← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 106

Sashe 56

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaune suke a gabaki ɗayansu palourn bayan sun gaisheda Baba (Alhaji habibu) Sannan yafara magana Toh Alhamdulillhi tsawon shekara da shekaru name buri da fatan Allah ya nunamin ranarda zanga iyalan Muhammad sun haɗe a waje ɗaya hakan bai yiwuba sai yau da dalili yayi dalili. Dalilim Aysha kuma dalilin marmeeyy na taraku anan ne danna sanar daku dalilin dayasa aka canja sure zuwa man aysha bayan kuma shi yaron saurayin Marmeeyy ne wannan abun yafaru batareda mun sanarwa kowanne daga cikinku dalili ba dagani sai mahaifin yaran sai yayanu Ahmadu gashi zaune shima kafin faruwar hakan akwai wani abunda yafaru wanda hakan shine Babban dalilin dayasa aka canja auren marmeeyy yadawo man ƴar uwarta Aysha bamu muka buƙaci hakanba mahaifin yaron suka nemi wata a cikinsu tunda hasu samu wacce sukazo nema ba. Naga baby dalilin da za'a hanasu sure kawai danya nemi ƙanwarta hakan yasa nabasu auren Aysha. Saboda its fadeeala akwai yaronda take zuwa wajanta itace ayshan dama batada manemi. Watannin baya da suka wuce yanzu haka ana neman shekara da faruwar wani lamari. Akwai wani yaro ɗan ƙasar Kuwait ɗan wasan ƙwallon kafa wanda nasan bazaku kasa jin sunansa ko'a bakin yara ba sunansa Hammood rana atsaka kawai Muhammad yafita sallar asubahi yadawo yasamh ana jiransa a ƙofar gida ana nemansa a gidan gobnati. Yayi mamamkin neman tunda shi ko aikin government bai taɓa yiba bare ajega siyasa. Toh sai suka ɗaukeshi suka tafi dashi anan yasamu wani labari wanda farkon jinsa hankalima bazai ɗauka wai shi wannan yaro Hammood shine yakeson Marmeeyy yanason aurenta yataso yazo gun daga can ƙasarsa neman izini a wajanmu toh shine daya sanarda abunda yazo dashi Governor da kansa ya aiko a ɗauko Muhammad aje dashi can toh alokacin basu samu wani ƙofa a wajan muhammad ba danshi yanda ya sanar dani dafarko hankalinsa bai kama zancenba. Akwai wani abokin shi muhammad ɗin dake yanzu senator ne sai suka biyo ta ƙafarsa sai yazo man dashi yaron wajan muhammad ɗin. Tun daga wannna lokaci yaron kullum sai yazo na yana neman auren Marmeeyy har saida ya kusan yanayin ƙasarmu dayake ya kasance babban mutum da wanda akeji dashi a duniya gabaki ɗaya mutane kala-kala suka ringa biyo sahu akan abawa wannan yaro auren Marmeeyy toh mudai dafarko zuciyarmu bata yarda da lamarinba amma ana tafe hankalinmu yafara ƙwanciya da irin ƙaunarda yake yiwa Marmeeyy mudai anan yaranmu da kuma al'adarmu abune mawuyaci asamu wanda zai iya yiwa mace wannan ƙaunar da yakeyi mata baiyi duba da matsayinka da dukiyarsa kowani mataki daya taka a rayuwa ba shidai hankalinsa yana kan marmeeyy gabaki ɗaya ya zuba waɗannan abubuwa a gefe yasanya neman aurenta agaba daga ƙarshe mun amince zamu bashi auren marmeeyy bayan tsananta bincike yarone mai hankali da matuƙar nutsuwa a tarihin shahararsa da rayuwarsa ba'a taɓa kamashi da wani mummunan hali ba. Bambamcin al'ada yare dakuma ƙasa bazaisa mu hanashi aure bayan nagartarsa ba. Duk wasu sharruɗanda namiji zai cika dan cancantar auren ƴa mace toh wannan yaro ya cikashi bamuda dalilin da zaisa mu hanashi aure bayan yarda da mukayi da irin sonda yake mata mahaifinsa cikekkekn ɗan ƙasar kuwait ne soja wanda yakai matakin Field marshall yana zaune a ƙasar kuwait da iyalansa sannan a bincikenmu ya nuna baya tareda mahaifiyar yaron saboda mahaifiyarsa baturiya ce. Alokacinda yadawo sun dawo tareda mahaifins sannan na amince masa nabashi auren Marmeeyy ambashi aurenta bisa yaƙininda mahaifinta yake dashi akan yarinyar nacewa kowane irin hukunci yayanke a kanta bada izininnta ba zata amshi wannan hukunci hannu bibbiyu. A lokacin mahaifin yaron ya nemi a ɗaura auren yaronsa da Yarinyarmu toh mun yarda an ɗaura auren ita Marmeeyy da Shi yaron batareda ɓata lokaci ba a wajan inda yayanta Yayi mata waliyyi sannann kuma muka nemi cewa karsu sanarwa da duniya wannan auren wato yatsaya a iya kanku dan wannan aure ba ƙaramin lamari bane da kai tsaye za'a fitarwa duniya abunda yake faruwa suma kuma sun amince da hakan ba fata mukeba amma saboda tsoron abunda zai biyo baya mun nemi ayi register auren tareda sanya hannun kowanne daga cikinmu. Mahaifinsa da kansa yayiwa hukumar aure magana aka bugo certificate kowa ya sanya hannu sannan suka bar mana shi nan a hannunmu yayinda su yaran suka fara rayuwa tare zasu karɓi kayansu su tafi dashi can su adana a wajansu mudai hankalinmu ya ƙwanta da wannan aure kuma munada dalilin dayasa ku iyayensu mata bamu sanar daku ba. yanzu da lamarin yazo ahaka yazama mana dole mu sanar daku dan itama kanta yarinyar a ranar yau zatasan cewa akwai aure akanta. Bance kowacce a cikinku ta sanarda itaba kubarshi shi mijin nata dakansa ya sanarda ita aurensa dayake kanta. Sannan abu nagaba abunda mukeso daku shine sanyawa wannan aure albarka dan anrigada anyishi bayan bincike da kiyaye ƙa'idoji. duk abubuwanda yakamata su sani gameda abunda yafaru da wanda suke son yafaru an sanar dasu. Har sadakinda suka biya saida aka nuna musu da certificate da komai. Sannan ya ƙarashe da Idan akwai mai magana muna saurarenku" mummy ce tafara magana.

"Kai Alhamdulillhi! Alhamdulillhi! Allah mungode maka kai amma wannan ai abun farin cikine dama wani hanin ga Allah baiwace dukda kasancewar Allah yafara bata abunda ya cancanceta kafin ya ɗauke wani daga gareta. Idan ana samun miji fiyeda Hammood Marmeeyy ta cancanceshi domin marmeeyy daban take a cikin ƴaƴanda muka haifa gabaki ɗayansu ita zinariya ce da Allah ya jefo mana ita acikin zuri'a. Wannan lamarine da bamu kaɗaiba gabaki ɗaya ƙasarnan zatayi alfahari da hakan kun rigada kun yanke hukunci daya dace mu bamu da abun cewa fatanmu kawai Allah yabasu zaman lpy yasa wannan aure ya amfani al'umna gabaki ɗaya" su duka suka amsa da Amin Antyma da mama gabaki ɗayansu hakan sukace. Baba yayi murna ganin yanda su dukansu suka amshi abun hannu bibbiyu ba kamar yanda yayi tunanin bazasu amshi abun da garaje ba.

Kiraye-kiraye sallar la'asar da aka fara ya sanya Alhaji Habibu yayi musu sallama ya tafi Baba ma yacewa Ya Ahmad suje suyi sallah sukayi alwala sannan suka fice."

Ana kiran sallah natashi naje nayi sallah sannan na gyara fuskata nasaka man baki da kajal sannan na ɗauko hijabi na ɗaura akan doguwar rigarda nasaka. Na suri jaka da takalmi ina shirin fita Mama tashigo ɗakin. Fuskarta babu yabo babu fallsa sannan bata nunamin komaiba tace nadawo na zauna. Ita aurenda akace anyimin bai dameta ba sannna kuma bataji bataso ko wani rashin daɗi akan hakan ba bawai dan ko mijinda akace an auramin ya kasance ɗaya acikin miliyan ba bawai danya kasance yanada kuɗi da ɗaukaka ko wata shahara ba itadai yanzu abunda takeso shibe samun ƙwanciyar hankali da nutsuwa ma ƴarta har indai auren Hammood zai kawowa ƴarta ƙwanciyar hankali da nutsuwa toh mai zai hanata yin maraba da shi? alokacin da Marmeeyy tarasa Hammood taji zafi sosai ta ƙullaci Baba amma yanzu ta fahinta ashe ya rabata da azurfa ne alokacin daya sama mata zinari. Tabbas marmeeyy tayi babbar sa'a dukda ita Mama batasan wasu ƴan wasan ƙwallo sosai ba amma tasan shaharar wannan bawan Allah. Jikina har rawa yakeyi ina kallon Mama data nutsa tunani.

"Mama! Please mana Yaya Ahmad fa yana jirana kuma hakanma sai nabi ta wajan Baba kafin muwuce" nafaɗa cikeda shagwaɓa saida tayi murnushi dan ta kwana biyu bataji nayi shagwaɓa ba.

"Marmeeyy kinsan Albishir É—inda yayanki zaiyi miki ne naga kinata É—auki da zumuÉ—i"

"A'a bansaniba kawai jikina ke bani wani Babban lamarine ke kinsani ne? FaÉ—amin idan kinsani? No barshi ma karki faÉ—a tunda aka kai wannan stage É—in gara nagani da idona" Murmushi Mama tayi.

"Duk ke kaɗai dai kince nafaɗa kince nabarshi toh nabarshi, naga kaman kin sake jikinkk ƙwana biyunnan kin cire komai aranki ne?" ta jefomin tambaya.

"Eh nacire" nabata amsa kai tsaye.

"ko meyasa?" tasake jefamin tambaya.

"Saboda shiÉ—in mijin aysha ne kuma dama nafaÉ—a miki inaji tun baya da zarar anyi auren zan cire komai araina" jijjiga kai tayi na gamsuwa da maganata"

"a kullun cikin miki addu'ar alkhairi nake duk abunda kikaga baki sameshi ba Allah ya amshi addu'ar mahaifiyarki ne ya kaudashi daga hanyarki" duk kuma abunda kikaga ya faru toh inaso ki tunkari wannan lamari gadan-gadan dan addu'ar mahaufiyarki ta karɓu kenan Allah ya baki alkhairi sannan ki buɗe zuciyarki" tafaɗa haɗeda ɗaura hannunsa akan zuciyata. Nabi hannun da kallo sannan nadawo da idona akan fuskarta. A kullum ina miki addu'a Allah yabaki miji nagari wanda zai soki ya ƙaunaceki fiyeda yanda uwa takeson ɗanta wani lokacin nakance har indai hakan bamai yiwuwa bane toh Allah yabaki koda kwatanƙwacin irin sonda uwa takeyiwa ɗanta ne. Ta'iya yiwuwa Allah ya amshi addu'ata tun kafin ki haɗuda Hamma shiyasa da Hamma yazo rayuwarki ya cireshi yabar miki irin mijinda mahaifiyarki take miki addu'a inason kafin ki yankewa wani abu hukunci ki tsaya kiyi nazari kinada hangen nesa da tunani mai kyau na tabbata tunaninki zai baki abu mai kyau Tashi kije yayanki yna jiranki" nayi wani tunani akan maganganunda Mama take faɗa amma nakasa gane komai daga ƙarshe kawai nayi mata sallama har nakai bakin ƙofa nadawo.

"Mama ƙwnaaki kin faɗi wata magana wai Baba yafison Mummy akanki, kina zaune da Baba kin kasa fahimtarsa inaga a duniya idan aka cire mahaifiyarda ta haifeshi baida wani abunda yakeso sama dake komu ƴaƴansa baya sonmu kamarki ke kina zaune dashi kin kasa fahimtar hakan aamma mu ƴaƴanki mun fahimta" baki tasake sannan tayimin danƙwalo.

"Ƙaniyatki kenan Marmeeyy maras kunya" ina dariya nafice nabarta a wajan tana auna maganganuna.

A É—aki nasamu Baba da Ya Ahmad bayan nashiga na zauna nace.

"Baba gani"
"Okay marmeeyy dama bawani abun bane zan baki hakuri gameda abunda yafaru sai yau naji ƙwarin guiwar tunkararki" na sunkuyarda kaina sai nkejin wani iri babu daɗi hawaye suka fara sauƙa akan kumatuna. Idon Baba yaga hawayen yacigaba da bani haƙuri." na girgiza kaina.
Chapter 56 · 0% Book details