Sashe 30
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sa? Amma meyasa Ayrah zata yi haka? Meyasa zata za6i d'a namiji akan iyayen su? Iyayen da suka d'auke ta tun ciki har tazo duniya suna d'awaeniya da ita har kawo yanzun basu gaji ba? Duk wani tunanin su akan ta ne, duk wani burin su akan ta, meyasa zata saka musu ta hanyar za6ar wanda ta had'u dashi rana tsaka a rayuwar ta? Ta fifita d'a namiji akan su??. ... Yana cikin motar har lokacin idanun sa na kan gidan yana tunanin yadda zeyi ya shiga cikin gidan, idan ya tuna maza ne har biyu suka d'auki Ayrahn suka shigar da ita cikin gida se yaji wani sabon tuk'uk'i da kuma wani zafi na cigaba da azalzalar sa cikin zuciya, seya bud'e murfin motar a hankali ya zuro k'afar sa dake cikin wani had'ad'd'en takalmi hannun sa akan goshin sa yana d'an murzawa, daga ganin mutanen da suka d'auke ta kasan sanya su akayi, kuma gidan da suka kawo ta babu alamar akwae mutum a ciki, kenan idan haka ne ogan nasu ze zo kuma ze nemi a bud'e masa k'ofar dan shiga gidan "Exactly" ya fad'a yana sake bud'e idanun sa, seda ya fesar da wata zazzafar iska daga bakin sa sannan ya cigaba da zama cikin motar har lokacin gaba d'aya hankalin sa na kan gidan gefe guda kuma yana jiran yaga ta inda wani ze 6ullo. ... Zubewa yayi a gaban me garin yana d'aga hannun sa alamar girmamawa "Allah ya taemake ka yalla6ae" wani matashi da zeyi 25 years ya fad'a kan sa a k'asa, me garin bece komae ba ya cigaba da kallan Mubarak yana jiran jin abinda ze fad'a "Yalla6ae acan gidan Alhaji Mato naga wasu bak'in fuska sun shiga gidan, ban ta6a ganin su ba kuma naga kamar basu da gaskiya" Mubarak ya fad'a har lokacin kan sa na a k'asa, seda me gari ya d'an numfasa sannan yace "Gidan Alhaji Mato?" Me gari ya fad'a, Mubarak ya sake jinjina kae kana yace "K'warae kuwa yalla6ae nima nayi mamaki" d'an shiru Me garin yayi sannan yace "Aje a zo min dasu" ya fad'a a nutse "An gama ranka ya dad'e" Mubarak ya fad'a yana mik'ewa ya bar wajen. ... Suna zaune a tsakar gidan Muttala ya kalli wanda suke tare yace "Kodae mu fito da ita, kada zafi ya mata illah" "A'ah mu k'yale ta, mu dae ba aekin da aka saka mu ba kenan? Ina ruwan mu? Gwara kawae mu jira yazo shi yasan yadda za'ayi da ita" jinjina kae Muttala yayi kana yace "Hakane kuma" babu wanda ya k'ara cewa komae a cikin su har zuwa sanda suka ji ana knocking k'ofar, da mamaki dukan su suka yi shiru suna saurarar knocking d'in sa ake dan tabbatarwa "Wallahi da gaske k'wank'wasawa akeyi, waye kenan?" "Ko dae Alhajin ne ya iso?" mutumin ya tambaya yana kallan Muttala, girgiza kae Muttala yayi kafin yace "No bana tunanin haka gaskiya, idan shine ae akwae mukulli a hannun sa" Muttala yayi maganar yana mik'ewa a hankali ya k'arasa dab da gate d'in sannan yace "Wanene?" Mubarak ne yace "Daga gidan Me gari ne, me gidan yana nan?" se Muttala ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "A'ah be iso ba tukun" "Toh Me gari na neman ku" Mubarak ya sake fad'a, kallan juna Muttala suka yi shida mutumin nan sannan Muttala ya d'aga kafad'a kafin a hankali ya furta "Babu wata matsala fa" jin abinda ya fad'a ne ya sanya mutumin k'arasawa ya bud'e gate d'in sannan suka fara k'ok'arin fitowa daga cikin gidan "Ku kad'ae ne a cikin gidan?" Mubarak ya sake tambaya, mutumin nan na shirin cewa "Ehh" Muttala ya girgiza kae da sauri kana yace "A'ah akwae matar Oga amma bacci take" "A taso ta itama ta fito, Me gari ke neman ku ku duka" had'iye yawu Muttala yayi kana ya koma cikin gidan ya k'arasa ya bud'e motar cikin tunanin yadda za'ayi ta farka saboda abinda suka shak'a mata, cikin sa'a seya hango wani ruwa wanda d'azun ya sha ya ajje ragowar, da sauri ya janyo kana ya bud'e ya fara zuba mata a fuska, seda ya kusa juye mata ruwan sannan ta fara bud'e dara daran idanun ta da suka sake komawa ciki saboda wahala, a hankali ta dinga bud'e su har ta gama ware su tarr cikin motar, idanun ta suka sauka akan Muttala, da sauri ta mik'e ta fara komawa baya tana shirin sakin k'ara Muttala ya girgiza mata kae da sauri yana d'ora hannun sa akan bakin sa sannan yace a hankali ganin yadda ta gama rikicewa gaba d'aya "Kada kice komae, kiyi shiru taemakon ki zan yi" yayi maganar har lokacin yana kallan ta, cigaba da girgiza kae tayi hannun ta d'ore akan bakin ta hawaye se sintiri suke akan fuskar ta "Ki dena kukan taemakon ki zan yi fa" ya sake fad'a ganin kamar bata ji abinda ya fad'a da farko ba "Kiyi shiru kada ki nuna a tsorace kike kin ji, ko me kuma za'a ce miki kada kice komae, komae kika ji an fad'a ke dae ki bisu a haka" ya fad'a a nutse dan gudun kada ta tona musu asiri a gaban jama'a, haka kawae taji tayi na'am da zancen mutumin dan haka seta jinjina kae sannan yace "Fito muje" babu musu ta sanya k'afa ta fito se dae har lokacin k'irjin ta be bar bugawa ba haka zalika tana mamakin ko nan d'in ina ne? Waye ya kawo ta? Yaushe suka zo? Ya akayi suka zo nan d'in? Su waye su? Meyasa suka kawo ta nan d'in? Amma koma dae menene tunda wannan mutumin ze taemaka mata bari ta zubawa sarautar Allah ido, seta sake bud'e idanun ta tana kallan gidan sanda Muttala ke fad'in "Yawwah ga ta" Mubarak ya kalle ta sannan yace "Toh ku wuce muje" babu musu duka suka fito daga gidan sannan suka kulle, tafiya take a hankali kamar wata mara laka tana cigaba da kallan garin da be mata kama da birni ba, ji take kamar ta saka kuka amma idan ta tuna abinda mutumin ya fad'a seta d'an lumshe idanun ta ta had'iye hawayen. Tunda suka fito idanun sa ke kan su, seya saki wata k'atuwar ajiyar sanda ya hange ta ta fito daga cikin gidan tana tafiya cikin k'oshin lafiya "Thank god" ya fad'a yana fitowa daga cikin motar gaba d'aya, seda suka kusa zuwa gidan Me garin yana hango su sannan yabi bayan su cike da tunanin inda zasu je d'in. A inda Me gari ya saba zama suka isa sannan dukkan su suka tsaya, Mubarak ya kalle su yace "Ku zauna dukan ku" Ayrah ta d'aga kae a hankali ta kalli Muttala seya jinjina mata kae irin kamar nufin sa babu wanda ya gan shi, bata iya zama ba seda taga shi kan sa Muttalan ya zauna sannan ta raku6e waje d'aya kamar munafuka tana matse k'walla, zubewa Mubarak yayi a wajen sannan yace kan sa a k'asa "Yalla6ae gasu nan" kallan su Me gari yayi su duka, ita kuwa Ayrah gaba d'aya jikin ta rawa kawae yake yi har yanzu ta kasa gane mak'asudin zuwan ta wajen, dan kuwa sam ta kasa tuna yadda akayi tazo nan wajen, gyaran murya Me gari yayi sannan ya fara magana a nutse "Meya kawo ku gidan nan? Ina Alhaji Mato?" dae_dae lokacin wayar Muttala ta fara ringing, seya fiddo ta daga cikin aljihun sa, ganin me kiran ya sanya shi d'aga kae a hankali ya saci kallan Me gari sannan ya maeda kan sa kan wayar kawae ya d'aga, ban ji me akace daga can 6angaren ba na dae ji Muttalan yace "Muna wajen Me gari dukan mu" se kuma yayi shiru can kuma yace "Toh seka k'araso" Muttala ya fad'a yana katse wayar sannan ya kalli Me gari yace "Yalla6ae yanzu ma Alhaji Maton ze zo da kan sa" "Ahh toh Masha Allah" Me gari ya fad'a yana gyara zaman sa. Shiru ne ya wanzu a wajen na tsawon mintuna har zuwa lokacin da Alhaji Mato ya k'araso wajen da sallama cikin shadda kamar ko da yaushe me babbar riga, tumbin nan nasa kullum kamar k'ara ha6aka yake yi ya samu waje ya zauna abin sa, haka jajayen idanun sa ma sun k'ara wani ja kamar me ciwon ido, ya zube gaban Me gari da fara'a akan fuskar sa "Barka da wannan lokaci Ranka ya dad'e yalla6ae" ya fad'a yana d'aga hannun sa alamar girmamawa "Barka dae Alaji Mato, ashe ma kana kan hanya, kasan mutane ba abin yadda bane shiyasa na saka amin bincike, amma tunda ga ka kazo seka d'auki bak'in ka ku koma" gyara zama Alhaji Mato yayi yana satar kallan sahibar tasa da yaga ta k'ara masa kyau yace "Wato yalla6ae dama wajen ka nazo gaskiya" "Toh Ikon Allah, Allah yasa dae lafiya" Me gari ya fad'a shima yana gyara zaman sa, seda Alhaji Mato yaja numfashi sannan ya sake gyara zaman sa yana tunanin ta inda ze fara "Yalla6ae wannan da kake gani mata ta ce, tsautsayi yasa na sake ta kuma ban maeda ta ba har ta gama idda, shine nake so a maeda mana auren mu yalla6ae dan nasan aekin ka ne wannan d'in" d'aga kae Me gari yayi ya kalli Ayrah dake zaune tana jin maganar da Alhaji Mato yake yi ba dan tana fahimtar sa ba, ko kuma ta fahimci akan ta ake magana ba "Ikon Allah" shine abinda Me gari ya fad'a kawae sannan ya sake yin gyaran murya yace "yanzu a take kake nufi?" da sauri Alhaji Mato ya sake yin wani murmushin kafin yace "Ehh Ranka ya dad'e yalla6ae" "Allah ya gafarta malam ni ne nake neman auren ta yanzu, kuma muna son junan mu" dukkan su suka d'aga kae suna kallan me maganar cike da mamaki, da wani irin sauri ta d'aga kae ta kalli me maganar dan ta tabbatar wa da kan ta abinda take tunani, ita gaba d'aya kan ta ya kulle, har tana so ta dena gane komae, magana ake tayi gashi dae a gaban ta amma bata ganewa, bata fahimta, bata fuskan ta, ji take kamar dukan su wani yare suke yi, shin akan wa suke magana? Akan wata mace suke magana? Cigaba tayi da kallan