Sashe 29
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tsakar gidan tana hange, babu kowa a tsakar gidan taji dad'in hakan dan bata so ta sake 6atawa Abba ko Umma rae daga dawowar ta jiya bayan 6acin ran data saka musu a jiyan, a hankali ta shiga takawa cikin tsakar gidan har zuwa sanda ta fice daga cikin gidan... ... Wanda ke driving d'in ya kalli Muttala yace "Nifa na gaji wallahi, tun jiya muke a wajen nan amma har yanzu banga alamar zata fito ba" tsaki Muttala yaja kana yace "Gaggawar ta menene? Wallahi idan ta nine bank'i mu sake kwana cikin motar nan ba tunda dae babu wanda ya ganmu har yanzun" Muttala ya fad'a har lokacin idanun sa na kan k'ofar gidan su Ayrah.. A dae_dae lokacin ne Ayrah ta fito daga cikin gidan, a hankali ta shiga bud'e manyan idanun ta dan hango inda motar sa take. A lokacin ne shi kuma kiran Abbu ya shigo wayar sa, seya d'auki wayar yana karawa a kunnen sa idanun sa a lumshe dan yanzu kuma be san da wanne Abbun yazo ba gashi kuma rok'on da yayi wa Ayrah baya tunanin taji ta kar6a zata fito, se abin ya sake masa yawa, daga can 6angaren Abbu yace "Ka shiga asibitin ne?" shiru yayi na d'an wani lokaci kafin a hankali ya bud'e bakin sa bayan ya kae hannu ya shafa kwantaccen sajen dake kwance luff luff akan fuskar sa "Abbu ban shiga ba tukunna" shiru Abbu yayi yana sake karanto yanayin Rk d'in daga cikin muryar sa, yace a hankali "Ko dae akan maganar dana maka jiya ce?" shiru yayi dan ko ya bud'e bakin sama be san abinda zece ba, Abbu yace "Toh ka bud'e kunnen ka da kyau kaji, in dae akan maganar nan ce ka kwantar da hankalin ka kamar an riga an d'aura muku aure ne da Muneerah, dan haka ina ganin ka ajje komae a gefe ka koma bakin aekin ka" kafin yace komae Abbun ya katse wayar, seya jefar da wayar yana sake jin yadda yanayin nasa yake sake ta'azzara, abubuwa na neman yiwa zuciya da k'wak'walwar sa yawa. A hankali ta cigaba da takawa har lokacin fuskar ta babu walwala manyan fararen idanun nan nata sun yi zuru zuru kamar mara lafiya, da sauri wanda ke driving cikin motar ya bud'e k'ofa ya fita yayin da Muttala ya koma mazaunin driver, seda ya kalli cikin layin ya tabbatar babu kowa sannan ya k'arasa inda Ayrah take, ita sam hankalin ta be kae kan sa ba yana kan motar Rk da take kalla dan tabbatar da tasan ce, beyi wata wata ba ya matsa bayan ta ya shak'a mata wani abu dake jikin handkerchief d'in hannun sa, lumshe idanun ta tayi tana jin wani irin yanayi cikin kan ta kafin a hankali ta kae hannun ta tana shirin dafe kan ta, take wani jiri ya d'ebe ta cikin sakannin da basu wuce 10 ba ta fice a hayyacin ta se kawae tayi baya zata fad'i mutumin ya saka hannun sa ya tare ta ya jata zuwa cikin motar har lokacin yana d'an juyawa bayan sa dan tabbatar da babu wanda ya gan shi, dae_dae lokacin da yake k'ok'arin k'arasa shigewa da ita cikin motar Rk ya bud'e idanun sa daga lumshe sun da yayi tun d'azun, kamar ance ya kalli wajen se kawae ya hange ta jikin wani mutum yana cusa ta cikin mota, seya sake rufe idon ya bud'e dan tabbatar da abinda ya gani d'in gaskiya ne ko kuwa idanun sa ke masa gizo, cikin wani irin zafin nama ya tura k'ofar side d'in da yake yana shirin fita zuciyar sa na wani irin zafi tana cigaba da harbawa kamar zata faso k'irjin sa, Muttala yaja motar da k'arfin gaske tun kafin ma mutumin ya gama saka Ayrahn cikin motar, seya koma da sauri zuciyar sa na bugawa yama kasa tunanin komae kawae ya figi motar da wani irin gudun da tunda yake ze iya cewa be ta6a yin irin sa ba, sosae su Muttala suke gudu kamar zasu tashi sama yayin da shima ya cigaba da bin su, kawae burin sa ya san inda zasu je, ina zasu kae ta? Me zasu mata? Meyasa suka d'auke ta? Kwata kwata tunanin sa be kae ya kira police ya sanar dasu ba kawae shi dae burin sa ya cim masu. Sosae suka cigaba da tafiya kuma inda Allah ya taemake su kwata kwata basu samu traffic jam ba, mamaki ya sake kama shi ganin se tafiya suke yi kamar baza su dena ba, har lokacin kuma bugun da zuciyar sa take be ragu ba, haka ya cigaba da bin su zuwa lokacin da yaga sun fara barin gari suna shiga cikin wani waje daya fi masa kama da k'auye, mamaki ya sake kama shi amma da yake baya so su gane akwae wanda ke bin su seya dakata har zuwa sanda suka masa nisa sannan ya cigaba da bin su a nutse yana yi yana lumshe idanun sa saboda yadda yake jin jikin sa ya masa wani iri ga yadda bugun zuciyar sa ke ta k'aruwa. Dae-dae wani madaedaecin gida ya hango su sun yi parking d'in motar su, ze iya cewa tunda suka shigo k'auyen bega gida me kyan sa ba dan kuwa duk gidajen k'asa ne yayin da wannan d'in ya kasance ginin bulo ne, Muttala ya fita ya bud'e k'ofar gidan da mukullin hannun sa sannan ya dawo ya tashi motar zuwa cikin gidan kana ya saka mukulli jikin gate d'in sannan ya sauke ajiyar zuciya "Da alama mun tsira fa" ya fad'a yana fesar da iska daga bakin sa, mutumin da shima ya fito daga cikin motar yace "Wallahi kuwa, kayi maza ka kira mana Alhaji ka sanar dashi mun gama aekin mu" murmushi Muttala yayi kana ya fito da wayar sa ya lalubo number Alhaji Mato, tun kafin Alhaji Mato yace komae Muttala yace "Yalla6ae albishirin ka?" daga inda Alhaji Mato yake ya saki wani murmushin jin dad'i yana shafa tumbin sa, ko Muttalan be fad'a ba yasan sun yi nasara, amma saboda ya sake tabbatar wa ya sanya shi fad'in "Goro.." "Mun gama aekin mu, yanzu haka gamu a cikin gidan yalla6ae" "Weldone, ku jira ni yanzu zan taho.." Alhaji Mato ya fad'a yana jin wani irin dad'i na ratsa shi, yasan tabbas yau d'in Ayrah zata kwana ne a matsayin matar sa, baya shakkar wannan tunda dae an riga da an samo masa ita. .... A 6angaren Ummee kuwa ganin har bayan wajen awa d'aya Ayrahn bata fito ba seta mik'e ta sake komawa d'akin nata, gwara ta rarrashe tan kawae ko zata samu ta saki ran ta ta cigaba da harkokin ta, a hankali ta yaye labulen d'akin idanun ta kan gadon data san akae zata sami Ayrahn, se dae ga mamakin ta babu kowa kan gadon babu ma alamar akwae mutum cikin d'akin, sauke labulen tayi a ran ta tana ayyana babu mamaki tana cikin toilet, se kuma kwanyar ta ta tuna mata ae yanzun ta fito daga ban d'akin, dan saboda ta tabbatar da gasken bata cikin band'akin ya sanya ta k'arasa toilet d'in, k'ofar sa a bud'e take amma duk da haka seda ta shiga ta duba bata ga kowa ba, k'irjin ta ya buga tana tuna yadda suka rabu da Ayrahn jiya, kada dae halin en yau zata nuna musu? Kada dae ace d'iyar ta ta ta chanja hali bata sani ba? Kada dae ace d'iyar ta ta ta za6i d'a namiji akan su? Tsara hakan cikin ran ta yasa ta sake jin jikin ta yayi mugun sanyi, a hankali taja k'afafun ta zuwa d'akin Abba, Abba ya kalle ta da mamaki ganin yanayin ta yace a hankali "Lafiya kuwa Ruk'ayyah?" "Bana tunanin haka" Umma ta fad'a tana jin wasu zafafan k'walla na zubo mata "Subhanallahi, meya faru?" Umma bata tabbatar ba dan haka a ran ta taji gwara ta bari ta sake tabbatarwa ko fita tayi ta siyo wani abun dan haka seta furta "Babu komae" "Ya zaki ce babu komae kuma? Bayan kin fita lafiya, yanzu kuma kin dawo kina kuka?" "Babu komae" ta sake fad'a tana cigaba da share k'wallar dake ta zubar mata. Wasa_wasa se gashi Ayrah har wajen azahar babu ita babu labarin ta zuwa lokacin tuni Umma ta gama na'am da abinda take zargi "Ina yarinyar nan ne? Ko har yanzu baccin take?" Abba ya fad'a yana kallan Umma, kawae seta fashe da kuka tana jin wani iri a cikin zuciyar ta, a yau d'aya tana jin kamar tayi danasanin haehuwar Ayrah amma ta kasa, amma duk da haka yarinyar ta shammace ta, ta shammace ta aenun, bata ta6a tunanin hakan daga gare ta ba "Abban su yarinyar nan ina tunanin ta gudu da wancan yaron, ashe shiyasa ta kasa ce min komae tunda taji abinda ya faru, ashe tace kya yi kya gama bazan rabu da shi ba, Abban su yarinyar nan ta bani mamaki" dafe saetin zuciyar sa Abba yayi yadda yaji ya wani irin buga, seya shiga tari, saboda tsananin tashin hankali babu wanda ya iya kula shi, seda Yah Sadeeq ya dawo daga shocking d'in da maganar Umman ta shigar dashi sannan ya d'auki ruwan gaban sa ya mik'awa Abba, kar6a Abba yayi ya sha kana ya koma sauke ajiyar zuciya, kafin ya d'ago ya kalli Umma da har lokacin take share hawaye a fuskar ta "Waye ya fad'a miki hakan?" "Tun d'azu na neme ta na rasa cikin gidan nan Abban su, ko ka ta6a ganin Ayrah ta fita babu izinin wani a cikin mu? Abban su yau nayi nadama.." "Ya isa haka Ruk'ayyah" Abba ya fad'a yana d'aga mata hannu "Bar ta taje, in dae bijirewa umarnin iyaye ne taje gata ga duniyar, kada muyi mata baki saboda ni uba ne ke kuma uwa ce kada ya kama ta, amma ni kae na yau Ayrah ta wulak'antani a rayuwa.." kallan su kawae Yah Sadeeq yake yi ya kasa cewa komae, ya kasa koda bud'e bakin sa ne ya furta wani abu, dan maganar ta shige shi, bashi da bakin da ze iya k'arya ta wannan maganar ko kuma ya musa, toh idan ya musa d'in mene hujjar sa ta yin hakan? Meze kawo a matsayin hujjar