← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 90

Sashe 27

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gudu kamar ze tashi sama. .. Akan la66an sa kawae Abba yayi sallamar dan baya jin ze iya d'aga murya sosae saboda yadda yake jin jikin sa, da kallo Umma ta bishi dashi sanda yake shigowa cikin d'akin, seta mik'e da sauri cikin mamakin yadda taga yanayin nasa ya sake chanjawa fiye da d'azun "Abban su" shine abinda ta iya furtawa tana cigaba da kallan sa, Abba ya nemi waje ya zauna amma har lokacin bece komae ba, fita Umma tayi ta d'ebo ruwa me sanyi cikin randa sannan ta koma d'akin ta mik'a masa a nutse tace "Gashi" babu musu Abban ya kar6a kofin ya sha ruwan sosae sannan ya ajiye shi yana sauke ajiyar zuciya "Don Allah ka dena d'aga hankalin ka haka nan, in dae akan wannan maganar ne nayi mata bayanin dalilin ka na hana ta auren sa" girgiza kae Abba yayi sannan yace bayan yayi murmushi me ciwo "Ba wannan kad'ae ba, yanzu fitar da nayi wae neman auren Ayrah akazo yi" "Ikon Allah.. Amma shine ka shiga damuwa haka?" Umma ta fad'a tana sake kallan Abban "Kin san wanene yazo neman auren nata?" Abba ya fad'a yana sake tuna fuskar Alhaji Maton, girgiza kae kawae Umma tayi sannan Abba yace "Alhaji Mato!" da mamaki Umma ta cigaba da kallan Abba har wajen second 30 ba tace komae ba se kuma can tace "Alhaji Mato kuma? D'an sa ko kuma shi kan sa?" "Shi dae kae.." Inji Abba "Wae Alhaji Maton dana sani Abban su?" "Ko shakka babu" Abba ya fad'a a gajarce, jinjina kae Umma ta shiga yi tana sake tuna waye Alhaji Mato, neman auren Ayrah yazo yi? Toh a'ina ma ya san ta? "Lallae mutanen duniya babu kunya" "Wallahi kuwa, ya d'auka wani banzan kud'in sa ze rud'e ni ne, in manta wane ne shi, Mutumin da be san k'addara ba, toh na d'auki 'yata kuma na bashi duk abinda ya same shi ae cewa zeyi itace" Abba ya fad'a yana sake jin takaecin Alhaji Maton "Allah ma ya kyauta Abban su" Umma ta fad'a tana sake jinjina wannan al'amari "Kamar fa har yanzu bata daena kuka ba, kije ki rarrashe ta mana" Abba ya fad'a bayan ya sake jiyo sheshshek'ar Ayrah daga cikin d'akin ta, Umma ta girgiza kae kana tace "Bar ta Abban su, bar ta tayi kukan, dole ne dama tayi, babu amfanin rarrashin yanzu dan koma nayi ba denawa za tayi ba, tun d'azun ta kasa furta komae tun bayan dana gama fad'a mata abinda Baban Raj ya aekata mana" "Allah ya kyauta" shine kawae abinda Abba ya fad'a kawae. ... A 6angaren Rk kuwa koda ya mik'e kae tsaye d'akin Abbu ya wuce yana jin yadda kan sa ya masa wani irin nauyi, haka zalika manyan k'wayar idanun nan nasa ta d'an lumshe kamar me jin bacci, ko sallama be iya yi ba ya fad'a cikin d'akin, dukan su suka kalle shi se dae babu wanda ya tanka masa har ya k'araso ya nemi waje ya zauna yana kallan su su duka, ganin basu da niyyar cewa komae ne ya sanya shi d'aga idanun sa da suka d'an lumshe yace "Abbu ko zan iya sanin dalilin ku na cewa bazan auri Ayrah ba?" yayi maganar yana jin zafin ta har cikin ran sa, dan ko maganar ma baya son furta ta dan kawae ya zama dole ne yayi ta dan sanin aenahin abinda ke faruwa, Abbu be kalle shi ba dan haka kawae yake jin kamar idan ya bari suka had'a idanu da Rk d'in nan take ze fahimto rashin gaskiyar dake tattare cikin idanun sa, Ummee tace cikin zafi "Ka tashi ka bamu waje Malam, idan kuma kana so a fad'a maka abinda ya faru ne mutuncin Baban Ayrahn ya zube a wajen ka toh se kayi magana" ta k'arashe maganar tana d'auke kan ta daga kallan sa, da sauri Abbu ya d'aga ido ya kalle ta cikin mamakin jin furucin ta, ita kam tak'i yadda ta kalli kowa dan bata so k'warin gwuiwar data tattaro su tashi a banza, da mamakin dae ya maeda idanun sa kan Ummee sannan murya a cunkushe yace "Mutunci kuma Ummee?" "Ehh mana, toh kasan abinda ya aekatawa mahaefin ka kuwa? Ina tunanin ae baka manta sanda mahaefin ka ke k'ark'ashin mahaefin Ayrah ba koh?" ta fad'a tana tsare shi da idanun ta, be iya cewa komae ba kawae ya cigaba da kallan Ummeen da lumsassun idanun sa, Ummee ta gyara zama tace "Toh duk uban aekin da mahaefin ka keyi masa cewa yake yi ze biya shi k'arshen shekara, amma da yake Abbun ka me hak'uri ne be ta6a nuna gajiyar sa ba koda kuwa a fuska ne, haka mahaefin ka ya duk'ufa yana masa aeki tuk'uru har zuwa sanda k'arshen shekarar tayi, amma kasan me mahaefin nata ya masa daga k'arshe? Guduwa yayi ba tare daya sallami Abbun kud'in aekin wahalar daya dinga masa kwana da kwanaki wata da watanni ba, ina ganin ko dan wannan abun ae yaci ace ka k'auracewa er mutumin daya yaudare ku koh?" Abba ya d'aga kae da sauri ya kalli Ummee da wani irin kallo irin kallan nan na "Meyasa zaki aekata haka?" se ita kuma ta d'auke kae bayan ta jinjina kae har lokacin fuskar ta a had'e, cigaba da kallan ta Rk yayi yana rarrabe maganar data fad'a d'in, shi sam yama kasa gane alk'iblar wannan magana "Amma kaga da yake Allah ba azzalimin bawan sa bane ae gashi nan yanzu mahaefin ka yayi arzik'in da ba'a so yayi" Ummee ta sake fad'a tana kallan Rk, lumshe idanun sa yayi yana cigaba da sauraron bugun zuciyar sa da yanayin fitar sa ya sauya cikin k'ank'anin lokaci, se a lokacin Abbu ya iya bud'e baki dan yin magana, dan shima ya tabbatar idan ba hakan suka yiwa d'an nasu ba baze ta6a hak'ura ya bar zancen ba, kuma yana ganin lokaci yayi da zasu sake yiwa tufkar hanci dan haka yace "Saboda haka ka bud'e kunnen ka da kyau kaji, ni na riga na yafewa Abban Sadeeq amma fa bazan iya had'a alak'a dashi ba.." Abbu ya fad'a yana jin maganar tasa wani banbarakwae da ita, ganin har I zuwa lokacin Rk be bud'e idanun sa ba ya sanya shi fad'in "Dan haka ina me farin cikin sanar da kae na nema maka auren er uwar ka Muneerah.. kuma an baka, yanzu abinda ya rage kawae shine tsaeda lokacin d'aurin aure!" idanun sa ya bud'e da wani irin sauri, wanda saboda jimawar da suka yi a rufe ya sanya suka sake lumshewa suka kuma chanja colour daga aenahin colour d'in su zuwa ja, wani irin kallo yake bin Abbun dashi ido cikin ido wanda shi kan sa Abbun ze iya cewa tunda yake be ta6a ganin Rk d'in ya masa irin wannan kallon ba, saboda ya sani Rk d'in yaro ne me tarbiyya da sanin ya kamata amma yau shine ke kallan sa ido cikin ido duk kuma da Abbun ma shima kallan sa yake amma hakan be sanya shi ya janye k'wayar idanun sa ba, cikin murya me kauri kuma a d'an fusace ya furta bayan ya sake k'ank'ance idanun sa "Muneerah!!?" Hhh jama'a ina tunanin kamar yanzu wasan ze soma fa, nasan kan ku ya kulle sosae toh babu damuwa ku dae kawae ku cigaba da kasancewa da alk'alami na zaku ji yanda komae ze tafi.. Mhiz Innocent..... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* *TITAN'S OF TALENT* Page 029_030 ___Kallan sa Abbu har ma da Ummeen suka yi jin yadda yayi maganar kamar ba shi ba haka zalika idanun sa sunyi jawur fuskar sa babu annuri ko kad'an "Raj!" Abbu ya kira sunan sa ganin har lokacin idanun sa na kan su ne, se a lokacin ya lumshe idanun sa zuciyar sa na wani irin tafasa, haka jijiyoyin kan sa sun firfito saboda tsananin 6acin rae, a hankali ya bud'e idanun nasa da suka sake lumshewa sannan cikin k'arfin hali ya furta "Abbu Muneerah fa kace" "Ehh ko nayi sa6o ne bansani ba?" Abbu ya fad'a yana kafe shi da idanun sa, be sake bi takan kowa ba dan a yadda yake jin ran sa na suya komae ze iya faruwa ya mik'e duk da yadda yake jin d'an jiri jiri na d'ibar sa amma haka ya fice daga d'akin, bin sa da kallo dukan su suka yi har ya fice d'in sannan Ummee ta maeda duban ta kan Abbu tace "Kaga kuwa yanayin yaron nan?" ajiyar zuciya Abbu ya sauke sannan yace "Nagani mana, 6acin ran sa ko wani abun ba shi ne ze sa mu fasa abinda muka yi niyya ba, ina ganin gwara ma ya kwantar da hankalin sa ya kar6e ta hannu biyu a matsayin mata, dan kuwa babu abinda ze hana mu d'aura musu aure idan ranar da zamu tsayar tazo" jinjina kae Ummee ta shiga yi cike da na'am da zancen Abbun sannan tace "K'warae kuwa, kuma ina ganin wannan ce kad'ae hanyar da zamu bi dan ya manta da batun waccan yarinyar" "Ni abinda ke bani mamaki ashe har yanzu Abban Sadeeq na cikin Kano amma bamu ta6a had'uwa ba?" Abbu ya fad'a cike da mamaki, murmushi Ummee tayi kana tace "Allah yana son ka ae shiyasa hakan bata ta6a kasancewa ba" .. Kae tsaye d'akin sa ya koma har lokacin zuciyar sa na masa wani irin zafi, ya kwanta kan gadon sa ringingine yana sauke wani zazzafan numfashi daga bakin sa, hannun sa ya d'ora a kan sa tunani barkatae sunk'i barin k'wak'walwar sa, abubuwa na neman cakud'e masa, ya Abbu yake so yayi da rayuwar sa? Tun farkon rayuwar sa be san wani abu wae shi bijirewa umarnin iyaye ba, se dae gashi yau sun zo masa da wani abu da yake ganin ze iya bijire musu a kan sa, Muneerahn da idanun ta ke a bud'e, wayayyiya wadda wayewar ta tayi yawa, gefe guda kuma ga Ayrah, Ayrahn da yake mutuwar so, son da be san iya adadin sa ba, se dae ga wata k'addara na neman giftawa cikin alak'ar su, meyasa Abban ta zece baze aure ta bayan shine yayiwa mahaefin sa laefi? Meyasa ze yanke wannan d'anyen hukuncin? Duk inda d'iyar sa take yasan tana can
Chapter 27 · 0% Book details