← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 90

Sashe 79

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da wadatar girma Abba ya zauna kan kujera yayin da Yah Sadeeq yayi waje, ya sanar da Abbun ya shiga sannan ya koma wajen Abokin sa suka cigaba da magana. .. Da sallama Abbu ya shigo cikin soron, hannun sa d'auke da wata bak'ar jaka, da kuma wani envelope. Amsawa Abba yayi da murmushi kan fuskar sa. Abbu ya ja kujera shima ya zauna sannan yace yana kallan Abba. "Barka da wannan lokacin Yalla6ae" Dariya Abba yayi jin sunan da Abbun ya kira shi da shi, ya girgiza kae yana fad'in "A'ah ka bari mana kae kuwa." Shi ma girgiza kan Abbu yayi yace "A'ah fa Abban Sadeeq bazan dena fad'a ba." "Yawwah toh ko kae fa yanzu naji batu, wannan d'in shi ne suna na dama" In ji Abba yana murmushi. Murmushi Abbu yayi a ran sa yana dad'a mamaki da hali irin na Abba, idan baka san abin da ya faru a baya ba yanzu ba zaka ta6a cewa ya faru ba idan ka gan su a tare. Gyara zama Abbu yayi akan kujerar yana sauke ajiyar zuciya sannan ya soma magana a hankali, "Wato dama zuwa nayi na kawo maka wad'annan, ba dan komae ba, ba dan zan iya biyan ka abin da na maka ba, a'ah wannan d'in ba kud'i na bane, kud'in ka ne nan d'in a cikin jaka wallahi babu ko sisi na a ciki." Abbu ya gama maganar yana d'akko jakar ya matsar da ita gaban Abba. Kallan jakar Abba yayi sannan ya maeda duban sa kan Abbu yace "Ina takaddu na suke?" cikin jin dad'in tambayar Abban Abbu yace yana mik'a envelope d'in hannun sa "Ga su" Hannu Abba ya saka ya kar6a sannan ya soma magana, "Takaddu na kawae nake buk'ata, amma kud'i bana buk'atar su, ba kuma wae dan ban yafe maka ba ne, a'ah.. Tun da nace na yafe maka toh ina nufin hakan, na yafe maka duniya wa lahira, saboda haka ka d'auki kud'in ka tafi dasu ka cigaba da juyawa, nima Allah ze kawo min wata hanyar da zan samu wasu." Girgiza kae Abbu yayi cikin rashin jin dad'i yace "Amma idan kayi haka se naga kamar baka yafe min abin da na maka ba, kuma wannan kud'in wallahi ba nawa bane, na ka ne." Murmushi Abba yayi kana yace "Ni ne fa na fad'a maka ba wani ba, na riga na shafe wannan babin se dae idan kae ne zaka dinga tunawa da shi, amma ni a waje na komae ya wuce." Duk da haka Abbu be saduda ba ya cigaba da rok'on Abba akan ya kar6i kud'in nan, amma fafur Abba yace baze kar6a ba ya bar masa. Daga k'arshe dae da yaga da gasken Abba baze kar6a ba se yace, "Toh wata alfarma zan nema a wajen ka, don Allah kada ka ce min a'ah, don Allah." Se da Abba ya jinjina kae sannan yace "Toh ina ji." "So nake ka bani Sadeeq na tafi da shi, da wannan kud'in ba da wani ba zan d'ora shi akan kasuwanci, ya juya su ya rik'a samun riba, don Allah kada kace min a'ah." Sauke ajiyar zuciya Abba yayi sannan yace bayan yayi murmushi "Shikenan, Allah ya taemaka." ya fad'a dan wannan d'in ya amince da shi. Sosae Abbu yaji dad'in hakan ya kuwa dinga godiya kamar shi aka yiwa abin alkhaeri. .. A zaune take akan kujerar d'akin idanun ta akan Ayrah da take kula da ita tamkar wadda za'a sace, haka kawae take kallan ta a matsayin amana, dan haka tun da ta tashi da safe bayan ta gama abin da zata yi ta dawo ta zauna tana a gaban gadon na ta, cikin zuciyar ta kuma tana addu'a. Sake bud'e idanun ta Ummee tayi tana kallan Ayrahn da tun d'azu taga tana d'an motsa hannun ta. Se ta mik'e da sauri tana kallan idanun Ayrahn da take motsa su sosae kamar zata bud'e su. Bata san sanda wani murmushi ya su6uce mata ba, tsabar farin ciki se ta kasa ko da yunk'urin fita ne ta kira Rk da fitar sa kenan daga cikin d'akin, ta sake matsawa dab da Ayrahn da dogayen lashes d'in ta ke cigaba da motsawa kamar me jin tsoron bud'e su... Mhiz Innocent... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* Page 057 ___Wajen sakanni 5 ta d'auka kafin a hankali ta bud'e idanun na ta gaba d'aya, se tayi sauri ta maeda su ta rufe kamar wadda ta ga abin tsoro. "Ayrah!" Ummee ta fad'a har lokacin fuskar ta d'auke da mad'aukakin murmushi. Ganin bata amsa ba kuma bata bud'e idanun ta ba ya sanya Ummeen kae hannun ta zuwa kan fuskar Ayrahn. Se a lokacin ta bud'e idanun na ta da sauri tana bin d'akin da take a ciki da kallo, bata ta6a tunanin zata bud'e idanu ta gan ta a waje makamancin wannan ba, hakan ne ya sanya ta kallan Ummee dake kusa da ita, ta d'an zuba mata idanun ta da suka fad'a suka jeme suka kuma kod'e na tsawon sakanni, tana shirin janye idanun na ta wani tari ya sark'e ta, se ta shiga yin sa babu k'ak'k'autawa. K'ok'arin tashi da ta soma yi ne har kuma lokocin tarin be tsaya ba ya sanya Ummee saurin rik'o ta tana fad'in "Subhanallahi, Sannu.." tayi maganar tana rik'o ta ta tayar da ita zaune. Cigaba da tarin da tayi ne wanda Ummeen ta rasa dalilin sa ya sanya ta sakin Ayrahn tana shirin fita Rk ya shigo cikin d'akin. Ajiyar zuciya Ummee ta sauke, dae_dae lokacin da ya k'arasa wajen Ayrah dake cigaba da tari tana kuma sauke ajiyar zuciya a lokaci d'aya. Rik'o ta yayi sosae dae_dae lokacin da tarin ya d'an lafa se ajiyar zuciya da ta koma saukewa idanun ta sun cika fall da k'walla, kawae se ya ja ta cikin jikin sa ya rungume ta tsam wani irin farin ciki na mamaye ilahirin jikin sa, lokaci d'aya kuma yana amfani da hannun sa wajen shafa bayan ta, da alama ya ma manta wacece a cikin d'akin, dan haka sum_sum Ummee ta fice daga d'akin kada ayi abin kunya. Wajen minti 1 suka d'auka a hakan, se da ya ji ta dena sauke ajiyar zuciyar, numfashin na ta kuma ya koma dae_dae sannan ya sauke ajiyar zuciya ya d'ago ta yana kallan fuskar ta da tayi mugun fayau kamar wadda ta shekara bata da lafiya, itama kallan sa take yi sosae kamar wadda taga sabon halitta, bata so tayi magana taje ta farka daga wannan mafarkin dake nuni da har yanzun tana duniya gata da ga Raj d'in ta, hakan ne yasa kawae tayi shiru ta cigaba da kallan sa. "Ayrah!!" ya ambata yana kafe da idanun sa. Kawae se ta lumshe idanun ta yadda ya kira sunan na ta na ratsa duk wata kafa ta jikin ta. Haka kawae ya d'an ji fad'uwar gaba ta ziyarce shi amma ya maaze kawae ya kama hannun ta ya taemaka mata ta sauko. Direct toilet ya wuce da ita, itama a yadda take jin jikin ta gaba d'aya babu dad'i zata so ta ji ta yanzun cikin ruwa me d'umi. Waje ya samar mata ta zauna har lokacin be sake cewa komae ba itama kuma haka se cigaba da bin sa da kallo kawae da tayi, yayin da bata san hakan sake jefa shi yake cikin tsoro ba, amma duk da haka be nuna komae ba ya bud'e brush ya saka mata maclean sannan ya mik'a mata, babu musu ta kar6a ta wanke bakin ta, yana kallan ta duk abin da take yi, se dae a hankali take yi kamar wadda bata da laka amma hakan ya san ba komae bane baze wuce yana da nasaba da ciwon jiki ba ko dan dad'ewar da tayi a kwance. Basu suka baro toilet d'in ba se da ya taemaka mata tayi wanka da ruwa me d'umi sosae, sannan ya taemaka mata ta saka wata doguwar riga mara nauyi. Da kan sa ya d'aga ta ya d'ora ta akan gadon sannan ya kalle ta, tsawon second 10 bece komae ba, se kuma ya bud'e baki a hankali yace "Babe, kina lafiya?" Lumshe idanu tayi, yanzu kam tabbas ta tabbatar ba mafarki take yi ba, amma dan sake tabbatarwa se ta bud'e bakin ta da suka mata nauyi tace da muryar ta da tayi kama da me mura "Na'am" Wata k'atuwar ajiyar zuciya da sautin ta se da ya fito fili ya sauke yana lumshe idanun sa, duk wata fargaba da yake ji ta tafi, sabon farin ciki yazo ya ziyarce shi, be san sanda wani murmushi ya su6uce masa ba lokaci d'aya yana furta "Alhamdulillah" se kuma ya bud'e idanun sa akan fuskar ta har lokacin murmushin yak'i 6acewa daga fuskar sa, babu 6ata lokaci ya janyo ta ya mata wata kyakykyawar runguma kamar ze maeda ta cikin sa, itama hannayen ta duka biyun ta saka ta rungume shi, wasu hawaye na zubowa daga cikin idanun ta zuwa kan fuskar ta. A nutse ya kae bakin sa cikin kunnen ta yace kamar me rad'a "Babu abin da ke miki ciwo?" Seta jinjina kan ta kawae duk da akwae inda ke mata ciwon, ya sake sauke ajiyar zuciya. "Kin tabbatar babu inda ke miki ciwo?" ya tambaya bayan ya d'ago ta daga jikin sa, yanzu ma jinjina kae tayi kana tace "Se kunne na kawae da yayi min wani iri" "Babu damuwa, In Sha Allah ze dena shi ma" yayi maganar cikin kwantar da murya. Fitowar sa kenan daga d'akin suka had'u da Umma da zuwan ta kenan, cikin farin ciki ya kalle ta ya rusuna sannan ya gaeshe ta, ta amsa cike da zumud'in jin abin da ze fito daga bakin sa, dan daga yanayin sa kad'ae ta san lallae akwae cigaba, se kuwa yace "Umma cikin yaddar Ubangiji ta farka" Sassanyar ajiyar zuciya Umma ta sauke kafin a fili tace "Alhamdulillah ya Allah" ta fad'a tana d'aga hannun ta sama cikin matuk'ar farin ciki. A hankali ta tura k'ofar d'akin ta shiga da sallama cike da zumud'in son ganin d'iyar ta, dae_dae lokacin da Ummee ke zaune kan kujera dab da gadon hannun ta d'auke da plate d'in da ta zuba abinci a ciki. K'arasawa Umma tayi tana
Chapter 79 · 0% Book details