Sashe 88
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kallan kyakykyawan Babyn. Se a lokacin ya maeda dubansa kan Ayrah dake zaune kan gado hannunta d'auke da cup da spoon a ciki, tana yamutse fuska tana kakkauda kae. Dariya ce ta k'wace masa wato dae me hali baya fasa halinsa. Cike da tsokana yace "Auta me ya faru?" D'aga kae tayi ta kalle shi, kafin tace komae Babyn ya soma mutsu_mutsu, hakan ne yasa Yah Sadeeq mik'ewa ya d'ora shi a kafad'arsa ya soma lallashinsa yana shafa bayansa a hankali. Ajiyar zuciya ta sauke tana komawa ta lumshe idanunta, tana shirin kwanciya Umma tayi murmushi tana girgiza kae dan ta san abin da Ayrahn take gudu, dan ko d'azu da za tayi feeding yaron se da tayi kuka, ita kanta Umman se da ta tausaya mata. "Ayrah kwanciyar ta isa haka!" Se da ta bud'e idanunta ta kalli Umman sannan tace "Umma don Allah.." "Kar ki damu kiyi zaman ki. Babu mamaki bacci yake ji, bari na goya shi." Umma ta fad'a tana kar6arsa daga hannun Yah Sadeeq. "Toh" Ayrah ta fad'a tana kallan Umman sanda take goya shi. Se kuwa yayi luff a bayan Umman kamar ba shi ne yake kuka yanzu ba. Murmushi ne ya su6uce mata akan fuska tana sake kallan fuskar yaron da koda yaushe bata gajiya da kallan nasa. Jin da Umma tayi yayi shiru ya sanya ta fita daga d'akin, se kuwa Yah Sadeeq ya taso ya matso kusa da gadon ya fito da wayarsa daga aljihu yace "Yawwah Auta zaku gaesa da Fatima" Wato ido tayi kana tace "Yah Sadeeq wace Fatima?" ta tambaya cikin jin dad'i cike kuma da k'aguwa da son jin amsar da zata fito daga bakinsa. "Matata!" Yah Sadeeq ya fad'a cikin basarwa. Bud'e baki sosae Ayrah tayi har da saka hannu ta rufe bakinta, lallae da gaske Yah Sadeeq d'in yake. Cike da zumud'i tace "Don Allah ka nuna min ita ka ji? Allah na k'agu na ganta." Murmushi yayi dama ya san Ayrahn ko da yaushe me taya shi farin ciki ce kana yace "Ku fara gaesawa tukun" Yayi maganar yana mik'a mata wayar bayan ya kira layin Fatima. Kar6a Ayrah tayi cikin k'aguwa da son Fatiman ta d'aga, babu dad'ewa kuwa ta d'aga tayi sallama da siririyar muryarta. Amsawa Ayrah tayi kafin suka gaesa, tayi mata barka da tambayar Baby, tace mata yana lafiya. "A shafa min kansa pls." Fatiman ta fad'a. "Tohm In Sha Allah Aunty Fati." Murmushi Fatiman tayi wanda har se da Ayrah ta jiyo sautinsa kafin suka yi sallama. Mik'awa Yah Sadeeq wayarsa tayi kana tace har lokacin murmushi be bar kan fuskarta ba dan kuwa haka kwae ta ji Fatiman ta burgeta. "Yah Sadeeq Allah kuwa na ji dad'i sosae, ta burgeni!. A unguwar nan take?" Murmushi Yah Sadeeq yayi yana jin dad'in yadda Ayrahn ta yabi Fatiman tasa hakan ne ya sanya shi fad'in "Kin fa santa!" Da sauri tace "Don Allah? Amma ban gane muryarta ba. Wace pls?" Wayarsa ya shiga ya d'an yi danne_danne ya kamo wani hoto kana ya mik'a mata. Kar6ar wayar tayi ta kalli hoton, da sauri tace "Laa, wae Fatima Basheer?" Jinjina kae yayi kana yace "Yep!" Mik'a masa wayar Ayrah tayi lokaci d'aya tana fad'in "Allah Yah Sadeeq ka iya za6e, ga ta kyakykyawa tubarkallah!" "Allah ko k'anwata?" Kafin ta kae ga bashi amsa Umma ta shigo cikin d'akin, se ya mik'e a hankali yace "Zamu k'arasa maganar" Se yayi wuff ya fice daga d'akin. Binsa da kallo Umma tayi kana ta maeda kan Ayrah da ke ta k'unshe dariya. Ta girgiza kae tana murmushi, da alama wani abun suka gama sak'awa ko suka warware. "A kawo miki abincin?" Umma ta fad'a tana kallanta. Girgiza kae tayi kana tace "A'ah Umma se anjima" tayi maganar tana yamutse fuska. Had'e face Umma tayi tace "Baki isa ba kuma Ayrah, haka kike so kiyi ta zama ba zaki dinga cin abinci ba ballantana shi kansa yaron nan ya samu abin da ze ci. Wannan cutar kanki da na yaron nan zaki yi, dan haka tashi tun kafin na 6ata miki rae na kawo miki abinci ki cinye tass yanzun nan." Umma ta fad'a tana ficewa daga d'akin dan kawo mata abincin. A hankali ta tashi daga kishingid'ar da tayi, ta gyara zamanta a hankali dan har yanzu jikinta be gama komawa daidai ba. Babu dad'ewa kuwa Umma ta shigo d'akin hannunta d'auke da plate da ta zubo abincin da ta mata na musamman. Babu yadda ta iya haka taci abincin saboda yadda ta ga ran Umman ya 6aci. Ta ci d'in ko dan ta faranta mata duk da ba dad'insa take ji ba. .. Se bayan maghrib sannan Ummee ta dawo gida. A parlourn Abbu ta tadda Rk yana jiran Abbu da ya shiga d'aki yanzun nan. Ganin ta da yayi ya sanya shi yi mata sannu da zuwa kana ya gaeshe da ita da murmushi kan fuskarsa ya d'ora da "Sannu da dawowa" ya sake fad'i duk da ya fad'i hakan da farko. "Yawwah, Abban Baby ya sunansa?" Se da ya kae hannunsa ya d'an shafa k'eyarsa yana murmushi kana yace "Abbu ne ae Ummee." "Wanne Abbun?" Abbu dake k'arasowa cikin parlourn ya fad'a. Dukansu suka kalle shi sanda ya nemi waje ya zauna, ya sake maemaeta tambayarsa a karo na 2. "Abbu kae" Rk ya fad'a. Jinjina kae Abbu yayi yana murmushi kana yace "Idan har kayi haka ne dan ka burgeni, toh na ji dad'i sosae, Allah ya raya mana Little Boy. Amma da zaka sake burgeni se a saka sunan Abban Sadeeq, ina ganin kamar hakan ze fi." Shiru Dukansu suka yi kowa yana nazarin maganar Abbun. Ta 6angaren Ummee ta amince da hakan, ko babu komae Abban ya cancanta a masa takwara. Se ta kalli Rk tana jiran jin amsar da zata fito daga bakinsa. "Amma Abbu.. Na so yi maka takwara!" Bud'e baki Abbu yayi yace "A'ah yau na ji d'an nan, jika d'aya zaku haefa min ne ko kuwa me kake nufi? Idan dae ba hakan kake nufi ba toh ina sake samun wani jikan se amin takwara. Ina shi kenan ba?" Murmushi Rk yayi kana ya jinjina kae yana sake jin dad'in yadda Abbun ya chanja gaba d'ayansa, se dae ta wani 6angaren ya so ya d'an ji kunya akan maganar Abbun amma ya fuske yace "Shikenan Abbu.." "Toh Masha Allah, Allah ya raya mana Ibrahim Khaleel." "Ameen_Ameen" Ummee ta amsa tana sake hango kyakykyawar fuskar jaririn da taji kamar kada ta taho ta bar shi dan kyawunsa da kuma shiga rae. .. Tun da Ayrah ta haehu ya kasance kullum se Rk ya je gidan dan baze iya kwanaki be ga matarsa da d'ansa ba. Mutanen da kullum yake ji kamar ana k'ara masa sonsu ne. Toh da dae ya fahimci bak'i sun fi zuwa da rana se ya maeda zuwan nasa da dare. Se dae idan yana da aeki ne shi ne baya zuwa. Se dae duk ranar da be zo d'in ba toh fa zaka same su kusan koda yaushe da waya a hannunsu. .. Ranar suna ta zagayo Baby yaci sunan Abba wato Ibrahim kamar yadda Abbu ya buk'ata. Sosae Abba yayi farin ciki da wannan takwara da aka masa, ya kuwa saki jiki ya yiwa takwaran nasa siyayya me yawa. Yaro ya sha kayayyaki da dama, daga wajen mutane daban daban, dan kuwa ko Abbu da Ummee akwati guda guda suka yi masa wadda ke dank'are da had'ad'd'un kaya, masu kyau, aji da tsada. .. Daga nan Ayrah ta cigaba da zama a gida Umma na kula da ita, lokaci zuwa lokaci Ummee kan je dan ganinta da kuma Little Khaleel da kullum k'ara wayo yake da kyau kamar d'an larabawa. Ta 6angaren Ayrah ma kulawa ta musamman take samu, ba daga wajen Umma ba, ba daga wajen mijinta ba, daga wajen kowa ma samu take yi. Hakan ba k'aramin dad'i yake yi mata ba musamman kulawar 'yan gidansu a kanta da kullum k'aruwa take yi. Cikin lokaci k'ank'ani ta warware, se jegon ya kar6eta ta sake murmurewa, ta murje, jikinta ya sake wani irin kyau da shek'i. Se da tayi kwana arba'in sannan Umma da kanta ta maeda ta gida, bayan ta mata gyara na musamman, ta gyareta tsaff, se ta sake wani shek'i kamar amarya. Shi kansa Little se ka d'auka d'an wata 3 ne saboda yadda jikinsa yake, ga wayo, ga kuma murjewar jiki da yake da shi, ga shi kuma fari sol tubarkallah, dukka wasu shika_shikan kyau yaron ya had'a su, hakan ne yasa ya zama na musamman, dan kuwa kyau ya ya d'akko na uwa da uba ne. .. Driving yake yi amma gaba d'aya hankalinsa yana kan gida. A haka dae har ya k'arasa gidan. Kae tsaye yana parking na motarsa ya sauka ya kulle gidan ya cigaba da takawa zuwa ciki cike da shauk'in son ganin iyalan nasa. Kae tsaye bedroom d'inta ya wuce, k'amshin da ya daki hancinsa ya sanya shi lumshe idanunsa kana ya tura k'ofar d'akin. Tana zaune akan stool d'in gaban mudubi tana taje yalwataccen gashin ta. Ya lumshe idanunsa kana a nutse ya cigaba da takawa zuwa ciki. Babu 6ata lokaci ya d'ora kansa akan farin gadon bayanta, ya kuma rik'o ta da hannayensa. Ko ba'a fad'a mata ba ta san shi ne, musamman da k'amshin turarensa ya fallasa shi, hakan ne yasa kusan a tare suka lumshe idanunsu. Numfashi ya ja ya fesar hakan ya bashi damar shak'ar daddad'an k'amshin dake tashi daga jikinta. Se da ya sake furzar da iska daga bakinsa kafin yace "Nayi kewarki Babe!" yayi maganar a d'an sark'e. Mik'ewa tayi har lokacin tana jikinsa, hakan ne ya bashi damar sake rik'eta sosae, itama rungume shin tayi dan ba k'arya tayi kewarsa. "Missed u too Babe" ta fad'a idanunta a lumshe. Sun kae wajen minti 1 a haka sannan suka saki juna. A hankali ya k'arasa wajen Little dake kwance idanunsa biyu yana ta wasa abinsa, d'aukarsa yayi yayi juyi da shi a hannunsa sannan ya dawo da shi ya rungume shi a k'irjinsa. Dariya sosae Little ya shiga yi kamar ya san wanda ya d'auke shi. Kallansu kawae Ayrah take tana jin zuciyarta k'al, k'aunarsu ta musamman na cigaba da ratsata. Juyawa yayi