Sashe 74
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
waya ba ko da a zahiri ne kada bakin ki ya sake kuskuren aebata koma waye ne bare mata ta, and ba ke kad'ae ba ko ma wacece a cikin ku bazan lamunta ba wanda ma ina da tabbacim ita baza ta miki haka ba duk da tazarar shekarun da ke tsakanin ku amma kike takewa" Daga haka ya fice daga d'akin ba tare da ya sake kallan ta ba. Bin sa da kallo tayi baki sake kamar wata doluwa, ita sam ta kasa gane inda maganar ta sa ta dosa. Shin meye had'in su da Ayrah? Menene garin gamin su da ita? Idan ban da aure da ya had'a Ayrahn da Rk bata ta6a sanin ta ba, amma gashi yazo yana fad'in wasu maganganu a cukurkud'e wanda zata iya cewa tun da ya fara har ya kae k'arshe bata fahimci zancen ba. Dae_dae nan Mummy ta k'araso inda Muneerahn ke zaune, ta sake kallan Muneerah da ta gan ta a dame tace "Muneerah!" seta d'aga kae ta kalle ta da sauri kuma ta amsa da "Na'am" "Ina mijin na ki? Ko wani abun kika yi ne?" se ta girgiza kae tana fad'in "A'ah Mummy, ba abin da nayi fa.. Amma Mummy.." se kuma ta d'an dakata tana tunanin ta inda zata fara fad'a mata abin da ya gaya mata, sam zancen na sa be samu gurbi a wajen ta ba, hakan ne ya sanya ta fad'in "Amma kamar dae kiran da Daddy ya masa ne ya sanya shi tafiya" Ta6e baki Mummy tayi kana tace "Toh Allah ya kyauta, zaki je gidan Zeenah ne?" da sauri Muneerah ta girgiza kae tace "A'ah babu inda zan je, ta dawo kenan?" "Aou bama ki san ta dawo ba? Lallae Muneerah wae me ke damun ki ne?" Mummyn ta tambaya tana kallan ta, ta6e baki tayi kana tace "Babu komae fa" "Kun fi kusa ae" Mummy ta fad'a daga haka ta mik'e ta fice daga d'akin. .. A d'aya 6angaren kuwa shiru ne ya wanzu cikin d'akin bayan wayar ta ta ta fad'i akan gadon, ta k'urawa waje d'aya idanu kamar wadda ke kallan wani abu, sosae zuciyar ta ke mata zafi ba dan zafin kalaman Muneerah ba, se dan yadda ya fad'a mata shi kad'ae ze je yanzu kuma alamu sun nuna tare suka je. A hankali kuma se ta zame akan gadon tana barin k'wallar da ta taru a idanun ta ta soma zuba akan kuncin ta, tun tana yin mara sauti har ta soma yin me sauti har lokacin zuciyar ta babu dad'i. Dae_dae lokacin Umma ta shigo cikin d'akin da sauri cike da mamakin abin da ya saka d'iyar ta ta kuka, ta k'arasa tana fad'in "Subhanallahi, Ayrah me ya saka ki kuka?" tayi maganar tana k'arasa zama akan gadon tana d'ago Ayrahn zuwa jikin ta. Bata iya cewa komae ba se cigaba da kukan ta da tayi, se Umman ta sanya hannun ta a bayan Ayrahn tana d'an shafawa alamar rarrashi, se da tayi me isar ta sannan ta soma sauke ajiyar zuciya tana jin wani sanyi na ratsa ta musamman da ta ji ta a jikin Umman. Se da Umman ta ji hatta da ajiyar zuciyar ta dena saukewa sannan tace "Fad'a min meya faru?" tayi maganar a hankali, se da ta lumshe idanun ta sannan ta soma magana muryar ta a sark'e "Umma..." "Na'am" Umman ta amsa mata tana d'ago kan ta, se ta koma ta zauna sosae sannan tace "Umma ce min fa yayi shi kad'ae ze je Zarian amma kuma na kira shi matar sa ta d'aga tana fad'a min magana" Ta fad'a ba tare da ta kalli Umma ba. Girgiza kae Umma tayi tana murmushi tana kuma cigaba da kallan Ayrahn sannan tace "Ayrah!" d'aga ido tayi ta kalli Umman fuskar ta a narke kamin ta maeda kan ta k'asa. "Mata ce da kuke auren miji d'aya, ina tunanin ta fiki yawan shekaru ta kuma fiki sanin rayuwa da sauran su, shiyasa zata iya amfani da wannan tayi miki wani abun, saboda haka ina so ki tsaya kiyi tunani anya kuwa yaron nan ze fad'a miki ba dae_dae ba akan yana so ya tafi wani garin da matar sa? Idan ma hakan ne yadda nake tunani ae tsayayyen namiji ne bana tunanin wani abun ze sanya shi chanja zancen sa. Abin da nake so da ke ki gane Ayrah wani abun ko da an miki ba se kin nuna kin gani ba, wani abun dan a zauna lafiya ake nuna ba'a gani ba, musamman kuma kishiya, dole se kin san yadda zaki zauna da ita, ba dan ta fad'i abu baki tabbatar da gaskiyar sa ba ki hukunta mijin ki akan hakan ba, dan haka ina so ki fara bincikawa ki tabbatar duk da ko kin tabbatar d'in bana so ki zama mace mara fahimta" se da Umman ta kae k'arshen maganar ta sannan ta sake d'aga ido ta kalle ta cike da jin dad'in maganganun Umman, tabbas ta ji matuk'ar dad'in kalaman Umman, ta kuma ji sanyi mara misaltuwa. "Toh Umma" shine abin da ta fad'a a sanyaye. "Amma shine da na tambaye ki kika ce babu wata matsala?" se ta d'an soma kame_kame, "Ae Umma.." murmushi Umma tayi kana tace "Ya isa haka, hakan da kika yi yayi kyau, dama ba kowanne abu ne se kin sanar da ni ba, ciki ba anyi shi ne kawae dan abinci ba, akwae wani abun da zaki dinga 6oyewa a cikin sa amma ba abin da kika san akwae cutarwa a cikin sa ba kin ji koh?" se ta jinjina kae tana murmushi, daga nan Umman ta cigaba da yi mata maganganu cikin hikima. ... Kallan Daddy Abbu yayi yace "Ina ganin ya kamata ka zauna ka ji abin da ya sa nake son muyi magana koh?" Daddy yace "Ba zaka gane ba ne, sauri nake yi na fita shiyasa, amma ina jin ka" gyara zama Abbu yayi kana ya sauke ajiyar zuciya yace "Ka harhad'o duk wasu takaddu ka kawo min ina so ne mu fitar wa da Abban Sadeeq kud'in sa" da mamaki Daddy ya kalli Abbu yace "Abban Sadeeq kuma? Ae bangane waye hakan ba" girgiza kae Abbu yayi dan ya san sarae Daddyn ya gane wa yake nufi amma dan ya sake gane wanda yake nufi d'in ya sanya shi fad'in "Kada kace min ka manta da kud'in waye muka fara gina kan mu?" Tsayawa Daddy yayi yana kallan Abbu sosae, kafin cikin er rud'ewa yace "Na.. Na gane mana" "Toh shi nake nufi, na had'u da shi, kuma na nemi yafiyar sa ya kuma yafe, abin da ya rage kawae maeda masa da kud'in sa" Abbu ya fad'a yana kallan Daddyn Muneerah "Wae wanene ya chanja ka ne cikin k'ank'anin lokaci haka? Waye yayi maka nasiha haka? Shi da kan sa yace ka maeda masa kud'in sa?" Daddy ya tambaya cike da mamakin Abbun. Murmushi Abbu yayi yana girgiza kae kafin yace "Ko d'aya, da ka san irin rayuwar da mutumin nan ke ciki se ka tausaya masa, da kasan irin yadda suke rayuwa se ka tausaya masa, shin ka kuwa san 'ya'yan sa makarantun gwamnati suka yi? Alhalin mu na mu 'ya'yan sun yi makarantu masu tsada, bama su kad'ae ba har wanda ke kusa damu bamu bari yayi makaranta mara kyau ba, yanzu duk wannan be isa abin da ze sa mu shiga taetayin mu ba? Mu gane illar abin da muka aekata ba?" shiru Daddy yayi na en wasu lokuta, kamar ba zece komae ba se kuma ya mik'e yana fad'in "Shikenan, zan yi tunani" be jira Abbu yace komae ba ya fice daga d'akin, bin sa da kallo Abbu yayi har ya fice daga d'akin sannan ya dawo da duban sa cikin d'akin yana girgiza kae. ... Tana zaune cikin d'akin ta kan gado, takaddu ne a gaban ta na makaranta da take dubawa, haka kawae yau d'in ta tashi da kewar makarantar, hakan ne ya sanya ta fiddo ta takaddun take dubawa, se kuma su Bahijja suka fad'o mata, musamman zuwan Bahijja gidan ta da kuma dawowar su ita da su Muneerah, ashe Bahijjan ba da zuciya d'aya take tare da ita ba? Ko da yake ta wani 6angaren ma Bahijjan ta taemake su tunda ta dalilin hakan kowa ya san da zancen auren su. Marar ta data d'an murd'a mata ne ya sanya ta dafe ta tana yamutsa fuska, dama tun d'azun take jin tana d'an murd'a mata, amma bata bawa hakan muhimmanci ba musamman da ta san ba lokacin period d'in ta ba ne, amma kuma yanzun se taji har yafi d'azun ma, hakan ne ya sanya ta maeda takaddun gefe ta kwanta har lokacin hannun ta dafe da marar ta ta, ta d'an lumshe idanu ko zata samu bacci ya d'auke ta ta dena jin zafin, bata kuwa dad'e ba baccin ya d'auke ta. Washe_gari da ta tashi se taji babu ciwon hakan ne ya sanya ta watsar da al'amarin bata fad'awa ko Umma ba. _BAYAN KWANA 2_ ... Tana zaune a cikin d'akin hannun ta d'auke da Quran tana muraja'a, Umma tayi sallama cikin d'akin, se da ta kae k'arshen ayar da take kae sannan ta amsa sallamar, Umma ta k'araso cikin d'akin hannun ta d'auke da wata leda, "Umma" Ayrah ta fad'a sanda take gyara zaman ta akan gadon, k'arasowa Umma tayi tana kallan Ayrahn sosae, tace sanda ta k'araso kan gadon tun kafin ta kae ga zama, "Me yake damun ki?" ba tare da fahimtar maganar Umman ba tace "Umma lafiya ta k'alau fa" girgiza kae Umma tayi kana tace "Anya kuwa?" Umman ta fad'a tana cigaba da kallan yadda idanun Ayrahn yayi zuru-zuru. Se a lokacin ta tuna da ciwon cikin da take yawan yi me wahala wanda yake lokaci zuwa lokaci, se dae bata san har hakan ya bayyana a fuskar ta ba, amma yanzun kwata-kwata bata jin komae, garau take jin ta, hakan ne ya sanya ta sake fad'in "Aah Umma babu komae fa" ta fad'a tana d'an d'auke idanun ta daga kan Umman. Sauke numfashi Umma tayi tana matso da ledar da ta shigo da ita tace tana fito da abun da ke ciki sannan ta, "Gashi nan wannan turaruka ne na jiki,