← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 90

Sashe 80

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kallan Ayrah da itama ita take kalla fuskar ta d'auke da murmushin itama. "Umma" Ayrah ta fad'a "Na'am Ayrah, ya jikin na ki?" Umma ta tambaya har lokacin farin cikin da take ji yak'i 6uya akan fuskar ta. "Ehh Umma" "Sannu da zuwa Umman Sadeeq" Ummee ta fad'a tana kallan Umma, murmushi Umma tayi dan se a lokacin ta tuna ko gaesawa basu yi ba hakan ne ya sanya ta fad'in "Ayyah sannu ka dae. Kun tashi lafiya? Ya kwanan jiyan, Allah ya bada lada" "Kae ba dae zaki dena ba" Ummee ta fad'a tana maeda duban ta kan Ayrah tace "Maza ki ci" Hannu Ayrah ta kae ta d'auki plate d'in dan Ummeen ta mata kwarjini sosae, ban da haka ba abin da ze saka taci abincin saboda yadda take jin bakin ta gaba d'aya babu dad'i. Se ta d'ora shi akan cinyar ta a hankali ta d'auki cokalin ta soma kaewa bakin ta kamar wadda ke cin magani. Murmushi Umma tayi tana neman waje ta zauna, itama taji dad'in yadda Ummeen da kan ta tace taci abincin dan ta san idan itace zata iya cewa a k'oshe take. Ba dan ta so ba haka ta dinga cusa abincin se dae kana kallan fuskar ta zaka fahimci tana ci ne kawae ba dan dad'i ba. .. Sanye cikin riga da skirt na atamfa ta fito da wani mayafi madaedaeci zuwa compound d'in gidan, se da ta isa parking space sannan ta dakata ta ajje key d'in hannun ta a saman motar sannan ta danno number d'in sa ta kara a kunnen ta. "Hello" ta fad'a tana saurarar muryar sa ko zata ji ta chanja daga yanayin data ji ta d'azu, se dae ga mamakin ta memakon ta ji muryar ta sa cikin k'unci se taji annurin da har cikin muryar sa se da ya bayyana sanda yake fad'in "Salamu Alaeki" Cikin rashin sani da su6utar baki ta furta "Ta farka ne?" Sam bata san abin da ta fad'a d'in a fili ta fad'a ba se da taji amsar da ya bata "K'warae kuwa, Alhamdulillah" Cikin sakannin da basu wuce biyu ba k'afar ta ta soma karkarwa haka zalika hannun ta har taso ta kasa rik'e wayar dake hannun ta, ta tsinto maganar sa na fad'in "Kin fito ne?" Se da ta runtse idanun ta tana jin yanda cikin ta ya hargitse lokaci guda, bata ta6a tunanin zata iya had'a kalma ta fad'a ba, se dae cikin k'arfin hali tayi k'ok'arin furta, "Ehh" ba dan tana da tabbacin ya ji ba. Se dae kuma ya ji ta dan yana jin abin da ta fad'a d'in ya katse wayar. Da gudu ta kwasa zuwa cikin gidan kae tsaye ta wuce toilet saboda yanda cikin ta ya hautsine lokaci guda. Ta kae mintina 2 akan shugaba sannan ta fito zuwa lokacin ta gama had'a gumi ta ko ina na jikin ta, jar fuskar ta ta sake had'ewa tayi wani yagwal kamar d'anyen nama, se a lokacin ta samu damar fashewa da kuka tana zubewa a wajen hannun ta a kan ta ta saki k'ara tana fad'in "Na shiga 3 na lalace" Ta kae wajen minti 5 a hakan, se kuma can ta mik'e ta soma dube_dube cikin d'akin, se kuma daga baya ta fito da sauri ta fad'a cikin motar ta ta tashe ta ta fice daga cikin gidan, ba tare da tunanin komae ba kawae ta d'auki hanyar Zaria. .. A nutse ya tura k'ofar d'akin kamar ko da yaushe idanun sa a kan ta, se ta juya da sauri saboda yanda taji a jikin ta shi d'in ne, se kuwa akayi sa'a idanun su suka sauka cikin na juna, suka sakarwa junan su murmushi, kana ya k'araso cikin d'akin. Lura da shi da Ummee tayi ne ya sanya ta fad'in "Wae ina Muneerah ne?" d'an shiru yayi na en wasu sakanni, shi se a lokacin ma ya tuna tun d'azu da suka yi waya da Muneerahn akan ta taho, amma kuma har yanzu bata k'araso ba. Se ya fiddo da wayar sa sannan yace "Tana kan hanya, dan mun dad'e da yin waya tace ta taho" "Toh Allah ya kawo ta lafiya" Ummee ta fad'a yayin da shi kuma ya danna kiran number ta. A karon farko ta shiga se dae lokacin Muneerah na driving ne tana kan hanyar ta ta zuwa Zaria, k'irjin ta ya wani irin bugawa da k'arfin gaske, kawae se ta janyo wayar ta kashe ta gaba d'aya tana cigaba da driving hawaye na cigaba da kwarara akan fuskar ta, tana share su kada su jawo mata matsala tunda tuk'i take yi. Mayar da wayar yayi cikin aljihu kana a ran sa ya sak'a "May be tana hanya ne" hakan ne ya sanya shi d'aga ido ya kalli Ayrah. Kallan sa take yi ido cikin ido kamar me son gano wani abu daga cikin idanun na sa, shi ma cigaba yayi da kallan ta cike da mamakin ta, dan kafin ta masa irin wannan kallan ana dad'ewa. Ta 6angaren ta kuwa se a lokacin ta shiga bitar abin da ya faru a ranar nan, tabbas idan dae har ruwan ta fad'a toh Muneerah ce ta jefa ta da sanin ta, ko kuma ma tace Muneerah ce ta tura ta, sannan yanzu taji ya ambaci sunan Muneerah ta taho asibitin, kenan me tazo tayi mata? Zuwa zata yi ta k'arasa ta ko menene? Me ta tsare mata a rayuwa? Me ta tsare mata da zata so ganin ta hallaka ta?. Sallamar da akayi ce ta ja hankalin duk wanda ke cikin d'akin, Abba, Abbu da Yah Sadeeq suka shigo cikin d'akin. Take idanun ta suka sauka akan Yah Sadeeq dake k'arasowa cikin d'akin, ji tayi kamar an k'arawa zuciyar ta rauni ne hakan ya sanya ta fashewa da kuka kawae tana sake lalubowa cikin k'wak'walwar ta ko akwae dalili ko kuma abin da ta yiwa Muneerah da ze saka taso hallaka ta. Kusan gaba d'aya en d'akin suka yo kan ta cike da mamakin abin da ya sanya ta kukan cikin lokaci k'ank'ani, musamman ma Rk da babu dad'ewa suka yi musayar murmushi yanzu kuma tana kuka, kusan a tare wasu daga cikin su suka furta "Meya faru?" d'aga jajayen idanun ta tayi ta kalle su su duka, tabbas nan d'in ta tabbatar masu k'aunar ta ne, ta san kowanne cikin zuciyar sa yana buk'atar sanin abin da ya kae ta bakin swimming, se dae yanayin da take ciki ya hana kowannen su tambaya, dan haka tana ganin mafita d'aya ce itace ta fad'a musu abin da ya faru, hakan ne ya sanya ta soma sauke ajiyar zuciya zuciyar ta a rauna ne tana kuma yi mata zafi, cikin raunanniyar murya tace "Muneerah!!" Da mamaki duk suke kallan ta, kowa na buk'atar k'arin bayani, amma jin tayi shiru ya sanya Yah Sadeeq matsawa kusa da ita yace a hankali "Kin ga ki nutsu ki fad'a mana meya faru? Wacece Muneerah kuma?" Umma da Abba har ma da Yah Sadeeq kan su ya kulle sosae, dan su sam basu san wacece Muneerah ba, yayin da Abbu, Ummee da Rk suka kasa furta komae kawae kallan Ayrah suke yi dan jin abin da ze fito daga bakin ta.. Mhiz Innocent... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* Page 058 ___Se da ta sake d'aukar wajen second 10 sannan tace "Muneerah ce.." ta d'an sake dakatawa tana runtse idanun ta tana kuma sake tuna abin da ze fito daga cikin bakin ta, yayin da gaba d'aya en d'akin su kuwa sun k'agu su ji abin da zata fad'a d'in. Se ta d'ora da "Muneerah ce ta jefa ni cikin ruwa!" Shiru ne ya wanzu cikin d'akin na tsawon sakanni, kowanne na maemaeta abin da ta fad'a d'in a cikin zuciyar sa. Ta 6angaren Rk kuwa ji yayi kan sa ya kulle gaba d'aya, man kan sa ya tsiyaye, gaba d'aya yama rasa abin da ya kamata yayi. Shin da gaske abin da ke fitowa daga bakin Ayrah gskiya ne? A zahiri ne take fad'ar hakan ko kuwa dae? Wace Muneerah take nufi? Muneerah dae Muneerahn da ya sani ko kuwa dae akwae wata daban ne?. Tambayar da Abbu yayi itace ta dawo da shi cikin hayyacin sa duk da ya dawo d'in ne kawae dan tabbatar da abin da kunnuwan sa suka ji, ba dan ya fita daga tsoro da kuma mamakin yadda Ayrah ke fad'in wata halitta ce ta jefa ta cikin ruwa ba. "Wace Muneerahn kike nufi?" itace tambayar da Abbu yayi k'ok'arin fad'a dan korewa kowa tantamar da yake ciki. A nutse Ayrah ta bud'e bakin ta tace "Abokiyar zama na!" Cikin lokaci k'ank'ani ya ji jikin sa yayi wani mugun sanyi, ya runtse idanun sa yana jin yanda bugun zuciyar sa ke chanja yanayin fitar sa, 6acin rae, mamaki, fargaba gami da tsoro suka had'u suka masa dirar mikiya. Ta 6angaren Umma, Yah Sadeeq har ma da Abba babu wanda ya iya cewa komae se Abbu da yayi k'arfin halin fad'in "Ya ilahy" Daga nan shi ma be sake cewa komae ba saboda tsananin mamakin abin da Muneerahn ta aekata. Har wajen minti 1 be bud'e idanun sa da suke masa wani zafi ba, a fili yana fidda numfashin sa dake fita a zafafe, se can kuma ya bud'e idanun na sa still dae akan Ayrah da yanzun kan ta ke d'ore akan kafad'ar Umma. Sam ya kasa gasgata cewar Muneerahn dake zaune a matsayin matar sa itace tayi yunk'urin kashe masa mata har ma da abin da ke cikin ta, be ta6a tunani kuma be ta6a kawowa cewar zata iya aekata haka ba, ya san Muneerahn na da bud'ewar ido amma be ta6a zaton zata iya k'ok'arin yin kisan kae ba, kenan tana sane ta aekata ko kuwa? So tayi ta kashe Ayrahn ko kuwa? Duk wasu alamu sun nuna so tayi ta kashe ta, dan ba dan haka ba ba zata bari Ayrahn ta gan ta ba kamin ta jefa ta cikin ruwan, wato ta bari ta gan ta ne dan tana da yak'inin idan ta jefa ta babu yanda za'ayi ta fito, babu kuma wanda ze taemaka mata ta fito ballantana ta rayu, kenan da gasken so tayi ta hallaka ta? So tayi
Chapter 80 · 0% Book details