← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 90

Sashe 57

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

duk dan ta farantawa d'an uwan na ta. A karo na barkatae ta sake mik'ewa dan tunawa da tayi akwae wani abun da take da shi wanda bata kawo masa ba Yah Sadeeq yace "Yi hak'uri Ayrah, ina zan kae wad'annan abubuwan haka?" tura baki tayi sannan tace "Kae Yah Sadeeq cikin ka mana" tayi maganar tana shirin tafiya, se yayi murmushi kana yace cike da tsokana "Lallae fa su Auta masu gida" dariya tayi tana komawa ta zauna saboda yadda Yah Sadeeq d'in yayi magana ya bata kunya, nan ta zauna ta d'an soma taya shi hira, suna yi yana d'an ta6a abinda ta kawo masa kasancewar safiya ce, babu laefi sun d'an ta6a hira ta en uwantaka zuwa can ya mik'e, kallan sa tayi fuskar ta a narke "Yah Sadeeq naga ka mik'e?" tayi maganar kamar zata fashe da kuka "Tafiya mana Ayrah, kin san yanzun nima zan dinga zuwa ina taya Abba zaman shago ne, kin san an kuma samun cigaba" ya k'are maganar yana murmushi, maganar da yayi ce ta sanya ta sakin murmushi kana tace "Allah ya taemaka mana Yah Sadeeq, amma dae.." "Amma me? Na miki alk'awari In Sha Allah zan sake zuwa muyi hira sosae har da shi mijin naki ma" tura baki tayi kafin tace "A'ah Yah Sadeeq Allah kuwa ka cire wannan zuwan, ba kazo ba" bud'e baki yayi yana kallan ta "Ohh haka ma kika ce koh? Toh yayi!" ya fad'a yana yin gaba, biyo shi tayi tana fad'in "A'ah kazo fa" se kuma suka had'u wajen yin dariya, har bakin gate d'in ta raka shi tana ji kamar tayi kuka, kallan ta yayi a nutse yace yana karantar yanayin ta "Kin tabbatar babu wata matsala koh?" ya tambaya yana kafe ta da idanun sa "A'ah Yah Sadeeq babu fa" "Kin tabbatar?" ya sake tambaya, nan ma ta jinjina kae kafin ta d'ora da "Ehh babu" ajiyar zuciya ya sauke kana yace "Toh madallah" daga haka suka d'an sake yin magana a tsaetsaye duk da yanda jikin Ayrah yayi sanyi, ya gaeshe da Abba da Umma kuwa ta maemaeta masa sau ba adadi sannan ya tafi, shi kan sa se da yaji babu dad'i daya tafi d'in, ta gefe guda kuma yaji dad'in yanda ya gan ta cikin kwanciyar hankali. .... Bahijja ce a baya, yayin da Aunty Zeenah ke driving Muneerah na gefen ta tana sake cika tana batsewa, mintuna kad'an ne suka kae su unguwar musamman saboda gudun da Aunty Zeenahn take, sannan ta soma gangarawa zuwa cikin layin da gidan yake, a dae_dae lokacin da suka shiga cikin layin shi kuma Yah Sadeeq ya fito daga ciki, be kawo komae ba ya cigaba da takawa ya fice daga layin, babu 6ata lokaci ya tsare Napep ya sanar da shi inda ze kae shi sannan ya hau. A k'ofar gidan Aunty Zeenah tayi parking motar, ta kalli gidan sannan ta waewaya ta dubi Bahijja da har lokacin jikin ta ke a sanyaye kamar ba Bahijjan ba "Kin tabbatar nan ne?" Aunty Zeenah ta fad'a, jinjina kae Bahijja tayi kana ta bud'e baki tace "Ehh nan ne" juyowa tayi da niyyar yiwa Muneerah magana, se dae bata ankara ba se ganin Muneerahn tayi a waje, a wajen ma har ta isa k'ofar gidan, da sauri ta sanya hannu ta bud'e murfin motar itama ta fita, kafin kace menene wannan se gasu su dukan su a k'ofar gidan. Tun fitar Yah Sadeeq ta kasa motsawa daga inda take, haka kawae take jin zuciyar ta a kusa, sam bata ji dad'in tafiyar Yah Sadeeq d'in ba, amma sanin tafiyar ta sa ta zama dole yasa babu yadda ta iya se cika da tayi tayi fam kamar wadda aka yiwa wani abun, ta shafe wajen mintuna 2 a wajen kafin ta soma jan k'afafun ta zuwa cikin gidan, kamar daga sama ta soma jiyo wani jahilin bugu da akewa gate d'in kamar za'a 6alla shi, cike da mamaki ta dakata daga inda take tana kallan gate d'in kamar wadda zata gano me knocking d'in kafin ta bud'e, cigaba da knocking d'in da akayi ne ya sanya ta juyowa gaba d'aya ta soma takawa zuwa gate d'in har lokacin bugun da ake ba'a sassauta shi ba se ma k'arawa da aka yi, cikin ran ta take sak'a ko wanene wannan me bugu irin na mahaukata? "Wae waye ne?" ta tambaya ran ta a 6ace saboda yanda ta sake fusata da irin bugun da ake cigaba da yi, jin shiru ya sanya ta sake fusata sannan ta k'arasa jikin gate d'in a fusace tana k'ok'arin bud'ewa "Ke karuwa la'ananniya me bin mazan mutane, zaki bud'e ne ko kuma sena saka an 6alla min k'ofar na shigo.." shine abinda Muneerah ta fad'a kuma ya sauka a cikin kunnen Ayrah da ta ida saka hannun ta zata bud'e k'ofar.. _A bisa uzururrukan da suka sake min yawa, xan rage kwanaki 2 daga cikin ranakun da nake posting, daga yau na dena posting ranar Litinin da Talata, wato kenan xan dinga update duk ranar Asabar, Lahadi, Laraba, Alhamis da kuma Juma'a In Sha Allah_ Mhiz Innocent... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* Page 045 ___Lokaci d'aya ta ji ran ta ya 6aci, dama gashi a kusa take, take bugun zuciyar ta ya tsanantu, kan ta ya kulle da maganar da take ji daga wajen, gaba d'aya burin ta se ya ta'allak'a ne da son ganin wacece wannan da take jifan ta da wad'annan munanan kalaman, hannun ta har rawa yake saboda yadda ta k'agu ta gani kuma taji dalilin me fad'a mata wannan maganar. Tun kafin ta gama bud'ewa Muneerah ta hankad'a k'ofar se gata a cikin gidan, Aunty Zeenah da Bahijja suka biyo bayan ta babu 6ata lokaci, wani irin bugawa k'irjin Muneerah yayi sanda idanun ta suka sauka akan Ayrah da ke bin su da wani kallo da ita kan ta ta kasa gane wane iri ne, seda wutar kan ta ta d'auke na tsawon sakanni sannan ta dawo, har lokacin dae ta kasa furta komae, take kuma taji wani irin rauni ya ziyarce ta, kyawun Ayrahn kad'ae ya isa ya sarar mata da gwuiwa, da dae taga babu wata mafita kawae, ta sake tuna abinda ya kawo ta gidan, seta soma takawa zuwa gaban Ayrah da har lokacin tak'i ce musu komae kamar yadda suma suka kasa cewa komae, seda ta tattaro duka k'warin gwuiwar ta da ya soma zagwanyewa sannan tace bayan ta jefawa Ayrah wani banzan kallo "Uban me ya had'a ki da miji na? Meyasa kike bibiyar miji na?" tayi k'arfin halin fad'ar hakan, kallan irin anya kuwa kina da hankali Ayrah tayi wa Muneerah, sannan ta maeda duban ta kan Bahijja dake tsaye tak'i kallan inda take, ita abin ya d'aure mata kae, meye had'in Bahijja da wad'annan mutanen? Su waye su? "Tambayar ki nake Malama, Uban meyasa kike k'ok'arin shiga gonar da ba taki ba?" yanzu kam seta gyara tsayuwar ta sannan ta hard'e hannayen ta a k'irji, ta bud'e baki zata soma magana, se wata zuciyar ta kwa6e ta, tana ganin kamar idan ta tsaya kula su ma ta fad'i ne, duk da zata so ta san su d'in su waye amma gwara ta bar halin ta yayi aeki, soma takawa tayi da nufin komawa ciki duk da yadda zuciyar ta ke azalzalar ta, haushi, takaeci, da 6acin rae su suka zo suka yiwa Muneerah dirar mikiya, duk da yadda Aunty Zeenah tace mata subi komae a sannu hakan be hana ta kukan kura ta kae wa Ayrah cafka ba saboda yadda ran ta ya 6aci da yadda Ayrahn ke neman nunawa kamar bata san da wanzuwar su a wajen ba wanda hakan ba k'aramin 6ata mata rae yayi ba, lokaci d'aya ta fara fad'i cikin d'aga murya "Don uwarki ina zaki je? Nima tashancin zaki nuna min? Toh nafi ki iyawa karuwa kawae" da sauri Ayrah ta juya ta watsawa Muneerah jajayen idanun ta da suka rine saboda tsananin 6acin rae, zuciyar ta na cigaba da bugu ta sanya hannu ta janye hannun Muneerahn a fusace sannan ta soma magana a kausashe se dae ba kamar Muneerah ba ita ba cikin d'aga murya take yi ba "Kada ki k'ara wannan kuskuren, kin kira ni da sunan da kike ganin kowa ma shi ne saboda ke kin kasance hakan, na miki shiru na d'auka kina da hankalin da zaki gane shiru ma magana ce a wajen me hankali, se kuma kika nuna min wacece ke, kin zo kina ta haushi se dae har yanzu kin kasa tsayawa kiyi magana ballantana na san abinda ya kawo ki, yi hak'uri fa idan kika gama ga hanya nan se kija tsummar k'afar ki kiyi gaba" ta k'arasa maganar tana d'auke idanun ta daga kan Muneerah. Tunda ta soma magana Muneerah ke kallan ta, bata ta6a tunanin yarinyar zata iya kallan cikin idanun ta ta fad'a mata wad'annan zafafan kalaman ba, kallan farko da tawa Innocent face d'in ta ta d'auka har ta gama ci mata mutunci tayi mata dukan tsiya ba zata iya cewa komae ba, se dae gashi ta shayar da ita ruwan mamaki, duk rashin kunyar ta da duniyancin ta ta rasa dalilin da yasa yau d'in jikin ta yake a sanyaye wanda ta kasa gane dalilin hakan. Aunty Zeenah ma kan ta ta sha mamaki bare kuma akae ga Bahijja da itama Ayrahn ta shayar da ita ruwan mamaki, a d'an zaman da suka yi a makaranta ta fahimci wasu halayen na Ayrah, akwae ta da shariya, miskilanci da kuma kama kan ta a lokacin da ta lura akwae raeni a wajen, amma bata ta6a tunanin zata iya gwa6awa wata magana irin wannan ba. "An fad'a miki d'in ke wacece? Wanene uban ki? Million nawa kika bawa baya? Me kike tak'ama da shi da kike kula miji na? Wallahi ko ki bud'e baki ki fad'a min kin rabu da shi ko kuma yanzun nan in yi miki shegen duka inga uban daya tsaya miki" Muneerah tayi maganar tana k'ok'arin sake rik'o Ayrah, rik'o hannayen nata Aunty Zeenah tayi sannan tace "Kada ki ta6a ta, akwae ta da k'arfin hali naga alama, tunda dae yanzu mun tabbatar da abinda muke zargi ina ganin kawae ki d'aga waya ki
Chapter 57 · 0% Book details