan. Haka muka sake zama a wajan na tsawon lokaci bamu sake maganaba na maida idanuwana na lumshe bansan lokacin da muka É—auka ahaka ba shikuwa kallona kawai yakeyi yana samun nutsuwa acikin zuciyarsa danshi Zamanda nayi a wajan kawai ya wadatar dashi koda bance masa komaiba. Ganin alamun nagaji da zaman wajan yasa yace.
"You can go" na ɗago kaina kamar wanda dama nake zaune akan ƙaya na ɗauki jakar kuɗin Ya Ahmad na fito daga motar nafara tafiya a hnakli. Kamar yanda nake tafiya a hankali haka shima yake tafiya a hankali a bayana. Da duhu a wajan sosai dakyar nake iya ganin yanda nake takawa gashi kayan yaɗan kamani shikuma yanabin bayana ina tafiya gabaki ɗaya cikin rashin kuzari ƙafafuna sai neman harɗewa sukeyi haka suka harɗe suka kusan yadani nayi gefe zan faɗi ya canja gefenda yake izuwa gefen da nake ƙoƙarin faɗuwa na faɗi a jikinsa yazame min madogara na rufe ido ina ƙoƙarin jina a ƙasa timm saina jini a jikinsa dasauri na buɗe idanuwana nayi saurin raba jikina danasa. Na juya nacigaba da tafiya idanuwana sun rufa bana ganin yanda nake takawa. Flash light ɗin wayarsa ya kunna yana haske footsteps ɗina ahaka nacigaba da tafiya da taimakon hasken da yake haskemin. Zuciyata ke karantamin son ganin fuskarsa na tabbata da zan juya dasauri idanna shammaceshi zan iya ganin ko wanene shi a wannan hasken, Dasauri na juya dan ganin fuskarsa amma kafin na juya ya kashe hasken bayan yin wani murmushi abun yabashi dariya sosai. Yana ganin yarinya ƙarama nason wai tayi masa wayo. Ƙyaɓe fuskata nayi cikin rashin jin daɗi bansan yaya akayi harya lurada jiyowata ya kashe hasken ba dukda banyi yanda zai gane ba, na juya nacigaba da tafiya ya maida flashlight ɗin ya kunna tunda muke fara tafiya bamu haɗuda ko mutum ɗaya ba kamar yanda nazo haka. a hankali muke tafiya harya sadani da ƙofarda zata kaini cikin wajan. Naja natsaya cakk shima ya tsaya sannan ya kashe hasken na juyo kamar wanda zanyi magana sai kuma nakaza cewa komai. najuya nashige ciki bansake waiwayowa ba.
Ina shiga gabaki ɗaya wutarda take wajan takawo na sauke ajiyar zuciya na daidaita nutsuwata sannan nashige ciki. Ga mamakina ina shiga na hangi Ya Ahmad yana wasa da kuɗi kamar bashi bane yacemin kuɗin hannunsa sun kusa ƙarewa. Jikina duk bbi kuzari na isa gareshi na miƙa masa kuɗin da key ɗin motarsa ya lurada yanayinda nake ciki amma saiya share kamar bai ganiba. Ina miƙa masa nabar wajan. Wajan zamanmu nayi har yanzu maryam bata dawoba na zauna da jakkunanmu duka a wajan ina buɗewa naga ƙaramar wayata sai alokacin na tuna nayi wurgi da babbar wayar alokacinda naji alamun mutum a atsaye a kusa dani. Inaso nafita na dubata amma bazan iyaba dole saina jira maryam idan tadawo ta rakani. Ina zama baifi 30minute ba tadawo. Ko kulata banyiba saboda haushinta danakeji. Saida ta lallasheni tacemin ta dawo bata ganniba shine tasake komawa, naduba time na daɗe a waje sosai dukda naga tsayin lokacin amma banyi tunanin nakai haka daɗewa ba.
bayan mungama pics da ya Ahmad ya kiramu akan muje sainace ta rakani na duba wayata.
Haka mukaje muka gama dubanmu amma babu komai a wajan muka dawo bamu daÉ—e da dawowa b aala fara tafiya muna cikin waÉ—anda suka fara barin wajan.
Anasa wajan kuma ina shiga ciki ya koma wajanda muka tsaya ya tattara wayata data fashe dama muƙarrabensa na jiransa a can wani waje daban yabisu wajan suka nufo masauƙinsu, P.A nataso yayi masa magana Akan yanayin yanda ya haɗuda ita Shi abunma gabaki ɗaya dariya yabashi saboda yaga soyayya a wajan manya baitaɓa kallon yanda ake soyayya haka abu kamar wasu dodanni. yana tunawa kawai ya fashe da dariya shi kaɗai. Mood ya ɗaga ido ya kalleshi cikeda tuhuma dan baisan dalilin dariyarba amma jikinsa yabashi dashi yakeyi, ganin mood na kallonsa yasanya ya shanye dariyarsa amma tana cinsa a ciki.
Har suka isa masauƙinsu babu wanda ya tanka wani bayan P.A yagama ajiye masa duk wani abunda zai buƙata domin asubahi zasubar ƙasar yagama yazo zai fita bayan yayi masa sallama Mood ya kirashi yazo ya tsaya yana jiran mood yayi magana ya nuna masa waje yabashi umarni
ya zaune. p.A yazauna yana kallonsa.
MOOD Yaɗanyi nazari haɗeda kaɗa kai ga dukkan alamu akwai abunda yake damunsa ya nisa sannan ya ɗan zoɓo daga kujerarda yake yana duban P.A yace."

Girgiza kai yayi ya fasa faɗin abunda yakeda niyya P.A yana ƙunshe da dariyarsa dan yaga alama ogannasa yanason ya zauce. Komawa yayi ya daidaita zamansa ya haɗe fuska kamar wanda yake ɓoyen wani abin sannan yabashi umarni daya tafi. P.A yatashi Harya kusan zuwa bakin ƙofa yasake dawo dashi yace yazo. Yadawo yazauna kamar yanda yayi datsu sannan yadubi ogannasa yana jira yayi magana. Yasake zoɓowa daga kan kujerar kaɗan sannan yaja iska ciki haɗeda yin nodding kansa ya kalli P.A cikin tuhuna da harshen larabci yace.
"Dariyar me kayi datsu?" saida P.A yasake wa dariyaar dan ganin yanda Mood ya susuce gabaki É—aya a haÉ—uwarsa na farko da ita. Ranarda akace Ta dawo hannunsa kuma gabaki É—aya baisan wani irin hali zata shiga ba. Yanzu ashe iya tambayarda yakeso yayi masa kenan yaketa gabas da Yamma. Mood Ya haÉ—e rai sosai Baice komaiba. Ganin haka yasa P.A ya gintse dariyarsa yaci murr shima sannan yace.
"Yanayin yanda ka haÉ—uda ita da hanyar da kabi wajan haÉ—uwa da ita ne abun dariya"
"Kamar Yaya?" ya jefo masa tambaya.
"Ita mace ai ba'a mata haka Mood sir maimakon ta kamu da soyayyarka sai kuma ta kamu da tsoronka. Tayaya zakaje mata kaamr wani dodo ko maras gaskiya. Yanzu Allah kaÉ—ai yasan abunda ta ayyana a ranta game dakai" zaro ido yayi yace.
"Me kenan ba?"