Sashe 31
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sa sanda yake neman waje ya zauna yana lumshe idanun sa saboda gudun da bugun zuciyar sa keyi wanda ya wuce misali, ba k'in biyan kud'in shekara ba baya tunanin ko da abinda yafi hakane ya shiga tsakanin Abbu da Abba ze iya bari Ayrah ta auri wanin sa, wanin ma a gaban sa, Abba yace baze auri er sa ba se gashi wani ya d'auko ta wata uwa duniya dan a d'aura musu aure, toh meyasa baze yiwa kan sa wannan fad'an har yayi winning ba? Ko me zeyi se yayi yadda yayi aka d'aura musu aure a garin nan ba da wannan k'aton mutumin ba dashi za'a d'aura, tun da yasan ko d'aukar ta yayi ya maeda ta gidan su daga nashi iyayen har nasa ba amincewa zasu yi da auren junan su ba, dan haka ze zage damtse yasan yadda zasu yi suyi auren sirri in dae hakan ce mafita, ya ceci zuciyar sa sannan ya ceci Ayrah daga hannun wannan mugun mutumin "Malam daga ina kae kuma?" Me gari ta fad'a yana kallan Rk, ajiye numfashi Rk yayi sannan yace har lokacin be kalli kowa ba "Soyayya muke yi da ita, kuma bazan iya bar wa wani ita ba" yayi maganar a nutse kae ba zaka ta6a cewa tsara zancen yayi ba, bin sa da kallo Alhaji Mato yake yi dae_dae lokacin da Rk ya d'aga kan sa ya watsa masa wani banzan kallo me nuni da abubuwa da dama, da sauri Alhaji Mato ya d'auke kan sa yana jin tabbas idan yace wani abun asirin sa ka iya tonuwa mutuncin sa ya zube a banza, dole yayi tunanin mafita, d'aga kae Me gari yayi ya kalli Ayrah dake zaune kamar wadda aka kafe ta yace "Toh ke kin ji? Shin kina da ta cewa?" se a lokacin Ayrah ta d'aga kae ta kalli Me gari tana jin zuciyar ta kamar zata tarwatse, kwata kwata ta kasa bud'e bakin ta ballantana tace wani abu, toh ta bud'e d'in ma tace mene? Gaba d'aya ta kasa fahimtar wannan wasan kwaekwayon da suke gabatarwa a gaban ta, a hankali ta shiga tuna maganar Muttala se kawae ta shiga girgiza kae kamar wata kad'angaruwa, sauke numfashi Me gari yayi sannan ya kalli Alhaji Mato da kuma Rk yace "Ina ganin dukan ku ku tashi ku tafi, zan rik'e ta a hannu na zuwa gobe kafin a kira magabatan ta, gobe bayan an sakko daga masallaci ni da kae na zan d'aura mata aure da wanda ta za6a a matsayin wanda take so!" dukan su kallan Me garin suke yi, Alhaji Mato yana ji kamar ya tashi ya rufe Rk da duka, idanun nan nasa suka k'ara yin jawur, ta 6angaren Rk kuwa gaba d'aya tunanin sa ya tafi yadda zeyi ya shawo kan Ayrahn ta amince da auren sa cikin garin nan. Kamar wata kurma doluwa kuma bebiya haka take bin wadda akace ta mata jagora zuwa cikin gidan Me garin, har lokacin ta kasa amincewa ba wasan kwaekwayo akeyi ba, a haka har suka k'arasa cikin wani madaedaecin d'aki seda ta zauna sannan wadda ta kawo tan ta fice daga d'akin. ... A zaune take kamar wata munafuka cure waje d'aya, kuka kawae take yi cikin rashin sanin abin yi, wannan mutumin kawae take jira yazo ya mayar da ita gida amma har yanzun shiru, ta rasa gane dalilin ta na zuwa k'auyen nan, abinda ya sake jefa ta cikin wani mad'aukakin mamaki shine ganin Rk da tayi, shin ko dae mafarki take yi ne bata sani ba? Tabbas ma babu mamaki mafarkin take yi dan kuwa wannan dae yafi kama da mafarkin. Tana nan zaune bata umm bata umm umm tunda kuma ta zauna ta kasa koda kae ruwa bakin ta ne ballantana akae ga cin abincin da aka dinga dire mata, ita bata ta su take yi ba, abinda kawae take buk'ata yanzu shine ta samu waya ta kira Abban ta ko Yah Sadeeq amma har yanzu bata ga wanda zata iya samun waya a wajen sa ba "Ki zo ana neman ki" wata mata ta fad'a tana kallan ta, da mamaki ta d'aga kae ta kalle ta sannan cikin k'arfin hali ta furta "Don Allah zan iya samun waya a wajen ki?" da mamaki matar ta kalle ta cike da mamakin yadda taji tayi magana dan kuwa ta d'auka bebiya ce, se kawae ta girgiza kae tana cigaba da kallan kyawun Ayrahn da duk da yadda take a firgice hakan be hana shi fitowa ba "Muje koh?" matar ta fad'a tana cigaba da kallan ta, se kawae ta mik'e cikin rashin sanin abinyi tabi bayan matar kamar rak'umi da akala, a soron gidan suka tsaya sannan matar ta kalli Rk dake tsaye jikin bangon soron idanun sa a lumshe kamar me bacci "Don Allah kada ku dad'e, kaga dae da yadda akayi na barka ka shigo gidan nan, da Baba ma ya sani baze bari ba wallahi" "Nagode" ya fad'a yana bin ta da kallo sanda ta koma cikin gidan, wanda Ayrah ta gani ne ya sanya tayi kicin kicin da fuskar ta tana shirin komawa ciki yace a nutse "Batu ne akan auren ki da za'a gabatar gobe" kamar wadda aka tsaeda ta seta dakata tana jin bugun zuciyar ta na k'aruwa, murmushi yayi ganin yaci nasara tunda gashi har ta tsaya, kafin yace komae ta juyo tana kallan sa murya a raunane tace "Bana buk'atar taemakon ka, ban ce ka maeda ni gida ba dan bana buk'atar hakan daga gare ka, abinda nake so kawae shine ka bani aron wayar ka zan kira Abba na na sanar dashi inda nake zezo ya d'auke ni" kallan ta ya cigaba dayi yana jin muryar ta ta dake fita a raunane har cikin kwanyar sa, wani irin tausayin ta mara misaltuwa na ratsa shi amma yasan abinda zeyi, ya furta "Kada kiyi wannan kuskuren, kada ki sake ki kira Abban ki, dan kuwa babu wanda ze yadda dake akan ba guduwa kika yi da kan ki ba, shawara d'aya ni kae na ba dan wani abun zan taemake ki ba se dan kasancewar ki er uwa ta musulma" ya d'an tsagaeta yana jin wani irin ciwo a cikin zuciyar sa wanda har hakan seda ya bayyana a cikin muryar sa da kuma kan fuskar sa sannan ya cigaba da fad'in "Taemako d'aya zan miki shine zan kar6i auren ki a matsayin wadda muke soyayya, sannan a bani ke na tafi da ke zuwa Kano, tun kafin ma mu shiga cikin Kanon zan sawwak'e miki seki tafi gidan ku, kin ga babu wanda ze ji labarin auren idan bake kika fad'a ba.." "Ya ishe ni haka malam, babu ruwan ka da rayuwa ta, na fad'a maka ka fita a rayuwa ta ni da iyaye na, ka bar ni zan auri koma wanene tunda ba zaka bani wayar ta ka bana buk'atar wani taemakon" ta fad'a sanda wasu kyawawan hawaye suka shiga zarya akan kuncin ta, runtse idanun sa yayi daga inda yake tsaye, baya tunanin kome zata yi a yanzu kam ze bata wayar sa tayi kira da ita, bama shi ba koda wani yaga ze bata wayar tayi kira toh ze san yadda zeyi ya hana wannan abin faruwa, kenan a 6ata masa budget? Kae ina hakan baze ta6a faruwa ba "Kina tunanin mutumin daze aure kin ze sake ki kafin ya maeda ki gida? Yana son ki fa, idan da baya son ki baze kawo ki wata uwa duniya a d'aura muku aure ba, ni kuwa fa? Yanzu babu ko d'igon son ki a cikin zuciya ta, dan haka kawae zan aure ki ne dan na taemaka miki ki fita daga hannun wannan mutumin, muna barin k'auyen nan kuma zan rubuta miki takaddar ki da sharad'in ba zaki sake neman inda nake ba" ya k'arasa maganar yana kafe ta da idanun sa masu kyau da kwarjini "Waye ze ne me ka? Tirrr!" ta fad'a tana sake tuna halin mahaefin sa, so take ta tambaye shi toh shi meya kawo shi nan d'in? Amma tasan idan tayi tambayar ze iya tunanin wani abun dan haka tayi shiru tana cigaba da kallan wani wajen, jin da yayi bata sake cewa komae akan zancen sa ba hakan ya alamta masa zata iya amincewa kenan da maganar tasa, lallae ya sake yadda Ayrahn har yanzu yarinya ce, seya saki wani shu'umin murmushi yana shafa bak'in sumar dake shimfid'e akan farar fatar sa da hannun sa kana yace cikin sake karantar yanayin kyakykyawar ta sa "Idan kin amince zamu iya yin hakan a rubuce saboda ki tabbatar da abinda na fad'a gaskiya ne, wato dae ina nufin zamu yi auren yarjejeniyar yini d'aya ne!!" ya fad'a dan cikin ran sa ya shiryawa kowanne irin k'alubale daze biyo bayan auren ta da yayi, baya jin ko d'arr akan abinda ya aekata d'in ko da zasu dawwama ne cikin auren sirri hakan ba damuwar sa bace, dan kuwa daya rasa ta gwara ya jurewa kowanne kalar abu daze tunkaro shi komae zafin sa kuwa... End of ZAZZAFAR KAUNA (CHAPTER ONE) In Sha Allah zamu d'ora da ZAZZAFAR KAUNA (CHAPTER TWO) nan da kwana 2 idan na huta, shima FREE ne duk dan jin dad'in ku Dan neman qarin bayani se a tuntu6e ni ta 08124818273 https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* Page 031 ___Manyan fararen idanun ta da colour d'in su ya sauya ta d'aga ta zube su a kan sa sanda yake maganar, ta cigaba da saurarar sa tana nazarin kowacce kalma da yake fad'a, sosae k'irjin ta ke mata wani irin suya yana zafi, seta shiga jera ajiyar zuciya kafin ta durk'ushe a wajen tana sakin wani marayan kuka na rashin sanin abinyi, a hankali kukan da take yake fita idanun ta a lumshe haka zalika zuciyar ta na cigaba da zafi, daga inda yake ya runtse idanun sa yana jin kukan nata har cikin jikin sa, seya sauke wata ajiyar zuciya yana d'auke kae daga inda take durk'ushe, ya zama dole ya koyi wofantar da al'amuran ta ko dan saboda wannan kasadar da yake neman aekatawa, idan ba haka ba tabbas ze koma shine me laefin ba wasu ba, duk da yadda kukan nata ke ratsa shi hakan