Sashe 47
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wajen kayan ta ta fidda wata riga kana ta koma toilet d'in ta saka sannan ta fito, babu 6ata lokaci ta tayar da sallah, har lokacin data idar idanun sa na a rufe ne, seta sake kallan sa kafin ta d'auke kae kawae. .. Wajen k'arfe 9pm ne, yana zaune kan kujerar d'akin yayin da take zaune akan gado tayi shiru kamar me tunanin wani abu, so yake ya kawar da wannan bak'untar data shiga tsakanin sa da Ayrahn amma kuma yanzu yana cikin wata matsalar ne yasan ba lallae ta saki jikin ta a yanzu ba kam, amma duk da haka ya gaji da ganin ta shiru haka nan, ba kuma yaso ya tuna mata da maganar da zata 6ata mata rae amma yanzu kuma ya zama dole ya mata d'in in dae yana son zaman lafiya, gwara ya fara gamawa da wannan matsalar kafin yazo yaji da waccan d'in. A hankali ya mik'e ya k'arasa kan gadon gefen ta, ya d'aga kae ya saci kallan ta yadda take zaune kan ta akan gwuiwar ta tayi shiru, hannu ya mik'a a nutse ya kamo tattausan hannun ta cikin nasa, janyewa ta soma yi, shi kuma ya sake rik'e hannun gam lokaci d'aya yana girgiza mata kae fuskar sa a narke, kallan sa tayi kafin ta d'auke kan ta tana jin kamar tayi kuka idan ta tuna wani abun "Ayrah don Allah kiyi hak'uri kin ji? Ki dena fushi da ni haka nan, yana ta6a zuciya ta, kin san yadda nake k'aunar ki, bana son ganin ki cikin damuwa, bansan da wane baki zan yi amfani wajen baki hak'uri ba, amma ni dae don Allah ki yafe min ki dena fushi da ni, ina so ne ki koma asalin Ayrahn ki, me so na, me yawan fara'a a gare ni, wadda bata son gani na cikin damuwa.." ya k'arasa maganar yana lumshe idanu, d'aga narkakkun idanun ta tayi ta kalle shi k'irjin ta na d'an bugawa, se taji tausayin sa ya kamata, ita kan ta zata so ta koma waccan Ayrahn amma bata san yanda zata yi hakan ba "Na dad'e banga murmushin ki ba, pls ki min ko da hakan ze faranta min.." yayi maganar har lokacin muryar sa a k'asa yana d'an murza hannun ta dake cikin nasa, bata san sanda tayi murmushin ba wanda ya taho da wani hawaye, seta saka hannu ta d'auke hawayen tana jan ajiyar zuciya, k'awataccen murmushi ne ya wanzu akan kyakykyawar fuskar sa kana yace "Dats my beauty.." seda ya d'an yi shiru yana tunanin ta inda ze fara mata magana, baya so ya sake 6ata mata mood amma wannan lokacin ne ya dace yayi maganar dan haka yace "Babe kina so ranar lahira na tashi da 6ari d'aya a shanye?" cikin rashin fahimta ta d'aga dara_daran idanun ta ta kalle shi, seda ya lumshe idanun sa saboda yanda yaji kallan nata har cikin jikin sa kana yace bayan ya jinjina kan sa "Kiyi hak'uri inaso naje wajen Muneerah in duba halin da take ciki" ya fad'a yana kallan cikin idanun ta, duk da yanda idanun nasu ke cikin na juna hakan be sanya ta janye nata ba "Muneerah!" ta maemaeta akan la66an ta cike da rashin fahimta "Ya ilahee kasa kada ta d'auka da zafi" ya fad'a cikin zuciyar sa har lokacin yana kallan ta "Matar da aka aura min yau nake nufi" cikin sauri ta fizge hannun ta daga cikin nasa wata k'walla na taruwa cikin manyan fararan idanun ta, ba ita taso kukan ya fito ba kawae seta fara kuka wani irin zafi cikin k'irjin ta, runtse idanun sa yayi yana jin babu dad'i har cikin ran sa, a hankali ya saka hannu ya jata cikin jikin sa, babu musu yanzu kam ta cigaba da rera kukan ta a hankali, seda tayi me isar ta sannan ta koma sauke ajiyar zuciya, se a lokacin ya cigaba da magana "Kiyi hak'uri..." ya fad'a, shiru tayi tana sauraron bugun zuciyar su daya had'u waje d'aya, ita wani lokacin har mamaki yake bata musamman yadda kalmar hak'uri bata masa wahala a bakin sa kamar ba Rk ba, cikin raunanniyar murya tace "Ka tafi toh" ta fad'a bayan ta tashi daga jikin nasa, shiru yayi yana bin ta da kallo cike da tausayawa "Kin amince naje?" seta jinjina kae tana saka hannu ta d'auke hawayen da suka k'i tsaya mata "I love u.." ya fad'a a nutse da tattausar muryar sa, bata iya cewa komae ba se bugun zuciyar ta daya k'aru, shikenan itama waccan d'in k'ila haka zeje ya fad'a mata yana son ta, wani kukan taji ya sake taho mata, se tayi saurin jan ajiyar zuciya dan bata so kukan ya fito, cigaba yayi da bin ta da kallo kamar me son gano wani abu, yana son watsa ruwa a jikin sa amma baya son ta zargi wani abun a ran ta dan haka kawae ya mik'e ya d'auki wayar sa ya fice daga cikin d'akin jikin sa a matuk'ar sanyaye lokaci d'aya kuma 6acin rae na taso masa daya tuna wannan k'ak'ababben aure da aka lak'aba masa. Bin sa tayi da kallo sanda ya fice daga d'akin zuciyar ta na sake karyewa, bata ta6a tunanin zata ta6a raba Raj ita da wata ba, se gashi k'addara tasa hakan ta faru, a hankali ta lumshe idanun ta tana bawa kukan daya taho mata damar fitowa ko zata samu sassaucin abinda take ji a cikin zuciyar ta. ... Kae tsaye gidan nasa ya wuce har lokacin fuskar sa a cunkushe, sosae yake jin takaecin zuwa gidan da zeyi wajen wata matar, amma haka dae ya cije kawae ya tafi gidan. Gida ne me girma wanda ke d'auke da part 2, nashi da kuma nata, gidan ya ginu ya had'u kuma iya had'uwa, yana parking motar ya sauka, baya son 6ata lokaci dan haka ya d'auki ledar daya shigo da ita kae tsaye ya wuce part d'in da yasan anan ze same ta. Bin parlourn yayi da kallo wanda shima an zuba kaya kamar babu gobe, be bi takan komae ba ya k'arasa bedroom, knocking ya fara yi bayan ya dakata, tana zaune kan gado sanye cikin lifaya, tun d'azu dama ta k'agu yazo hak'uri kawae take yi, dan haka tana da tabbacin shine "A bud'e take" ta fad'a bayan ta bud'e fuskar ta dake rufe, wadda itace ta fara rufe ta se taga ba zata iya ba kawae ta bud'e ta, kallan sa tayi sanda ya shigo cikin d'akin tana jin wani irin farin ciki musamman idan ta tuna yau d'in ta mallake shi bayan duk wannan gwagwarmayar da ta sha. A nutse ya k'araso cikin d'akin har lokacin be kalli inda take ba, seda ya ajje ledar sannan ya nemi gefen k'aramar kujerar dake cikin d'akin, wajen minti 1 bece komae ba, ita kuma ji take kamar ta tashi ta rungume shi dan dae ta tuna fad'an da tasha a wajen Aunties d'in ta ne da babu abinda ze hanata aekata hakan, shiyasa yanzun ma kamar yadda suka umarce ta tayi shiru tana saurarar sa "Kina lafiya?" ya fad'a bayan ya daddanne zuciyar sa, murmushi ta saki jin tambayar tasa me nuni da kulawa ga wanda ake tambaya, hakan ne ya sanya ta karyar da kae sannan tace "Lafiya k'alau Baby, se dae gajiyar biki kuma!" "Ga abinci nan idan kina buk'ata, akwae komae a kitchen shima in kina buk'ata, bayan nan akwae wani abun da kike buk'ata?" ba tare da tunanin komae ba tace "A'ah Baby.." "Ohk" ya fad'a yana mik'ewa a nutse ya fice daga d'akin. Bin sa tayi da kallo sannan ta kalli ledar daya shigo da ita, wani murmushi ya su6uce mata data tuna yau d'in ita da Rk zasu zama abu d'aya. Tana zaune kan gadon ta cigaba da jiran shigowar sa, har wajen minti 30, awa 1, bata sare ba har lokacin, se dae gajiyar zaman da tayi, da kuma wannan shegiyar lifayar dake jikin ta, dan haka kawae ta sauko daga kan gadon ta ware lifayar gaba d'aya ta jefa ta gefe sannan ta koma ta zauna tana cigaba da jiran sa, tun tana cigaba da saka ran shigowar sa har ta sare, a lokacin ne kuma ta fara tunanin ko dae ta bishi d'akin na sa? Maganar Aunties d'in nata suka sake dawo da ita hayyacin ta seta koma tayi zaman da6aro kan gadon tana jin kamar ta rusa ihu, ita kam da sun bar ta da yanzun bin sa d'akin nasa za tayi ita babu abinda ya dame ta, basu san halin Rk bane, ita data san shi ita ta san shi, tun tana kokawa da baccin da ke ta kawo mata hari har ta bada kae bori ya hau kawae ta shiga sharara baccin ta. .. Shi kuwa 6angaren sa yana komawa d'aki wanka kawae yayi ya fito ya shirya cikin k'ananan kaya sannan yabi lafiyar gado, gaba d'aya tunanin sa da hankalin sa na kan Ayrah ne daya baro ita kad'ae cikin d'akin, dan ma dae daga waje ya kulle ta ne in case, saboda akwae komae na buk'ata a cikin d'akin, a hankali ya lumshe idanun sa zuciyar sa fall da tunanin Ayrahn barkatae. Muneerah kuwa ba ita ta farka ba se wajen k'arfe 8 na safe, da sauri ta mik'e mamaki ya sake kamata ganin har lokacin babu shi cikin d'akin, kae tsaye wanka ta fad'a tayi sannan ta fito tayi Sallahr asuba, dan dama tun a gida ta riga ta saba bata tashi Sallahr asuba se 8 wani lokacin ma har fin 8 d'in ma, duk da kasancewar safiya ce hakan be hana ta d'aukar nighties ta saka ba, wata shu'umar riga ce irin me net d'in nan kuma me bin jiki, gaba d'aya undies d'in ta ana ganin su saboda yanda rigar take me raga raga kamar gidan sauro kuma dududu da kad'an ta wuce gwuiwa, seda ta sake gyara fuskar ta sannan ta fito daga d'akin zuwa part d'in sa. Tura k'ofar tayi cikin sa'a ta jita a bud'e seta k'arasa fuskar ta d'auke da murmushi ta tura kan ta cikin d'akin, wani sassanyan k'amshi ne ya ziyarci hancin ta wanda ya tilasta mata lumshe k'ananun idanun ta kana ta cigaba da tafiya bayan ta