← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 90

Sashe 22

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da alama ko soyayya za'ayi da ita ba zata zama cikin mak'aryata ba, cikin k'asa da murya ya furta "Amin afuwa Uhmm? Raj ne fa" ya fad'a da er tsokana a maganar sa, se tayi murmushi kawae "Ina Umma? ina Abba? Ina Yah Sadeeq?" yayi maganar kamar ba Rk ba, seta sake gyara zama sannan tace "Alhamdulillah kowa lafiya k'alau, ina Abbun ku" "Abbu yana lafiya.." "Raj!" ta fad'a dan ta k'agu ta masa tambayar data tsaya mata arae sosae "Na'am" ya fad'a a nutse "Kae likita ne?" murmushi yayi daga inda yake sannan yace bayan ya d'an lumshe idanun sa kad'an "Yeah! likita ne, ki gyara zama na baki labarin rayuwa ta tun bayan rabuwar mu" kamar tana kusa dashi ta shiga gyara zama, dae_dae lokacin da Bahijja ta farka daga bacci saboda wani fitsari daya matso ta, ta kalli Ayrah dake zaune kan gadon ta sannan ta furta "Ayrah" cike da mamakin ganin ta, da sauri Ayrahn ta juyo tana kallan ta, se dae ba tace komae ba har Bahijjan ta shige toilet d'in, babu dad'ewa ta fito memakon ta nemi waje ta kwanta seta zauna tana cigaba da kallan Ayrah, haushi ya kama Ayrah ta had'e face d'in ta tsaff, sannan cikin had'e ran dae ta furta "Gobe zamu yi wayar" bata jira yace komae ba ta katse wayar sannan ta juya ta kwanta tana jin kamar ta tashi ta rufe Bahijja ta duka, cigaba da zama Bahijjan tayi dan so take ta gane da wanda take waya saboda abu ne da basu ta6a gani ba a wajen Ayrahn tunda tazo ba, kamar wadda aka tsikara ta janyo wayar data wulla gefe ta lalubo number Yah Sadeeq ta danna kira, se dae har ta tsinke be d'aga ba, ta sake kira nan ma dae be d'aga ba, a ranta kawae ta bada cewar may be ko bacci yake shiyasa be d'aga ba, duk da dae ta saba kiran sa a irin wannan lokacin kuma ya d'aga amma jiki da jini, k'ilan yau yayi wani aekin ne me wuya yasa yayi bacci da wuri, haka ta koma ta shiga lalubo number Abba.. se wata zuciyar ta zuga ta akan labarin baze musu armashi ta waya ba, kawae seta ajiye wayar tana murmushi a ranta tana sak'a gwara ta bari idan ta koma gida gata gasu Abban ta fad'a musu wannan babban albishir na cewar taga Raj, tasan suma za suyi farin ciki matuk'a k'ilan ma su fita farin cikin ko dan sanin da tayi iyayen nata na son farin cikin ta fiye da nasu.... Mhiz Innocent...... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* *TITAN'S OF TALENT* Page 021_022 ___Bata dad'e da kwanciyar ba taji wani bacci na sakad'ar ta, se dae har lokacin bata hak'ura ba ta sake juyawa ta kalli inda Bahijja ke zaune tun d'azun, ga mamakin ta a wannan karon ma seta sake ganin ta zaunen dae tana danna waya, bata san sanda wani tsaki ya su6uce mata ba, se kawae ta hak'ura ta lumshe idanun ta amma mamaki ya cika zuciyar ta na Bahijjan, babu 6ata lokaci kuwa wani daddad'an barci me cike mafarkan Rk ya kwashe ta, ba ita ta farka ba se asuba. Yau ma kamar kullum da wuri suka gama shiryawa kasancewar ranar Monday ce, Monday d'in data kasance daga ita seta exam d'in da zasu fara, haka kawae taji tana jin haushin Bahijja amma kuma data tuna za tayi tozali ne da Rk se wani murmushi ya su6uce mata, a wannan karon Jidda ce kawae ta lura da murmushin wanda tun jiya ta lura da sauyawar Ayrahn, ta kasa hak'uri seda ta kalle ta tace "Ayrah wae meya faru naga daga jiya zuwa yau yanayin ki ya chanja?" d'an kallan ta tayi sanda take saka wani littafi cikin jaka sannan ta d'an ta6e baki kamar wadda ta gaji kana tace "Ni fa ba komae nace" "Haka kike ta fad'a tun jiya, Allah yasa haka n e" Jidda ta fad'a tana cigaba da nazarin ta, ba tace komae ba se d'an tura bakin ta da tayi tana k'arasa shirya kayan jakar ta, a ran ta se k'una k'uni take akan takura mata da suka yi tun jiyan. .. Tunda suka zauna jin su kawae take suna hira amma bama ta jin abinda suke cewa ballantana ta fahimta, gaba d'aya hankalin ta ya karkata ne ga son ganin ya shigo cikin ajin, ba'a k'ara minti 1 ba kuwa se gashi ya shigo cikin ajin dae_dae lokacin da ilahirin ajin ya d'auki shiru, lumshe idanun ta tayi tana shak'ar k'amshin sassanyan turaren sa me dad'in gaske sannan ta bud'e tana maeda duban ta kan fuskar sa da taga ta k'ara kyau fiye da jiya, se kawae ta shagala da kallan sa, yau d'in duka ya juye mata ya sake komawa Doctor Rk d'in sa babu fara'a yana yin komae ne cikin tsare gida, yau karon farko taji yanayin da yake d'in ya burge ta, ta san da yana sakin fuska kuma matan da za suce suna son sa se sun fi na yanzu yawa, tana jin sa ya fara magana cikin nutsuwa k'warewa da kuma takatsantsan amma sam bata fahimtar abinda yake fad'a d'in, kawae dae ta san magana yake amma ita bin sa kawae take da kallo kamar wata doluwa tana jin kamar ta had'iye shi amma duk bata san dalili ba, wayar ta dake rik'e a hannun ta ce tayi vibrate daga hannun ta, ta d'an dakata tana jin kamar ta share wayar se kuma tayi k'asa da kan ta ta duba wayar, d'an k'aramin sak'o ya bayyana akan wayar, seta shiga da sauri ta shiga karantawa ganin daga number da yake "Kallan fa?" shine abinda ke rubuce cikin message d'in daga number Rk, a'ah mamaki ne ya kamata har bata san sanda ta d'aga kae ta kalle shi ba, gashi dae anan lecturing d'in sa yake hankali kwance, toh kenan yaushe ya turo mata da message d'in? Toh yaushe ma ya gan ta tana kallan nasa, dan dae tunda ta zauna ba taga idanun sa akan kowa ba ballantana tace ya gan ta, a hankali ta sake maemaeta message d'in, se ta kae hannun ta ta rufe fuskar ta tana murmushi tuna duk kallan data masa ashe yana ganin ta? Lallae shi d'in na musamman ne "Ke meye haka wae?" Bahijja da tun d'azu take lura da duk wani motsin Ayrahn ta fad'a k'asa k'asa, da sauri Ayrah ta kalle ta ba tare da tace komae ba ta d'auke kae "Anya kuwa wannan yarinyar?" Bahijja ta fad'a a k'asan ran ta cike da mamaki, ita dae Ayrah bata sake bi ta kanta ba ta koma maeda hankali kan karatun da yake koya musu, amma duk iya k'ok'arin ta na ganin ta fahimta d'in ta kaasa, se kace wadda aka sanyawa hannu, a haka dae har ya gama lectures d'in baza tace ga abinda ta d'auka ba. ... Sanda suka koma Hostel bata lura da message d'in sa ba har seda ta zauna sannan taga message d'in nasa, da sauri ta shiga message d'in tana jin zuciyar ta na wani d'an bugawa a hankali kamar me jin tsoro "Nan gaba da face mask zan dinga shiga class, idan ba haka ba wataran za'a neme ni a rasa kin cinyewa su Abbu ni" komawa tayi ta kwanta kan gadon ta tana sakin wata dariya gami da rufe fuskar ta, ashe dae duk yana sane da ita duk kallan da take bin sa da shi yana gani, ita kan ta ta rasa gane abinda ya shiga kan ta ta kasa d'auke idanun ta daga kan sa, tana ji kuma kamar idan ta dena kallan sa zata bud'e ido taga baya nan, mik'ewa tayi ta fita daga cikin d'akin dan lokacin duk su Jidda suna ciki, suka bita da kallo kowacce da abinda take sak'awa a ran ta, amma abinda yafi damun kowaccen su shine chanjawar ta ta cikin lokaci k'ank'ani. .. Gyara zaman sa yayi kan kujerar da yake zaune kana a hankali ya furta "Kin wuni lafiya?" seta lumshe idanun ta sannan tace "Ehh.." murmushi yayi bayan ya d'an yi jimm kad'an yace "Ina fatan bakya fita daga cikin makarantar nan?" seta d'an bud'e manyan idanun ta kamar tana gaban sa, sosae yadda ta bud'e idanun yayi mata kyau, sannan ta rufe bakin ta tace a hankali "Ta66, ae na yiwa Yah Sadeeq alk'awarin bazan ta6a fita ba" ta fad'a a sakarce, yayi murmushi yana sake gyara zama muryar ta na masa wani irin dad'i yace "Dats my Ayrah" itama murmushin tayi sannan ta dakata sanda yake furta "Next week exam Uhmm?" kamar tana gaban sa ta jinjina kae kawae, shi kuma kamar yaga abinda tayi d'in yace "Idan anyi hutu In Sha Allah zan zo, may be ma har da su Abbu" yayi maganar a nutse, hakan ba k'aramin dad'i ya mata ba tana murmushi tace "Buhh baka bani labarin ba" ta fad'a tana tura bakin ta gaba, iska ya d'an fesar daga bakin sa sannan yace "Ohh am sorry.." yayi maganar yana d'an dakatawa, yana tunanin tsayin maganar da zeyi, ya san tabbas ze dad'e yana yin ta abinda ya tsana kenan, dan haka ya janyo rubber water ya tsiyaya cikin tambulan ya sha, ya d'an sauke numfashi a nutse sannan ya d'ora da "Tun bayan rabuwar mu, Allah ya bud'ewa Abbu sosae, harkokin da yake yi sosae suka samu kar6uwa a wajen mutane, ban san meyasa tun bayan rabuwar mu daga mu har ku babu wanda ya sake waewayar wani ba, bansani ba, abinda kawae na sani na sha tambayar su Abbu ku amma bana samun cikakkiyar amsa wadda zan kama daga wajen sa, tun ina tambayar sa har nazo na dena tambayar sa, se dae har lokacin kina nan manne a rae na, ina jin ki ne acan cikin zuciya ta wanda hakan ne yasa na kasa manta ki a duk tsayin shekarun nan, a cikin wannan lokacin ne na gama secondary school kullum arzik'in Abbu yana yin gaba, dan haka dana tashi yin University ba'a nan nayi ta ba, sena tafi can Cyprus na karanci Medicine, yanzu haka ni cikakken likita ne, muna zaune anan cikin garin Kano saboda harkokin Abbu da suka cigaba, yanzu haka ina
Chapter 22 · 0% Book details