← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 106

Sashe 20

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"wa lirrijjaali 'alaihinna darajat" وللرجال عليهنّ درحة"
yafaÉ—a acikin alqur'ani yabaku daraja ya É—auka muku nauyi a kafaÉ—arku ya baku iko akan iyalanku
Sannan kuma ya ɗauraku akanmu cikin suratul nisa'i Yace "Al rijalu Qawwamuna alal nisa'i" ya dauraku akan mata to take care of to look after' duk yanda aka ambaci Qawwamun ana nufin ruler shugaba Allah da kansa ya kiraku da Qawwamun yana nufin the one incharge, You're the protector kaine ginshiƙi wala Allah mahaifiyarka ƙanwarka matarka ko ƴarka. Ita mace gabaki ɗaya rayuwar a ƙarkashin wani take dafarko mahaifinta daganan saita koma hannun Mijinta sai kuma ɗanta idan ta girma. yanzu haka kana zaune amma itake juya maka yaranka yanzu wannan lokacin yawuce Baba kaiya kamata ace ka isa da yaranka ka sanyasu subi umarninka" tunda nafara magana Baba yake kallona harna ida sannan yace.

"Marmee shekarunki nawa?"

"Sha tara" nabashi amsa ya jijjiga kai yace.

"Nasani kawai ina sake jaddada shekarunne banyi tsammanin za'a samu wannan basira a shekarunki ha ni aganina komai ya rigaa ya ɓaci bazai taɓa dawowa muhallinsa ba aganina komai yadawo muhallinsa shine zai dawo da ahlina gabaki ɗaya. Sai kika nunamin dawowar al'amura muhallinsu wani gyarane amma ba itace dai-dai da samun farin cikiba yanzu tawace hanya kike ganin za'a gyara komai akan dai-dai?"

"Na nisa nace yanzu zaka fara da abunda ya tunkareka acikin gidanka shine farko Mummy nason Su anty fadeelah su koma a yau ko gobe, sun gama haɗe kayansu sun shirya yanzu umarninta suke jira da zaka jeka ka samesu kuyi magana ka fahimtar dasu sannan ma ɗaura da umarninka akai yna baka yarda su tafi ba da ka ɗauki hanyarda al'amura zasu dawo muhallinsu wanda tun abaya yakamata a ajiyesu amma yanzuma bai ɓaci ba za'a iya ajiyesu. Sannan Baba mai yasa koda sau ɗaya baka taɓa bin Mummy ba?" baka tunanin Hakan dakayi shine yasake zurfafa lamarin?" Baba ya furzarda iska sannan yafara magana.

"Wato waɗannan Yaranma so take ta sake ƙarɓesu? Tayi gangancin aikominsu dan haka banajin zan iya maidasu zanyi kamar yanda kikace zan zama mai iko acikin gidana mai faɗa aji bazan barsu su sake tafiya ba. sannan zancen binta kuma da ban yiba dalilin alwashinda taci. Bazan iya sakin Habiba ba saboda alƙawarina da mahaifinta shiyasa ban bitaba dan karna sake rikita lamarin.
Kince kina neman wata alfarma wajena inaso ki faÉ—amin wace alfarma ce nikuma zanyi miki Na murmusa sannan nace.

"Na rigada na faÉ—eta kuma kayarda zakayi banason rabuwa da Æ´an uwana akaro na biyu bansansu ba ban taso dasuba amma inaso na rayu dasu" Baba ya jinjina kai yace.

"Allah nagode maka wannan shine alfarmar da kike nema? Wannan kamar kaina zanyiwa alfarmar amma tunda hakane na ɗauka alƙawarin in sha Allah bazan barsu su tafi ba, dama kullum inaji ajikina ta dalilinki kan ahlina zai sake dawowa ya haɗu kamar yanda ya haɗu abaya ta dalilinki. Kuma yanzu alamu sun fara nuna hakan Allah yayi miki albarka. Yanzu zan fita amma kafin na fita zanbi muyi magana dasu sannan akwai wani abunda yake faruwa wanda abaya naso na faɗa miki amma yanzu ganin cewa zaki iya karɓan kowane hukuncin dana yanke akanki yasa zan yanke hukunci da saran zaki amshi kowane irin hukunci" Batareda kawo wani tunani acikin rainaba nace.

"Karkaji komai Baba kowani irin hukunci na yarda ka yanke akaina"

"Allah yayi miki albarka" na amsa da Amin yace zaki iya tafiya kiyi shirin makaranta yanzu zanje na samesu zan fita ta iya yiwuwa nakai dare irin jiya idan baku ganni ba karku damu" naso na tambayeshi abunda zai fitayi dan jiyama hankalinmu yatashi kuma shi bai saba fitanba amma ganin bai sanarda abunda ya fitarda shiba ya tabbatarmin bayason asasnine nikuma bazan takurashi ba dan haka na can miƙe nayi masa sallama nafice"

Banbi ɗakin Mama ba dayake har yanzu ban sauƙo a fushin da nakeyi da itaba. Nashiga ɗaki nayi wanka na shirya zuwa makaranta sukuma sun ijiye kayansu kamar jira sukeyi gari yagama wayewa su tafi ko kuma akwai wanda suke jira zaizo ya ɗaukesu duk cikinsu babu wanda na kula na lanƙaya jakata ina shirin fita mukaji sallamar Baba saida muka amsa muka bashi izinin shiga sannna ya shigo. Ban tsayana nace.

"Baba nikam nawuce makaranta" Yace.

"Dawo ki zauna zanyi magana da Æ´an uwanki agabanki. Nadawo na zauna acan gefensa suka gaisheshi tukunna ya nemi kujera ya zauna yana kallon jakarsu yace.

"Har kunyi shirin tafiya kenan? Zaku tafi batareda kun faÉ—aminba badan Æ´ar uwarku ta sanar daniba toh sai dai acemin bakwanan" su dukansu suka sunkuyarda kansu Baba yacigaba da faÉ—in.

"Ko bakwajin daÉ—in zama danine da zaku tafi?" su duka suka girgiza kai yace.

"Macece matsalar? Nasan bazan iya baku abubuwanda kuke buƙata kamar yanda kuke samu acanba amma zanyi iya ƙoƙarina a matsayina na mahaifi naga na tanada muku abubuwan buƙata a rayuwarku. Shekarun baya da bakwa tare dani babu yanda na iyane yanzu kuma inajin akwai abunda zan iya a matsayina na mahaifinku nace kuzauna ku rayu tare dani da ƴan uwanku kuskurenda yafaru abaya bazai sake faruwa ba bazan sake yarda ƴaƴana su fita agidannan da sunan komawa wani wajan rayuwa ba, ko Mummynku ta kiraku kuce mata ni mahaifinku nace bazaku tafiba. Koda zata tsoratar daku kar wacce a cikinku da yarda tafita bada izinina ba. Kuma daga yanzu dukanku ku tattara ku koma ɗakin mamarku da zama Acan zaku zauna Har Allah yasa na ɗagaku daga gidannan na kaiku gidan mijinku.
Idan Mummynku nason ganinku ta biyoku gidan mahaifinku ta ganku dan babu wacce zataje ko'ina acikinku" Sun rasa murna zasuyi ko akasin haka dama sam basason tafiya amma basason mahaifinsu yashiga matsala saboda su."

Baba yana gama faÉ—in Haka yace. Zaki iya tafiya nagama magana ta Anty fadeelah ce tace.

"Kayi haƙuri Baba in sha Allahu babu yanda zamu sake tunanin komawa" Baba yace.

"Babu komai Allah yayi muku albarka" muka amsada Amin. sai bayan yafita natashi nafice É—akin Mama nafara zuwa na gaisheta babu yabo babu fallasa nayi mata sallama ina shirin juyawa naji tace.

"Marmee" na jiyo na dubeta fuskata babu fara'a tace.

"Zonan ki zauna" nadawo bazauna ina jira tafaÉ—i abunda zata faÉ—a.

"Fushi kikeyi dani Marmee?" ta jefomin tambaya saida na haÉ—e rai sannan nabata amsa da faÉ—in.

"A'a" tayi murmushi tace.

"Yaro man kaza fushi kikeyi mana, inbanda yarinta wayake fushi da mahaifiyarsa?" nan da nan idanuwana suka ciko nafara magana ina mai ƙoƙarim fashewa da kuka nace.

"Mama daga zuwanki fa kika mareni bakisan abunda ya haɗamu ba kika yanke hukunci kinsan yaya naji araina kuwa? Niba zafin dukan da kikamin bane ko nagwada baki isa hukuntani ba haka bane. Itace ta cancanci hukunci alokacin magana tafaɗa akan mahaifina nikuma bazan iya juraba" ina maganar nakasa ƙarasawa saboda yanda kuka yake ƙoƙoarin ƙwacemin tajawoni tasaka kaina akan cinyarta tana rarrashi tana ɗan bubbuga bayana har nayi shiru sannan tace.

"Marmee banason fitina ne bakisan wacece mahaifiyarsu ba yanzu wwannan dalilin saiki jawo mana nida mahaifinki masifa amma kiyi haƙuri nikaina marinda nayi miki ƙwana nayi ina tunaninsa"

"Nasanta Nasan wacece ita" nabata amsa dasauri ta É—agoni tace.

"Ke marmee aina kika santa?"

"Babane ya faÉ—amim wacece ita kuma yacemin sunanta ya sakamin duk wani abinda yafaru ya faÉ—amin kuma nace masa shine yayi kuskure a zaman gabaki É—aya" mama ta zaro ido tace.

"kehh ma babannaku kika cewa yayi kuskure?" na jijjiga mata kai alamun tabbatarwa tamun danƙwalo haɗeda faɗin.

"Ungo naki" naturo baki nace.

"Toh Mama fisabillihi idan ba'a faɗa masa yayi kuskure aka faɗa masa abunda ya kamata ya gyaraba ya gyara a'ina kike tunanin za'a samu maslah? Karkuga Baba yana nuna kamar bbu wata damuwa alamunsa ya nuna deep down cikin zuciyarsa akwai abunda yake damunsa, idan bai tashi yayi yaƙi da lamarinba ba fata akeyiba sai kiji ana cewa baida lafiya gara ya fuskanci komai asamu mafita. mama tace.

"Toh naji uwar ƴan sanin dai-dai tashi kitafi makaranta na miƙe nayi mata sallama nafice." ina fita tanufi ɗakin Baba ganin baya cikin yanayin damuwa yasa hankalinta ya ƙwanta. Tashiga ta zauna ta zauna sai bayanda ta daɗe sannna tace.

"kunyi magana da marmee ce?" Baba yace munfi awa muna magama da ita. Saida taÉ—anyi shiru sannan tace.

"Danasan zata tambayeka abunda ya faru a shekarun baya dana ƙwaɓeta batasan yanda lamarin yake damunka bane shiyasa ta tayarda zancen" Baba yayi dariya sannan yace.

Zancen nayi da ita nagano kurakuraina kuna nasanu mafita in sha Allah daga yanzu babu wani abunda zai sake É—agamin hankalina komai ya wuce yanzu zamu fuskanci abinda zai tunkaremu gabane kuma yarannan zasu É—awo É—akinki da zama Extra room dake É—akinki su tare acan ki saka musu idanuwa sosai idan sukayi ba dai-dai ba kiyi musu faÉ—a kiji aranki kamar Marmee suke" Mama tace.

"toh shikenan in Sha Allahu zanyi hakan" Suna zaune wayarsa tafara ruri ya duba batareda ya É—aga ba ya dubi Mama yace.

"Zaki iya tafiya zanyi magana" miƙewa tayi tafita amma tana tunanin akwai wani abunda yake farawa ga fitarda yayi jiya zazzafe gashi yanzu zaiyi waye yanemi privacy wanda bai saba hakanba duk wani abunda zaiyi agabanta yakeyi koma menene."

Ƙarfe biyar da rabi 5:30 aka tashemu dan haka kafin muzo gida 6:00 tayi dan ahankali muke tafiya muna shan soyayyarmu nida Hamma har mu iso yana driving a hankali cikin ƙwanciyar hankali. Bayan sun sauƙeni banshiga gidaba saida naga tafiyarsu danji nake kamar nabisu hirarda mukayi bata isheni ba a kullum soyayyarsa ƙaruwa takeyi araina idan muka haɗu bamason rabuwa"

Najuya na shige gida ina shiga wani sihirtacce kamshin turare ya bugi hancinta bata taɓajin makamancinsa ba kuma batayi tunanin anan duniya akwai wani turare mai makamancin kamshin wannan ba har saida yanzu tayi arba dashi.

Zaynab Alabura
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.
Chapter 20 · 0% Book details