← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 90

Sashe 81

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta mutu shikenan a shafe babin ta daga ita har abin cikin ta, ita kuma tazo ta bud'e sabon bakin rayuwar ta? Tuna hakan da yayi ya sanya shi furzar da zazzafar Iska daga bakin sa yana jin wani irin abu da be san menene ba ya tokare masa mak'ogaro, 6acin rae, takaeci da kuma tirr da halin Muneerah yayi. Ba tare da bi ta kan kowa ba ya d'aga k'afafun sa ya soma takawa cike da sassarfa ya fice daga d'akin. Da sauri Ummee ta mik'e dan tun d'azun take lura da yanayin sa har kuma yanzun da ya fita duk akan idanun ta "Maza bi shi, kada yaje ko ina" Abbu ya fad'a yana kallan Ummee. Jinjina kae Ummee tayi kana ta fice daga d'akin. Shi dae Yah Sadeeq har zuwa lokacin ya kasa furta komae, dan tsananin mamakin abin da ya faru yanzun. Umma kuwa tana zaune kan gadon kan Ayrah kwance akan cinyar ta tana d'an shafawa a hankali, ita bama ta san abin da ya faru yanzu a cikin d'akin ba dan kuwa gaba d'aya hankalin ta ba'a wajen yake ba, ta dad'e da fad'awa duniyar tunani. Ta sha jin abubuwan da kishiyoyi ke aekatawa akan abokan zaman su, se gashi hakan ya faru akan d'iyar ta, wadda ita kishiyar ta ta so take ma ta raba ta da duniyar gaba d'aya. Tabbas dole su d'auki mataki, ba kasancewar su marasa k'arfi ne ze sa su bar komae haka ba, ya dace su d'auki mataki akan abin da ya faru d'in duk da Allah ya tak'aeta, se dae ba'a san nan gaba kuma da abin da zata zo da shi ba Allah ya kiyaye, ba'a san nan gaba me zata yi mata ba, dan haka ko da zasu cigaba da zama ne a k'ark'ashin Rk bata tunanin zata kuma barin d'iyar ta su zauna gida d'aya da matar da bata da imani, wadda zuciyar ta ta kasance kamar ta kafirae, babu komae a ran ta se mugunta da kishin ta na hauka wanda ke k'ok'arin kae ta ya baro ta. Yanzu ba dan Allah ya tak'aeta ba da yanzu ba wannan zancen ake ba, kenan se dae su zauna suyi zaman makokin Ayrahn watak'ila ma har da Muneerahn ba tare da sun san cewar itace ta kashe ta ba. "Ya Salaam" Umma ta fad'a a hankali tana sake jin yanda zuciyar ta ta karye. Da sauri Umma ta cigaba da bin sa ganin yadda yake cigaba da tafiya da sauri_sauri, ganin dae ta kasa kamo shi ya sanya ta bud'e baki tace "Raj!" Kamar daga sama ya jiyo muryar Ummeen na kiran sa, ya dakata a inda yake yana runtse idanun sa lokaci d'aya kuma ya bud'e. K'arasowa Ummee tayi ta kalli yanayin fuskar sa dake a d'inke tsaff kamar wanda be ta6a dariya ba, dama ya aka cika bare an masa wani abun? Cikin kwantar da murya tace "Kayi hak'uri tukunna, kada kaje kace zaka yanke hukunci cikin gaggawa kuma cikin 6acin rae, saboda haka ka wuce mu koma ka fara samu zuciyar ka ta d'an yi sanyi sannan se kaje koma ina ne." Kallan Ummeen kawae yayi da idanun sa da suka yi ja kamar mara lafiya, gaskiya Ummee ta fad'a amma ya san ko menene, zuciyar sa ba zata ta6a yin sanyi ba in dae har beje ya aekata abin da yayi niyya ba, hakan ne ya sanya shi bud'e baki yace "Ummee!" Hannun sa Ummee ta kamo tace "Mu je, kayi hak'uri zuwa anjima" Kamar yace wani abu, amma se yayi shiru kawae, haka Ummee ta ja shi suka cigaba da tafiya, kae tsaye Office d'in sa suka wuce. ... Da sauri Mummy ta mik'e tana kallan Muneerah da ta shigo afujajan kamar wadda aka koro, ta rik'o ta da sauri tana fad'in "Ke lafiya, meya faru?" Kuka ta fashe dashi tana fad'in "Mummy mun shiga 3, Mun shiga 3 Mummy ta farfad'o fa" K'irjin Mummy ne ya buga lokaci d'aya tana d'aga ido ta dubi Daddy dake zaune kujerar dake kallan wadda suke tsaye a kusa da ita. Da kallan tuhuma ya bi su su dukan su, kafin yace "Meya faru? Wace ce ta farfad'o?" Ba tare da bi ta kan maganar sa ba Mummy tace tana kallan Muneerah "Maza tashi ki wuce d'aki, yanzun nan zan shigo" Babu musu Muneerah ta wuce d'akin, dan itama bata san da zaman Daddy a d'akin ba. Bin ta da kallo Daddy yayi a ran sa yana tsara lallae akwae abin da suka shuka, kuma basa son a sani, se dae be san menene ba, hakan ne ya sanya shi kallan Mummy yace "Zaki fad'a min abin da ya faru ne ko kuma na d'auki waya na kira mijin na ta?" ya tambaya yana tsare ta da idanu. Cikin kumfar baki Mummy ta soma fad'in "Amma dae a gaban ka yarinyar nan ta shigo koh? Kamar yadda baka san abin da ya dawo da ita ba haka nima ban sani ba." Be sake bi ta kan ta ba ya zaro wayar sa daga cikin aljihu ya danna kiran number Rk. Da sauri Mummy ta matso tace "A'ah me kuma zaka yi?" kamar ba zece komae ba se kuma yace "Ki je kawae, zamu yi maganar anjima.." Katsar nunfashin sa tayi ta hanyar fad'in "A'ah don Allah kada ka kira shi, be wuce wata er hatsaniya ce ta had'a su ba, ka san halin Muneerah kuma may be shiyasa ta taho gida kawae" "Toh" shi ne abin da Daddy yace kawae, abin da ya fusata Mummy kenan ta shak'a sosae, kawae se ta wuce daga wajen zuwa d'akin da Muneerah ta shiga. Sake kiran layin Rk Daddy yayi a karo na barkatae, cikin sa'a memakon ce masa da take yi ba zata shiga ba yanzun se ta shiga, ya kara wayar a kunnen sa yana jiran d'agawar Rk d'in. .. A can 6angaren kuwa Abbu da ya d'aga wayar ne yace "Hello" Da mamaki Daddy yace "A'ah, wae kae ne? Ina Raj d'in?" "Yana nan k'alau.." "Toh kenan menene ya faru Muneerah ta dawo gida?" Daddy ya tambaya "Zaria ta taho?" Abbu ya fad'a da mamaki dan dae Rk d'in be sanar dasu akwae inda zata je ba. "Ehh shigowar ta kenan tana kuka, ban san abin da ya faru ba" Ajiyar zuciya Abbu ya sauke kamin ya soma fad'in "Wato wani abu ne ya faru mara dad'in ji.." Daga nan Abbun ya shiga fad'awa Daddy abin da ya faru, dan wannan d'in babban abu ne, da k'arami ne shi da kan sa zeyi k'ok'ari wajen ganin an magance matsalar ba tare da sanin Daddyn ba, se dae da yake itama ta san ta aekata laefi da kan ta ta kae kan ta gida. Shiru ne ya wanzu na en wasu lokuta bayan da Daddy ya gama jin abin da Muneerahn ta aekata, dana sani gami da takaeci ya lullu6e shi, ace wae er cikin sa ke k'ok'arin yin kisa? Kisan ma na matar mijin ta? jin shirun ne ya sanya Abbu fad'in "Kuma bana fad'a maka bane dan ka d'auki hukunci da kan ka ba, saboda haka ba'a ce ka d'auki hukunci ba ka bar komae a hannu na zan yi abin da ya dace" Har zuwa lokacin da Abbu ya gama magana Daddy bece komae ba, dan shi kam gaba d'aya ya rasa ma me zece, ya kasa bud'e baki yayi magana, toh ya bud'e d'in ma yace menene? Ya bud'e baki ya kare er sa ne akan abin da tayi? Ko kuwa ya bud'e ya bawa yarinyar hak'uri da iyayen ta? Lallae Muneerah ta bashi kunya, ta shayar da shi mamakin da be ta6a tsammani ba. .. Kallan Abbu da ya ajiye waya Rk yayi yace a nutse se dae a kausashe "Abbu ku ne kuka aura min Muneerah, ba dan nace muku ina son ta ba, ba dan na ta6a cewa ina son ta ba, na kar6i auren ta, na kuma zauna da ita dan nayi muku biyayya, nayi k'ok'arin yin adalci tsakanin ta da Ayrah, na kuma soma tirsasawa zuciya ta soma k'aunar ta, se dae a halin yanzu Abbu bana tunanin zan iya cigaba da zama da Muneerah bayan k'ok'arin hallaka Ayrah da tayi da kuma abin da ke cikin ta!!" Ummee da Abbu kallan sa suka yi sosae cikin mamakin abin da ya fad'a, kasa shiru Ummee tayi har seda ta furta, "Me kake fad'a? Kana nufin a lokacin da ta jefa ta ruwan tana d'auke da juna biyu?" Se kuma a lokacin ya d'an ji wani abu me kama da kunya ya kama shi, yadda ya manta ma sam da wad'anda yake tare se yanzun, amma tunda ya riga ya fad'a gwara kawae ya k'arasa maganar, hakan ne ya sanya shi jinjina kae. Cikin tsananin farin ciki se dae da er fargaba Ummee tace "Ya lafiyar Babyn toh? Bayan faruwar wannan al'amarin?" "Alhamdulillah, babu wata matsala se dae da wani abun ya same ta ya kan iya shafar abin da ke cikin na ta." Ajiyar zuciya Ummee ta sauke tana fad'in "Toh Masha Allah" Tun d'azun da ya fara magana Abbu bece komae ba dan gaba d'aya jikin sa ya gama yin sanyi da al'amarin Muneerah, se a lokacin ya bud'e baki yana k'ok'arin magana wayar Rk dake hannun sa ta d'auki ruri, ya kalli me kiran sannan ya d'aga. "Ina son magana da Raj" Shi ne abin da Daddy ya fad'a bayan Abbu ya d'aga wayar. Babu 6ata lokaci Abbu ya ajje wayar a kusa da Rk kana ya sanya ta a handsfree, ya kalli Rk ya jinjina masa kae cike da bashi k'warin gwuiwa. A hankali yace "Hello Daddy!" "Na'am kana ji na?" Daddy ya fad'a, a hankalin dae ya sake fad'in "Ehh" "Ka yanke hukuncin da zaka yi wa Muneerah ne?" Da mamaki Rk ya d'aga ido ya kalli Abbu sannan ya maeda kan wayar kamar me kallan Daddy a ciki yace "A'ah Daddy.." Se da Daddy ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "Toh yanzun nan ba se anjima ba ina so ka turo min da takaddar ta." Cike da mamaki ya sake kallan number dake yawo akan wayar, anya kuwa da gaske Daddyn ne? Daddyn Muneerahn ne ke fad'in ya turo da
Chapter 81 · 0% Book details