← Book details Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 106

Sashe 103

Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Masoyi" na kira sunansa cikin siga mai kamada lallama ko lallashi ko son wani abu daga gareshi, idanuwansa yana lumshe ya amsa da"Uhmm". "Masoyi please don't get angry inaso muyi magana" yayi ƙaramin murmushi"Rouhi dama ina fushi ne?" "No amma kana canjawa a lokacin da mukayi maganar" "Okay toh i won't me kikeson faɗamin" Saida nayi shiru ina tunanin ta yanda zanyi maganar ya fahimci nufina sosai, "Masoyi dan Allah ina neman alfarma nasan karayu tsawon shekaru cikeda kaɗaici duk kuwa da soyayyar da kake samun wajan mahaifinka amma kaso soyayyar Uwa ka rayu da ita nasan bazaka ƙi abie su Rayu da Mum ba despite abubuwan da suka faru, a zahiri yanda gangar jikinka da mu'amalarka suke nunawa ba hakan bane wannan yasa abie ko yanada niyyar sake zama da Mum zaiga bai samu fuska a wajanka ba kuma itama ko tanason komowa zataga bazata samu fuska a wajanku ba, duk wannan yafaru dalilin abubuwan da suke kallo a zahiri zai hanasu ɗaukan wani matakin dawo da rayuwarsu tare, amma ni nasan ba haka yakeba a wajanka kanason Mum tadawo rayuwa tareda abie saboda zamanta da take ita ɗaya nasan baya maka daɗi" idanuwansa yana rufe kuma baza'a iya predicting yanayinda yake ciki ba yayi magana Cikin muryarsa mai daɗin sauraro.
"Yaya akayi kikasan ba hakan bane bayan ga abunda na nuna a zahiri cewa bana buƙatar kusancinsu rayuwa ahaka tafimun daɗi" na juya ina kallon kyakkyawar fuskarsa idanuwansa a lumshe saida na sumbaci lips ɗinsa na ɗaura Hannuna saitin zuciyarsa da take bugawa da sauri sannan nayi magana. "Wannana a zahiri kenan ni kuma ba zahiri nake kallo ba ba ina kallon abunda yake ƙunshe a cikin zuciyarka ne, sai alokacin ya buɗe idanuwansa akaina dake nima shi nake kallo idanuwansa suna cikin nawa nacigaba da magana, "Bazakayi mamaki ba ace zuciyar da nakeda muhalli mafi girma a cikinta bansan abunda yake gudana a cikinta ba? Kana tunanin akwai abunda zai gifta a cikinta batareda nasani ba bare abunda yake zaune a ciki yana damunta tsawon shekaru idan hakan ta kasance yazama yana kulada abunda yake mallakina yanda ya dace, kumani bana cikin wannan sahun duk wani abu daya zama mallakina inayi masa rikon da bana tunanin duk ƙarfin mutum zai iya yimasa kwatankwacin wanda nayi saboda nima da zuciyar nake riƙe shi" na canja maganar ta sigar zolaya ina faɗin. "Shiyasa tun wuri kada kabawa wata mace ƙofa tayi ƙoƙarin shiga zuciyarka saboda tana Hannuna kuma nasan duk wani abunda yake faruwa a cikinta" yayi murmushi sannan ya furzar da iska mai cikeda damuwa sannan yace "Yanzu yaya za'ayi inaga kaman lokaci ya ƙure aikoh? Tswon shekru ashirin da basa tare wane zama kuma zasu yi yanzu? Its too late Rouhi kawai kibarsu sucigaba da Rayuwarsa zan jure tunda na jure shekarun baya ma when i was a little boy a lokacin nema nake buƙatarsu atare kusa dani". "No is not masoyi ko kwana ɗayane ya rage musu a duniya let them live together na wannna ƙwana ɗayan kaji idanma bazakayi tunanin kanka ba think of nawrah bance ba amma tanajin daɗin rayuwa ahaka? Tana samun kulawa yanda yadace? Sam fa ita batama fita tunda mukazo sua 1 muka taɓa haɗuwa da ita" "Okay toh yanzu yaya za'ayi?" "Kaje kasmu abie kace masa kanaso yadawo da auren Mum kansa zai dawo dashi" "Toh kawai ya amsa with cconfident""Amma ke zaki rakani" na zaro ido "Nikuma masoyi" "Ehem naga kinfini son Mum tadawo ai" na girgiza kai "Mahaifinka nefa" "kema mahaifinki ne ai" "Bahaka nake nufi ba masoyi" "Toh kawai afasa" na girgiza kai "No zan rakaka amma zan tsaya sai kayi magana ya jijjiga kai, "Okay hakan yayi" muka zauna a wajan na awanni sannan muka tashi muka fara tafiya zuwa ciki ina saƙale da hannunsa cikin nawa na ƙwantar da kaina a kafaɗarsa, "Rouhi Kin gaji na ɗaukeki?" "Masoyi nifa ba ƙaramar yarinya bace" ya zare hannunsa cikin nawa ya tsugunna a gabana yanamun alamun nahau bayansa" "Zan iya tafiya da ƙafata" nafaɗa ina ƙoƙarin wuceshi ya kamo ƙafata "Banason gardama Rouhi nasan kingaji zoki hau" "juyowa nayi nahau bayan a miƙe na ƙwantar da kaina a faffaɗan gadob bayabsa na lumshe ido ahaka muka isa har zuwa masauƙinmu. Bayan sallar isha'i muka fita cin abinci dukanmu tunda mukazo a wajanmu mukecin abinci amma Yau abie yace yanaso muyi diner gabaki ɗayanmu tare na shirya cikin doguwar rigar atampha nayi kyau sosai. tunda mukayi aure nadaina saka atampha sai yau kawai naji sha'awar hakan. Hammood kallona kawai yakeyi saboda nayi masa kyau sosai wajan da aka shirya zamuyi dinner nan muka nufa ina tafiya. Munsamu ƙannen Hammood da Nawrah da matan Babansu duka sun iso abie kaɗai bai iso ba, waje daban muka nema nida Hammood muka zauna, dayaga Abie har lokacin bai isoba yatashi ya tafi neman abie inajin Ɗaya daga cikin matan abie cikin harshen larabci tana magana da ɗiyarta wacce take 16yrs "Kalar zaren baiyi kama da zanin ba" tafaɗa suka fashe da dariya har suna rufe baki, Ban kulaba amma tabbas jikina yabani dani suke na sake haɗe rai, sukaci gb da maganarsu da larabci ina tunanin basuyi zaton inajin abunda suke faɗa ba saboda koda zuwana da turanci suka tarɓeni nima saina bisu ahakan, saida Nawrah tabari sun gama Gulmarsu itada ƴarta sannan tayi magana da turanci, "She speaks 94% fluent arabic Arabic better watch what you are saying kafin abie da mijinta suzo su ɗauki mataki akanku" tayi magana hankalinta nakan waya, sub tsorata da maganar ta amma sai matar ta dake Dariya sosai tayi "Tanajin larabci dakyau kuma tana mayarwa toh tayaya? Oh sorry ashe she's a muslim ba laifi" Nawrah tasan magana takeson yaɓa mata saboda mahaifiyarta ba musulma bace kuma ba yanzune farkon hakanba koda yaushe ita wannan tana yawan yaɓa mata magana shiyasa ma bata shiga harkarsu sam ko yanda suke bata zuwa idanba Abie ya buƙaci hakanba, Cikin ɓacin rai tace. "Oh speaking fluent arabic yazama requirenent da za'ayi considering mutum Muslim kenan?" Shiru sukayi saboda su san zata yaɓa magana zuwa gaba, adai-dai lokacin abie da Hammood suja shigo Hammoid ya nufoni ko kaɗan ban bashi fuskar da zai gane wani abu yafaru ba toh Mahaifiyarshi ma tayimin bandamu ba bare matar mahaifinsa.

Zama mukayi akan dining ma'aikata sukazo suka fara serving mutanen wajan banjira sunzo kanmu ba natashi nafara serving Hammood nayi nasa da nawa nazauna, nakasa cin abinci saboda kasantuwar Abie awajan dakyar na iya kai spoon ɗaya bakina Ganin hakan yasa Hammood ya tsaya da kaiwa abincin bakinsa ya ɗebo ya miƙa zuwa bakina, a hankali na girgiza kaina, Nawarh wacce take kallonmu sai muryarta mukaji,"Ai bazata iyaci ba yanzu Ummi da salima suka yi magana maras daɗi akanta da Mum kuma tanaji a idanuwanta sunaji kamar bata dace da aurenka ba Mum kuma akan addininta Ummi take habaici" dasauri na ɗago ido ina kallonta bantaɓa tunanin Nawrah zata sake tada maganar ta faɗawa Hammood ba itama ni take kallo tanaci gaba da maganarta ko ajikinta."

PAID BOOK

Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."

ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun banking Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.

Ba Hammood kaɗai ba Har abie ransu yayu mummunan ɓaci yadubi Ummii cikin ɓacin rai yafara maganganu dake tana tsoronsa kamar mutuwa yasa tafara bashi haƙuri. Hammood kuwa iska kawai yake furzarwa yanajin ransa yana masa zafi ba abunda sukayimin kaɗaiba harda Mum data sako ciki ya ɓata masa rai. abie yace mani zasu bawa haƙuri bawa shiba haka suka juyo suna bani haƙuri kai kawai na gyaɗa musu alamun nayi. Shima Abie haƙurin yake bani kunya ta sakani sunkuyarda kaina, dinner ɗinda ba'ayiya ta daɗin rai ba kenan da ɗai-ɗai da ɗai-ɗai suka fara watsewa yazama saura nida Nawrah da Hammood sai abie kawai.
Chapter 103 · 0% Book details