Sashe 86
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
k'are da fad'in "Ke har yanzu shashasha ce wallahi Muneerah, abin da Daddyn ki yake ae shi ne ze sa ki fahimci shi ne mahaefin na ki, baki san son ki yake ba shiyasa yake nema miki 'yanci ba? Ke bari kiji na fad'a miki mu ne fa bamu da gaskiya, mun riga mun sani Raj ba son ki yake ba, ke kuma kin je kin yi abin da ze sa ya k'ara tsanar ki, toh Daddyn ki ze so ki sake komawa inda ba'a son ki ne?" "Toh me kike nufi ne wae?" Muneerah ta katse Mummy jin tana ta karanto mata maganganun da suke nuni da kamar itama tana bin bayan Daddy. "Kin ji dae abin da ya fad'a ba zaki koma gidan Raj ba, saboda haka ki tashi kije ki ga wannan d'in idan yayi miki kawae ki hak'ura da Raj! Fak'at!" "Mummy!" Muneerah ta fad'a tana bud'e idanun ta, shikenan Daddy ya sauyawa Mummyn ta ta ra'ayi, ae ita kuma tata ta k'are. Had'e rae Mummy tayi tace "Toh maza ga waje ki zauna, kada ki dinga tuna abin da Daddyn ki ya fad'a kin ji?" Mummy ta fad'a tana maeda duban ta kan T.V. Kuka kawae ta fashe da shi tana ganin ita kam k'arshen ta ya zo. Da k'yar dae da sid'in goshi Mummy ta lalla6a ta ta tashi taje wajen bak'on. Ba laefi ya d'an yi mata kad'an musamman da taji ba shi da aure se dae yace mata yana da marayu a wajen mahaefiyar sa, ita bata damu da wannan ba tunda dae ba'a wajen ta zasu zauna ba. Daga k'arshe dae bayan Mummy ta sake yi mata fad'a da nuna mata idan ta bari wannan d'in ya kufce mata ba samun Rk zata yi ba, kuma shi wannan d'in ya amince ze aure ta duk da kasancewar ta bazawara. Se kuma a lokacin ta ji sanyi a ran ta ko babu komae shi wannan d'in a bazawara ze aure ta hakan na nufin ko da ya same ta ba Virgin ba baze kawo komae ba tunda ya san bazawara ya aura. Cikin k'ank'anin lokaci Daddy ya saka aka masa bincike akan mutumin, a yanzu mutumin arzik'i ne se dae shekarun baya da suka wuce ya ta6a duniyanci amma daga k'arshe ya shiryu dan har aure yayi yana da yara ma, matar kuma ta mutu a kwanakin nan shiyasa yake so ya sake yin aure. Tare da amincewar Muneerahn da kuma Mummy aka d'aura auren Muneerah da Alhaji Sageer. A lokacin ne kuma Abbu yayi tawa Daddy fad'a akan abin da yayi, Daddy ya toshe kunnen sa yaji fad'an amma a ran sa ya san abin da yayi shi ne dae_dae. (Daga haka ni dae se nace Muneerah Allah ya bada zaman lafiya, ya k'ara shirya ki kuma.) *** *** *** .. A karo na barkatae ta sake kallan sa yadda yake ta wani ciccin magani, se k'unshe dariyar ta take yi bata bari ta fito ba. Takalmi ya saka mata tana zaune kan gado ta sake wani shahararren kyau, fatar ta har wani shek'i take yi, jikin ta ya murje sosae ta zama kamar wata babbar mace. Ita cikin na ta wani kyau ya k'ara mata, komae na ta ya sake zama na musamman, wannan na d'aya daga cikin abin da yasa ko kad'an baya son yin nisa da ita, idan kuwa yana gida ko da yaushe tana jikin sa. Se ga shi tun jiya Ummee ke kiran sa akan ya d'auke ta ya maeda ta gida saboda lokacin haehuwar ta da ya gabato. Tashi tsaye yayi ya kamo tattausan hannun ta cikin na sa kana ya taemaka mata ta mik'e, a nutse ta mik'e saboda yadda taji yau d'in jikin ta ya k'ara nauyi, a haka suka fita daga d'akin har lokacin bece komae ba se dae komae yake yi cike da takatsantsan yake yi. A bakin gidan su yayi parking na motar sa, ya kashe ta gaba d'aya sannan yayi shiru yana jira ta sauka. Shiru tayi kawae se ta cigaba da kallan sa har da matsar da fuskar ta tana lek'en sa kamar me son gano wani abun a cikin fuskar sa. Jin da yayi idanun ta a kan sa ya sanya shi juyowa se ta narkar da fuskar ta tana ta6e baki. Tilas yayi murmushi, se kuma ya ja hannayen da ya nad'e su a k'irji yace "Ae naga kema farin ciki kike zaki tafi ki bar ni koh?" Bud'e idanun ta tayi da yanzun suka k'ara kyau da maek'o, se ta soma jan jikin ta dan matsawa kusa da shi, hakan da ya lura da shi ne ya sanya shi sauk'ak'a mata ya matso kusa da ita, ya zamana tazarar dake tsakanin su bata da yawa. A hankali ta kamo hannun sa cikin nata tace fuskar ta a narke "Allah ba haka bane bafa" "Toh menene?" ya fad'a lokaci d'aya yana d'ora hannun sa akan fuskar ta. "Zan yi kewar ka!" ta fad'a a narke "Really?" yayi maganar yana d'age duka girar sa da murmushi akan fuskar sa. Jinjina kae tayi kafin tace komae yace "Be kae yadda zan yi ba. Am eager ma ki haehu a ranar za'a bani mata ta!" Kamar tace wani abu se kuma ta fasa kawae tayi murmushi se dae zuciyar ta na hasaso mata yadda zata haehu d'in, Allah dae ya bata da sauk'i kawae. "Zaka shiga?" ta tambaya tana kallan idanun sa saboda yadda fuskokin su ke kusa da na juna. Jinjina mata kae yayi lokaci d'aya yana lumshe idanun sa, se kuma ya d'ora bakin sa akan na ta ya shiga kissing na ta a zafafe, babu sanya itama ta shiga kissing na sa. Idan ya tuna yanda ze yi kewar ta na kwanaki se yaji kamar ana k'ara masa k'aemi kamar kada ya sake ta, haka dae ba dan yaso ba ya sake ta yana sake lumshe idanun sa. Itama na ta idanun ta d'an lumshe tana tuna yanda zata yi kewar sa, lips d'in sa na k'asa ya mayar cikin bakin sa ya taune. "Ko in k'ara sau 1, lips na ki kamar ana k'ara musu taushi kullum." ya fad'a a hankali yana kallan ta. Kawae se ta rungume shi sosae tana sauke ajiyar zuciya, duk da yadda tirtsetsen cikin ta ya tokare shi hakan be hana shi rungume ta ba, sun kae wajen minti 2 a haka sannan ya sake ta. "Ki kula min da kan ki da na Babyn mu" ya fad'a a nutse, lumshe idanun ta tayi kafin ta jinjina kae tana murmushi. Da sallama ta shiga gidan na su, Umma dake cikin kitchen ta fito, da sauri ta k'arasa da murmushi kan fuskar ta tace "Oyoyo Auta, sannu da zuwa." "Yawwah Umma" ta fad'a tana cigaba da takawa, a haka suka k'arasa har cikin d'akin na ta, Umma na jin tausayin ta cikin ran ta yadda take takawa a hankali kamar me tsoron k'asa, se dae ta wani 6angaren tana jin dad'i dan daga yanayin Ayrahn kad'ae zaka fahimci tana cikin kwanciyar hankali da jin dad'i. Har kan gado Umman ta taemaka mata ta zauna sannan itama ta nemi waje ta zauna "Tare kuka zo ne?" "Ehh Umma" mik'ewa Umma tayi tace "Toh a waje ya tsaya?" jinjina kae tayi tana yada hak'ark'arin ta akan gadon kana ta amsa da "Ehh.." Daga haka Umma ta fice daga d'akin. .. Shigowar Yah Sadeeq cikin d'akin itace ta sanya ta kallan sa tana murmushi, ya k'araso yana kallan Autar ta su da ta kusa zama uwa yau ko gobe. Cike da farin cikin ganin ta yace "Oyoyo Auta, saukar yaushe?" itama murmushin tayi kana tace "D'azun nan.. Ina yini Yah Sadeeq" yamutse fuska yayi yana d'an shafa cikin sa kana yace "Lafiya k'alau Lily.. Umma ina abinci na?" yayi maganar lokaci d'aya se dae ya k'arasa ne yana kallan Umma. "Sannu da zuwa.." Umma ta fad'a "Yawwah Umma" yayi maganar dae_dae lokacin da wayar sa tayi ruri, se ya kalli Umma da Ayrah kana ya d'an fuske sannan ya mik'e, se da yayi gyaran murya alamar rashin gaskiya sannan yace "Umma bari naje naci abinci. Auta zan dawo muyi hira." daga haka ya fice daga d'akin da sauri. Kallan Umma Ayrah tayi tana murmushi tace "Umma anya kuwa Yah Sadeeq d'in mu..?" Tashi Umma tayi itama tana murmushin "Kun fi kusa" se ta fice daga d'akin. Dariya sosae Ayrah tayi da alama Yah Sadeeq d'in ya fad'a soyayya, idan kuwa haka ne zata fi kowa farin ciki. Gyara zaman ta tayi tana janyo ninkin da Umma ke yi ta shiga k'arasa mata. Bata wani yi da yawa ba dama karambani ne kawae dan Umman ce ta hanata yi, se ta maeda su gefe kana ta d'ora kanta a gefen gadon. Shigowar Umma ne ya sanya ta d'an soma d'aga kanta daga kwantar da shi da tayi. K'arasowa Umma tayi tana kallanta tace "Kin gaji ne?" Se da ta yamutsa fuska sannan tace "Ehh" "Toh tashi maza ki kwanta" Umma ta fad'a tana k'arasowa inda take, ta taemaka mata ta koma kan gadon ta kwanta, ba dan taji dad'in kwanciyar ba haka dae ta kwanta d'in tana yamutsa fuska saboda yadda taji mararta ta mata nauyi, se dae ta maaze kawae. .. Yarfe hannu take yi duka biyun tana jin marar ta kamar zata 6alle. Ta d'auka kamar ciwo ne da lokaci d'aya ze yi ya tafi se dae taji ciwon bana k'are bane, dan kuwa k'aruwa ma yake yi, hakan ne ya sanya ta yin iya k'ok'arin ta ta bud'e baki da k'yar tace "Umma!" tana cigaba da yarfe hannun ta, duk da yadda ake sanyi amma ita gumi take yi. Sam dama baccin Umman be yi wani nisa ba hakan ne yasa ta mik'ewa da sauri ta k'arasa kan gadon tana fad'in "Subhanallahi..!" Da sauri ta rik'o ta yadda ta ga tana cigaba da yarfe hannu se dae ta kasa koda tashi ne. Gaba d'aya se ta rud'e amma duk da haka bata dena jerawa Ayrahn sannu ba, cike da tausayawa. Fitowa tayi daga d'akin cikin sauri daidai lokacin da Abba ya fito daga nasa d'akin. Da sauri Umma tace "Abban su.. Ayrah babu lafiya." "Subhanallahi.. Me ya faru?" "Haehuwar ce Abban su,