Sashe 12
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
suna gaesawa sosae kamar abokae, sanda Baban Zaenab d'in ya fahimci yadda Ayrahn ke zuwa makaranta a k'afa se be cewa Abba komae ba washe gari kawae yazo k'ofar gidan su Ayrahn ya d'auke ta da yake yana da babur wanda a shi yake d'aukar Zaenab ya kae ta makaranta, sosae Abba yaji dad'in hakan ya yiwa Baban Zaenab d'in godiya. Tun daga ranar ya kasance kullum Baban Zaenab d'in ke zuwa ya d'auki Ayrah su wuce makaranta tare.. Sanda Yah Sadeeq ya warke bayan doguwar rashin lafiyar da yayi Abba da kansa yaje wajen Baban Zaenab d'in ya sake masa godiya sannan ya fad'a masa zancen warkewar Yah Sadeeq d'in kuma shine ze cigaba da tafiya da Ayrah makaranta, dan zuwa lokacin abubuwa sun d'an yiwa Abba kyau ba kamar da ba, da farko Baban Zaenab d'in ya nuna k'in amincewar sa akan hakan, ya nuna ze cigaba da kae Ayrah tare da Zaenab makaranta, se da Abba ya ganar dashi sosae kafin ya hak'ura... Haka rayuwar tasu ta cigaba da kasancewa wataran su samu suci abinci wataran kuma se dae suyi hak'uri, ko kuma su samu suci abincin sau 2 a rana, harkokin yau da kullum kuma wasu se dae ayi hak'uri, idan kuma abu ya zama dole toh Abba kanyi iya k'ok'arin sa wajen samar da abun... _BAYAN WASU SHEKARU_ __A cikin shekarun da suka shud'e sosae abubuwa suka cigaba da faruwa, ta 6angaren su Ayrah dae babu wani chanji dan kuwa har zuwa lokacin Abba aekin Companyn nan yake yi, yayin da Yah Sadeeq ya gama Secondary School har da shekara 3 da wani abun ma amma saboda yanayin rayuwa yasa har lokacin be cigaba ba, se dae wani lokacin ya kan bi Abba Company ya d'an taemaka masa da wasu auyukan.. .. Shigowar ta gidan kenan da sallama sanye cikin Uniform riga da wando blue da kuma hijab me d'an girma fari, k'afar ta tana saye cikin wani takalmi sau ciki bak'i me d'an madaedaecin kyau, matashiyar budurwa er kimanin shekaru 15, fara k'all da ita, zuwa lokacin data fara zama budurwa sosae kyawun ta ya k'ara fitowa sosae, haka zalika hasken fatar ta ya k'aru, Umma dake zaune cikin d'aki tana cigaba da sak'ar wata hula da yanzun take yi tana d'an samun kud'i, ta amsa sallamar Ayrahn, k'arasawa Ayrah tayi zuwa cikin d'akin sannan ta zube akan ledar tsakar d'akin hannun ta kan k'afar ta tana k'ok'arin cire takalmin k'afar ta tace bayan ta d'an tura k'aramin bakin ta gaba "Washh Allah na" ta fad'a tana cigaba da cire takalmin ta, Umma da take kallan ta ta girgiza kae tace "Sannu malalaciya" dae_dae lokacin data gama cire takalmin ta juyo tana kallan Umma seta sake maraeraece fuska tana fad'in "Allah kuwa Umma na gaji da gaske" ta fad'a tana d'ora kanta akan cinyar Umman, ajjiye sak'ar hannun ta Umma tayi sannan tace bayan ta d'ora hannun ta akan Ayrah "Qualifying d'in ta fito?" seta tashi da sauri wani murmushi na k'wacewa akan kyakykyawar fuskar ta, ta saka hannu ta janyo jakar ta data ajje a gefe sannan ta bud'e ta d'akko wata farar takadda ta mik'awa Umma har lokacin murmurshi be bar kan fuskar ta ba "Umma naci.." ta fad'a dae_dae lokacin da Umman ta kar6i takaddar, ta karanta sannan ta d'ago tana kallan Ayrahn itama da murmushi kan fuskar ta tana jin wani irin dad'i mara misaltuwa "Alhamdulillah, Alhamdulillah" shine abinda Umman ke fad'a har cikin ranta tana jin dad'i "Umma nayi k'ok'ari koh? Abba ya dawo yaji abin farin ciki, dama Yah Sadeeq yace ze siya min waya idan naci" murmushi Umma tayi tana kallan Ayrahn sannan tace "Sosae ma kuwa Auta, kinyi k'ok'ari, Allah ya k'ara miki baseerah" "Ameen Umma na" ta fad'a tana maeda kan ta ta d'ora akan cinyar Umman "Toh a tashi ayi Sallah koh?" seta jinjina kae tana tashi zaune ta cire Hijab d'in jikin ta sannan ta zame k'aramin d'an kwalin da yake kanta wanda hakan ya bawa dogon bak'in kwantaccen gashin ta damar zubowa akan kafad'ar ta kasancewar ko Ribbon bata saka ta d'aure shi ba, duk da bata saka komae a kan ta wanda ya danganci relaxer hakan be hana gashin ta kwanciya kamar ta saka masa wani abun ba "Je kiyi wanka kizo na miki kitso.." Umma ta fad'a tana kallan ta, seta 6ata fuska kamar me shirin yin kuka, k'uruciyar ta na bayyana sosae tace "Don Allah Umma bana so.." ta fad'a tana maeda d'an kwalin kanta ta d'aure, seya kasance gashin nata ya d'an lek'o ta baya, mik'ewa tayi hannun ta d'auke da takalmin ta data cire dae_dae lokacin da Yah Sadeeq ya shigo cikin gidan da sallama, dukkan su suka amsa masa sallamar sanda ya k'araso cikin tsakar gidan, matashi ne kyakykyawa shima kamar er uwar sa, sedae bashi da wani jiki dan zamu iya kiran sa da siriri, da sauri Ayrah ta koma cikin d'akin ta d'akko takaddar nan sannan ta kalli Yah Sadeeq daya ida shigowa cikin d'akin tace tun kafin ya kae ga zama "Yah Sadeeq albishirin ka?" seya kalle ta yana murmushi kana yace "Goro fari tass" seta maedo da hannun ta data 6oye a bayan ta tace "Naci qualifying" ta fad'a tana mik'a masa takaddar, cikin farin ciki ya sanya hannun sa ya kar6a seda ya karanta sannan ya maeda duban sa kanta har lokacin yana murmushi yace "Dat's my lily, kinyi k'ok'ari sosae" ya fad'a yana dan jan kumatun ta, murmushi tayi kana tace "Yah Sadeeq alk'awarin mu.." "Ohh kinga har na manta kuwa" ya fad'a yana fiddo ido, seta d'an tura bakin ta kad'an sannan tace "Kae Yah Sadeeq.." dariya yayi yana d'an satar kallan Umma kana ya maeda duban sa kanta yace "Kada ki damu, ina d'aukar albashi zan siya miki Uhmm?" (shima yanzu ya samu aeki a wani company inda yake zuwa yayi aekin a biya shi k'arshen wata) er k'ara kad'an ta saki tana rungume Yah Sadeeq d'in cikin farin ciki tace "Nagode sosae Yah Sadeeq.." Umma dake gefen su tace tana kallan su "Gwara ma ka chanja wani abun ba dae waya ba, du du du ma yaushe ta dena shashanci balle kuma a d'auki waya a bata?" d'agowa tayi tana kallan Umma idanun ta sun cika taff da hawaye tace "Allah kuwa Umma na girma fa" "Toh in gani a k'asa" Umman ta fad'a tana mik'ewa ta fice daga d'akin, seta sanya hannu tana goge hawayen idanun ta, Yah Sadeeq yayi murmushi yana kallan ta yace "Kiyi shiru zan taushi Umma ta bari na siya miki er k'aramar waya ki dinga yin game, amma fa se kin min alk'awari.." "Ehh wallahi na yadda nayi" ta fad'a tana d'aga yatsan ta d'aya, dariya ta bashi dan haka seda yayi dariyar kana yace "Ohk toh yanzu yaushe zaku fara Neco?" "Aou na manta" ta fad'a tana dafe bakin ta kana ta ta6e bakin se kuma tace tana kallan Umma data dawo cikin d'akin "Umma wae kuma kinji se mun biya wani kud'in kafin mu fara Necon" da mamaki dukkan su suke kallan ta, Yah Sadeeq yace "Wane kud'in kenan?" seta k'ara ta6e baki kafin tace "Nima bansani ba" "Yanzu kuma naga kin ci exam d'in ae.." Umma ta fad'a tana kallan ta "Ehh Umma haka dae suka ce" "Toh Allah ya kyauta" Umma ta fad'a tana jinjina kae... Lokacin da Abba ya dawo yaji labarin Ayrahn taci exam d'in sosae yayi farin ciki, duk da kud'in da akace zasu bayar a makarantar hakan be wani dame shi ba, tunda dae gwamnati ta biya kud'i masu yawan da dama yake tunanin idan Ayrahn bata ci ba ya zeyi ya same su, se gashi cikin ikon Allah ma taci exam d'in.. ... Littafi ne a hannun ta na English tana duba wani aeki da yanzun malamin dake koyar dasu ya gama musu aekin ya fita, seta d'auki littafin tana d'an dubawa ko akwae abinda bata gane a ciki ba, k'awar ta Zaenab wadda suke kiran ta da zee ce ta ta6o ta tana fad'in "Kefa er raenin hankali ce, hala baki ji abinda ake fad'a ba" seta d'aga kae tana kallan ta kana tace bayan ta d'an 6ata fuska "Karatu fa nake, Allah kuwa banji abinda akace ba" "Toh cewa akayi wad'anda suka ci Qualifying suje PC na neman su" "PC kuma?" ta fad'a tana fiddo da manyan fararen idanun ta waje, sosae ta bawa Zee dariya dan haka tayi dariyar tana fad'in "Matsoraciyar banza, toh meze mana?" seta sake maraeraece fuska sannan tace "Allah kuwa ni dae tsoro nake ji" "Toh ae dad'in ta bake kad'ae bace ba koh? Ki tashi mu tafi kina gani duk wad'anda suka ci d'in sun fita" Zaenab ta fad'a tana mik'ewa, itama Ayrahn mik'ewa tayi ta ajje littafin hannun ta kan bench d'in su sannan suka fito daga ajin zuwa office d'in Principal d'in su, suna tafiya jefi jefi suna d'an ta6a hira kasancewar akwae sabo me k'arfi a tsakanin su, dan kuwa unguwar su d'aya su biyun, kuma Islamiyya ma d'aya suke zuwa "Ace yace dukkan mu mu wanke toilets" Zee ta fad'a tana satar kallan Ayrah, seta 6ata fuska gami da shagwa6e face tace "Don Allah ki bari" ta fad'a tana ta6e baki.. Akan ta idanun sa suka fara sauka sanda yake sakkowa daga cikin wata bak'ar hamshak'iyar mota, bak'i ne sosae sannan kuma me jiki babu laefi, sanye cikin wata Ash d'in shadda wadda ta sake fiddo da bak'in sa sosae, hannun sa d'auke da irin wannan sandar girman yana sanya ta duk inda k'afar sa zata taka, a kallan farko zaka iya bashi shekaru 40 zuwa 45 amma idan ka masa kallo irin na sosae zaka fahimci kud'in daya gama wadatar sane ya 6oye aenahin shekarun sa dan kuwa ak'alla ze kae shekara 55, seya lumshe idanu yana jin wani irin maganad'iso na fuzgar sa zuwa ga yarinyar, yanayin yadda take magana a shagwa6e hakan ba k'aramin burge shi yayi ba, seya bita da idanu kamar wani maye sanda suke k'ok'arin shiga Office d'in principal, nan ma seda suka tsaya suka d'an yi magana kafin suka tu6e takalman su duka suka shige ciki, wani numfashi ya fesar me k'arfin gaske lokaci guda kuma yana saeta numfashin sa da yanayin fitar