← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 90

Sashe 11

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya fad'a. Abba na komawa gida ya sanar da Umma abin alkhaerin daya same su, sosae Umman ma taji dad'i dan haka babu 6ata lokaci Abba ya gabatar da isthikara, kafin ya fara zuwa aekin kuwa sosae yaji ya kwanta masa, har ya k'agu ma ya fara aekin.. Ranar litinin kuwa Abba ya fara aekin, kuma a ranar aka fad'a masa albashin sa, duk da kud'in basu taka kara sun karya ba amma shi a wajen sa da iyalin sa sosae suka ji dad'i, suka kuma godewa Allah.. Babu 6ata lokaci k'arshen wata nayi Abba ya sanya su Ayrah a makarantar gwamnati d'an nesa da gidan su, yayi amfani da kud'in ya siya musu duk wasu kaya na buk'ata da yasan zasu buk'ace su, farin ciki a wajen Ayrah kamar zata yi mene, dan sosae tayi missing School, yadda suka samu background me kyau ya sanya yanzun abin bezo musu da wahala ba, duk da yanayi na chanji da yake tsakanin government school da private school, dan haka suka cigaba da karatun su.. Kud'in Abban gaba d'aya yake k'arewa a wajen hidimar makaranta, kud'in mota da kuma kud'in cefane dan haka akwae wani mutum da yake siyar da kayan abinci a wajen sa yake kar6ar bashin abinci duk k'arshen wata, wani watan kuma seya bashi kud'in sa ya sake kar6ar wasu, haka rayuwar tasu ta cigaba da kasancewa. Tun daga wancan lokacin Abba be sake bi takan Alhaji Mato ba dan ya riga yasan babu abinda ze saka ya sake bashi wani abun ko kuma jari, dan haka kwata kwata ma bebi ta kansa ba, ya fita harkar sa kamar yadda shima ya fita tasa. A 6angaren Ayrah kuwa zuwa lokacin tun tana zancen Raj har ta gaji ta dena yi, dan tun iyayen na biye mata har suka zo suka dena kula ta idan tayi zancen nasa, basu san me zasu ce mata akan Raj d'in ba dan kuwa a lokacin shekarun ta sunyi kad'an ta fahimci irin abinda Abbun yayi wa Abba. .. Kwanaki nata tafiya, haka watanni ma suna ta shud'ewa suka had'u suka bada shekaru, izuwa lokacin sosae hidimomi suka taru suka k'ara yiwa Abba yawa, ga kuma kullum yadda tsadar abubuwa ke k'aruwa amma kuma albashin sa kamar na da ne, ba'a k'ara musu ba ballantana su samu sauk'in yadda abubuwa ke ta tashi, k'arshen wata ne a lokacin sanda aka musu albashi, dama kuma kafin zuwan albashin ya riga ya kashe su da bashi, kae tsaye seda ya fara zuwa kasuwa ya siyowa su Ayrah sabbin Uniform, a yadda yaso ma har da jaka da takalma ze siya musu saboda yadda nasun suka tsufa amma kuma yasan idan yayi hakan zasu takura ne matuk'a, dan haka kawae daga Uniform d'in ya baro kasuwar, daga nan ya wuce ya biya wad'anda ke binsa bashi wanda bashi da yawa, ya zama na saura kud'in daya san na cefane ne kawae dana kud'in motar su Ayrahn. Wajen da yaje na k'arshe shine wajen wanda yake kar6ar kayan abinci a wajen sa, ya k'arasa da sallama yana neman waje ya zauna, amsa masa sallamar mutumin yayi sannan Abba ya d'an yi shiru yana tunanin ta inda ze fara, seya sanya hannu cikin aljihu ya d'akko kud'in daya ware wanda ze bashi, ya mik'a masa yace "Gashi.." kar6a mutumin yayi yana karkad'e hannun sa da fulawa ta 6ata, ya k'irga sannan ya kalli Abba "Wani abun za'a baka da kud'in ne?" girgiza kae Abba yayi cikin sarewa da yadda yaga mutumin kamar wanda ze bashi kayan kyauta yace "A'ah kayi hak'uri don Allah, kasan lamarin ne se a hankali, ka rik'e wannan, a bani kayan kamar yadda aka saba bani idan yaso se a d'ora akan wad'ancan" tun kafin ya kae k'arshen maganar mutumin ya fara girgiza kae, yana gamawa yace "A'ah wallahi bazan iya ba, kae ma kayi hak'uri, duk lokacin daka gama biyan bashin se kazo mu san yadda za'ayi, shine kawae alfarmar da zan iya maka" Abba ya runtse idanun sa yana jin gaba d'aya jikin sa babu dad'i, dama daga yadda yaga yanayin mutumin yasan ba lallae ya yadda da abinda yazo masa dashi d'in ba, dan haka ya mik'e yace a hankali "Toh nagode, zan kawo maka cikon kud'in In Allah ya yadda.." Abba ya fad'a yana yin gaba, mutumin ya bishi da kallo yace bayan yaja tsaki "Ayi mutum kullum cikin neman alfarma yake, na tsani irin haka wallahi" ya fad'a yana d'aura wani mae a cikin leda.. ... Da sallama Abba ya shiga gidan, Ayrah ta k'arasa ta rungume Abban tana fad'in "Abba sannu da zuwa" "Yawwah sannu Auta" ya fad'a yana sakar mata ledar hannun sa daya shigo da ita, tana shirin juyawa yace "Ina d'an kwalin kuma?" "Abba tsifa Umma ke min, yanzun na cire shi" ta fad'a tana d'an murmushi gami da shafa kanta "Toh ayi maza a gama tsifar a rufe kan" Abba ya fad'a sanda yake kallan Umma dake masa sannu da zuwa, Ayrah ta k'araso ta ajje ledar hannun ta, sannan ta tafi da d'ayar kitchen dan ko Abban be fad'a ba tasan tsarabar tace, er madaedaeciyar roba ta d'akko ta zuba mangoron nata a ciki sannan taje ta wanke shi kana ta dawo cikin parlourn dae_dae lokacin da Abba ke fad'in "Lafiya kuwa Sadeeq ke bacci da yamman nan?" "Wallahi kuwa Abban su kamar zazza6i ne a jikin sa d'azun" "Toh Subhanallahi Allah ya sawwak'e... Ga rama can ki kwad'a mana ita muci yanzun, kafin dare kuma mu san yadda za'ayi.." babu musu Umma ta mik'e ta fita daga d'akin zuwa kitchen ta gyara ramar tass ta kwad'a ta sannan ta kawowa Abba tasa kana ta zubo musu ita da Ayrah har ma da Yah Sadeeq, kallan Ayrah dake ta shan mangoron ta hankali kwance tayi ta girgiza kae tana murmushi tace "Tashi Sadeeq ya tashi haka nan yaci abinci.." da "toh" ta amsa sannan ta mik'e ta fita bayan ta wanke hannun ta ta dawo cikin d'akin, hannun ta ta saka a hankali tace "Yah Sadeeq, Yah Sadeeq.." a hankali ya shiga bud'e idanun sa da suka masa nauyi saboda wani azababben ciwon kae daya rik'e masa kae, kallan sa su duka suka yi sanda yake k'ok'arin tashi zaune kan kujerar, Yah Sadeeq ba gwanin raki bane dan haka kana ganin sa kasan da gaske rashin lafiya ce ta kama shi "Yah Sadee q baka da lafiya?" Ayrah ta fad'a tana kallan sa da idanun ta da suka yi rau rau, seya jinjina kae kawae yana lumshe idanun sa "Kayi wanka se kazo kaci abinci ko zaka ji d'adin jikin ka" Umma ta fad'a tana kallan Yah Sadeeq, seya mik'e a hankali ya fita daga d'akin hannun sa dafe da k'irjin sa ya wuce toilet d'in yayi wanka sannan ya fito.. Tare suka ci ramar cikin kwano d'aya, yana ci Umma na lura da yadda yake ta 6ata rae alamar kawae ci yake babu taste a bakin sa, wani iri da yaji a k'irjin sa ya sanya shi d'aukar ruwan da Ayrah ta kawo yanzu ta ajiye ya kafa bakin sa ya fara sha, se dae kafin ya ida shan ruwan wani irin amae ya taso masa, dan haka babu 6ata lokaci kuma cikin hanzari ya jefar da cup d'in yayi waje, aekuwa ya dinga kwara aman kamar ransa ze fita, dukkan su biyo shi suka yi wajen cike da tausayawa babu ma Ayrah data fara matse k'walla saboda tausayin d'an uwan nata "Sannu" suka dinga jefa masa sanda Umma ta taemaka masa ya tashi ta k'arasa dashi zuwa parlourn nata, Abba ya kalle ta yace "Ina ga ki shirya kawae mu wuce asibiti.." Yah Sadeeq dafe da k'irjin sa yace yana d'an girgiza kansa dan shi kad'ae yasan yadda yake ji a cikin jikin sa "Abba bacci nake ji, a bari na tashi tukunna se muje don Allah" "Abba don Allah a barshi yayi bacci" Ayrah dake rik'e da hannun Yah Sadeeq ta fad'a, jinjina kae Abba yayi kana yace "Shikenan, kayi baccin.." babu musu Yah Sadeeq ya koma ya kwanta yana lumshe idanun sa k'irjin sa na bugawa da k'arfin gaske, cikin en mintuna kad'an wani nannauyan bacci yayi awon gaba dashi, duk da kuma baccin daya d'auke shi hakan be sanya ya d'auke hannun sa dake kan k'irjin sa ba, ita kuma Ayrah na zaune gefen sa har lokacin hannun sa cikin nata tana jin tausayin d'an uwan nata rabin jikin ta......... Mhiz Innocent.... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* *TITAN'S OF TALENT* Page 009_010 ___Sosae jikin Yah Sadeeq yayi tsanani a daren ta yadda dole seda suka mik'a shi asibiti, da kud'ad'en da suka ragewa Abba a hannu dasu yayi amfani wajen bada kud'in gwaje gwaje da sauran abubuwan da ba za'a rasa ba, tashin farko aka tabbatar da Yah Sadeeq d'in na d'auke da chronic ulcer ne, ga kuma matsananincin zazza6in daya sake rufe shi a ranar, dan haka asibitin suka rik'e shi ya kwana acan d'in, magunguna sosae aka had'a masa wad'anda suka janyo k'arewar kud'in daya rage a hannun Abba tass, sosae Yah Sadeeq d'in yaji jiki ya rame dama ba wani jiki gare shi ba, kamar wanda ya shekara a kwance, seda yayi sati 1 sannan aka sallame shi, zuwa lokacin kam tuni Abba ya fara tunanin mafitar daze samar musu wadda zasu dinga samun abincin da zasu dinga ci da sauran kayan amfani na yau da kullum. Sanda suka dawo gidan ma seya zama na basu da komae na dangane da abinci, dan haka Abba beyi k'asa a gwuiwa ba ya nemi bashi a wajen ogan su na company kuma cikin ikon Allah ya bashi, da wannan kud'in suka yi amfani har zuwa k'arshen wata, sedae fa a cikin watan dama Ayrah ce kad'ae ke zuwa makaranta saboda Yah Sadeeq har lokacin be gama warkewa ba, itama kuma babu kud'in da za'a dinga bata na mota dan haka Abba da kansa ke raka Ayrahn har makaranta a k'afa sannan ya wuce company shi kuma. A cikin wannan d'an tsukun ne Ayrah tayi k'awa Zaenab a makarantar bokon nasu, wadda take cikin unguwar su d'an nesa kad'an da gidan su, sosae suka k'ulla k'awance wanda har hakan ya janyo Abba yasan mahaefin ta ya zamana
Chapter 11 · 0% Book details