← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 90

Sashe 2

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dalilin da yasa Abban nata yace haka ba. Kae tsaye parlourn k'asa ya sauko cikin nutsuwar data zame masa jiki, dae_dae lokacin da wata farar mata wadda ak'alla zatayi shekaru 45 zuwa 50, kyakykyawa ce kamar yadda d'an nata yake, tana sanye cikin wata atamfa me kyau d'inkin riga da skirt, jera warmers d'in data fito dasu daga kitchen akan dinning take, ta kalle shi da murmushi kan fuskar ta sannan tace "Ka k'araso ka fara cin abinci koh?, semu zauna mu samu muyi hira.." d'an murmushi ya saki kad'an kamin ya shafa sumar kansa yace "Tohm Ummee.. Amma inaso ne muyi wata magana me muhimmaci.." ya fad'a yana d'an lumshe manyan idanun sa kad'an, dae_dae lokacin Ummee ta gama jera kayan data fito dasu seta k'araso inda yake tsaye tace tana murmushi "Shikenan Raj, ni dama daga yadda na ganka nasan akwae magana a bakin ka" shima murmushin ya maeda mata sannan dukkan su suka wuce zuwa cikin k'aton parlourn daya k'awatu da had'ad'd'un kujeru, suna zama Alhaji Kabeer ya shigo cikin d'akin da sallama sanye cikin manyan kaya da babbar riga, dukan su suka amsa masa ya k'araso yana kallan su su duka kuma a lokaci guda yana amsa sannu da zuwan da suke masa, akan kujera ya zauna, yayin da Raj ya sauko daga kan kujerar yana shirin zama a k'asa Alhaji Kabeer yace "A'ah kayi komawar ka ka zauna, yau ae hira zamuyi.." murmushi ne ya wanzu akan kyakykyawar fuskar sa seya koma ya zauna yana kallan Alhaji Kabeer yace "Barka da dawowa Abbu.." "Barka kadae Raj" "Ko dae a kawo maka abincin nan ne?" Ummee ta fad'a tana kallan Abbun, girgiza kae yayi kafin yace "A'ah fara kawo min dae juice na sha.." mik'ewa Ummee tayi ta wuce inda ze sadata da dinning area, yayin da Abbu ya dawo da duban sa kan Raj yace "Ya hanyar dae? Kuma ya karatun?" "Alhamdulillah Abbu..ina tafe da wani albishir fa.." ya fad'a da murmushi kan fuskar sa, dae_dae lokacin da Ummee ta k'araso hannun ta d'auke da juice d'in ta ajjiye sannan ta fara k'ok'arin zubawa a cikin tambulan "Toh ko zamu bari mu fara cin abinci?" Abbu ya fad'a yana kar6ar juice d'in da Ummee ta mik'a masa kana ta nemi waje ta zauna, hannun sa ya kae kan sumar kansa ya d'an shafa sannan yace "A'ah Abbu.. Na k'agu na sanar daku ne.." Ummee ta kalli Abbu tana murmushi tace "Ae kawae ka k'yale shi ya fad'a dan tun d'azu ya kasa komae har abincin ma shima beci ba.." "Ohk ina jin ka.." Abbu ya fad'a yana kae juice d'in bakin sa "Abbu na samu matar aure.." dukkan su suka kalle shi cike da mamaki da kuma farin ciki duka a lokaci guda, mutumin da suka san kwata kwata baya kula wasu mata amma yau shine ke fad'in ya samu matar aure? Toh ta yaya? "Wacece wannan Raj?" Ummee tayi k'arfin halin fad'in haka, wani k'ayataccen murmushi ne ya su6uce masa sannan yace bayan ya lumshe idanun sa ya bud'e "Ayrah.." "Wacece Ayrah?" Ummee ta fad'a tana kafe shi da idanun ta "Ayrah dae wadda kika sani Ummee, kada kice min har kin manta ta, Ayrah dae tawa wadda kika sani.." k'warewar da Abba yayi ne ya sanya su duka suka kalle shi, babu k'ak'k'autawa ya shiga yin tari sosae, da sauri Raj ya mik'e ya isa fridge ya d'akko ruwa ya kawowa Abbun, da k'yar ya iya kar6a yasha ruwan, ya shiga sauke ajiyar zuciya kamar wanda yayi gudu "Sannu Abbu..sannu.." shine abinda Ummee keta maemaetawa amma Abbun bebi ta kanta ba ya kalli Raj yace "Ya..akayi ka had'u da ita?" yayi maganar a rarrabe yana kallan Raj, sosae Raj ke binsa da kallo yana so ya gano abinda ya sanya shi lokaci d'aya ya zama wani iri "Abbu.." "Ya akayi ka had'u da ita? Ko dama kuna tare tsawon lokacin nan?" Abbu ya katse masa maganar da yayi niyyar yi, girgiza kae Raj yayi har lokacin idanun sa nakan Abbu "Tun wuri ka rabu da ita Raj, ka rabu da ita dan auren ku baze ta6a yiwuwa ba, tun wuri ma ka cire ta a ranka zefi maka.." Abbu ya fad'a yana mik'ewa yayi hanyar d'akin sa, da kallo yabi Abbun sannan ya maeda duban sa kan Ummee yana jin yanda k'irjin sa ke bugawa "Ummee.." ya fad'a yana kallan ta, seta mik'e kawae tabi bayan Abbun a ranta tana sak'a yadda zasu 6illowa al'amarin, lallae idan ba suyi wasa ba suna cikin matsala.. Runtse idanun sa yayi har lokacin yana jin yadda bugun zuciyar sa ke k'aruwa, me yake faruwa ne? Yakae wajen minti 5 zaune a wajen yana sak'awa da warwarewa sannan ya d'auki wayar sa ya lalubo number ta ya danna kira. A 6angaren ta kuwa har lokacin tana kwance kan madaedaecin gadon d'akin, kanta d'ore akan pillow hawayen da suka k'i tsayawa se zuba suke akan pillown, kanta babu d'an kwali hakan ya bawa sumar kanta damar bajewa akan pillown, dae_dae lokacin da kiran wayar tasa ya shigo wayar ta yayi dae_dae da lokacin da Umma ta yaye labulen d'akin ta shigo, ringing d'in da taji ya sanya ta kallan wayar, Ayrah ta tashi zaune tana kallan Umman lokaci guda tana maeda duban ta kan wayar "Mik'omin wayar.." Umma ta fad'a tana mik'a hannun ta, lumshe manyan idanun ta tayi wasu hawaye masu d'umi suna zubowa akan kuncin ta, ganin bata da niyyar mik'o mata wayar ne yasa Umman ta k'arasa da kanta ta d'auki wayar ta kashe ta gaba d'ayan ta sannan ta kalli Ayrah data fashe da wani irin kuka tace "Kiyi shiru ki dena kuka, ki tsaya ki saurare ni, base kin tada hankalin mu muma mun tayar da naki ba.." kafin Umman ta kae k'arshen zancen ta Ayrah tace cikin kuka tana girgiza kae "Umma meyasa haka? Shin baku san wanene Raj ba? Baku san halin sa ba? Ko kuwa iyayen sane baku sani ba.." K'arasawa Umma tayi ta zauna akan gadon kana ta kamo Ayrahn cikin jikin ta, bata fara magana ba seda taji ta fara sauke ajiyar zuciya, sannan ta kama dogon gashin Ayrahn ta d'aure a tsakiyar kanta kana ta fara magana a nutse tana jin zuciyar ta na mata wani irin zafi... B'angaren sa kuwa runtse idanun sa yayi bayan ya sake kiran layin Ayrah yaji shi a kashe, yaja wani dogon numfashi sannan ya mik'e akan k'afafun sa yana daedaeta nutsuwar sa a ransa yana jin ya zama dole yasan aenahin abinda yake faruwa kafin k'wak'walwar sa ta tarwatse, dan kuwa tabbas akwae rina a kaba, me yake faruwa haka?..... _*TUSHEN LABARI*_ ZARAH AUTA (Mhiz Innocent) https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* *TITAN'S OF TALENT* Page_002 ____kyakykyawa ce fara sol me manyan idanuwa, haka zalika kuma me k'aramin jiki da dogon hanci, a kallan farko zaka iya k'iyasta shekarun ta, san haka baza ta wuce shekaru 4 ba, tana sanye cikin Uniform dake a goge fes fes dasu, hannun ta d'auke da basket d'in ta dake d'auke da flask d'in abinci na yara en makaranta da kuma rubber ruwa, da d'an gudun ta take fitowa daga cikin d'akin daya kasance mallakin ta, fuskar ta d'auke da murmushi, seda tazo dab da Abban nata sannan tace cikin muryar ta da bata gama fita sosae ba "Abba na shirya.." "Yawwah..Ayrah" Abba ya fad'a yana jan kumatun ta kafin ya d'ora da fad'in "Ina yayan naki?" d'an k'aramin bakin ta ta tura gaba kad'an kana tace "Abba Yah Sadeeq fa be shirya ba" kafin Abban ya sake cewa komae sega Sadeeq d'in ya fito, fari ne se dae ba can ba, amma kamar su d'aya da Ayrahn, wanda hakan ze alamta maka da cewar yayan tane, shima yana sanye cikin Uniform d'in kamar nata, sedae akwae d'an banbanci a Uniform d'in nasu wanda hakan ke nuni da ita a primary take yayin da shi kuma yake a secondary, shima nasan a wanke suke tass kuma a goge hannun sa rik'e da jaka yana k'ok'arin goyawa a bayan sa yace sanda yazo kusa da Abba bayan ya watsawa Ayrah harara "Abba ka ganni fa a shirye nake.." mik'ewa Abba yayi yana rik'e da hannun Ayrah dae_dae lokacin da Umma ta fito daga kitchen tana kallan Sadeeq tace "Ba zakayi break bane?" kallan Umman yayi kafin ya saci kallan Abba "Wato so kake ka janyowa kan ka wata cutar koh?" sosa kansa yayi kana yace har lokacin kan nasa a k'asa "A'ah fa Abba, ae ina siyar wani abun a school.." "Toh yayi kyau, amma ko tea ne ka dinga sha ko ka samu hanjin ka ya warware" "Toh Abba.." ya amsa a hankali "Toh Allah ya tsare, ya bada sa'a.." Umma ta fad'a tana binsu da kallo su duka, suka amsa da "Ameen" sannan suka fice daga d'akin... Kae tsaye fire service suka wuce inda Abban ke ajiye motar sa k'irar Civic Honda, suka jira shi a bakin wajen, ya shiga ya d'auko sannan suka shiga ya wuce dasu zuwa makarantar kamar koda yaushe, a bakin makarantar ya ajiye su bayan ya sallami kowannen su sannan shi kuma ya wuce wata makarantar government da yake koyarwa a cikin garin nasu.. Hannun Ayrah cikin na Yah Sadeeq har suka k'arasa bakin ajin su Ayrahn, sannan ya sakar mata hannun yace yana kallan ta "Ayi karatu sosae, banda k'iriniya" "Toh" ta fad'a kawae tana yin cikin ajin nasu, seda yaga ta shiga sannan ya wuce nasu ajin.. Wajen k'arfe 10 aka fito break, kamar koda yaushe ita da k'awayen ta kan fito harabar makarantar suyi wasa bayan sun gama cin abincin, yau ma hakan ce ta kasance, dan kuwa suna gama cin abincin suka fito wajen suka fara wasan su irin na yara.. A hankali idanun ta suka sauka akan sa kamar koda yaushe yana zaune akan wani d'an dandamalin dake k'ofar wani aji, yayi shiru wani lokacin yana d'an kallan abinda ke faruwa a cikin makarantar, wani lokacin kuma idanun sa na kallan k'asa ko wani wajen, cigaba tayi da wasan ta sedae lokaci zuwa lokaci takan juya ta kalle shi har zuwa lokacin da aka koma break d'in suka koma aji bayan sunyi butu butu da Uniform d'in nasu. Suna zaune cikin ajin
Chapter 2 · 0% Book details