Sashe 40
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dukan su sun gamsu da zancen d'an nasu, a gefe guda kuma dukan su sun so su fahimci kamar sun yi laefi, k'in tsayawa suji abinda ze fito daga bakin Ayrahn, yanke mata hukunci tun kafin su san aenahin abinda ya faru, koma menene ya faru 6acin rae ne "Je ka kira min d'iya ta!" Umma ta fad'a tana kallan Yah Sadeeq lokaci guda kuma tana jin yadda wani nauyi dake k'irjin ta ya d'an ragu, seta saka hannu ta goge hawayen fuskar ta dae_dae lokacin da Yah Sadeeq ya saki murmushi kana ya mik'e yana kallan Abba yace a hankali "Abba in kira ta?" seda Abba ya runtse idanun sa sannan ya bud'e kawae ya jinjina kae, cike da farin ciki ya sanya k'afa ya fice daga cikin gidan yana d'an d'ingishi dan har lokacin k'afar ta sa bata ida warkewa ba. ... Dae_dae lokacin daya fito titi yayi dae_dae da lokacin daya hango Ayrahn cikin motar Rk, yana k'ok'arin k'arasawa wajen motar Rk ya tashi motar ya bar wajen, se yayi sauri ya tsaeda Napep ya sanar dashi yabi masa motar Rk d'in, babu musu me Napep d'in ya bi shi, dae_dae wani waje motar Rk d'in ta dakata wanda yafi kama da Hotel, Yah Sadeeq ya sauka ya biya me Napep d'in kud'in sa sannan ya cigaba da tafiya zuwa wajen motar. Saukowa Rk yayi daga driver seat ya zagaya zuwa wajen me zaman banza ya bud'e k'ofar yana kallan yanda take a cure waje d'aya, yanzu ta dena kukan se dae ita kad'ae tasan abinda take sak'awa a cikin zuciyar ta "Don Allah ki fito!" ya fad'a cikin rarrashi, idan motar da take ciki ta d'aga kae ta kalle shi toh itama ta kalle shi "Ayrah!" Yah Sadeeq ya fad'a sanda ya k'araso dab da motar, da wani irin sauri ta d'aga kan ta ba tare data shirya ba, nan take idanun ta suka sauka akan Yah Sadeeq, seda ta d'an lumshe idanun ta sannan ta bud'e dan tabbatar da Yah Sadeeq d'in ne ba gizo yake mata ba sannan ta sauko daga cikin motar a million ta k'arasa ta fad'a jikin Yah Sadeeq d'in tana sakin wani irin kuka, a hanzarce ya d'aga kan sa ya kalli wanda ta rungume d'in, ko wani be masa bayani ba ya fahimci wanene shi, amma me kuma ya kawo shi nan d'in? Shima Yah Sadeeq d'in rungume ta yayi yana jin yanda take kuka sosae, tana shirin fara magana duk dae cikin kukan yace "Ya isa! Ki bari mu zauna, ina buk'atar jin gaskiyar al'amari, bana son k'arya Ayrah.." kamar wata k'adangaruwa ta shiga jinjina kae har lokacin tak'i sakin sa, d'aga idanun sa yayi ya kalli Rk da har lokacin yake tsaye se dae basu yake kalla ba yace "Raj?" se a lokacin ya juyo ya kalle shi cike da mamakin yadda ya kama sunan sa, seya jinjina kae yana lumshe idanun sa, d'an murmushi kad'an Yah Sadeeq yayi kana ya furta "Sad..." "Sadeeq!" Rk ya k'arasa sunan yana nuna Yah Sadeeq "Ehh" shine abinda Yah Sadeeq ya furta sannan ya d'ago Ayrah dake jikin sa ya rik'e hannayen ta kana yace "Ina son magana da kae idan babu damuwa" "Why not?" Rk ga fad'a bayan ya d'aga kafad'a "Mu k'arasa can.." Rk ya fad'a yana nuna wani d'an madaedaecin waje dake d'auke da wasu kujeru masu kyau, babu wanda ya sake cewa komae cikin su Rk na gaba yayin da Yah Sadeeq ke a bayan sa suka cigaba da tafiya zuwa wajen, ita dae Ayrah babu abinda tace ta cigaba da rik'e hannun yayan ta dan tana ji kamar idan ta sake shi zata bud'e ido taga baya nan, a haka suka k'arasa wajen, Rk ne ya fara neman waje ya zauna sannan Yah Sadeeq ya zauna, ita dae Ayrah ko zaman ma kasawa tayi seda Yah Sadeeq ya kalle ta yace a hankali "Ki zauna kin ji?" kamar bata san da wata halittar a wajen ba taja kujera ta zauna har lokacin idanun ta na kan Yah Sadeeq, shiru Rk yayi kawae yana jiran jin abinda Yah Sadeeq d'in zece, kamar ya sani kuwa seya sauke ajiyar zuciya sannan ya furta "Menene gaskiyar barin Ayrah gida don Allah? Menene gaskiyar auren ka da tace tana d'auke da shi a kan ta?" shiru ya d'an yi yana nazarin tambayar Yah Sadeeq d'in, kamar ba zece komae ba se kuma ya d'an lumshe manyan idanun sa sannan ya bud'e yana tunanin tsayin adadin maganar da zeyi, amma ya zama dole yayi ko dan hakan ze wanke Ayrah daga wajen iyayen ta, sannan kuma su yafe mata koda ze samu kan ta ta dawo asalin Ayrahn sa, a hankali ya shiga labartawa Yah Sadeeq abinda ya faru, duk wani abu daya sani seda ya fad'a masa, yana kaewa k'arshe yayi shiru yana d'an aje numfashi kad'an, shiru Yah Sadeeq yayi tun lokacin da Rk d'in ya fara bashi labari, mamaki, tsoro gami da al'ajabin wannan al'amari yak'i barin sa, ya rasa ma me zece kwata kwata, ya rasa ma wane tunani ya kamata yayi, abin ya bashi tsoro da mamaki aenun, a hankali ya dubi inda Ayrah take zaune duk tayi wani iri da ita kamar ba Ayrah ta asali ba, se yaji wani matsananincin tausayin ta ya mamaye shi, Allah sarki baewar Allah, ashe dae Ayrahn er halak ce, ta haefu cikin Umma da Abba, tana k'aunar farin cikin Abban ta dana Umman ta haka zalika kuma tana k'in abinda basa so, tunda gashi nan duk irin yawan k'aunar da take wa Raj daga ji iyayen ta basa son shi itama ta sauya masa "Amma pls ko zan iya sanin dalilin Abba na cewa bazan auri Ayrah ba?" tambayar data katsewa Yah Sadeeq tunani kenan, seya d'aga ido ya kalli Rk sannan ya girgiza kae yana kallan sa har lokacin yace "Kada ka nuna kamar wani baka sani ba mana!" iska Rk ya fesar daga bakin sa sannan yace "Wallahi ban sani ba!" ya fad'a dan ya cire duk wani kokwanto dake tattare da Yah Sadeeq d'in, shiru Yah Sadeeq yayi na en wasu sakanni, sam bega amfanin 6oyewar ba gwara ma ya fad'a masa ya sani d'in kada ya zaci haka kurum za'a hana shi auren ta ne bayan tana son shi yana son ta "Mahaefin ka.." Yah Sadeeq ya fad'a masa duk abinda ya faru kamar yadda ya sani, tun daga lokacin da suka zo hawa mota da kuma sanda suka dawo Kano, daskarewa Rk yayi akan kujerar da yake zaune yana cigaba da kallan Yah Sadeeq kamar wani sak'ago ko kuma wani mara wayo, anya kuwa Yah Sadeeq d'in yasan abinda ke fitowa daga cikin bakin sa? Shin me yake k'ok'arin cewa Abbun sa ya aekata? Anya kuwa ba ya fad'i hakan bane dan ya kawar dashi daga kan k'anwar tasa ba? A hankali ya shiga tariyo abinda Abbu ya fad'a masa da kuma wannan maganar da Yah Sadeeq d'in ke fad'a masa, seya shiga had'a su waje d'aya yaga ko iri d'aya ce, shin zasu zauna a mizani d'aya? Se dae ina, kwata kwata ba iri d'aya bace, sam babu ma ta inda suka had'u ko kad'an, toh kenan me yake faruwa?? Mhiz Innocent..... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* Page 036 ___Ya d'auki wajen mintina 2 a haka, zuciyar sa a matuk'ar cunkushe, gaba d'aya ya rasa meke masa dad'i, duka tunanin sa ya tafi ne wajen tunanin menene gaskiyar abinda yake fitowa daga bakin Yah Sadeeq, shin me ya kamata ya amince da shi? Maganar Abbu n sa ko kuma maganar Yah Sadeeq d'in? Iska me zafi ya fesar daga cikin bakin sa lokaci d'aya yana lumshe idanun sa, har lokacin kuma yana jin yanda zuciyar sa ke ta azalzalar sa "Yah Sadeeq ka tashi muje wajen su Abba" shine abinda Ayrah ta fad'a tana d'an jan hannun Yah Sadeeq d'in, kallan ta yayi sannan yace a nutse "Ina zuwa, yanzun zamu tafi.." ya k'are maganar yana maeda duban sa kan Rk da har lokacin ya gaza furta ko kalma d'aya, shi dae Yah Sadeeq abinda be fahimta ba shine..tsananin mamakin abinda Abbun nasa ya aekata ne ya sanya shi kasa furta komae ko kuma maganar ce tazo masa a bazata "Are u ohk?" Yah Sadeeq ya tambaya yana kallan yanda har lokacin idanun sa ke a lumshe, se a lokacin ya shiga bud'e manyan idanun sa a nutse wad'anda lokaci d'aya colour d'in su ya chanja, akan Yah Sadeeq d'in ya sauke su se dae har lokacin bece ko uffan ba in ban da jinjina kae kawae da yayi "Can i just go with her pls?" Yah Sadeeq ya fad'a har lokacin yana kallan Rk, a nutse ya d'aga kan sa ya kalli Ayrah dake zaune gefen Yah Sadeeq kamar bata san da zaman sa a wajen ba, dan kuwa har cikin ran ta tana ji in dae har Abba da Umma basu yafe mata ba ba zata ta6a yafewa Rk ba "Yeah" ya furta a hankali kamar wanda akawa dole, daga haka ya mik'e ba tare daya sake cewa komae ba ya fara barin wajen zuwa wajen motar sa, bin sa da kallo Yah Sadeeq yayi sanda yake barin wajen, gaba d'aya yanayin sa ya chanja cikin k'ank'anin lokaci wanda har hakan seda ya bawa Yah Sadeeq d'in mamaki, se dae hakan kad'ae ya isa ya nuna masa halin su ze iya kasancewa mabanbanta ne da shi da mahaefin sa. "Auta.." Yah Sadeeq ya fad'a yana kallan ta da murmushi saman fuskar sa, dan so yake ya d'an kawar mata da wata damuwar kamin su k'arasa gida, aekuwa yaci nasara dan kuwa seda tayi murmushin itama kafin ta sanya hannun ta akan fuskar ta ta goge hawayen fuskar ta still dae tana cigaba da murmushin "Tashi mu tafi.." ya fad'a bayan ya mik'e, babu musu ta mik'e suka bar wajen zuwa titi, suka samu abin hawa. A 6angaren Rk kuwa a nutse ya k'arasa wajen motar sa ya bud'e ya fad'a ciki, babu 6ata lokaci ya tayar da motar, sam gudu ba d'abi'ar sa bace amma yau seya tsinci kan sa da yin gudun sosae dan so yake ya samu nutsuwar da ze zauna yayi tunani akan wannan