← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 90

Sashe 14

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zauna a k'asa, seda suka gaesa sannan Abba yace "Dama magana ce akan yarinyar nan" yayi maganar yana nuna Ayrah da kanta ke k'asa, sannan ya cigaba da fad'in "Abubuwa da dama sun faru se dae ban samu damar zuwa wajen ku ba, toh shiyasa a wannan karon nace bari nazo naji daga bakin ku.. Naji yau ma ance wae za'a biya mata kud'in registration na Jamb?" murmushi Principal yayi kana yace bayan ya had'e hannayen sa cikin juna "Ae wato Alhaji Ibraheem ka godewa Allah, Allah ya baka yarinya me hazak'a, saboda haka dan mun d'auki nauyin ta wannan ba komae bane, In Sha Allah ma zamu d'auki nauyin ta ne har ta gama karatu.." dukkan su se suka kalle shi suna jin wani irin farin ciki na ratsa ilahirin jikkunan su "Toh Alhamdulillah, Masha Allah, muna godiya sosae Principal, Allah ya k'ara arzik'i" Inji Abba "Ameen_Ameen.." .... A kwanakin da suka biyo ne Ayrah suka zana jarabawar Jamb d'in, babu wani dad'ewa kuma result d'in ya fito, cikin ikon Allah kuma ta doko point dae_dae da course d'in data ke so dama kuma a Neco ma ta fito da 9 credit, dan haka komae yazo cikin sauk'i, wani malamin su ne ya shige mata gaba bayan fitowar result d'in nasu wanda shima Alhaji ne ya sanya shi yin hakan, sosae suka yi fafutuka wajen sama mata admission har Allah yasa ta samu Medicine a A.B.U Zaria. Ba k'aramin farin ciki Abba, Umma, Yah Sadeeq har ma ita kanta Ayrahn suka yi ba sanda suka ji an sama mata Admission d'in ta hanyar wannan malamin nasu, amma sanda duk suka ji a inda ta samu Admission d'in se duk jikin su yayi sanyi. Umma dake zaune kan tabarma ta kalli Abba dake fad'in "Duk da naji dad'in wannan Admission d'in da aka samu, amma bana tunanin zan yadda Ayrah ta tafi har Zaria karatu, ina tunanin kawae a bashshi.." Yah Sadeeq da shima yake kusa da Abba yace "Abba ni ina ganin kawae a batta d'in ta tafi, tunda duk da k'arancin shekarun Ayrah tana da hankali.." ya k'arasa maganar yana kallan Ayrah gami da sakar mata murmushi, itama murmushin ta saki tana jin dad'in wannan yabon na Yah Sadeeq duk da dae ita kanta ji take kamar ta hak'ura da makarantar, dan bata masan yadda rayuwar ta zata kasance acan wani waje babu Umman ta, ba Abban ta sannan kuma ba Yah Sadeeq d'in ta ba, Umma taja doguwar ajiyar zuciya sannan tace "Abban su barin wannan Admission d'in kamar mun saka k'afa ne munyi fatali da damar mu, ina ganin meze hana tunda mun yadda da d'iyar mu, mu barta taje d'in idan yaso mu dinga binta da addu'a kuma mu dinga kae mata ziyara..?" shiru Abba yayi na wasu en dak'ik'u kana yace "Zan sake tunani.." daga haka be sake cewa komae ba.. A cikin satin Abba ya amince da zuwa makarantar Ayrahn, dan haka daga shi har Yah Sadeeq suka tashi tsaye sosae wajen fara siya mata abubuwan da zata tafi dasu, duk da ba wasu kaya ne na azo a gani ba amma dae sun samu sun siya mata abubuwan da suka san zata buk'ata.. Cikin d'an k'ank'anin lokaci aka gama komae, duk wasu abubuwa da suka kamata aka gama su daga 6angaren Abban har daga can 6angaren Alhaji.. ..... Zubewa yayi a k'asan carpet kansa a k'asa yana jira Alhajin ya gama wayar da yake yi, seda ya shafe wajen rabin awa yana wayar da duk da ganin wani ya shigo besa ya katse ta ba "Muttala ina jin ka" yayi maganar sanda yake aje wayar akan kujerar gefen sa "Yalla6ae jibi ne tafiyar tasu fa" murmushi yayi kana yace "Toh madallah, yanzu abinda za'ayi.. ga kud'i nan kaje duk inda ya dace ka siyo duk wani abu da kasan yarinya budurwa nada buk'ata idan zata je makarantar kwana.." ya fad'a yana ajje masa wasu uban kud'i a gaban sa "Toh shikenan, amma bana tunanin a had'a da kayan lokacin da zasu tafi can makarantar, inaga gwara daga baya kayan su bita.." jinjina kae Alhajin yayi sannan yace "Hakan ma yayi.." ya d'an dakata kana ya d'ora da "Kana ganin idan naje wajen mahaefin ta a yanzu banyi gaggawa ba?" girgiza kae Muttala ya shiga yi ya d'an yi murmushi kana yace "A'ah ranka ya dad'e ka bari tukunna, kada su fahimci dalilin hidimar ka tun yanzu, zefi kyau mubi komae daki_daki.." "Gaskiya a haka ma nayi k'ok'ari wallahi, bari dae zan bar ta ta gabatar da first semester kawae zuwa lokacin zan je wajen baban nata" ya fad'a yana girgiza kae shima "Toh hakan ma babu laefi" Inji Muttala.. .... Tana sanye cikin doguwar rigar atamfa da hijab kasancewar sa favourite nata, sosae kyakykyawar fuskar ta tayi fayau kamar mara lafiya, fararen manyan idanun ta sunyi ja, hannun ta cikin na Umma tana kallan ta da idanun nata da suka sake yin rau rau, Umma tayi murmushi dan tana so ne ta kwantar mata da hankali tace "Ya isa haka shalele, kada ki 6ata fuskar nan taki yanzun nan mana Uhmm?" Umma ta fad'a tana sanya hannu ta d'auke k'wallar dake zuba akan kuncin ta "Umma ta zanyi kewar ki" ta fad'a tana kwantawa a jikin Umman, hannu Umma ta saka ta rik'o ta bayan tayi murmushi tace "Banda abin ki Ayrah ae ba dad'ewa zaki dinga yi ba, ko kin manta zaki dinga dawo mana hutu?" seta jinjina kae kawae "Toh idan kin gama kukan seki taho mu tafi" Yah Sadeeq daya shigo ya fad'a, seta d'aga kae tana kallan sa gami da murgud'a mitsitsin bakin ta "Iyeee.. Lallae ne yarinyar nan" Yah Sadeeq ya fad'a yana rik'e ha6a. Har k'ofar gida Umma ta rako su inda motar da zata kaesu Zarian take, seda taga tashin motar tasu sannan ta koma cikin gidan tana matse k'walla, dan kuwa tun tasowar Ayrahn baza tace ga ranar da suka ta6a rabuwa ba, dan tun tana yarinyar ta mayyar Umman ce, ko yadda da mutane ba wani sosae take ba ballantana ace taje ta kwana. ... "Ki maeda hankali kiyi karatu, sati d'ayan nan da aka wuce ki ki samu wata ta koya miki, banda yin k'awar da zaki zauna kina fad'a mata cikin ki duk da dae nasan halin ki amma dae gwara na tisa miki" Yah Sadeeq ya fad'a sanda suke tsaye a wani ke6antaccen waje, seta jinjina kae kawae dan bata tunanin zata iya magana, idan kuwa tace zatayi maganar toh tabbas kuka zata saka, Abba daya fahimci haka se yayi murmushi dan shi kansa har ya fara kewar Autar tasa, ya matsa kusa da ita yace "Ayi karatu sosae koh?" nan ma dae seta jinjina kan tana kae hannun ta idanun ta ta goge hawayen daya sauko akan fuskar ta, hannu Yah Sadeeq ya sanya cikin aljihun sa ya zaro wata k'aramar waya yace yana kallan k'anwar tasa "Yau dae ga alk'awarin mu.." seta kalli hannun nasa sannan ta kalle shi, bata san sanda murmushi ya su6uce a kyakykyawar fuskar ta ba, ta saka hannu ta kar6a cike da farin ciki kana ta d'an jujjuya ta sannan tace lokacin da wasu kyawawan hawaye suka samu damar zubowa akan kuncin ta "Amma nagode sosae Yah Sadeeq, Allah ya k'ara arzik'i" "Ameen" dukan su suka amsa da hakan cikin jin dad'in yadda ta d'an saki jiki.. seda suka d'an dad'e suna sallamar zuwa lokacin ta saki jiki suna ta d'an hira, se kuma daga baya tayi kukan ta ta godewa Allah, sannan su Abban suka tafi bayan sun kwantar mata da hankali... ... A hankali ta tura k'ofar d'akin hannun ta jaye da er trolley d'in ta da aka kar6o mata a wajen k'anwar Umma da itama zama ya dawo dasu cikin kano, dukkan su suka d'aga kae suka kalle ta sanda tayi sallama da kyakykyawar siririyar muryar ta data sake sirancewa saboda kukan da tayi, su 3 ne zaune a cikin d'akin, d'aya na daga gefe tana danna waya yayin da biyun ke zaune kusa da juna suna hira "Wa'alaeki Assalam" suka amsa dukan su suna bin bak'uwar fuskar da suka gani da kallo "Wow, tubarkallah Masha Allah" d'aya daga cikin su ta fad'a a ranta lokaci d'aya kuma tana mik'ewa tsaye ta k'arasa inda Ayrah take tace tana d'an yin murmushi "Anan d'akin kike?" tayi maganar tana kallan idanun ta da suka yi ja alamar kuka tayi, seta k'ak'alo murmushi ta wanzar akan fuskar ta wanda kana gani kasan beje ko'ina ba tana jinjina kae "U're highly welcome.." ta fad'a tana d'aukar bagcon data gani a gefen Ayrah tayi gaba, babu musu Ayrahn tabi bayan ta a hankali "Ruks ki tashi me waje tazo fa" wadda ta kar6i jakar Ayrahn ta fad'a tana kallan wadda ke zaune kan gado tana danna waya, wadda aka kira da Ruks d'in ce ta mik'e tana kallan Ayrah itama tayi murmushi tace "Barka da zuwa bak'uwa" "Umhum" Ayrah ta fad'a kawae tana jefa mata kalar murmurshin data yiwa Jidda, seta k'arasa ta zauna akan gadon tana jin ta gaba d'aya a wani irin takure, musamman yadda taga su duk lokaci d'aya suna neman sakin jiki da ita, seda Jidda ta ajje mata kayan ta gefe guda sannan ta dawo ta zauna kusa dasu Ruks ta zauna, Bahijja da tun d'azun ba tace komae ba se kallan Ayrah da take tace "Bak'uwa ya sunan ki?" a hankali ta bud'e bakin ta daya mata nauyi tace "Ayrah.." "Awwwn, sunan en gayu, suna me dad'i.." kusan a tare suka fad'i hakan, har seda hakan ya sanya ta tayi murmushi "Toh barkan ki da zuwa" Bahijja ta fad'a... Suna nan zaune d'akin har bayan isha'i suna hirar su, hirar da kusan duk akan abu d'aya suke yin ta, ita dae tana zaune a gefe guda se dae ta bisu da ido kawae, so take ta ke6e ita kad'ae tayi kukan ta ko zata ji sauk'in kewar gida data fara damun ta tun yanzun. "Ruks ki tashi ki d'ora mana ko Indomie ce pls, kinga bak'uwa ma ba taci komae ba" Jidda ta fad'a, Ruks ta kalli Ayrah tace "Ayrah kina jin yunwa ne?" seta girgiza kae kawae tana yabawa da kulawar mutanen da bata ta6a ganin su ba
Chapter 14 · 0% Book details