Sashe 16
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta mana k'erere, don Allah befi wancan satin kyau ba?" ajiye maggin hannun ta Ruks tayi sannan ta juyo tana rik'e ha6a kana tace tana murmushi "Umhum wallahi ke kam ki bari kawae.., shi fa kowacce shiga yayi naga alama kyau take masa, wallahi guy d'in ya had'u iya had'uwa" ta fad'a tana jan baki kamar wadda taci abu me yaji, daga nan fa hirar tasu ta soma, maganar tasan nan dae da kullum ita suke yau ma dae ta san suke, da alama basa gajiya da hirar tasa kamar wani abinci "Wae Bahijja meye haka naji kinyi shiru?" Jidda ta fad'a tana jefa mata harara, seta yamutse fuska kana tace "Ke kam ki bari kawae, kae na ke ciwo" itama tayi maganar tana yamutse ta ta fuskar "Toh Allah ya sawwak'e.. Ayrah ki sauko muci abinci" Ruks ta fad'a tana kallan Ayrah dake kwance kamar me bacci, se a lokacin ta tashi dan daga inda take zaune tun d'azu ji take kamar ta tashi ta musu duka, tana jin kamar tace musu sun ishe ta da maganar wannan mugun mutumin, haka dae ta mik'e ta sauko suka ci abincin. ...... Washe_gari k'arfe 7:40 dukan su suka gama shiryawa har da Ayrah, yau ma cikin hijab d'in dae ta shirya kamar jiyan, suka fito tare suna tafiya su Jidda na hira yayin da ita dae tayi shiru kawae, a dae_dae inda ze sada su da ajin nasu dukkan su suka ji wata murya na fad'in "Ayrah Ibraheem Khaleel.." kusan a tare dukan su suka juya, se duk suka tsaya suna kallan mutumin daya kira sunan nata kafin suka kalli Ayrah, itama da kallan rashin sani take bin sa dan tunda take bata ta6a ganin fuskar ba "Sak'o aka bani na kawo miki.." yayi maganar yana kallan ta "Sak'o kuma? Ni ban sanka ba" ta fad'a cike da sakarcin nan nata, se yayi murmushi kana yace "Ehh Hajiya, dama nasan baki sanni ba ae amma daga makarantar ku ne aka turo ni" seta d'an samu relief amma duk da haka tace "Toh mene?" "K'awa ta zo mu tafi 8 ta kusa, kuma kin san yau yana da first period a farko" Ruks ta fad'a tana jan hannun Ayrah, seta d'an maraeraece fuska sannan tace "Uhmm daga makaranta ne fa.." "Kinsan yadda za'ayi? Mu bari muyi gaba ke kuma kiyi sauri kiji abinda ze fad'a, but u should make sure dat kin shigo class before 8" seta jinjina kae tana bin su da kallo sanda suke wucewa ajin kana ita kuma ta dawo da duban ta inda mutumin yake, kafin tace komae yace "Kayan abinci ne dana sakawa Hajiya akace mu kawo miki daga makaranta" seta tsaya ta cigaba da kallan sa kamar me tunani se kuma tace "Kaya kuma?" yace "Ehh.." "A'ah Abba ya siya min" ta fad'a tana girgiza kae, seya sake yin murmushi kafin yace "Ehh wannan ae daban yake Hajiya, kuma kinga daga makaranta ne" seta d'an yi jimm kafin tace "Toh zan kira Yah Sadeeq na fad'a masa tukunna" mutumin ya sauke ajiyar zuciya yana mamakin wannan yarinya haka amma gudun kada ya takura ta shinshino wani abun ya sanya shi fad'in "Toh kira shi" "Ae ba yanzu ba.." tayi maganar cikin turo baki duk da bata san tayi hakan ba "Meyasa?" "Sauri nake" ta fad'a tana gyara tsayuwar ta, seya fesar da iska daga bakin sa kafin yace "Toh shikenan, bari na jira ki" ba tace komae ba ta juya zuwa ajin nasu, dae_dae lokacin da wani d'alibi yayi sauri ya shige cikin ajin, seta ji dad'i hakan na nufin 8 ba tayi ba kenan, dan haka da confidence d'in ta ta sanya k'afa cikin ajin, tayi wajen taku 5 a cikin ajin tana jin dad'in yadda yau ta samu class d'in, se dae ga mamakin ta seta jiyo kamilalliyar muryar sa na fad'in "Go out.." seta ta6e baki a ranta tana sak'a may be tana shigowa k'arfe 8 d'in ta cika, gashi nan har ze kori wata ko wani, dan haka ta cigaba da tafiya har zuwa sanda ta samu waje ta zauna tana lumshe idanun ta kana ta bud'e, abinda ya bata mamaki yadda taga kusan idon kowa na cikin ajin akan ta yake, seta sake kallan wani 6angaren taga still dae ita suke kalla, a hankali tabi jikin ta da kallo zuciyar ta na bugawa tana fatan ba wani abun ne ta manta bata saka ba, ta kalli jikin ta hijab d'in ta gashi nan har kusan k'asa, ita kanta kawae dae ta duba d'in ne amma tasan da akwae abinda beyi ba a jikin ta su Jidda zasu fad'a mata, inda taga kuma sun maeda hankali suna kalla itama ta d'aga raunannun idanun ta da suka cika taff da k'walla saboda wannan kallan da suke mata duk ya rikita ta, a hankali idanun ta suka sauka akan kamilalliya kuma nutsatsiyar fuskar sa me cike da wani irin zati, da kwarjini na musamman har bata san sanda ta d'auke idanun ta da sauri ba tana dafe k'irjin ta daya wani irin buga a lokaci guda "Kurma ce?" yayi maganar kamar baya so kuma ba tare daya kalli en ajin ba "Dake fa yake.. Ki tashi ki fita kin makara.." wata dake kusa da ita ta ankarar da ita, seta d'aga kae cikin rashin fahimta ta kalle shi dae_dae sanda shima ya d'ago nasa firgitattun idanun da suka ida rikita ta, ta sake jin zuciyar ta ta buga da k'arfin da yafi na d'azu, a hankali ya janye nasa idanun fuskar sa ba yabo ba fallasa ya sake fad'in "Fita!" yanzun kam ta tabbatar da ita yake, dan haka jiki a matuk'ar sanyaye taja k'afafun ta ta fice daga cikin ajin, tana jin yadda idanun en ajin suka mata chaaa aka wanda har hakan ya jawo tafiyar ta ta sake chanjawa tana tafiya tana wani rangaji kamar er maye, tun kafin ta ida fitowa daga cikin ajin wani kuka ya k'wace mata, dan haka ita tama manta da wannan mutumin dake jiran ta kawae ta wuce Hostel, akan gadon ta ta zube tana fashewa da kuka, ta san mutumin be santa ba bata san shi ba ba dan haka ba se tace tsanar ta yayi shiyasa yake korar ta kullum, ban da haka meyasa wani ya shiga kafin ita be kore shi ba se ita, wayar ta data ajiye akan gadon dama bata tafi da ita class ba ce ta fara ringing seta janyo wayar ta d'aga tana k'ok'arin tsayar da kukan "Subhanallahi Auta meya faru? Har yanzu baki dena kukan ba?" Yah Sadeeq ya fad'a, seta sake hasaso fuskar Rk cikin idanun ta kana ta harari iska tana murgud'a baki sannan tace "Toh ba wani malami bane, Yah Sadeeq wallahi mugu ne kuma.." "Kae Subhanallahi, Ayrah bakya so karatun naki yayi albarka?" "Toh Yah Sadeeq sau biyu fa yana hana ni shiga aji wae na makara" murmushi Yah Sadeeq yayi daga inda yake kafin yace "Toh kiyi hak'uri, kuma kada na sake ji kince bashi da kirki, daga yanzu ki dinga shiryawa da wuri kina tafiya class kin ji?" seta d'aga kae kamar yana kallan ta sannan tace "Ehh" "Dats my sister.." ya fad'a yana murmushi, seda Yah Sadeeq ya ajje wayar sannan tace bayan ta sake tuna fuskar Rk "Mugu kawae.." K'arfe 3 suka fito daga lectures d'in, Jidda, Ruks Bahijja har ma da Ayrah suka fito daga class d'in dan komawa Hostel, suna cikin tafiya kafin su k'arasa Hostel d'in Bahijja ta kalle su tace "Ku wuce pls yanzu zanje na dawo" "Ina zaki je?" Ruks ta fad'a tana kallan ta, seta d'an yamutse fuska kafin tace "Yanzun zan dawo pls, akwae sak'on da zan kar6a wajen wata cousin sister d'i ta data fara zuwa school d'in nan" "Ohk" suka fad'a kusan a tare, suka cigaba da tafiya yayin da ita kuma Bahijja ta juya.. A hankali take takawa zuwa wajen, seta kalli gefe da gefe ganin babu idon wad'anda ke kanta yasa ta wuce wajen, seta dakata a bakin k'ofar office d'in nasa sannan ta kalli wani wanda ke tsaye a wajen tace "Pls Doctor na ciki?" "Yeah.." ya fad'a yana kallan ta "Pls taemaka kamin iso mana" ta fad'a tana maraeraece fuska, seya d'aga kafad'a yana wucewa ciki, wajen minti 2 se gashi ya fito yace "Ki shiga.." murmushi Bahijja tayi cikin jin dad'i kana tace "Nagode sosae.." ta fad'a tana zame takalmin k'afar ta ta shige cikin office d'in, dae_dae lokacin Rk yana tsaye gefen kujerar office d'in, da sallama ta shiga ba tare daya kalle ta ba yace "Come in" seta lumshe idanu tana jin yadda muryar tasa ke k'ara dad'i, ta k'arasa ta zube a k'asa tana fad'in "Sir barka da rana.." kamar be ji ba seda ya nemi waje ya zauna ya bud'e wani littafi sannan yace "Barka..how can i help u?" yayi maganar a had'e "Sir.. Pls zuwa nayi na rok'i alfarma" "Umhum.." yayi maganar har lokacin yana kallan littafin hannun sa, sosae taji dad'in yadda ya amsa matan, dan haka seta gyara zama tace "Sir dama Mama na ce tace a cikin malamae na samu wanda ze d'an dinga taemaka min da abinda bangane ba, shine.. Shine nace bari nazo na kar6i koda contact naka ne, idan ina da buk'atar taemako sena kira ka.." a hankali ya ajje littafin dake hannun sa ya d'aga kyawawan idanun sa ya zube su kan Bahijja, be san sanda ya basu fuska da har irin wannan raenin ze shiga tsakanin su ba, seya kwantar da kansa akan kujera hannayen sa duka biyun ya sark'e su cikin juna kana ya sanya su a ha6ar sa yana d'an juya kujerar daya ke kae, jin shiru ya sanya ta fad'in ba tare data d'ago ta kalle shi ba, dan tasan idan tace zata kalle shin wannan kwarjinin nasa da idanun nan nasa zasu sanya ta kasa fad'ar abinda tayi niyyar fad'a, koma gaba d'aya ta manta abinda zata fad'a d'in "Shine dama abinda ya.." "U shut up bloody fool.." ya fad'a cikin er d'aga murya yana sake watsa mata idanun sa, tuni ta rikice ta d'ago kamar zata yi kuka dan gaba d'aya ya gama rikita ta da wannan razananniyar muryar tasa, bata jira ya sake cewa komae ba ta