Sashe 4
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
takaddar hannun sa tana kallan abinda ke ciki, ta karanta da karatun data iya sannan ta kalle shi yadda shima ita d'in yake kalla, seta saka dariya kawae hadda toshe baki kamar wata babba, dama fuskar tasa babu annuri yanzu kuma da yaga tana masa dariya seya sake tsuke ta ya sanya hannu ya kar6i takaddar hannun ta ya juya da nufin barin wajen, hannun ta ta saka ta rik'o nasa hannun, manyan idanun ta sun cika da k'walla tace "Yi hak'uri, gani nayi kae babba ne fa.." ta fad'a abinda take ganin shine ya dace ta fad'a "Allah kuwa idan kana so zan fad'awa Yah Sadeeq ya dinga kowa maka karatu.." seya juyo gaba d'ayan sa yana kallan ta lokaci d'aya murmushi na su6ucewa akan fuskar sa yace "Da gaske?" karo na farko kenan da yayi magana, seta jinjina kae kawae tana d'an murmushi... Ku sani wannan book d'in ina yin sa ne based on experience, zan iya cewa wani abun ma true ne wlh nake had'a muku dashi duk dan labarin ya k'ara armashi kuma ku fahimci sak'on da nake son isarwa, Allah yasa mu dace.. *ZARAH BINT YUSUF (Mhiz Innocent)* https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* *TITAN'S OF TALENT* Page_003 ___"Ke Ayrah!!" Yah Sadeeq ya fad'a yana k'arasowa wajen, dukkan su suka d'aga kae suka kalli inda yake, bata motsa daga inda take ba sedae ta cigaba da kallan sa har ya k'araso wajen, ya kalli inda yaron nan ke tsaye na tsawon sakanni sannan ya maeda kan Ayrah, kama hannun ta yayi ba tare da yace komae ba suka bar wajen, yayin da shi kuma ya bisu da ido har suka bar wajen, seda suka isa bakin ajin su sannan ya tsaya ya kalle ta fuskar sa a had'e yace "Meya kae ki can?" rau rau tayi da idanun ta, tana ta6e d'an k'aramin bakin ta kamar zata yi kuka "Ba nace miki ba'a wasa da maza ba?" jinjina kae kawae tayi, yace "Bari na sake ganin ki da wani!" ya fad'a yana sake had'e rae dan ta fahimci da gasken yake "Ya hak'uri Yah Sadeeq.." ta fad'a tana share k'wallar idanun ta, seya d'an yi murmushi kana yace "Yawwah..toh maza ki koma aji.." daga haka ta shige class d'in su shima ya tafi nasu ajin. .. Washe gari ma haka ta sake ganin yaron nan yana lek'e ta window, koda aka fita break seta ajjiye basket d'in ta a cikin ajin sannan ta fita zuwa inda ta ganshi a bayan ajin nasu yau sa6anin da da yake zama a gaban ajin nasu, yana zaune yau ma kamar jiyan yana karanta wata takadda dake hannun sa, seta k'arasa ta zauna tace "Wae kae ba'a saka a makaranta ba?" tayi maganar cike da sakarci, da sauri ya juyo yana kallan ta dan besan da zuwan ta wajen ba maganar ta kawae yaji, ganin ta ya sanya shi sakin ajiyar zuciya sannan ya jinjina kae "Kawo na koya maka toh" ta fad'a tana kallan sa, seya lumshe manyan idanun sa sannan ya mik'a mata takaddar hannun nasa, ta kalla abinda ke cikin takaddar, abinda aka koya musu yau ne seta dinga fad'a masa yadda ta fahimci aekin, shi kuma yana biye mata yana jin abinda take koya masan, kasancewar k'wak'walwar tasu ba d'aya bace kuma karatun su Ayrahn na yara ne yasa cikin k'ank'anin lokaci tana masa yake ganewa, tunda ta fara bece komae ba yayi shiru yana saurarar ta yana kallan ta yadda take maganar duk da ba wani iya magana tayi ba amma yana ganewa, wani abun ne dae sedae idan ta fad'a ya gyara da kanshi, idan ya fahimci bata san yadda zata fad'a ya gane ba, tana ji an kad'a k'ararrawa alamar an koma break seta yarda takaddar hannun ta ta mik'e tana waro idanun ta "Na tafi.." ta fad'a tana shirin wucewa yace "Nagode..ya sunan ki?" seta juyo ta zuba masa manyan idanun ta sannan tace bayan tayi murmushi "Ayrah.." ta fad'a tana juyawa, kamar wadda ta tuno wani abun seta juyo da sauri tace "Kae fa?" murmushi ne ya su6uce a kyakykyawar fuskar sa sannan yace "Suraj..." "Suraj!!" ta maemaeta sunan a la66an ta sannan ta wuce ba tare da ta sake cewa komae ba ta koma ajin su. ... Abba na sauke su a inda ya saba sauke su se suka tafi gid a, kamar kullum da sallama suka shiga gidan nasu, Umma na zaune kan dadduma da alama sallah ta idar, tayi musu sannu da zuwa tana rik'e Ayrah data rungume ta "Tashi ki kae basket d'in kitchen.." Umma ta fad'a tana kallan Ayrah "Umma akwae abinci a ciki fa" da mamaki Umma ta kalle ta kana tace "Baki cinye ba?" girgiza kae Ayrah tayi tace "A'ah banci ba fa" mik'ewa Umma tayi rik'e da Ayrahn a hannun ta tace bayan ta zauna "Baki da lafiya ne ko a k'oshe kike?" "Ehh" Ayrahn ta fad'a tana cire hannun ta daga cikin na Umma ta wuce d'aki, Umma ta bita da kallo tana girgiza kae sannan ta dawo dashi ga Sadeeq dake tsaye tace "Meya hana ta cin abincin?" girgiza kae Yah Sadeeq yayi sannan yace "Wallahi Umma bansani ba, kuma amma banga alamar rashin lafiya a tattare da ita ba ballantana ace koh?" "Ehh hakane, may be ko yau a k'oshe take, ko kuma kana so ka koya mata halin ka" Umma ta fad'a tana kallan sa, murmushi Sadeeq yayi yana wucewa d'aki.. ... Suna zaune a parlourn suna cin abinci, ita a d'an k'aramin plate d'in data saba cin abinci a ciki wanda indae ba'a ciki aka zuba mata ba bata ta6a cin abincin, yayin da Yah Sadeeq ke zaune kan kujera shi kuma yana rubutu a littafi, ita kuma Umma tana zaune kusa da Ayrahn itama tana cin nata abincin a plate, kallo suke a er madaedaeciyar Tvn su, tashar MBC bollywood suke kalla inda suke nuna film d'in Mujhse Dosti Karoge, sosae Ayrah ke kallan duk da ba wani fahimta take ba, daga film d'in hausan har na Indian kawae tana zama ne idanun ta duka akan Tvn amma in za'a tsare ta a tambaye ta ba ganewa take ba "Raj.." taji an fad'a a cikin film d'in, seta sake kallan cikin Tvn sosae, shiru tayi tana tuna sunan wannan d'in nan daya fad'a mata "Suraj.. Raj.." ta fad'a a fili tana saka hannun ta a kumatun ta kamar me tunani "Ayrah.." Umma ta fad'a tana kallan ta, seta kalli Umman kafin Umman ta sake cewa komae tace "Umma irin sunan wani d'an ajin mu.." "Wanne?" Umma ta fad'a tana kallan ta "Raj.." "Anya kuwa?" Umma ta fad'a tana kallan ta, jinjina kae tayi kana tace "Allah kuwa Umma, shima sunan sa Raj" "Toh yayi, k'arasa cin abincin ki" babu musu ta cigaba da cin abincin ta tana yi tana kallan Tvn. ... "Monitor jeka taho min da yaron can.." Uncle Abdoul ya fad'a yana kallan Monitorn ajin su Ayrah, tashi yayi ya fita daga ajin, ya zagaya inda Uncle d'in yake nuna masa, yana zaune gaba d'aya ya gama muzanta haka kuma ya tsorata, yana ganin shikenan daga yau korar sa za'ayi a hana shi shigowa makarantar gaba d'aya, be ta6a tunanin za'a iya ganin sa ba dan yadda yake takatsantsan akan kar wanda ya ganshi, se gashi yau malami da kansa ya ganshi, ya d'an runtse idanu kad'an yana jin kwata kwata babu dad'i "Wae kazo inji Uncle" maganar data sanya shi saurin bud'e idanun sa kenan yana kallan yaron da yazo kiran sa, k'irjin sa na bugawa haka ya mik'e yana jin kamar ya gudu amma beyi hakan ba yabi bayan sa har zuwa cikin ajin, a k'ofar ajin ya tsaya ya kasa yin gaba ko baya har zuwa sanda monitorn ya wuce wajen zaman sa ya zauna "K'araso ciki" Uncle d'in ya fad'a yana kallan Suraj, ya kasa d'aga ido gaba d'aya ya kalli cikin ajin dan yasan idanun kowa na kansa ne "Me yake kawo ka nan?" Uncle Abdoul ya tambaya, kasa cewa komae yayi dan baya jin ze iya fad'in wani abun "Wani abun kake siyarwa?" k'arya bata daga cikin halayen sa amma yau yana ganin gwara yayi tan, dan haka kawae ya jinjina kae "Toh kada ka sake zuwa nan wajen siyar da abu saboda kana d'aukewa wasu hankali, ka tafi can harabar makaranta ka dinga siyarwa.. Ina kayan siyarwar taka?" "Toh.. Suna waje.." ya fad'a a hankali "Tashi kaje toh.." Uncle ya fad'a, da sauri ya mik'e cike da sassarfa ya fice daga ajin, binsa tayi da kallo dan tunda ya shigo take kallan sa har zuwa sanda ya fita d'in.. Ana fita break kuwa ta zagaya inda ya saba zama, yana zaune se dae sa6anin yadda take ganin sa da takadda a hannun sa yanzu ya d'ora kansa akan cinyar sa ne, ta k'arasa ta zauna sannan tace a hankali "Raj.." maganar da yaji ya sanya shi d'aga idanun sa ya kalle ta, seya maeda kansa kawae yayi shiru "Toh na dena kula ka" ta fad'a tana tura d'an k'aramin bakin ta gaba kuma tana shirin mik'ewa, da sauri ya juyo yana kallan ta se tace "Toh me aka maka?" ta fad'a har ranta tana jin ba dad'i na yanayin data ganshi, seya sake d'agowa ya kalli idanun ta da suka yi rau rau kamar za tayi kuka, da sauri ya girgiza kae kafin yace a nutse "Ance kar na sake lek'awa cikin ajin.." "Ya hak'uri" ta fad'a kamar me shirin yin kuka, bece komae ba illah kallan ta kawae da yake yi, ta rufe idanun ta sannan ta bud'e tace "Kawae ka dena lek'awa zan dinga koya maka komae kaga ni babba ce" ta fad'a tana murmushi, shima murmushin yayi sannan yace "Tohm nagode.." "Ae ni babba ce koh?" ta fad'a tana kallan sa, ya sake yin murmushi sannan yace "Ehh sosae ma" "Yeah" ta fad'a tana dariya har da rufe fuskar ta. Tun daga ranar ya kasance kullum taje makaranta idan aka fita break bata cin komae sedae ta tafi wajen Raj ta zauna ta koya masa duk abinda aka koya musu, kuma In Sha Allah kullum ta koma gida se tayi wa Umma zancen Raj, babu ranar banza da za'a tashi a kwanta Umma