Sashe 67
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gaban ta ta shiga jinjina kae "Wallahi Mummy aure yayi, shikenan ni kuma ya fara nuna min banbanci, wallahi Mummy kashe ta kawae zan yi na huce takaecin da nake ji" ta k'arasa maganar muryar ta na rawa, tsaki Mummy ta ja kafin tace "Ina Zeenah take?" harara Muneerah tayi kamar Aunty Zeenahn ce a gaban ta kafin tace bayan ta goge hawayen fuskar ta. "Nima ban sani ba" da mamaki Mummy tace "Baki sani ba kuma?.. Yanzu dae ba wannan ba ki bar maganar a hannun Zeenah, wae ko kina nufin ba tazo gidan na ki ba?" da sauri Muneerah tace "A'ah Mummy ki raba ni da wata Aunty Zeenah, itace taso 6ata min komae fa, ni kam ki bar ni inyi abinda nayi niyya shine kawa ze samamin farin cikin da kowa ya gaza samar min" sauke numfashi Mummy tayi kafin tace "Ni na kasa gane abinda kike nufi fa Munee, wane irin aure ne wannan, dududu yaushe akayi naku ke da shi, amma ace har ya k'ara wani?" "Ba kuyi magana da Aunty Zeenah ba?" Muneerah ta tambaya, Girgiza kae Mummy tayi kana tace "A'ah ni kam ba mu yi wata magana ba, amma dae yanzu abinda nake so dake ki kwantar da hankalin ki, bana so kiyi amfani da wannan shegen fushi da wautar taki kice zaki aekata abinda kika yi niyya, yanzu dae ina da bak'i ne amma zuwa anjima zan kira ki muyi magana.. " murmushin yak'e Muneerah ta saki, dan kuwa sam maganar Mummy ba shigar ta take ba, ta riga ta k'udurcewa kan ta seta aewatar da abinda tayi niyya dan haka tace "Bazan yi yadda za'a gane ba Mummy, bazan bar wata shedar da zata saka a fahimci ni na kashe ta ba, saboda haka ki kwantar da hankalin ki, ki bar ni na aekata abinda nayi niyya dan samawa kae na salama da kuma kwanciyar hankali.." daga haka ta katse wayar kana ta kashe ta ma gaba d'aya. .. A 6angaren sa kuwa kae tsaye part d'in sa ya wuce, da sallama ya shiga bedroom d'in bayan ya saka key ya bud'e, daga inda take zaune ta d'aga kae ta d'an saci kallan sa tana amsa sallamar akan la66an ta kana tayi saurin d'auke kae ganin yana shirin kama ta, murmushi yayi yana k'arasowa cikin d'akin yayin da tayi k'asa da kan ta har yanzu ta kasa dena jin kunyar sa. Kallan ta ya cigaba dayi bayan ya nemi gefen gado ya zauna yana ji kamar ya had'iye ta, ita kuma se kakkaucewa take yi. "Kin tashi lafiya? Ya k'arfin jikin?" wannan tambayar ma da ya mata duk se ta sake diriricewa ta dinga mutsu_mutsu a inda take zaune kamar me shirin tashi daga wajen, ganin yadda ta tura bakin ta gaba ne ya sanya shi sakin wani murmushin yana jin duk wani 6acin rae da ya taho da shi daga 6angaren Muneerah yana zagwanyewa yana yin nasa wajen. A hankali kuma ya sauko daga kan gadon zuwa kan daddumar da take kae ya zauna k'afar sa a tank'washe dab da ta ta k'afar, se tayi saurin yin baya, yayi saurin rik'o k'ugun ta da hannun sa na dama kafin ya saka d'ayan hannun na sa ya d'ago da fuskar ta cikin tafin hannun sa ya d'aga ta tana kallan sa kana ya zuba mata idanun sa, lumshe idanun ta tayi ko zata samu bugun zuciyar ta ya saetu, ya d'an sauke numfashi kafin ya kae hannun sa kan fuskar ta ya ta6a, har yanzun dae da zafi, hakan ne ya sanya shi sakin ta, ta sauke numfashi a hankali tana jin dad'in yadda ya sake tan, be san sanda murmushi ya k'wace masa ba, se ya saka hannu ya janyo abincin daya shigo da shi ya saka shi a tsakiyar su kana ya kalle ta yace "Zaki iya ci? Ko na taemaka miki?" girgiza kae tayi tana d'an yamutsa fuska dan so take ta sake kwanciya saboda yadda kwanciyar ta mata dad'i, be d'auka za tace komae ba se yaji ta furta "Baki na ba dad'i" shiru ya d'an yi yana nazarin ta kafin yace bayan ya lumshe idanun sa "A fara yin allura toh?" ya fad'a har lokacin yana kallan ta, dan so yake yaga reaction d'in ta, da sauri kuwa ta d'aga ido ta kalle shi, idanun ta suka fad'a cikin nasa, ya kashe mata ido d'aya cikin wani irin salo, lumshe idanun ta tayi tana sauke numfashi kafin ta bud'e baki da k'yar tace "A'ah ni dae.." "Toh mu ci abincin" ya fad'a yana sake matsar da abincin gaban ta, hannu ta saka ta d'auki spoon d'in ta fara coccokala shi a ciki kawae ba tare da ta soma ci ba, yana sane da ita dan haka kawae seya kar6e spoon d'in ya rik'e shi a hannun sa ya d'iba ya kae bakin ta "Bari na baki.." ya fad'a sanda ya d'ebo abincin ya kae bakin ta, kamar tayi musu se kuma kawae ta kar6a duk da yadda bakin ta yake babu d'and'ano ko kad'an. Babu laefi ta d'an ci babu laefi, se da ta sha ruwa sannan ya mik'a mata magani yace "Pls kada kice a'ah ki kar6a ki sha" narkar da fuska tayi tana langa6ar da kae gefe "Allah ni na warke" ta fad'a a narke kamar zata saka kuka, jinjina kae yayi yana d'age girar sa duka biyun kafin yace da wani miskilin murmushi akan fuskar sa "Uhmm, haka nake so Baby gurl, kalli cikin ido na ki fad'a min kin warke koh?" se yanzu da yayi maganar kuma sannan taji wata matsananciyar kunya ta kamata hakan ne ya sanya ta kasa kallan shi, yayi murmushi kana ya kamo hannun ta cikin na sa yace bayan ta saka mata maganin a hannu "Ki sha don Allah.." tun kafin ya k'arasa ta d'auki ruwan ta kae maganin bakin ta cike da fatan kada taji d'and'anon sa ballantana ya dawo mata, cikin ikon Allah kuwa har ta had'iye bata ji d'and'anon sa a bakin ta ba, se ajiyar zuciya kawae da ta dinga saukewa kamar zata yi vomiting. Jan ta yayi cikin jikin sa ya rungume yana shafa mata baya a hankali, tayi lamo tana cigaba da sauke ajiyar zuciyar, ta kae wajen minti 1 sannan ta koma sauke numfashin a dae_dae har lokacin idanun ta na rufe. "Babe!" ya fad'a a saetin kunnen ta yana hura mata iska a ciki, da sauri ta bud'e dara_daran idanun ta da suka d'an sake tasawa suka kuma yi d'an ja, se idanun nata suka fad'a cikin na sa, kashe mata idanu yayi kafin yace cikin wata irin murya kamar ba ta sa ba "I luv u!" lumshe idanun ta tayi tana sake shigewa cikin jikin sa, murmushi na su6uce mata, karo na farko tun jiya rabon da tayi murmushi se yanzun, lokaci d'aya kuma tana shak'ar daddad'an k'amshin da ke tashi daga jikin sa, ajiyar zuciya ya sauke yana sake yi mata rumfa da duka hannayen sa biyun. Haka yinin ranar ya cigaba da kula da ita kamar wata jaririya, babu laefi ta d'an ji dama_dama a gaba d'aya jikin ta, se dae har zuwa lokacin jikin ta be gama yin k'wari ba, zazza6in kuwa babu jimawa ya sauka, ranar dae gaba d'aya yinin na ta a kwance tayi shi, ko tana jikin sa ko kuma tana kan gado saboda kwanciyar tafi mata dad'i, shima be hanata ba ya bar ta musamman da ya fahimci hakan na mata dad'i, kuma a yanayin da take ciki ya san kwanciyar se ta fi mata dad'i. Ba shi ya bar d'akin ba se bayan Isha'i sannan ya koma part d'in Muneerahn saboda kwanan ta da ya bawa Ayrah a jiya. ... Wajen k'arfe 10pm yana zaune a parlourn Muneerahn TV na kunne tana aekin ta se dae shi sam hankalin sa baya wajen, da dae yaga ba abinda kallan ze k'ara masa se ya tashi kawae ya kashe T.Vn ya wuce bedroom na ta, kamar koda yaushe yanzun ma da sallama ya shiga d'akin, ba tare da ya jira ta amsa ba ya shige ya k'arasa kan gadon ya d'auki blanket da pillow ya soma takawa zuwa kan kujerar dake cikin d'akin, da sauri ta kalle shi sanda take zura rigar bacci ganin ko inda take be kalla ba. "Baby ina kuma za ka je? Bayan ga kan gado na" "Bana buk'ata" ya fad'a ba tare da ya kalle ta ba, ya ajjiye pillown kan kujera sannan ya hau kan kujerar, da sauri ta sake fad'in bayan ta soma takowa zuwa inda yake "Haba Baby yau fa kwana na ne, me kake shirin yi haka?" wani banzan kallo ya watsa mata ganin tana so ta maeda shi wani wawa, kamar ba zece komae ba se kuma can yace "So kike na k'ara miki gajiya akan wadda kika yi? Pls ki je kiyi baccin ki Madam" yayi maganar yana jan blanket ya lullu6e jikin sa da shi. Ji tayi kamar ta fashe da kuka, ta cigaba da kallan sa duk da yana cikin bargo, se kuma ta juya tana murmushi, ta k'arasa bakin gadon ta, ta bud'e side drawer ta d'auko kwalbar turaren nan da Aunty Zeenah ta ba ta ta bud'e shi. Tun kafin ta shafa k'amshin sa ya soma karad'e d'akin, daga cikin bargon ya soma jiyo k'amshin yana d'an 6ata rae gami da tuna inda ya ta6a jin wannan k'amshin, se kuma ya yaye bargon yana kallan inda ya tabbatar daga nan k'amshin yake fitowa, yamutsa fuska yayi tsigar jikin sa na tashi yarr, dae_dae lokacin da idanun sa suka yi tozali da Muneerah rik'e da kwalbar turare a hannun ta, cike da mamaki ya cigaba da kallan ta kafin a hankali ya mik'e fuskar sa a matuk'ar tamke ya k'arasa inda take, tunda idanun ta suka yi tozali da shi sanda yake takawa zuwa inda take jikin ta yayi matuk'ar sanyi, ta kasa ko da motsi ne, se d'aukar hannun ta da tayi wanda ke d'auke da murfin turaren ta kifa akan kwalbar turaren, tana k'ok'arin yadda kwalbar ya k'araso wajen, bata ta6a tunanin ze gan ta ba, bata ta6a tunanin ze gane itace ke amfani da wannan turaren me d'aga hankali da tunani ba. Wani kallo