← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 90

Sashe 45

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fusace tana shirin shigewa cikin d'aki Umma ta rik'o ta "Ki tsaya tukunnah" ba dan taso ba haka ta zauna d'in har lokacin kan ta na kan cinyar Umma kuma har zuwa lokacin zafin da zuciyar ta ke mata be ragu ba, haka zalika ji take kamar tayi ta kukan kar ta dena, sam bata san kuma meya shigo dashi cikin gidan ba, me yake nufin zece mata ta yadda dashi? "Ina jin ka Allah yasa lafiya" Abba ya fad'a bayan ya zauna akan tabarmar dake shimfid'e a tsakar gidan, seda ya d'an yi shiru kad'an kana ya saci kallan inda Ayrah ke zaune sannan yace "Abba dama akan maganar aure ne da nayi yau d'in nan, naso na yiwa Ayrah bayani se dae tak'i fahimta ta, Abbu be san da maganar aure na da ita ba shiyasa, kuma dama tun farko yana da burin aura min ita kasancewar er k'anin sa ce, se kuma yanzu Allah yayi za'a yi auren amma sam bani da laefi Abba" ya k'are maganar a maraeraece dan yana da tabbacin Ayrahn na jin sa, ajiye numfashi Abba yayi sannan yace "Ikon Allah, dama namiji ba dan mace d'aya akayi shi ba, kuma hakan ya sake nuna min kae d'in yaro ne me biyayya, dan haka ka tashi kaje Allah yayi maka albarka.. Ke kuma Ayrah ki tashi ki bi mijin ki dan banga amfanin zaman naki cikin gida bayan da auren ki ba" ya k'are maganar yana kallan Ayrah, da sauri ta d'aga narkakkun idanun ta ta sauke su kan Abban da yayi magana, ita kan ta Umma tayi mamakin maganar Abban, amma shi kam da yayi maganar da alama ko a jikin sa "Abban su.." Umma ta fad'a tana cigaba da kallan sa "Babu damuwa, ta tashi ta bishi d'in" shine abinda Abban ya sake fad'a, ajiyar zuciya Umma ta sauke sannan ta kalli Ayrah dake girgiza kae kamar k'adangaruwa cikin kuka tace "Abba don Allah ka bar ni a gidan nan kaaji" dama saboda hakan Abban yace tabi mijin ta, dan kuwa yasan idan ba yanzun ba nan gaba ma se gwagwarmayar tafi hakan dan haka ya kalle ta yace "Babu komae kinji, ki tashi kije.. Zamu yi komae daga baya" ita sam ba fahimtar Abban take yi ba dan kuwa kishi ya riga ya gama rufe mata ido, duk kuwa da irin bayanin da yayi ita har yanzun bata gamsu ba, kawae ji take yi kamar yaudarar ta yayi. Umma ce ta mik'e ta fad'a cikin d'aki ta shiga had'awa Autar ta ta kayan da tasan zata yi amfani dasu ko kuma ta buk'ata kafin komae ya daedaeta sannan ta fito har ran ta tana jin babu dad'i, a yadda ta bar ta a tsakar gidan a haka ta same ta, zaune ta d'ora kan ta akan k'afar ta tana sheshshek'ar kuka, seda ta fito d'in sannan Abba ya kalli Rk "Ku tashi kuje Allah yayi muku albarka, In Sha Allah zan neme ka ko ta layin Sadeeq ne" sosae yaji dad'in abinda Abban yayi dan haka yace "Nagode sosae Abba, Allah ya k'ara girma" "Ameen" d'ago da fuskar Ayrah Umma tayi tana kallan yanda fuskar ta tayi kace_kace da hawaye, seta girgiza kae tana jin tun yanzu har kewa ta fara kama ta "Kukan ya isa haka Ayrah, ki tashi kije zamu yi waya Uhmm?" Umma ta fad'a cikin rarrashi, tausayin Ayrahn na kamata yanda take yarinya da ita amma yanzu haka tana da kishiya wadda za'a kira da Amaryar mijin ta, d'aga ido tayi ta kalli Umma, tana shirin fara magana Umma ta girgiza kae tana murmushin yak'e "Ya isa haka ki tashi ki je kin ji?" sam bata so wani 6acin ran ya sake shiga tsakanin ta da iyayen nata dan haka ta mik'e tana jin jiri na d'ibar ta "Allah ya tsare Auta" shine abinda Abba ya fad'a sanda take shirin gifta inda yake zaune, bata iya amsawa ba dan ita kad'ae tasan yadda take ji a cikin zuciyar ta, shine ya d'auki kayan sannan yayi gaba ita kuma ta rufa masa baya, suna fita kuwa Umma ta mik'e da sauri ta shige cikin d'aki saboda kukan da taji ya taho mata, bin ta da kallo Abba yayi sannan ya dawo da kallan sa tsakar gidan da murmushi kan fuskar sa gami da girgiza kae. A hankali take takawa kamar mara laka zuwa wajen motar tasa, shi ya saka hannu ya bud'e mata, yanzu kam babu musu ta shiga sannan ya zagaya driver seat ya shiga ya zauna, kallan ta yayi yanda yaga tana ta curewa waje d'aya kamar me jin sanyi lokaci d'aya kuma tana matsar k'walla, lumshe idanun sa yayi a ran sa yana sak'a gwara ya bar ta tayi kukan dan yasan kuka dole ne musamman gare ta data shak'u da iyayen ta haka, bugu da k'ari kuma ga wannan maganar da itama ta sake tada mata da hankali. ... A cikin wani k'ayataccen Hotel yayi parking, a nutse ya juya ya kalli inda take kwance kan kujerar tayi shiru kamar me tunani, haka kawae yaji wani tausayin ta ya lullu6e shi, ya lumshe idanu lokaci d'aya wani haushi na taso masa tunawar da yayi yanzu haka akwae auran wata a kan sa "Ayrah!" ya fad'a a nutse kuma cikin tausashshiyar murya, a hankali ta bud'e lumsassun idanun ta ta watsa su a kan sa wanda har seda hakan ya sanya shi lumshe idanun sa, se kuma data ga hakan sannan tayi maza ya janye nata idanun tana iya bakin k'ok'arin ta wajen ganin ta dena ganin laefin sa albarkacin maganar daya fad'awa Abba cewar bashi ita akayi amma har zuwa lokacin ta kasa, ta kuma k'i dena ganin laefin sa, se dae an samu ragin kaso me d'an yawa daga laefin sa data fara gani a farko. "Ki goge idanun ki pls, zamu sauka.." ya fad'a yana mik'a mata handkerchief d'in hannun sa, kamar ba zata kar6a ba se kuma a hankali ta saka hannun ta ta kar6a kana ta goge hawayen da ba dan kan ta suke fitowa ba da kan su kawae suke fitowa. Seda suka k'ara wajen minti 2 a haka sannan ya fita ya bud'e mata k'ofa ta fito kana ya koma ya d'auki kayan ta sannan suka wuce, yana gaba tana bin sa a baya kamar wata mara laka saboda yanda tafiyar ta ta ta k'ara sanyi, be damu da hakan ba ya cigaba da tafiya har zuwa sanda ya gama komae ya kar6i mukulli sannan suka wuce cikin d'akin. Madaedaecin bedroom ne me d'auke da babban gado, wardrobe da kuma mirror da sauran abubuwa dae da aka san bedroom na d'auke da, a hankali ya saci kallan yanda ta tsaya daga k'ofar wajen kamar me tsoron wani abun, bece mata komae ba ya k'arasa ya ajje jakar hannun sa sannan ya dawo cikin d'akin, tana nan dae inda ya bar ta, ya kalle ta bayan ya karyar da kae yace "Don Allah ki shigo ki zauna" ba tace komae ba kuma bata motsa daga inda take ba, a hankali ya sanya hannun sa d'aya saman goshin sa ya murza kana ya juya, wayar sa ya ajje kan k'aramar kujerar d'akin sannan ya soma takawa da niyyar juyawa, kamar jira wayar take ya ajiye ta ta soma ringing, kamar wadda aka tsikara ko kuma ake ja ta sauke idanun ta akan wayar "Muneerah!" taga ya bayyana akan wayar, dama kukan be ishe ta ba dan haka nan take idanun ta suka sake tara k'walla, dawowa yayi da baya dae_dae lokacin da kiran ya katse, ya k'araso ya d'auki wayar yana kallan kiran waye? Ganin me kiran ya sanya shi d'aga kae ya kalli Ayrah dake tsaye yanayin ta ya sake chanjawa daga d'azun, bata iya kallan fuskar sa ba se cigaba da rik'e kukan daya taho mata take yi, idan har bata man ta ba waccan d'in da aka d'aura musu aure ae sunan ta Muneerah, d'an runtse idanun sa yayi kafin ya ajje wayar inda ya d'auka sannan ya k'araso inda take beyi wata wata ba ya saka hannu ya d'aga ta gaba d'ayan ta ya d'auke ta kamar Baby, da sauri ta fara hantsilawa da niyyar sauka amma be sauke ta ba har seda ya k'arasa kan gado ya zauna sannan ya jata zuwa cikin jikin sa, kamar jira take yi kuwa ta saki kukan data kasa rik'ewa "Oh god" ya fad'a yana lumshe idanun sa, meyasa ita kuka baya mata kad'an ne? Yana jin ta sanda take cigaba da kukan, shiru yayi yana cigaba da saurarar ta ko zata yi shiru, da yaga dae bata da niyyar yin shirun seya d'auki hannayen sa duka biyun ya d'ago kan ta dake kwance male_male akan k'irjin sa, ya gaji da jin kukan nan na ta, d'an mitsitsin bakin ta red colour kamar wanda aka sakawa jan baki yabi da kallo yanda take motsa shi, ya d'an sake lumshe idanun sa sannan babu 6ata lokaci ya kama bakin nata cikin bakin sa, lokaci d'aya kukan nata ya tsaya saboda yanda taji bak'on al'amarin da tunda take bata ta6a ji ba, cikin sauri ta bud'e idanun ta a razane k'irjin ta na bugawa jin kukan nata yak'i cigaba da fita, fahimtar abinda ke faruwa ya sanya ta soma janye bakin ta da k'arfi lokaci d'aya kuma tana k'ok'arin tashi daga jikin sa cike da tsoro, sam be kula ta ba sema sake rik'o ta da yayi gam cikin jikin sa ya shiga kissing nata a hankali cike da matsananciyar k'aunar ta, idanun sa a lumshe haka zalika yana sake cigaba da shigar da ita cikin jikin sa, kuma yana cigaba da kokawa da numfashin sa daya soma chanjawa, ya d'auki wajen minti 1 yana kissing nata zuwa lokacin jikin sa ya gama yin sanyi, wani bak'on al'amari ya soma ziyartar gangar jikin sa, yanda ya d'an sassauta rik'e bakin nata ne yasa tayi amfani da wannan damar ta k'wace lips d'in ta tana jin yadda k'irjin ta ya cigaba da bugawa, ajiyar zuciya ya sauke sanda ta cire bakin nata daga cikin nasa har lokacin idanun sa na a lumshe ne, hannu ta saka ta dafe bakin ta da kuma iya k'arfin ta ta soma k'ok'arin mik'ewa tana ajje
Chapter 45 · 0% Book details