← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 90

Sashe 34

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ciki tabbas da baze ambaci Rk a matsayin mijin ta ba, daga lokacin da aka fad'i hakan tana sake jin kan ta ne dumu_dumu a mae laefi, wadda ta bijirewa umarnin iyayen ta, se dae tasan wannan d'in bame yiwuwa bane, kwangila ce suka k'ulla tsakanin ta da Rk d'in kuma nan da anjima zata k'are, dan haka wannan d'in kamar wani wasan kwaekwayo ne aka gabatar dashi cikin k'auyen. Sosae Rk yayi wa Me gari godiya sannan ya mik'e yana kallan er rigimar tasa, be san yanda zasu k'arke ba, be san kuma meze faru anan gaba ba "A'ah ba dae tafiya ba?" Me gari ya fad'a yana kallan Alhaji Mato daya mik'e shima, dan so yake ya fara yin gaba kafin Rk ya riga shi, dan kuwa tun kafin ya isa gida yake so ya gama dashi, se dae da alama Me garin na son jik'a masa aeki "Ehh.. A'ah.." Alhajin Maton ya fad'a cikin inda inda yana komawa ya zauna "Yawwah koda naji, ae ka zauna muyi hira koh?" bece komae ba dan a yadda yake ji ze iya sussurfawa Me garin zagi ne "Allah ya tsare" Me gari ya sake bin Rk da addu'ar sanda ya k'arasa dab da ita, ya rasa yanda zeyi ya mata magana, mik'ewar da tayi ne ya sanya shi d'an lumshe idanun sa sannan yayi gaba yayinda ta bishi a baya hannun ta rik'e da kan ta da har lokacin be bar sara mata ba, hannu ya saka ya bud'e mata k'ofar wajen me zaman banza, zata iya cewa ta fishi k'aguwa su bar k'auyen nan ko dan a warware wannan auren wasan sannan ta tafi gidan su, uwa uba kuma ga yadda take ji a yanzun koda wane lokaci zata iya zubewa idan bata nemi wajen zama ba, dan haka babu musu ta shige cikin motar ta kwantar da kan ta tana sakin wata ajiyar zuciya lokaci d'aya kuma kan ta na sake juya mata ta fara ganin ko ina na juya mata, sam be lura da yanayin da take ciki ba ya koma mazaunin driver yana sauke ajiyar zuciya, seda ya kalli inda take zaune sannan ya sake lumshe idanun sa kana ya d'auke kae yana jan motar ya fara tafiya.. .... A d'aya 6angaren kuwa a ranar da Ayrahn ta bar gidan gaba d'aya cikin su babu wanda ya rintsa, Yah Sadeeq zuciyar sa sosae take masa zafi idan ya tuna halin kafiya irin na k'anwar tasa data kasa barin d'a namiji duk da yadda Abba yace ba zata aure shi ba, ta 6angaren Umma kuwa kwana tayi tana kuka a ranar, ta kasa sakewa, koda tayi k'ok'arin tunanin ba hakan ne dalilin rashin ganin d'iyar ta ta ba se kuma ta kasa samun hujjar da zata rik'a akan hakan, koda tayi tunanin d'iyar ta ta bata da bud'ewar ido ko wayon da zata bi saurayi ta gudu se kuma ta tsaya ta tuna tasirin soyayya, musamman yadda Ayrahn ke k'aunar Raj d'in, da yadda taga rikicewar ta a jiya da Abba ke fad'a mata ba zata aure shi ba seta sake jin jikin ta yayi wani mugun sanyi, dan haka tayi kukan ta ta godewa Allah sannan tayi shiru, 6angaren Abba kuwa ranar da bugun zuciya ya kwana, wanda hakan ke alamta masa tashin ciwon sa, haka dae ya dinga daurewa baya so 6acin rae ya sanya yayi wa d'iyar tasa fata mara kyau. ... Washe_gari da safe Umma ta fito ta shiga kitchen dan ta samu ta sarrafa musu wani abun da zasu ci a matsayin abun karin, ta dad'e a kitchen d'in tana nazari se kuma ta fito kae tsaye ta wuce d'akin Abba, tana shirin shiga Abban ya fito seta dakata lokacin da shima ya dakata yana kallan yadda idanun ta suka yi ja da alama jiya kwana tayi tana kuka "Har yanzu kukan kike yi?" Abba ya tambaya yana cigaba da kallan ta, hannu Umma ta kae fuskar ta ta d'auke hawayen daya zuba, tun jiya take k'ok'arin cire damuwar daga cikin ran ta amma ta kasa, ta kasa mantawa, ko dae_dae da minti d'aya zuciyar ta ta kasa sukuni da wannan al'amari "Aou cigaba kuma zaki yi?" seta girgiza kae sannan tace bayan ta runtse idanun ta ta bud'e "Abban su bansan ina yin kukan ba, ko da nayi k'ok'arin mantawa hakan yana gagara ne a cikin zuciya ta, Abban su har yanzu na kasa amincewa ba mafarki nake yi ba" jinjina kae Abba ya shiga yi cike da gamsuwa da maganar Umman, shi kan sa jiya be rintsa ba ya zauna ne kawae se sak'e sak'e yake yi "Kiyi hak'uri ki dena kukan haka nan kin ji?" ya fad'a yana kallan ta "In Sha Allah, zan yi k'ok'ari naga hakan ta kasance.." Umma ta fad'a tana sake goge idanun ta. ... Driving yake a nutse kamar koda yaushe, jefi jefi yana juyawa yana duban inda take a takure cikin hijab ko k'wak'wk'waran motsi ba tayi, bece mata komae ba dan baya so ya tado da rigima tun yanzun dan haka ya mata shiru a ran sa yana tunanin mafita. Tafiya me tsayi suka yi kafin suka fara shiga garin Kano, zuwa lokacin kam mamaki take bashi ganin har lokacin bata motsa ba, a hankali ya fesar da iska daga bakin sa sannan yaja motar ya gangara gefen titi ya kashe ta ya d'an jinginar da kan sa akan steering na tsawon sakanni kana ya d'ago kan nasa ya dubi inda take, seda ya lumshe idanun sa kafin a hankali yace "Ayrah!!" beji ta amsa masa ba ko kuma ta d'ago har bayan wajen minti 1 sannan a hankali ya kae hannun sa kan hijab d'in nata ya d'an yi tapping nata, nan ma dae ba tayi motsi ba, seya ware manyan idanun sa akan ta sannan ya kae hannun sa a nutse gaba d'aya ya rik'o ta, se kuwa tayo baya zuwa jikin sa, k'irjin sa ya wani irin buga lokaci guda yana mamakin yadda yaji jikin ta yayi wani irin zafi daya wuce na k'a'ida, idanun sa akan kyakykyawar fuskar ta da tayi fayau kamar wadda tayi wata da watanni tana rashin lafiya, idanun ta a rufe suke, dogayen zara zaran eye lashes d'in ta sun kwanta sunyi luff akan idanun ta, a hankali ya sake bud'e bakin sa se dae yanzu a cunkushe ya furta "Ayrah!!" nan ma dae ba tace komae ba, runtse idanun sa yayi yana jin wani abu me kama da tsoro na shigar sa "Meya same ta?" ya tambayi kan sa, seya kae kunnen sa saetin dogon hancin ta da yayi ja kamar me mura, cikin lokaci k'ank'ani hucin numfashin da take fitarwa me zafi da kuma hucin zafin dake jikin ta ya sauka akan fuskar sa, seya sake lumshe idanun sa yana d'an tsayar da numfashin sa har lokacin cike da tsoro, cikin ikon Allah yaji numfashi kad'an na fita, be san sanda ya saki wata ajiyar zuciya ba sannan ya maeda ta kan kujerar ya kwantar kana ya tashi motar da gudun gaske ya wuce asibiti, sam gaba d'aya ma ya manta, haka zalika beyi tunanin komae ba ya wuce asibitin sa. Parking d'in motar sa yayi har lokacin bugun zuciyar sa be koma dae_dae ba, ya fito daga cikin motar cike da sassarfa wanda komae abin ka baka isa ka gane a yanayin da yake ciki ba, dan kuwa fuskar nan haka take babu yabo babu fallasa amma cikin zuciyar sa shi kad'ae yasan abinda yake ji, bud'e inda take kwance yayi beyi wata wata ba ya d'auke ta gaba d'ayan ta a hannun sa, sam be lura da kallan da en cikin asibitin ke bin sa dashi ba, yama manta abinda ya aekata haka ya wuce da ita cikin Office d'in sa, duk wad'anda ke kallan sa mamaki ne ya kamasu yadda suka ga Doctor Rk d'in da kan sa ya d'akko wata mace a hannun sa, nan take aka fara gulmammaki cikin asibitin, seda ya tsaya ya kar6i spare key d'in Office d'in sa dake ajje sannan ya wuce ya bud'e ya shiga har lokacin tana rik'e a hannun sa ya kwantar da ita kan gado. .. Hannun ta har rawa yake yi ta d'auki wayar ta ta nemo number Abbu ta kira, babu jimawa Abbu ya amsa wayar "Yalla6ae Doctor Rk ya shigo yanzun nan" daga inda Abbu yake ya saki ajiyar zuciya yana jin dad'i har cikin ran sa dan kuwa tun d'azun yake kiran layin Rk d'in amma se ace masa a kashe yake "Ohk ina nan zuwa nan da 10 minutes" shine kawae abinda Abbu ya fad'a yana katse wayar sannan ya chanja akalar tafiyar tasa zuwa asibitin. .. Kamar wanda aka jefo haka Abbu ya fad'o cikin asibitin, dae_dae lokacin da Rk ya fito daga cikin Office d'in sa, Abbu ya sake sauke ajiyar zuciya ganin d'an nasa, seya k'arasa kafin yace "Raj!" muryar wanda yaji ne ta sanya k'irjin sa ya d'an buga sannan ya d'aga idanun sa ya kalli Abbun dake k'arasowa inda yake "Ina ka shiga ne haka? Kasa hankalin mu duka ya tashi?" d'an yatsine fuska yayi lokaci guda kuma yana kae hannun sa kan sa sannan yace "Amm... Abbu ina so ne nayi settling abubuwa da dama, bana buk'atar takura ne yasa na kashe waya ta, ina fatan dae ban yi laefi ba?" ya k'arasa maganar yana kallan Abbun "Ohk tohm muje cikin Office d'in akwae maganar gaggawa da nake so muyi" be san sanda yayi gaba ba yana tarewa Abbu k'ofar shiga Office d'in ba sannan yayi wani murmushin yak'e yace "Abbu pls.." "Shikenan, kayi k'ok'arin gamawa, koma dae baka gama ba ka tabbatar ka dawo gida dan akwae muhimmiyar maganar da zamu yi bamu da ishashshen lokaci" Abbu ya fad'a yana d'an nazarin d'an nasa, ganin yanda idanun sa suka d'an tasa kamar wanda baya samun bacci, se kuma daya tuna yanzu yake fad'a masa aeki ne ya rik'e shi sannan ya d'an ji dama dama "In Sha Allah" shine abinda Rk ya fad'a yana d'an kaucewa kallan da Abbun ke masa, dan gani yake kamar yana kallan k'wayar idanun sa ze karanto rashin gaskiyar dake tattare da shi "Allah ya yadda" Abbu ya fad'a yana juyawa daga
Chapter 34 · 0% Book details