← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 90

Sashe 23

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da asibiti na kae na wanda shima Abbun ne ya bud'e min, abinda ya kawo ni garin nan kuwa, sanadin k'anin mahaefi na ne da nazo sanda ze bud'e wani Company, tunda nazo kuma Abbu yace kar na zauna haka nan shi ya nemar min wannan lecturing d'in cikin makarantar nan duk da ni ba za6i na bane, da son raena ne aekin da nake kawae ya ishe ni, toh dae dan farin cikin Abbun yasa na fara lecturing d'in, se dae yanzu maganar da nake miki tuni Daddy (k'anin Abbu) ya gama bud'e Companyn komae ya kammala, dan haka ina saka ran ni kam daga wannan semester na gama koyarwa a makarantar nan... And.. ina me tabbatar miki In Sha Allah duk sanda muka had'u zan baki labarin a nutse" ya k'arasa maganar yana sauke wani gauron numfashi lokaci guda kuma yana 6alle murfin gorar ruwan daya ajje ya shanye tass sannan ya ajje ta yana sauke numfashi, dariya ya bata daga inda take zaune jin yadda yake sauke numfashi kamar wanda yayi wani aekin wahala, se dae kuma a ran ta tana cigaba da mamakin rayuwar Rk d'in, lallae Allah abin godiya ne da kuma d'aukaka, dan kuwa shine me yin yadda yaso a kuma lokacin daya ga dama "Uhmm, fad'a min kad'an daga naki kafin mu had'u" sauke numfashi Ayrah tayi sannan a hankali ta shiga sanar dashi makarantar da tayi da er gwagwarmayar da tasha har zuwa yanzun, duk da ba wasu shekaru ne da ita na azo a gani ba, ga kuma ga6un ta dake damun ta, amma duk yadda take ganin Raj d'in take kuma jin sa a jikin ta bata sanar dashi abubuwa da dama daga rayuwar su ba wanda take ganin kamar sirrin su ne wannan da ba kowa ya kamata ya sani ba, shiru Rk yayi yana nazarin maganganun Ayrah a ran sa yana sake tsarkake sunan Allah "Ikon Allah" kuwa ya maemaeta yafi sau nawa "Akwae wata magana dana ke so muyi, amma kafin nan ina so ki gama exam kafin ki koma gida.." "Wace maganar toh?" ta fad'a kamar za tayi kuka, murmushi me sauti yayi sannan yace "Ae nace se kin gama exam tukunnah" shiru tayi tana tuna yanayin Rk d'in a cikin aji da kuma yanzun kamar bashi bane, kamar mutum biyu ne masu kama d'aya wanda wancan da yake shigar musu aji daban shi kuma wannan da suke waya daban "Promise?" ta fad'a tana d'aga yatsan hannun ta kamar yana gaban ta "Yeah.." "Ohk". Wayar sa da tayi k'ara bayan ajiye wayar Ayrah yabi da kallo, ji yayi kamar kar ya d'aga dan a yanzun yana so ne ya dinga samun lokacin daze zauna kawae ya dinga hasaso kyakykyawar fuskar ta, kallan wayar yayi dan ganin me kiran nasa, seya kae hannu ya d'auki wayar ganin Daddy ne ke kiran, ya kae kunnen sa da sallama d'auke a bakin sa "Likita kana ina ne?" "Ina d'aki" yayi maganar cikin girmamawa "Ohk ka same ni a d'aki na idan babu abinda kake" babu musu ya amsa da "toh" sannan ya mik'e bayan ya jefa wayar a aljihun sa ya zura takalmi ya fito daga d'akin nasa cikin nutsuwa. Kae tsaye parlourn Daddyn ya wuce, a hankali ya zura kan sa ciki yanzun ma da sallama a bakin sa cikin nutsatsiyar muryar sa, amsawa Daddy yayi yana kallan sa lokacin da yake k'ok'arin zama a k'asa "Tashi ka zauna akan kujera magana nake so muyi ae" seya d'an yi murmushin nan nasa me tsada wanda ke sake fito da aenahin tsagwaron kyawun sa ya zame akan kyakykyawan Carpet d'in dake shimfid'e a k'asan d'akin yace "Daddy nan ma ya isa" murmushi Daddy yayi a ransa yana sake jaddadawa kan sa lallae abinda suka yanke ba suyi laefi ba "Amm yaushe zaku yi hutu ne?" seda ya d'an yi shiru sannan yace "Ina tunanin baza mu wuce 1 month ba" "Toh Allah ya taemaka, me kake shirya mana zuwa lokacin?" yamutse fuska yayi dan shi sam bema fahimci maganar Daddyn ba dan haka ya furta abinda ke ran sa "Daddy ina ganin zan ajiye lecturing d'in nan gaskiya am tired" ya fad'a dan da gasken ya gaji da lecturing d'in musamman daya kasance dama ba za6in sa bane, ga kuma muhimmiyar maganar da yake so daya koma yayi wa Abbun magana akae, wadda yake had'e da albishir d'in daze fad'a musu su duka cewar bayan tsawon shekarun nan ya had'u da Ayrah, wanda hakan na nufin Abbu ze had'u da Abba, may be ma abotar su ta da ta dawo sabuwa duk da be san abinda yasa kowa yayi watsi da d'an uwan sa ba "Haba haba dae Raj ka gaji kuma?" jinjina kae yayi ba tare daya kalli Daddy ba "Toh ya za kayi da Abbun ka kuma?" Daddy ya tambaya yana kallan sa "Zan same shi da maganar In Sha Allah" "Toh hakan ma yayi, seka maeda hankalin ka waje guda kenan, Allah ya taemaka.. Ameen" shiru ne ya biyo baya Daddy na tunanin ta inda ze farawa Rk maganar se can dae yayi k'arfin halin fad'in "Kana jina koh?" "Ehh.." Rk ya fad'a, kafin Daddy ya kae ga cewa komae wayar sa ta shiga ruri, seya janyo wayar yana kallan me kiran, da sauri ya kalli Rk yace "Raj je ka, za muyi maganar In Sha Allah, zan yi waya ne yanzun" jinjina kae kawae yayi ba tare da yace komae ba ya mik'e ya fice daga d'akin. ... A d'aya 6angaren kuwa Umma ce ta fito daga d'akin ta, dae_dae lokacin da Yah Sadeeq ke tsaye bakin k'ofar d'akin sa hannun sa dafe da k'ofar d'akin yana sauke numfashi kamar wanda yayi tsere, da sauri Umma ta k'arasa tana kallan sa "Sadeeq lafiya kuwa?" tayi maganar tana rik'o shi "Haki kake?" ta fad'a sanda ta gama d'ago shi tana kallan fuskar sa, da sauri ya k'ak'alo murmushi ya wanzar a fuskar sa dan bega sanda ta fito ba se maganar ta kawae yaji, sannan yace bayan ya ida mik'ewa tsaye "A'ah Umma me kika gani? Kawae gajiya ce" ya fad'a cikin k'arfin hali, seta saki ajiyar zuciya sannan tace "Toh jeka kwanta ka huta haka nan Uhmm?" jinjina kae yayi kawae yana juyawa ya koma cikin d'akin a hankali, ya baje kan gado yana jin yadda k'irjin sa ke masa wani irin zafi kamar ze rabu da jikin sa. Komawa Umma tayi ta zauna tana d'ora hannun ta akan kuncin ta, lamarin duniyar nan sosae yake bata tsoro musamman a en kwanakin nan da abinda zasu ci yake gagarar su, dae_dae lokacin da Abba yayi sallama cikin gidan, Umma ta mik'e cikin son kawar da damuwar dake shimfid'e kan fuskar ta tace "Sannu da zuwa" "Yawwah sannu ka dae" ya fad'a yana son karantar yanayin ta, seta riga shi yin gaba dan bata so ya karanto raunin dake tattare da ita ballantana har shima yaji ya sake karaya "Wallahi ban samu komae ba" Abba ya fad'a muryar sa a raunane gwanin ban tausayi bayan ya zauna, ajiyar zuciya Umma tayi sannan tace "Babu komae, Allah ze kawo ko zuwa gobe ne In Sha Allah" seya jinjina kae kana yace "Ina wannan yaron? Allah yasa yaci wani abun ko dan rashin lafiyar sa" kallan d'akin da Yah Sadeeq ke ciki Umma tayi sannan tace "Ehh toh yaci zance, amma kasan halin sa ba son cin abincin nan yake ba, yanzu haka ma yayi bacci" "Bacci kuma? Lafiya dae koh?" Abba yayi tambayar cike da fatan lafiyar ce, ba tare da tunanin komae ba Umma tace "Ehh lafiya k'alau" "Toh madallah, bari na kira mana Ayrah" Abba ya fad'a yana fiddo wayar sa daga aljihu, da sauri Umma ta kalle shi tace "A'ah Abban su kada ka kira ta, bana so ta fahimci ko da akwae wata matsala daga nan wajen mu, kasan halin yarinyar nan" shiru Abba yayi cikin na'am da zancen nata kafin yace "Toh shikenan.." daga haka yayi shiru yana cigaba da tunanin rayuwar su ta baya data yanzu, shida yake ajiye abincin wata a gidan sa tafi tafi ya koma siya kad'an kad'an, yanzu kuma da yanayin rayuwar ya sake juyawa se gashi wataran a cikin gidan sa an tashi babu ma abincin da za'a ci, ya riga yayi na'am da k'addara, ya yadda da ita kuma yasan Allah ne ya k'addaro masa ita amma ta sanadin Abbu, Abbu yayi musu wani gi6i a rayuwar su da baza su ta6a mantawa ba, ta dalilin sa abubuwa da dama sun faru kuma suna kan faruwa ma, baya tunanin ze iya yafewa Abbu abinda ya masa koda kuwa basu sake had'uwa a duniyar nan ba, yana jin koda yace zeyi hakan ma toh kuwa wani 6angaren nashi baze ta6a yafewa kan sa ba, abinda ma baya tunanin ze faru kenan, wanda shi a gare shi ma baya fatan sake had'uwa da koda me irin halin Abbu ne ballantana kuma shi kan sa Abbun...... Mhiz Innocent...... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* *TITAN'S OF TALENT* Page 025_026 ___Kae tsaye Hostel suka wuce su biyun har lokacin suna tattauna maganar da tak'i k'arewa, dukan su mamaki yak'i sakin su, a haka har suka k'arasa d'akin su Jidda, ko sallama babu wadda ta iya a cikin su saboda yadda suka k'agu su isar da labarin nan, Jidda dake facing k'ofar d'akin tace "Kae jama'a lafiya kuwa?" bud'a hanci Abeeda ta shiga yi ita a dole ta kawo musu abu me muhimmaci "Jarida na kawo muku me tsada!" tayi maganar sanda take neman waje ta zauna, sakkowa Ruks tayi daga kan gadon ta sannan ta k'araso tana kallan Abeeda tace "Kinga kawae ki fad'a mana meya faru?" "A'ah wallahi nawa zaku siya?" Abeeda ta fad'a tana sake gyara zaman ta, k'aramin tsaki Bahijja ta saki kafin tace "Don girman Allah ki fad'a mana, haba mana" dariya Abeeda tayi kana ta sakko da jakar ta dake mak'ale a kafad'ar ta ta sanya hannu ta d'akko wayar ta tace lokaci guda kuma tana danna wayar "Ke kam Bahijja Allah ya shirye ki da son gulma wallahi" "Oho dae, mu dae fad'a mana kawae" "A'ah an shiga 3" Abeeda ta fad'a tana d'an bud'e ido ganin da tayi wayar ta ta
Chapter 23 · 0% Book details