Sashe 43
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
amsa masa sallamar sanda yake k'arasowa cikin gidan, a nutse ya tsuguna daga gefen tabarmar da Yah Sadeeq ke kae kan sa a k'asa ya furta "Barkan ku da wannan lokaci.." cigaba da kallan sa Umma tayi, da alama har yanzu nutsuwar sa tun ta yarinta tana nan, haka zalika kamannin sa suna nan se dae kamar ma yanzun an k'ara masa kyau ne "Barka dae.." Abba ya fad'a "Ka zauna mana" Yah Sadeeq ya fad'a ganin har lokacin be zauna ba, shiru ya d'an yi yana jiran jin ta bakin wani daga cikin Abba ko Umma, kamar sun san me yake nufi kuwa se Umma tace "Ka zauna mana" se a lokacin ya zame takalmin k'afar sa sannan ya zauna har kuma lokacin be kalle su ba, ya ajje envelope d'in dake hannun sa a gefen sa, seda ya d'an numfasa sannan ya fara magana a nutse "Abba.. Zuwa nayi in rok'i alfarmar ka don Allah.. Sannan kuma in baka hak'uri akan abinda ya faru.. bazan 6oye maka ba Abba a lokacin da naga wani na na neman auren Ayrah hankali na ya matuk'ar tashi, nasan abinda ya kamata inyi shine in d'auko ta in dawo muku da ita, toh amma bani da tabbacin idan na dawo da ita zaku aura min ita, ko kuma ita ta amince da aure na saboda yadda ta nuna a lokacin kwata kwata itama ba zata ta6a aure na ba, kuma a lokacin bansan dalilin ta na hakan ba Abba yasa kawae na yanke shawarar neman auren ta acan d'in idan yaso idan muka dawo na shirya kar6ar koma wane irin hukunci ne, duk da banyi la'akari da ku yaya zaku d'auki al'amarin ba, amma don Allah kuyi hak'uri Abba, ku min afuwa don Allah.." ya k'are maganar yana sauke numfashi kamar baze d'ora ba se kuma ya janyo envelope d'in gefen sa ya cigaba da fad'in "A yanzu na gano dalilin da yasa kuka hanani auren Ayrah Abba, ku dubi girman Allah ku yafe mana mu masu laefi ne, kuma yanzu haka gashi na dawo maka da takaddun ka badan mu biya ka abinda muka yi maka ba, a'ah inaso ne na fara warware wannan matsalar kamin inje gata gaba.." kallan envelope d'in Abba yayi sannan ya girgiza kae yana murmushi "Shi Kabeerun ne ya aeko ka?" seda ya d'an yi shiru sannan ya girgiza kae cike da takaeci kana yace "A'ah Abba.." sake girgiza kae Abba yayi dama yasan za'a rina "Ka d'auki takaddun ka maeda su inda ka gan su, duk lokacin da Kabeeru ya gane yayi laefi kuma yana neman yafiya ta seya d'auko yazo ya bani, kada ka sake saka kan ka cikin wannan maganar.. Zancen aure kuma dani da mahaefiyar ta duk bamu so ba, ba kuma mu ta6a tunanin hakan ze kasance ba saboda abinda mahaefin ka yayi, se dae ya zamuyi? Allah ya riga ya rubuta ita matar ka ce, ko da ba ta hakan ba in dae Allah ya nufa se anyi auren nan se kaga dukan mu ma mun mutu kuma a d'aura muku auren, dan haka ni na yafe maka daga kae har Ayrahn in dae akan auren nan ne, na san iyayen ka ma basu sani ba saboda haka wannan ya rage naka kaje kayi musu bayani da kan ka, ku sasanta da kan ku.." a hankali ya lumshe idanun sa yana jin wani nauyi na raguwa daga cikin k'irjin sa, ko babu komae ya samu matsala d'aya ta kau, yanzu se yaji da d'ayar data rage masa "Nagode sosae Abba.. Allah ya saka da alkhaeri.. Umma nagode" ya fad'a yana mik'ewa "Allah ya tsare" Umma ta furta da murmushi kan fuskar ta dan seta ke ji kamar little Raj ne wanda ta sani tun shekarun baya, d'aukar envelope d'in yayi a ran sa yana sak'a lallae akwae aeki a gaban sa, Yah Sadeeq ne ya mik'e ya taka masa zuwa k'ofar gidan, be baro wajen ba seda Rk d'in ya hau motar sa sannan ya juya, ya kasa hak'urin rashin ganin ta tun shigowar sa dan haka ya furta "Amm pls Yah Sadeeq bata nan ne?" juyowa Yah Sadeeq yayi kana ya d'an yi murmushi sannan yace "A'ah tana d'aki, ko a kira maka ita ne?" da sauri ya girgiza kae yana d'an lumshe idanun sa, duk da yanda idanun sa ke k'ishirwar ganin ta amma gwara ya hak'ura dan haka ya furta "A'ah barshi kawae nagode.." daga haka yaja motar sa ya bar layin yayin da shi kuma Yah Sadeeq ya koma cikin gida. Kallan Abba Umma tayi bayan fitar Rk d'in "Abban su yaya wannan auren ze kasance kenan?" d'an shiru Abba yayi sannan yace "Wannan ya rage nasa Ruk'ayya.." "Ina ganin kafin ta koma ko kae zakawa Baban nasa bayanin yanda auren ya kasance?" da sauri Abba ya kalli Umma cike da mamakin jin kalaman ta "Ruk'ayya kin san me kike cewa kuwa? Ashe har Kabeeru yayi arzik'in da zan je wajen sa yi masa bayanin wani abu? Bakya tunanin wani abu ze d'arsu a cikin ran sa?" ya k'are maganar yana girgiza kae sannan ya d'ora da "Bana fatan wannan ranar tazo.." se kuma a lokacin itama Umman ta fahimci hakan dan haka ta furta "Toh Allah ya kyauta, zamu iya bashi ita?" "K'warae babu damuwa.." Abba ya fad'a. A hankali Umma ta yaye labulen d'akin ta shiga, tana kwance akan gadon ta kamar me bacci, k'arasawa Umma tayi kan gadon tana fad'in "Ayrah wae bacci kike yi ne?" da zata iya shiru zata yi dan haka kawae take jin kunyar Umman tun zuwan Rk "A'ah Umma" ta fad'a har lokacin tana kwance "Toh tashi zamu yi magana.." Umma ta fad'a bayan ta nemi waje ta zauna, tashi zaune Ayrahn tayi tana had'e jikin ta kamar me jin sanyi "Meyasa kika k'i fitowa ko gaesawa kuyi?" tura d'an k'aramin bakin ta tayi sannan tace "Ummaaa.." taja k'arshen sunan, murmushi Umma tayi tana girgiza kae sannan tace "Ki bar damun kan ki, In Sha Allah in dae mu ne mun amince da auren ku, dan haka ki bar damun kan ki haka nan, Allah ya tabbatar da alkhaerin sa" hannun ta ta d'auka ta rufe fuskar ta tana murmushi, duk da har lokacin akwae d'an haushin sa kad'an da take ji amma yanzu da Umman tayi magana taji matuk'ar dad'i, seta d'ora kan ta akan cinyar Umman kawae ba tare da tace komae ba "Ayrah.." Umma ta fad'a tana murmushi.. ... Kwanakin da suka biyo baya amarya Muneerah ta cigaba da shirye_shiryen aure, yayin da 6angaren ango Raj yama manta da maganar auren musamman ma daya kasance shi kan sa Abbun ya fita a harkar sa saboda yadda ya lura sam auren baya gaban sa, dan haka hatta lefe Ummee ce ta saka aka had'a aka kae, be tashi sanin suna nan kan bakar su ba duk da yanda aka bashi katin d'aurin aure wanda tunda ya ajje su be sake bi ta kan su ba ballantana ko gayyata ce yayi, se ana i gobe d'aurin aure ya sake tabbatarwa sanda yaga gidan nasu ya fara cika da jama'a, haka zalika har lokacin be huta da sak'onni da kuma kiran wayar Muneerah ba, wanda gaba d'aya baya kulawa ita kuma kamar tsohuwar mayya bata hak'ura duk da yadda Mummyn ta tace tayi watsi da shi ze neme ta da kan shi amma ita ta kasa hak'uri, shi gaba d'aya hankalin sa da tunanin sa ya ta'allak'a ne akan yanda ze sami Abbu suyi magana akan zancen Abba amma be san ta inda ze soma ba shi kan sa. .... Washe_gari, fitowar sa kenan daga wanka wayar sa dake ajje kan gado tayi k'ara, seya k'arasa da mamakin me kiran nasa ganin asuba ce "Abbu" ya bayyana akan screen d'in, seda ya sake kallan agogon wayar dan sake tabbatar da lokacin da gaske ne ko dae shine yayi mistake, haka d'in ne dae dan haka kawae ya d'aga wayar yana karawa a kunnen sa "Raj!" "Na'am" ya fad'a muryar sa a d'an cunkushe "Ina fatan kana sane da d'aurin auren ka yau d'in nan koh?" Abbu ya fad'a shima ran sa a 6ace kuma babu fara'a dan yadda ya fahimci Rk d'in akwae rashin daraja a al'amarin sa kwana biyun, shiru na wajen second 30 sannan yace "Ehh.." daga haka Abbu ya katse wayar sa, gefen gadon ya nema ya zauna hannun sa dafe da kan sa yana jin yanda yake cigaba da sara masa, ga kuma bugu da k'irjin sa ke tayi kamar wanda yayi gudu, shi har yanzu ya rasa gane matsalar Abbu, Ummee, Daddy da kuma ita kan ta Muneerahn, shin ita bata da zuciya ne a k'irjin ta? Ya fad'a mata baya son ta baya son ta amma tak'i hak'ura, ya share ta ya share ta duk da haka tak'i hak'ura, toh ya suke so yayi da ran sa ne shi kam? Me zeyi da wata Muneerah a matsayin mata? Sam bata a gaban sa, kwata kwata yana ganin kamar za'a k'ware shi ne kuma itama a k'ware ta, amma tunda sun nace kuma sun dage bari ya bar su suyi auren duk abinda ya biyo baya kuma suyi kuka da kan su ba dae shi ba, tunda shi kam ya riga ya nuna musu baya ra'ayin ta ko kad'an. .. A cikin garin Kano aka d'aura auren Raj Kabeer da kuma Muneerah Abubakar, wanda saboda Abbu shine waliyyin amarya shi ya nemi da akawo auren Kano, shi kuma mahaefin ta bek'i hakan ba ya kawo shi nan d'in, daga lokacin da aka d'aura aure aka nemi ango aka rasa dama kuma da k'yar yazo wajen, seda Abbu ya masa tass sannan yazo wajen dan da farko cewa yayi ba zeje ba. Kae tsaye gida ya wuce ya sauya jamfa da wandon dake jikin sa da k'ananan kaya, fuskar nan kamar wanda akawa albishir da mutuwa, ya had'e ta tsaff kamar ze rufe wanda ya masa magana da duka, babu 6ata lokaci ya hau motar sa yaja be tsaya ko ina ba se gidan su Ayrah, dan yanzun ita kad'ae yake son gani ko ze samu sassaucin abinda yake ji a cikin zuciyar sa, a k'ofar gidan ya dakata ya lalubo number Yah Sadeeq