Sashe 9
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Abba don Allah zan bi ka" Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Tohm shikenan bari naje na dawo zan taho miki da tsaraba" d'aga idanun ta tayi ta kalli Abban tana murmurshi tace "Abba ni kad'ae ni da Raj zaka siyowa banda Yah Sadeeq koh?" shima murmurshin yayi sannan yace "Ehh.." seta saki Abban tana shirin shiga d'aki tace "Abba ada lafiya" kallan Umma yayi bayan ya amsa addu'ar Ayrahn yace "Ina tunanin zan d'akko Raj in had'a su da Sadeeq su cigaba da karatun su anan ko ya kika gani?" jinjina kae Umma tayi cikin na'am da zancen Abban sannan tace tana murmurshi "Hakan yayi Abban su, Allah ya k'ara taemaka maka, in dae hakan yayi maka nima ya min" "Toh gaskiya hakan ya min, ina tunanin zamu dawo ne tare da Raj yau d'in nan" "Toh Allah ya tsare" Umma ta fad'a.... K'arfe 2 Abba ya sauka a unguwar su Raj bayan ya sake trying number Abbu a kashe, ya sauka daga adaedaetar data kawo shi dan be kae ga d'akko motar sa ba, da k'afar sa ya k'arasa cikin layin cikin nutsuwa, tun daga nesa yake hango gidan kamar da kwad'o a jiki, amma be gasgata hakan ba seda ya k'arasa bakin gidan ya tsaya, kwad'on ne kuwa a jiki, mamaki ya sake kamashi kawae ya tsaya cikin rashin sanin abinyi, ya kae wajen minti 5 tsaye a wajen lokacin ya sake gwada kiran number Abbu har kusan sau 5, sega wani mak'ocin su Abbun yazo wucewa, ya kalli Abba dake kallan wayar sa yace "Salamu Alaekum" ya fad'a yana mik'awa Abba hannu, d'agowa Abba yayi yana kallan mutumin seya mik'a masa hannu suka yi musabaha sannan mutumin yace "Malam Kabeeru kake nema ne?" murmurshi Abba yayi yana jin In Sha Allah mutumin yasan inda yake sannan yace "Wallahi kuwa, tun jiya nake gwada kiran layin sa amma ban same shi ba, gashi kuma nazo gidan a kulle" "Ikon Allah" mutumin ya fad'a yana jinjina kae, jin abinda ya fad'a ne ya sanya Abba sake kallan sa sanda yake fad'in "Aekuwa da alama kunyi sa6ani dan kuwa jiya jiyan nan kafin azahar nazo na same shi suna had'a kaya shi da matar tasa a cikin wata mota, har nake tambayar sa dalilin tafiyar tasa haka babu sanarwa shine yake shaeda min tafiyar gaggawa ce ta kama shi da iyalan nasa shiyasa basu sanarwa da kowa ba amma muyi hak'uri zasu bar garin ne gaba d'aya" da sauri Abba ya sake kallan mutumin yana mamakin jin abinda ke fitowa daga bakin mutumin, cikin watsi da kuma kokawa da abinda ya fara zuwar masa k'wak'walwa da zuciya yace "Anya kuwa? Magana nake fa akan Kabeeru.." "Shi dae Malam Kabeeru baban Suraj, ni kae na nayi mamakin tafiyar tasu kamar wad'anda ake kora, babu wanda suka yi sallama da su se wad'anda suka gansu sanda suke k'ok'arin barin layin nan, kuma har yanzu maganar da nake maka bamu san takamaemae dalilin barin su garin nan ba" "Innalillahi wa inna ilaehi rajiun" shine kawae abinda Abba ke maemaetawa a cikin zuciyar sa, yayin da mutumin ya kalle shi cikin mamakin ganin yadda Abban yayi shiru bece komae ba amma gaba d'aya yanayin sa ya nuna yana cikin tashin hankali, d'an baya kad'an Abban yayi zuciyar sa na wani irin bugawa da k'arfin gaske "Subhanallahi" mutumin ya fad'a yana rik'o Abban, da sauri Abba ya nemi waje ya zauna dan yadda yaji kansa na wani irin juya masa ga wani jiri da lokaci d'aya ya nemi ya kayar dashi "Lafiya dae koh?" mutumin ya fad'a yana nazarin yanayin Abban, cikin k'arfin hali Abba ya furta "Lafiya k'alau, Nagode" "Babu damuwa" mutumin ya fad'a yana yin gaba. Seda Abba ya k'ara wajen minti 20 a wajen sannan ya mik'e zuciyar sa a cunkushe, yama rasa meya kamata yayi tunani, anya kuwa da gaske Kabeerun guduwa yayi masa da kud'i da takaddun sa masu muhimmaci? Anya kuwa ya kamata ya yadda da wannan maganar? Yana so ta k'aryata hakan se dae kuma duk wasu alamu dake nuna Abbun guduwa yayi sun bayyana "Innalillahi wa inna ilaehi rajiun" ya sake maemaetawa sanda ya ida fitowa titi, sam bashi da k'arfin gwuiwar yin tuk'i dan haka bebi takan fire service da yake ajje motar sa ba ya tari mota wadda zata kae shi tasha ya hau motar Kano.. Ko a cikin motar ma gaba d'aya zuciya da k'wak'walwar sa sun kasa sukuni, so yake ya gane cewa mafarki ya yi ba gaskiya bane ace Kabeeru wae ya gudar masa da dukiyar daya dad'e yana tarawa wata da watanni, takaddun karatun sa daya dad'e yana yi shekara da shekaru, anya kuwa ba'a chanja Kabeerun ba, Kabeeru mutum me kirki mutunci da kawaeci, rik'on amanar da shine ya zamo abinda ya birge Abban har ya koma yana masa kallan d'an uwa, kamar d'an uwan da suka fito ciki d'aya, yana ganin kamar ya samu wanda ze iya kular masa da dukiya koda baya wajen, wanda ze rik'e masa amana ko da a bayan idanun sa ne, se dae kashh ashe be sani ba duk wannan a banza ne, ashe Abbun ya yaudare shi ne da halayen bogi, yayi amfani da yaddar daya bashi ya yanke shi son ransa, ashe tun farko akwae k'udurin da yake son cikawa shiyasa ya kwantar da kae, ya nuna kamar shi na Allah ne "Meyasa zaka min haka Kabeeru?" Abba ya fad'a a fili yana dafe da k'irjin sa da har lokacin yake jin ya masa wani irin nauyi. ... Bin Abban tayi da kallo sanda ya shigo cikin gidan, a hankali ta bud'e baki ta amsa sallamar sa da taji yayi ta a hankali, seta mik'e tana goge hannayen ta daga cikin ruwan d'aurayar wanke wanke ta k'araso tana kallan sa tace "Sannu da zuwa Abban su" "Yawwah.." ya fad'a yana yin gaba, haka nan kawae taji zuciyar ta ta buga, seta lumshe idanun ta a ranta tana fatan Allah yasa ba wani mummunan abun ne ya faru ba, a hankali ta yaye labulen d'akin ta shiga da sallama seta nemi gefen gadon ta zauna tana cigaba da kallan sa tace "Ko na had'a maka ruwan wanka ne?" girgiza kae Abba yayi kafin yace "A'ah" cike da damuwa ta furta "Abban su lafiya dae koh?" Abba ya runtse idanun sa yana jin zafin abinda ze fito daga bakin sa "Kabeeru.." tun kafin Umma taji k'arshen maganar ta dafe k'irjin ta dan ita ta d'auka ko wani abun ne ya samu Kabeerun, se dae sa6anin abinda tayi tsammani se taji Abban yace "Kabeeru yaci amana ta, ya tattara kayan sa ya gudu da kud'ad'en nan da kuma takaddu na.." runtse idanun ta Umma tayi a ranta tana fatan ta bud'e idanu taga ba gaskiya bane abinda take ji a kunnuwan ta ko kuma ya kasance mafarki ne take yi, se dae har zuwa sanda ta bud'e idanun ta se taga Abban a yadda ta barshi "Anya kuwa Abban su?" ta fad'a cikin k'arfin gwuiwa, murmurshin takaeci Abba yayi wanda ake cewa yafi kuka ciwo kana yace "Tabbas haka ne, ban dawo gidan nan ba seda na bincika, har unguwar su naje aka tabbatar min a jiyan shima ya bar garin shi da iyalin sa" "Inna lillahi wa inna ilaehi rajiun" Umma ta shiga nanatawa tana kallan Abban tana jin da wani ne ya fad'a mata wannan zancen har abada ba zata ta6a yarda ba "Abban su.. Abbun Raj fa kake magana, mutumin da kullum zancen sa a bakin ka baya wuce na alkhaeri kirkin sa da kuma rik'on amanar sa, koda sau d'aya ban ta6a jin ka fad'i aebun sa ba, se dae gashi yau ina jin wata magana mara dad'i akansa tana fitowa daga bakin ka, Abban su kana nufin duka kud'ad'en nan ya gudu dasu don Allah.." "Toh ina suke Ruk'ayya? ae yanzu kinga irin sakayyar da yayi min na d'aukar amana ta da nayi na bashi koh?" wani numfashi me zafi Umma taja ta fesar sannan ta sake yin salati, daga nan kuma tayi shiru ta kasa cewa komae, dan kwata kwata ma bata san me za tace ba, mamakin ta d'aya yadda Abban da kansa yake fad'in Abbu ya gudu da kud'in sa, abin kamar almara, gaba d'aya k'wak'walwar ta ta tafi can tana mata bitar alak'ar Abban da kuma Abbu.... Sanda Yah Sadeeq yaji zancen nan seda yayi kuka sosae cikin tausayin Abban nasa, yana tuna irin gwagwarmayar da Abban yasha kafin ya samu wannan damar amma lokaci d'aya wani yazo yayi masa awon gaba da komae nasa, ya kuma yi alawadae da hali irin na Abbu, ya kalli Umma dake zaune ta jinginar da kanta kan kujera kamar me tunani "Umma bansan meyasa ba ni gaba d'aya daga shi Raj d'in har mahaefin sa ba suyi min ba Umma, Umma mutumin nan ya cuci Abba ya cuce mu, Allah ya isar mana wallahi" kallan sa Umma tayi, bata jin komae idan ta tattauna magana da Yah Sadeeq d'in dan k'ananun shekarun sa basu hana shi hankali ba, idan yayi wani abun kamar wani babban mutum tace "Bama seka fad'a ba Sadeeq, sakayya kam se Allah yayi mana ita, shi kuma yaje ya gani idan haram wata abace" dae_dae lokacin da Ayrah ta shigo d'akin ta k'arasa ta kwanta akan cinyar Umma kamar zata fashe da kuka ta furta "Umma Raj.." Yah Sadeeq dake zaune kujerar kusa da Umma ne ya janyo ta da k'arfi cikin fad'a yace "Wallahi idan kika sake mana maganar Raj a cikin gidan nan sena miki duka kinji na fad'a miki" ya fad'a yana d'aga hannu kamar ze mare ta, kuka ta fashe dashi kamar wadda ya ida dukan nata, Umma ta kae hannu ta rik'o ta ta d'auke ta zuwa kan cinyar ta ta kwantar sannan ta kalli Yah Sadeeq tace "Ita me ta sani? Wannan fad'an babu abinda ze janyo se rigimar ta kasan hali dae" "Umma ba duk itace ta janyo ba, da bata san Raj d'in bama ta yaya Abba ze had'u da baban sa ballantana har ya cuce shi" Umma na cigaba da rarrashin Ayrah tace a nutse "Ya zamu yi da k'addara Sadeeq?" ... Sau wajen 3 Umman na farkawa daga baccin da babu dad'i cikin sa