Sashe 44
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sa suka yi exchanging ya kira, bugu 1_2 ya d'aga, a dak'ile ya furta "Pls.. Idan tana nan, ina waje zamu d'an gaesa ne.." "Ohk" Yah Sadeeq ya amsa yana ajje wayar, sannan ya k'arasa cikin d'akin Ayrah dake zaune ita da Umma yace "Umma Raj na k'ofar gida, wae zasu gaesa da Ayrah.." da sauri Ayrah ta d'aga kae ta kalli Yah Sadeeq se kuma ta sadda kan ta k'asa cike da kunya "Tohm shikenan" Umma ta fad'a tana kallan Autar ta ta dake ta sussunne kae "Toh tashi ki shirya ki je.." "Kae Umma!" ta fad'a bayan ta d'ago kan ta ta kalli Umman, girgiza kae Umma tayi tana murmushi sannan ta mik'e tana fad'in "Idan kin gama jin kunyar seki tashi ki je" daga haka ta fice daga d'akin, bin Umman tayi da kallo har ta gama ficewa daga d'akin sannan ta dawo da duban ta jikin mudubin d'akin nata ta kalli fuskar ta, babu komae akan fuskar ta ta, kuma itama bata buk'atar wani abun, se kwae ta mik'e ta ciro wani gogaggen hijab d'in ta a cikin wardrobe ta zura sannan ta fito tana kallan tsakar gidan nasu, ajiyar zuciya ta sauke ganin babu kowa sannan ta fice daga cikin gidan. Tunda ya hango ta yaji wani irin sanyi na ratsa shi, wannan bak'in cikin da yazo dashi ya shiga kwaranyewa yana yin nasa waje, be san sanda ya saki murmushi ba lokacin data dakata daga inda take tsaye ba, bud'e murfin motar yayi ya fita sannan ya k'arasa ya bud'e wajen me zaman banza kana yace yana kallan ta "Bismillah gimbiya.." wata kunyar ce ta sake lullu6e ta dan haka da er sassarfa ta k'arasa ta shiga cikin motar, se da ta shiga sannan ya zagaya ya koma mazaunin driver har lokacin yana jin wani irin farin ciki mara misaltuwa musamman daya tsinci murmushi akan kyakykyawar fuskar ta daya dad'e be gani ba, koda ya shiga motar ma juyowa yayi gaba d'aya yana kallan ta kamar ze cinye ta, hannu ta kae taja hijab d'in jikin ta tana rufe fuska da shi sannan tace "Kae don Allah!" wani k'ayataccen murmushi ne ya su6uce masa sannan yace "A'ah ki bar ni na kalla ni kam, kin san kuwa yanda na zak'u da ganin fuskar ki, nayi missing naki irin sosae d'in nan" ya fad'a yana ji kamar ya janyo ta ya rungume ta, se dae yasan halin abarsa dan haka ya d'an lumshe idanun sa dae_dae lokacin data d'ago kan ta "Ina fatan an yafe min abinda na aekata, kae na bisa wuya na" ya fad'a yana d'an rank'wafar da kan sa, bin sa tayi da kallo sanda ya rank'wafar da kan nasa, dae_dae lokacin da idanun ta suka sauka kan wasu jerin gwanon invitation card dake ajje a waje guda, haka kawae taji sun d'auki hankalin ta saboda yanda taga kamar idanun ta sun hangi sunan da take da tabbacin babu me irin shi a yankin su, dan haka babu 6ata lokaci ta d'auki katin sannan ta sauke manyan kyawawan idanun ta kan katin ta shiga karantawa, katin gayyatar d'aurin auren Raj Kabeer ne da kuma Muneerah Abubakar, idan har bata manta ba ko kuma kamar yanda ta sani sunan sa ne wannan, take kuma a lokaci guda k'afafun ta suka fara rawa kamar wad'anda ake kad'asu, tun kuma lokacin data karanta sunan wata mace tare da sunan Rk taji kamar wani abu ya gifta ta wajen idanun ta ne dan haka bata sake ganin wani abu dake a cikin katin ba, k'irjin ta ya shiga bugawa da k'arfin gasken gaske hannun ta kuma dake d'auke da katin ya shiga rawa shima dan haka cikin k'ank'anin lokaci katin yayi nasa wajen saboda yanda hannun ta ya gaza rik'e shi, gaba d'aya kan ta ya kulle, k'wak'walwar ta ta toshe haka zalika idanun ta sun makance kunnuwan ta kuma sun kurumce, babu abinda take iya tunani da hangowa se sunan sa dake jikin katin tare da sunan wata mace... Mhiz Innocent..... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* Page 038 ___Jin da yayi shiru har lokacin ba tace komae ba ko tayi wani abun da zesa ya fahimci tana wajen ba ya sanya shi d'ago da kan sa a nutse ya sauke su a kan ta lokacin da jajayen idanun ta da k'walla ta gama cika su taff ke kan sa, abu kad'an ne ze sanya su zubowa, kallan sa kawae take yi kamar me son gano gaskiyar abinda ta gani a cikin katin nan daga cikin fuskar sa, da mamaki yake kallan ta ganin tana masa wani kallan tuhuma ga kuma kyawawan narkakkun idanun ta da suke cigaba da bin sa da kallo, a hankali ya kae hannun sa yana shirin rik'o ta lokaci guda kuma yake fad'i a nutse "Meya faru?" ya fad'a cikin damuwa, dae_dae kuma lokacin daya ida kae hannun sa jikin ta, se a lokacin ta soma dawowa hayyacin ta, ta kautar da jikin ta daga k'ok'arin rik'o ta daya ke yi, sannan cikin sake k'arya ta zuciyar ta da abinda ta gani tace "Aure kayi?" ta k'are maganar lokacin da hawayen da suka taru a cikin idanun ta suka samu damar zubowa akan fuskar ta, runtse idanun sa yayi lokaci d'aya k'irjin sa ya d'an buga "Ya akayi ta sani?" tambayar data fara zuwa masa a cikin kae kenan, kamar ta san me yake tunani seta saka hannu ta d'auko katin daya fad'i daga hannun ta d'azun duk da har lokacin jikin ta be bar rawa ba "Wannan katin auren waye?" iska ya fesar daga bakin sa sannan ya dafe kan sa daya sara masa, a hankali ya sake d'aga idanun sa ya zuba su a kan ta sannan yace "Ayrah pls ki tsaya zan miki bayani kin san.." "Na auren waye?" ta sake katse masa maganar daya fara yi, dan haka kawae taji jikin ta ya sake yin sanyi, seda ya sake lumshe idanun sa sannan yace "Nawa ne amma.." kukan data keta rik'ewa ne ya k'wace mata gaba d'aya, bata da k'arfin da zata iya ficewa ta shige gida tayi kukan ta dan haka ta d'ora kan ta akan cinyar ta ta shiga rera shi tana jin yanda wani irin takaeci, bak'in ciki da kuma k'unar zuci ke addabar ta "Yah ilahee.." ya ambata akan la66an sa, shi kam yau yaga ta kan sa, hannun sa duka biyun ya saka ya janyo ta cikin jikin sa har zuwa lokacin kuma kukan take har da sheshshek'a, fuzge jikin ta ta shiga yi amma ya k'arasa shigar da ita sannan ya zagaye ta da duka hannayen nasa yana lumshe idanun sa, har lokacin bata hak'ura ba ta cigaba da k'ok'arin tashi lokaci d'aya kuma tana furta "Ni ka sake ni, bana son ka, bana son ka" be san sanda murmushi ya k'wace masa ba yana girgiza kae, ban da abin Ayrah idan bata son shi mene na kishin sa haka? Sake rungume ta yayi tsam cikin jikin sa kamar ze maeda ta cikin sa, sannan ya d'ora kan sa akan ta dake kan k'irjin sa, da dae ta gaji da k'ok'arin tashin se kawae ta sake fashewa da wani kukan tana komawa jikin nasa gaba d'aya, hakan ne ya sake bashi damar rik'e ta sosae, be hana ta kukan ba dan yasan dole ne se tayi kukan musamman wannan abu data gan shi kawae daga sama, ta d'auki wajen minti 2 tana cigaba da rera kukan se kuma daga baya ta koma tayi lak'was tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya cike da jin haushin sa, se kuma a lokacin ta cigaba da kicin_kicin tashi, a wannan karon be hana ta tashin ba ya sake ta a hankali, kae tsaye ta ta6a k'ofar fita se ta ji ta a rufe, dan haka ba tare data kalle shi ba ta furta "Ka bud'e min na fita" shiru yayi yana bin ta da kallo duk da baya iya hangen fuskar ta "Don Allah ki tsaya ki saurare ni" kamar jira take seta juyo tana kallan sa, kafin ta fara magana fuskar nan ta ta tayi jajur haka zalika sassanyar muryar ta ta sake rusuna "Babu abinda zaka fad'a min Raj, ka bud'e min na koma gidan mu, kaje kayi rayuwa da wadda kake so nima yanzu bana son ka.." ta fad'a tana jin wani irin zafi da bata ta6a jin sa ba cikin zuciyar ta, zazzafar iska ya fesar daga bakin sa kana ya d'an lumshe idanun sa yace "Ayrah, wallahi Abbu ne ya aura min ita, akwae maganar auren dama tun kafin sake had'uwar mu, don Allah kiyi shiru ki dena wannan kukan wallahi yana nakasta min zuciya" hannu ta saka ta toshe kunnuwan ta, tana ji a ran ta kamar wad'annan d'in kalaman yaudara ne kawae yake fad'a mata, meyasa zeyi mata haka? Meyasa ta yadda dashi shi kuma yaci amanar ta? Meyasa ze had'a ta da wata bayan ita tunda take bata ta6a had'a shi da wani ba, tana cigaba da tare sabon kukan daya taho mata ta furta "Ni ka bud'e min k'ofa na fita.." yanzu kam babu musu ya bud'e mata k'ofar, da sauri ta saka hannu ta bud'e murfin motar sannan ta fad'a cikin gidan nasu, a tsakar gida ta taradda Umma babu 6ata lokaci ta fad'a jikin Umman tana sake sakin wani sabon kukan "Subhanallahi Ayrah.. Meya faru?" Umma ta fad'a tana rik'o Ayrahn dake cigaba da kuka kamar wadda akama mutuwa, bata iya cewa komae ba saboda yanda zuciyar ta ke cigaba da tafasa, haushi da kuma takaeci suna sake cika ta, seda ta gama kukan tsaf sannan ta d'ago tana kallan Umma da zuwa lokacin ta gama rud'ewa da yanda taga d'iyar ta ta na kuka haka "Umma wae aure yaje yayi! Umma ya yaudare ni bansan yadda zanyi ba zuciya ta na dab da bugawa" ta fad'a tama manta Umman ta take fad'awa maganar, da mamaki Umma take kallan Ayrahn kafin cikin k'arfin hali ta furta "Ay..." sallamar da Abba yayi cikin gidan itace ta katsewa Umma maganar da take k'ok'arin fad'a, seta d'aga kae ta kalli Abban, ga mamakin ta seta gan shi sun shigo tare da Rk, maganar sa da Ayrah ta jiyo ne ya sanya ta shirin mik'ewa a