← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 106

Sashe 33

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hamma yayi wani reaction akai koh? Kaine randa zasu tafi kanata kallona kuma kasanfa da mutane a wajan na faɗa muryata tana rawa" saida yayi ƴar dariya sannan ya Matsao ƙarshen kujerarsa yayi kusanci da tawa kujerar. sosai turarenda nasaka yake fisgarsa yana sauƙar masa da kasala. A sanyaye ya miƙa tausasan hannunsa ya kamo nawa hannun yace.

"Calm down baby bawani abun bane fa alamu ma ya nuna yayi farin ciki da hakan sosai dukda bai fito ya nunamin cewa yagane wani abunba" na sauƙe ajiyar zUciya haɗeda zame hannuna daga cikin nasa ka kunshesu a jikina bance komaiba" Mun ɗauki samada 1hour muna hira a palourn nayi tunanin Maryam zata nemeni amma batayi hakanba.

"Baby kicemin kina sona yau da ya kasance babu kowa a wajan dagani saike kunnena kaÉ—ai zai saurara" na sunkuyarda kaina ina wasa da zobben hannuna wanda shima zoben yake kallo nakasa magana saima shine yasake faÉ—in.

"Please Baby ko bakyasona ne" nayi saurin girgiza kai yace.

"Okay tell me inajinki ya lumshe idanuwansa yace na rufe idanuwa kinga bana kallonki harna fara ƙoƙarin faɗa sai kuma na miƙe nace.

"Maryam na jirana barina tafi ya buɗe idanuwansa a lokacin" bafara tafiya ina faɗin basai ka kaimu ba kayi zamanka kawai zamuyi waya" har nakai kusan ƙofa ya miƙe taku ɗaya biyu uku yazo yanda nake saiji nayi ya kamo hannuna ta baya yace.

"Baby wani irin turare kika saka?"

"Humarne da kulaccam nabashi amsa" ya sauƙe ajiyar zuciya ya ƙarasa takowa dai-dai yada nake batareda yasake hannun ba nikuma damuwata ya sakemin hannunta dan ƙirjina sai bugawa yakeyi.

"Baby waya faɗa miki humra da kulaccam turaren ƴan mata ne? Na mamane kika saka koh?" na gyaɗa masa kai a tsorace dan ganin yanayinsa ya canja. Nasake ƙoƙarin ƙwace hannuna ya kamashi gam-gam ganin yana shirin haɗa jikina da nasa yasa nafarayin baya ahaka har saida muka isa ƙofar dake a tufe take gm naji na bugeta ya iso yamun rumfa ya haɗe jikina danasa sannan yafara faɗin.

"Meyasa kika saka turare? Daga yau karki sake sakawa idan zaki fita dan Allah baby na roƙeki yafaɗa cikin mawuyacin hali dasauri na jijjiga masa kai a tsorace nace.

"Hamma menene kakeyi hakan? Kabarni natafi Maryam na jirana"

"Okay you can go but after kincemin kina sona" Ganin yanayinda yake ciki yasa na yanke shawarar fa Faɗan dan kawai yabarni natafi. Na buɗe bakina da niyyar faɗa han ankara ba naji ya haɗe bakinmu waje ɗaya yafara tsotsansu a matuƙar tsorace na fara ƙoƙarin tureshi dan son ƙwatar kaina amma nakasa ya ɗauki lokaci narasa ta wace hanya zanbi na ƙwaci kaina saida shida kansa kamar wanda aka zabureshi ya sakeni haɗeda yin baya. Yana sakeni na zube a wajan nasaka kuka sosai. Lips ɗina wani irin raɗaɗi da zafi sukeyi amma zafinda zuciyata takemin yasa banajin zafin lips ɗin. Shikuma yayi baya ya zauna ya dafe kansa baisan dalilin dayasa ya aikata hakan ba. Saida kukan nawa ya tsagaida na tashi dasauri namiƙe nafice a ɗakin. Ko takan maryam banbi ba Allah dai kawai yasa tafito harabar gidan tana waya taga fitowata dasauri hankali tashe ta kashe wayar ta yi kaina ban kulata ba saida nafice daga gidan. Taja trolley tabiyo bayana tana tambayata abunda yafaru ban kulataba nacigaba da tafiya a titin napep na zuwa ta tsara suka yiyo wajena babu yanda batayiba na shiga naƙi har saida ya sauƙo taturani ciki. Juyin duniya tayi dani nafaɗa mata abinda yafaru naƙi Tayitamin tambayoyi amma naƙi bata amsa ita taɗauka faɗa mukayi ma. Ganin mun kusa isowa yasa tace.

"Babe koma menene yafaru ki share hawayenki dan munkusa isowa gida idan baso kike ki tadawa su Mama hankaliba, koma menene yafaru a tsakaninku zakuyi sorting komai tunda bakyaso ki faɗamin nasan bazaki faɗawa kowa ba so ki share hawayenki dan idan anganki haka za'a tuhumeki idan bawai so kike kiyiwa aurenku tun kafin lokacinsa giɓi ba" na share hawayen fuskata amma har lokacin bance komaiba, mai keke napep yakaimu har ƙofar gida ya ajiyemu. Aharabar gidan muka ga motar Yaa Ahmad da alamun yazo kenan. Muka shige ciki su Mama suna zaune cikin gida banyi sallama ba saboda nasan dole muryata ta canja maryam ce tayi sallama suka amsa muka shige ina zuwa na nufi ɗaki. Mama najiyo tana faɗin.

" Marmeeyy zo nan" gabana yahau faÉ—uwa zuciyata na bugun uku-uku."

ZAYNAB ALABURA

Wannan littafin na kuɗine kibiya  ₦300 ta asusun  bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.

Dan tun jishowata gidan nake tsarge gani nakeyi kamar kowa ya fahimci abunda yafaru tsakanina da Hamma. Kiranda Mama tayimin ya tsurardani sosai ina tunanin tagama ganewa shikenan nashiga uku nafaÉ—a acikin zuciyata. Nayi kamar banjiba ba nacigaba da tafiya. Tace.

"Marmeeyy zonan nace. Kamar zan saki fitsari a jikina. Najuyo naƙarasa wajan batareda nayi magana ba naja natsaya jikina sai rawa yake a hankali. Mama tace

"ÆŠauki wannan kikai É—aki ta faÉ—a haÉ—eda nunamin wasu turamen zannuwa guda huÉ—u dasuke gefenta na isa waja har alokacin gabana faÉ—uwa yakeyi na É—ebesu"

"Wannan turare mai ƙarfinfa marmeeyy?" a'ina kima samoshi?" Mama ta tambaya. Rass rass rass naji narasa abunda zance dannasan turarem Hamma ne daya mannu ajikina yakama jikin. Maryam tayi saurin faɗin.

"A ɗakina ta fesa saida nace mata yayi ƙarfi shiyasa nima na ajiye shi bana amfani dashi" mama tace.

"Yayi ƙarfi kam amma kuma yanada daɗi na maza ne" Nayi saurin na ɗebi kayan nabar wajan. Maryam kuwa ta faɗi hakanne dan ta fahimci turaren Hamma ne tun a napep taji ƙamshinsa amma ganin halinda nake ciki yasa hankalinta bai kawo mata wani abunba sai yanzu dataji Mama tayi tambaya sannan ta fahimci wani abin yasa tayi saurin shiga ta kareta.

A É—akin Mamana zuba kayan nakoma É—akinmu na zauna nayi tagumi abun duniya yataru yayimin yawa kawai sai naji hawaye sunabin kumatuna.
Meyasa Hamma zaiyimin haka?" Mai yasa zaiso shiga gonarda bata riga tazama mallakinsa ba? Meyasa zai lulluɓe soyayyarda nakeyi masa da haushinsa? Tabbas yau Hamma ya bani haushi kuma ya ɓata mun rai dan ban taɓa tsammanin haka daga gareshi ba. Toko dama Hamma basona yakeyi bane?" idan yana sonta bazai taɓa aikata mun wannan abunba. Nafaɗa tunani mai zurfi zuciyata ganata kawomin abubuwa kala-kala kawai saina fashe da kuka. Ana haka maryam tashigo ganin ina kuka ta nemi waje ta zauna cikeda tausayina jikinta yamutu takasa rarrashina. Nayi kuka yakai na tsawon 30minute Har yadawo shassheƙa. Sai asannan maryam ta tattaro ƙwarin guiwarta tace.

"Babe please. Dan Allah kiyi haƙuri haba mana. Tundaga kallon yanayinda kika shiga nasan Hamma ya ɓata miki sosai amma yaya zakiyi? Zaki kashe kanki akan namijine? Bayan shi yanacan zaune may be ma harya manta da abunda yafaru. Koma me yafaru nasan Hamma nasonki sosai tnda mece first-love nasa kamar yanda yake a wajanki everything wil be alright okay' just take it easy. Hamma nasonki sosai koma meya faru may be saiya fiki dana sani banajin zai yarda ya saɓa miki dason ransa"

"Na É—ago idanuwana wanda harsun canja kala sunkuma dawowa fararensu nace dagaske kike yana sona?" amma yanzu kika gama cewa may be ma yanacan yama manta da abunda yafaru"

"Uhum yana sonki sosai wancan na faÉ—ane kawai"

"Bakya kallon wani abun bayan soyayya a idonsa" ta jijjiga kai tace.

"absolutely nothing babe" nasauke ajiyar zuciya. Nazuba tagumi ta zauna kawai tana kallona" sai bayan nasamu sauƙin abunda nakeji sannan nashige toilet nayi wanka nafito. Duk yanda naso mu haɗuda Yaya Ahmad bansamu wannan damar ba dan ko palour bansake leƙawa ba har dare yayi. Maimakon nayi karatu dai kuma na lula tunani. Gashi ko message Hamma baiyi minba abunda ya sake ɓatamin rai kenan bare ajega kira ya kirabi yabani haƙuri. Na buɗe littafin amma bana gane komai aciki daga baya kanma zazzaɓine ya rufeni. Haka na ƙwana a daren zazzaɓin bai sakeni ba sai asubahi bayan ya sakeni kuma sai bacci haka na daure nayi sallar asubahi gashi da sassafe mukeda exam bansamu na goma bacci ba haka na tsaya na dudduba littafi ga rashin bacci ga rashin ƙarfin jiki dakuma raunananniyar zuciya"

6 da wasu abubuwan nayi wanka kafin nagama shiri 7 yayi nafito nayi É—akin Mama maryam itama ta shirya na gaisheda Mama. Ta kalleni jin muryata sai taga fuskata ta kumbura.

"Marmeeyy badai karatun kika kwana kinayi ba idonki yayi haka?" nayi yaƙe kawai tace.

"Aikuwa dai da kinyi baccinki kinga yanda fuskarki ta kumbura? Ana kallonki ansan baki samu bacci ba ana ƙare exam ɗinnan kidawo ki ƙwanfa" toh nace sannan canja zancen da faɗin.

"Babe muje Maryam tataso cikeda tausayinta dan ita tasan abunda yafaru muka yiwa Mama sallama muka fita" kamar yanda nayi tsammani babu motar Hamma a ƙofar gida. Maryam ma tasha mamaki muka wuce muka tafi abunmu"

Kusan nice ƙarshen fita a hall ɗin exam ɗinnan dan abubuwanda nasani basuda yawa bana tunanin sun isheni naci jarabawarnan gashi wani irin bacci nakeji ina zaune har saida lokacin fita yacika likacin 11:00am ina fita nawuce yanda nasan zan samu Maryam. Tana kallona tamiƙe kawai ta isoni muka kama hanyar fita.

"Babe ya exam É—in dai ta tambaya dan tasan anfafata saboda yanda taganni wujiga-wujiga"

"Hmm kibari kawai sai dai mu nemi taimakon Allah"

"Jiya baki samu bacci ba babe ga dukkann alamu karatunma bakiyishi ba. Babe you have to be strong fa Hmmm tun ba'aje ko'ina ba kina irin haka? Idan iyayenmu suka faɗa miki baƙin cikin maza da suke shanyewa su zauna kamar komai bai faruba zakisha mamaki. Bayin Allahan nan sun shanye abubuwa dayawa sai dai Allah yasaka musu da alkhairi"

Inajinta kawai amma ban tankata ba har muka shiga fita gate muka tsari napep takaimu har gida. Ɗakinmu nawuce ina shiga na canja kayana na ƙwanta sai alokacin nasamu bacci har azahar ban tashiba ina tashi nayi wanka saboda yanyin zafi da ake agarin na shirya nafita palour anan nasamesu duka da zannuwan dana ɗebo jiya nashigo dashi. A gefn Mama. Ina fita palour Mama tace.
Chapter 33 · 0% Book details