← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 90

Sashe 65

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

taune lips d'in sa na k'asa, ganin da yayi har lokacin idanun ta na a rufe ne tak'i kallan sa ya sanya shi d'ora bakin nasa akan na ta, da sauri ta bud'e idanun ta dan ba tayi tsammani ba, seta soma mutsu_mutsu tana soma amfani da d'an k'arfin da take da shi dan ture shi, saboda yadda jikin ta yake babu k'wari yasa ko jin ta ma beyi ba, seda yayi kissing na ta na wajen minti 1 sannan ya sake ta yana lumshe idanun sa k'awataccen murmushi akan fuskar sa na cigaba da fita. Kuka ta fashe da shi tana tashi daga jikin sa, yayi saurin rungume ta yana fad'i a hankali "Yi hak'uri, na tuba na bi Allah, bazan sake ba kin ji?" ko bi ta kan sa ba tayi ba ta cigaba da kukan ta, amma duk da haka be sake ta ba. Se da yaji ta dena kukan sannan ya sassauta rik'on daya mata dae_dae lokacin da tace "Allah ni ka sake ni" ajiyar zuciya ya sauke kana yace "Toh Madam rigima, bari nayi wanka na samo miki magani zaki sake jin k'arfin jikin ki" ya fad'a yana sakin ta gaba d'aya, ya kwantar da ita kan gadon gami da ja mata blanket kana ya wuce toilet har lokacin murmushi be gushe akan kyakykyawar fuskar sa ba. Lumshe idanun ta tayi akan gadon tana sake jan bargo ta cukuikuye jikin ta a ciki saboda sanyin dake ratsa k'asusuwan ta, duk da dae yanzun ta d'an ji dama_dama a jikin ta ba kamar d'azu ba, se dae har lokacin be koma normal ba, so take bacci ya d'auke ta amma kuma taji alamar bashi da niyyar d'aukar ta ta, hakan ne ya sa kawae ta sadak'ar ta dae cigaba da kwanciyar. Bayan mintuna masu d'an dama ya fito ya shirya cikin jallabiya me kyau da ta matuk'ar amsar fatar jikin sa. Kallan ta yayi daga inda yake tsaye, ganin ta da yayi tayi lamo cikin blanket d'in yasa yayi tunanin ko tayi bacci ne, dan haka gudun kada ya tadata ya sanya shi ficewa daga d'akin kawae ya wuce masallaci. Se da aka idar da Sallahr Asuba sannan ya dawo da sauri cike da fatan bata tashi ba, addu'ar ta sa kuwa ta kar6u dan kuwa lokacin da ya koma d'in bacci ya d'auke ta. Ajiyar zuciya ya sauke sanda ya yaye bargon yana kallan innocent face d'in ta, ya sake k'ura mata idanu ganin da yayi kamar an k'ara mata wani kyau ne. A nutse ya kae bakin sa yayi kissing goshin ta kafin ya kae bakin sa cikin kunnen ta ya soma hura mata iska idanun sa a lumshe. Da farko sam ba ta ji ba se daga baya sannan ta soma bud'e idanun ta da har lokacin basu koma aenahin colour d'in su ba, se kuma ta lumshe su kamar wadda taga wani abun sannan ta sake bud'e su. Taemaka mata yayi ta mik'e zaune kafin yace a hankali "Sallah.." tura d'an k'aramin bakin ta tayi ganin har lokacin be sake ta ba, ya kalli hannun sa da take kalla sannan ya d'auke kae ya maeda kan ta, da alama bashi da niyyar sakin na ta, kafin tace komae ma se kawae ya d'aga ta zuwa toilet d'in dan ya san idan da kan ta yace ta je za'a dad'e bata k'arasa ba, shi ya taemaka mata tayi alwalar sannan ya sake fito da ita zuwa kan dadduma, saboda jirin da take ji da kuma yanayin jikin ta ya sanya a zaune tayi Sallahr, tana idarwa ya d'aga ta zuwa kan gadon, ta d'auka akan gadon ze ajiye ta, se taga ya d'ora kan ta akan k'irjin sa hadda d'ora nasa kan akan nata, tana k'ok'arin tashi yace "Ki yi baccin ki Uhmm?" ya fad'a tare da fesar da sassanyar iska me dad'in shak'a daga bakin sa zuwa kan fuskar ta, wanda hakan ya tilasta mata lumshe idanun ta, shi kuma ya sake shigar da ita cikin jikin na sa, hak'ura tayi kawae ta kwanta d'in idanun ta a lumshe, cike da fatan baccin yazo ya d'auke ta, bata dad'e ba kuwa wani bacci me dad'i yazo yayi awon gaba da ita, seta soma sauke numfashi, lumshe idanun sa yayi saboda yadda yaji d'umin jikin ta ya soma ratsa shi, janyo wayar sa yayi ya duba lokaci sannan a hankali ya soma zame ta daga jikin sa dan fita ya samo mata magani da kuma abinda zata ci, se da ya kwantar da ita ya kuma gyara mata kwanciyar ya k'arasa wardrobe ya sauya kaya sannan ya koma wajen ta ya bata light kiss a gefen kumatun ta kana ya fice daga d'akin. .. Tun kafin ya k'araso wajen yake ganin kamar itace a zaune zaman dirshan a wajen, mamaki ya sake kama shi ganin kamar d'azun da ya wuce be gan ta ba, "amma me take yi a wajen?" ya tambayi kan sa, ganin dae babu me bashi amsar ya sanya shi yin gaba kawae. Mik'ewa tayi da sauri tun kafin ya k'araso inda take, tana ganin sa ta fashe da kuka kamar wadda akama wani abu, hankalin ta idan yayi dubu ya tashi, dan daga yanayin yadda ta gan shi ta riga ta san dole wani abun ya shiga tsakanin sa da waccan shashashar me kama da aljanu, hakan da ta tuna ne ya sanya ta sake jin wasu k'wallar na ta tsere wajen sakkowa kan fuskar ta. Tsayawa yayi a wajen hannayen sa sak'ale a k'irjin sa ya kafe ta da idanun sa, se dae bece komae, kamar ba zece komae ba se kuma yace "Lafiya kike kuka?" kamar jira take yi se ta saka hannu ta share hawayen fuskar ta sannan ta soma magana "Wannan ma ae rashin adalci ne, ta yaya zaka d'auki kwana na ka bawa wata shashasha can a gefe, bayan ina nan da rae na, da lafiya ta, wallahi bazan yadda ba se an bi min hak'k'i na" cigaba da kallan ta yayi fuskar sa na sake tamkewa, cike da takaecin Muneerahn, abubuwan da suka faru jiya na dawo masa, muryar sa har wani amo take saboda tsananin 6acin rae ya furta "Kada bakin ki ya sake furta kalmar nan ta rashin adalci, kada na sake ji, ni zaki mayar d'an iska? Ni zaki wa iya shege?" yayi maganar yana sake zuba mata idanun sa, se kuma ta d'an so diriricewa amma kuma ta kawar da tsoron da taji ya shige ta sannan tace "Wallahi bazan yadda ba, ta yaya ma za'ayi haka ta faru, yau d'in nan sena nunawa wannan shegiyar yarinyar ni ba sa'ar ta bace wallahi" Muneerah ta fad'a tana shirin wuce shi "Kuull, kada ki soma taka inda take, idan kuma ba haka ba zan kautar da alak'ar aure dake tsakani na dake, na kauda alak'ar en uwan ta ka dake tsakani na dake na nuna miki other side of me" ya k'are maganar a zafafe. Hannu ta kae kan fuskar ta da saboda kukan da ta sha tayi wani mahaukacin ja, jan da ya sake tona asirin jahilin bleach d'in da take yi, ta goge hawayen sannan tace cike da sarewa "Wallahi se Allah ya saka min, kuma ko menene se na d'auki mataki akan ta wallahi" tana gama fad'in hakan ta wuce buguzum buguzum kamar mahaukaciya sabon kamu zuwa part d'in sa. Tsaki ya ja yana fesar da iska daga bakin sa hannun sa akan goshin sa yana d'an murzawa, meyasa Abbu ze had'a shi da Muneerah? Muneerahn da wani lokacin take acting kamar mara hankali ko tunani? Be bi ta kan ta ba saboda ya san k'ofar d'akin a kulle take ya wuce ya hau motar sa ya ja ya fice daga gidan. Kae tsaye asibitin sa ya nufa ya samarwa Ayrah maganin da ya san ze dace da abinda ke damun ta sannan ya koma motar sa, har ya fara driving dan komawa gidan sa, se kuma ya chanja akalar sa zuwa nasu gidan. A compound d'in gidan yayi parking na motar sa kafin ya sauko, dae_dae lokacin Abbu ke shirin shiga part d'in Ummee, seya k'arasa a nutse ya gaeshe da Abbun cike da girmamawa, ba tare da nuna wani abun da zesa ya fahimci ko Abbun na fishi da shi ba ya amsa masa kamar yadda ya saba, hakan ba k'aramin yi masa dad'i yayi ba har seda hakan ya bayyana akan fuskar sa. "Wuce mu je, dama ina son magana da kae.." muryar Abbun ta dawo dashi hayyacin sa, se kuma duk yaji jikin sa ya d'an yi sanyi duk da be san abinda Abbun ze fad'a masa ba. "Toh" kawae ya iya amsawa da ita yana bin bayan Abbun da yayi gaba zuwa d'akin Ummee. Da sallama su duka biyun suka shiga d'akin, Ummee dake zaune kan kujera ta amsa musu kana duk suka nemi waje suka zauna. "Barka da safiya Ummee" "Barka dae, ka tashi lafiya?" Ummeen ta fad'a kamar ba itace ta kira shi d'azun cikin fad'a ba, hakan seya sake sanya jin wani irin sanyi kafin yace "Alhamdulillah.." d'an shiru ne ya wanzu a cikin d'akin kafin can Abbu yace bayan ya d'an yi gyaran murya "Raj!" ya fad'a yana kallan Rk, d'aga idanun sa yayi ya kalli Abbun sannan ya maeda k'asa, Abbu ya cigaba da fad'in "Ka maedo min da takaddun nan, ni da kae na zan je wajen Abban Sadeeq d'in na nemi yafiyar sa!" da sauri Rk ya d'aga kae ya kalli Abbu jin abinda ke fitowa daga cikin bakin sa, Abbun kuwa ya kafe shi da idanun sa yana jiran yaji abinda ze fito daga bakin sa, kamar wanda akawa dole yace "Abbu..!!" d'aga masa hannu Abbu yayi kafin yace "Kada kace zaka ce min takaddun nan basa wajen ka, daga ni se mahaefiyar ka muka san da wannan maganar, daga baya ka had'u da Abban Sadeeq da kuma d'iyar sa, na san dole kaji labarin nan, ka kuma zo kayi bincike akan hakan, ka kuma samu abinda kake nema, Raj kae ka d'auki takaddun nan!" seya d'an dakata anan sannan ya d'ora da "Idan ka san ba cewa zaka yi takaddun na wajen ka ba kamin shiru kawae bana buk'atar jin komae daga bakin
Chapter 65 · 0% Book details