← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 90

Sashe 3

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wani malami na musu karatu, seta d'an saci kallan tagar su da take kallan k'ofar ajin, kamar yadda ta tsammata kuwa seta hange shi d'an nesa kad'an yana lek'owa cikin ajin yana kallan malamin, cigaba tayi da kallan sa ba tare da ta cigaba da saurarar malamin ba "Ayrah!!" taji malamin ya ambata, seta juyo da sauri tana gyara zaman ta, idanun ta da suka yi rau rau akan malamin, maeda duban sa yayi kan inda take kalla, ganin haka ya sanya yaron saurin yin k'asa da kansa dan kar a gansa, hakan yasa malamin bega komae ba, da mamaki ya tako zuwa inda take yace yana kallan ta "Me kike kalla acan?" kamar zata fashe da kuka tace "Ba komae.." ta fad'a d'an k'aramin bakin ta a gaba, sake kallan wajen malamin yayi sannan ya dawo da duban sa kanta yace "Ohk toh me muke cewa?" ita sam bama ta gane tambayar da yake mata ba dan haka kawae ta bishi da kallo, ya girgiza kae kawae sannan ya koma ya cigaba da abinda yake yi, bata sake kallan wajen ba ta bada hankalin ta wajen karatun da ake musu, dan kullum ne idan ta koma gida se Yah Sadeeq ya sanya ta a gaba ta masa bitar abinda aka koya musu.. K'arfe 2 da en mintuna Abba yazo ya d'auke su a motar sa kamar koda yaushe, tunda suka shiga motar Ayrah keta basu labarin abinda ya faru a makaranta, Abba nata biye mata, yayin da wani lokacin Yah Sadeeq ya amsa mata wani lokacin yayi shiru har zuwa sanda suka isa gida, Abba ya sauke su a inda ya saba sauke su sannan ya wuce da motar tasa zuwa inda ya saba ajiye ta.. Sun riga shi shiga gida, da gudu Ayrah ta shige gidan tana k'walawa Umma kira, Umma dake kitchen ta fito tana kallan su tace "Sannun ku da zuwa yaran kirki" Yah Sadeeq ne ya amsa da "Yawwah Umma" yana cire jakar bayan sa, kallan sa Umma tayi sannan tace "Zaka fara cin abinci ne ko seka yi wanka?" "A'ah Umma bari nayi wankan, ina so ne nayi muraja'a kafin muje Islamiyya" "Ohk tohm" ta fad'a tana maeda duban ta kan Ayrah dake rik'e da hannayen ta "Umma kinsan me?" ta fad'a tana ware manyan idanun ta, murmushi Umma tayi sannan tace "A'ah sekin fad'a.." seta ta6e baki kamar wata babba sannan tace "Umma wani yaro a makarantar mu kullum sena ganshi idan Uncle ya shigo yana lek'e ta window" "Shi ba d'an makarantar bane?" Umma ta fad'a tana kallan sa "Ehh Umma" Ayrahn ta fad'a kawae ba dan tana da tabbacin abinda ta fad'a ba "Ke banda sharri.." Yah Sadeeq dake shirin mik'ewa ya fad'a "Allah kuwa da wasa nake.." ta fad'a dan ita a hausar ta idan tace da wasa take toh tana nufin da gaske take, idan kuma tace da gaske take toh tana nufin da wasa take, ta fad'a tana d'an rufe idanun ta hannun ta a saetin bakin ta "Lallae.." Yah Sadeeq ya fad'a yana mik'ewa da dariya akan fuskar sa na wannan hausar ta Ayrah "Toh yanzu dae muje na shirya ki ku wuce makaranta.." Umma ta fad'a dan tasan shirmen Ayrahn, Umman da kanta ta mata wanka ta sanya mata kayan Islamiyyar sannan suka fito suka ci abinci kana suka wuce Islamiyyar.. Washe gari ma hakan ce ta kasance koda suka je makarantar seda taga wannan yaron yana lek'e ta taga har zuwa sanda Abba yazo ya d'auke su, tunda suka shiga motar Yah Sadeeq ya fahimci akwae matsala dangane da mahaefin nasu saboda gaba d'aya yanayin sa ya chanja, amma ita kuwa Ayrah yarinta besa ta fahimci hakan ba ta cigaba da hirar data saba musu, inda Abban ke iya k'ok'arin sa wajen biye mata.. Tunda suka shiga gidan ya kasa mik'ewa ya tafi d'aki yayi wanka, dan haka sallah kawae yayi ya cigaba da zama cikin d'akin har zuwa sanda Abban ya shigo da sallama zuwa cikin d'akin, shi da Umma suka amsa sallamar tasa suna binsa da kallo, haka kawae k'irjin Umma ya buga da ganin yanayin Abban da bata saba gani a tattare dashi ba, amma se ba tace komae ba ta barshi ya zauna tace a hankali "Sannu da zuwa Abban su.." "Yawwah" ya fad'a ba tare daya kalle ta ba "Abba sannu da zuwa" Yah Sadeeq ya fad'a yana kallan Abban, mik'ewa Umma tayi da niyyar samo masa ko d'an ruwa ne wanda ze sanyaya masa zuciya, amma se taji yace "Dawo ki zauna kiji abinda ya same mu kuma.." babu musu ta dawo ta zauna tana jin k'irjin ta na cigaba bugawa, ganin kamar zaman nasa beyi bane ya sanya shi mik'ewa tunda duk alama ta nuna iyayen nasa magana zasuyi "Sadeeq dawo ka zauna.." Abba ya fad'a yana kallan Yah Sadeeq, komawa yayi daga niyyar tashin da yake yi, Abba ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "Wato ina chanjin dana fad'a miki anyi na principles da sauran manyan masu muk'ami?" Umma ta lumshe idanun ta sannan tace "Ehh.." "Toh tsautsayi ya biyo ta kanmu, an sallame mu..wae zasu kawo wasu sababbi.." Abba ya fad'a yana jin ciwon hakan har cikin ransa "Innalillahi wa inna ilaehi rajiun.." Umma ta fad'a tana jin wani iri, lokaci guda kuma tana kallan Abban cike da tausayawa "Abba me kuka yi musu?" Yah Sadeeq ya fad'a fuskar sa cike da alhini, d'an murmushi Abban ya saki me cin rae kafin yace "Kada ka damu Sadeeq In Sha Allah ae Allah ba azzalimin bawan sa bane, da sannu duk wani me mugunta a fad'in duniyar nan ze girbe abinda ya shuka.." Abba ya fad'a kafin ya maeda duban sa kan Umma da har lokacin ta kasa furta komae bayan salatin da tayi "Ina ganin lokacin hak'ura da aekin gwamnati yayi, tunda nayi har sau 2 Allah beyi zan d'ore ba.." da sauri Umma ta d'ago ta kalle shi tace "Toh Abban su idan ka hak'ura ya za'ayi kenan?" murmushi me ciwo yayi sannan yace "Kinga dae aekin Bank d'in nan seda na sakankance suka zo suka dakatar damu, yanzu ga wannan ma, bana so na sake neman wani shima na sakankance kuma azo a samu matsala, yaran nan karatu suke yi, muma akwae buk'atun mu na yau da kullum, saboda haka.." seya d'an dakata kad'an kafin ya d'ora da fad'in "Ki nutsu ki kwantar da hankalin ki, maganar wannan shagon In Sha Allah zan maeda hankali a kanta, Allah ya saka mana" Abba ya fad'a yana mik'ewa, dukkan su suka bi Abban da kallo cike da tausayawa, dan Abban wani mutum ne wanda kafin ka ganshi cikin 6acin rae se an dad'e, se an matuk'ar kaeshi bango sannan hakan kan bayyana akan fuskar sa, Umma ta sauke ajiyar zuciya sannan tace "In Sha Allah se Allah ya sakawa me gaskiya.." ta fad'a itama tana tashi, Yah Sadeeq ya amsa da "Ameen Umma.." dae_dae lokacin da Ayrah ta fito daga d'aki kamar koda yaushe da d'an gudun ta "Umma ba'a min wankan ba fa" ta fad'a tana ta6e baki, Umma tace bayan ta d'an yi murmushi "Gani nan, dama yanzu can zance muje.." ta fad'a tana kama hannun Ayrahn zuwa d'aki.. .... Duk da abin nan daya faru hakan be hana Abba d'aukar 'ya'yan nasa yakae makaranta ba, sedae har lokacin bashi da walwala dan gaba d'aya hankalin sa na kan abinda ze cigaba dayi dan cigaba da kula da harkokin iyalin sa, ga rashin bacci daya samu a jiyan hakan ya k'arawa yanayin nasa rashin armashi, bayan ya sallame su suka masa a dawo lafiya sannan ya tashi motar sa, Yah Sadeeq ya kalli Abban nasu dan shi kanshi jiya kafin ya kwanta da Abban nasu ya kwana, duk da k'ananun shekaru irin nasa wanda ba zasu wuce 12 ba yana da hankali da nutsuwa, shiyasa wani lokacin Abban ke d'aukar sa kamar d'an shekara 20 dan ko shawara zeyi da Umma yana barin Yah Sadeeq d'in ya zauna a wajen suyi shawarar tare "Abba Allah ya bada sa'a, ya tsare, Allah ya kiyaye hanya.." ya fad'a kamar yadda suka sabawa Abban addu'a idan ze fita, murmushi Abba yayi kana yace "Ameen Sadeeq, Allah ya baku sa'a kaji, ka cigaba da taya ni da addu'a.." "Toh Abba.." Yah Sadeeq d'in ya fad'a yana wucewa... ... Sanda aka fito break bayan sun gama cin abincin kamar yadda suka saba, se suka fito zuwa harabar makarantar, ta kalli inda ta saba ganin sa kamar koda yaushe yana zaune yanzun idanun sa kan wata takadda yana kalla, a hankali ta fara takawa zuwa inda yake zaunen idanun ta a kansa "Ayrah..er carafke fa muma yau zamu yi" wata k'awar ta da itama ba zata wuce sa'ar ta ba ta fad'a da maganar ta me cike da tsamin baki, bata ma jita ba dan gaba d'aya hankalin ta yayi kansa, har zuwa sanda wata a cikin k'awayen nata ta dafa ta tana fad'in "A'ah ki taho enter zamu yi" ta fad'a tana dariya, hannu Ayrah ta saka ta zame hannun k'awar ta ta dake kan kafad'ar ta sannan tace "Ke ni ba zanyi ba.." daga haka tayi gaba, su kuma yaran duk basu bi ta kanta ba suka cigaba da wasan su, seda ta isa inda yake d'in sannan ta tsaya tana cigaba da kallan sa da kuma kayan dake jikin sa, a k'alla zeyi shekaru 12 ne, fari ne sosae kyakykyawa ajin farko, me manyan idanu da dogon hanci, ga wata bak'ar suma dake kwance akansa sedae daga gani kasan bata samun yadda take so dan haka ta d'an cukurkud'e kad'an, kayan jikin sa ma haka kana ganin su kasan sunji jiki amma da alama shi duk wad'annan basu dame shi ba dan kuwa har lokacin idanun sa na kan takaddar hannun sa ne "Kae!!" Ayrah ta fad'a tana kallan sa, da sauri ya d'aga manyan idanun sa ya sauke su akan Ayrahn, bece komae ba seya maeda kansa kan takaddar sa "Kae!!" ta sake fad'a a karo na, d'an lumshe idanun sa yayi sannan ya ninke takaddar a hannun sa ya mik'e, yana k'ok'arin barin wajen Ayrah tace "Kawo na koya maka.." seya d'an dakata kad'an kafin ya juyo yana kallan ta, hannu ta mik'a ta kar6i
Chapter 3 · 0% Book details