Sashe 28
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
zuciyar ta a cunkushe da hukuncin da mahaefin ta ya yankewa rayuwar su, seya mik'e zaune yana mantawa da rayuwar wata Muneerah dan kuwa yasan abu ne me matuk'ar wuya auren su ya yiwu dan baya tunanin ko da bashi da wadda yake so ze iya auran Muneerah duk da kasancewar ta er uwar sa ballantana kuma yana da ita. Wayar sa ya d'auka ya sake kiran number Ayrah se dae kamar d'azun yanzun ma abinda take fad'a masa shine wayar a kashe take, jefar da wayar yayi yana runtse idanun sa lokaci guda kuma yana sanya hannayen sa duka biyu ya cusa su cikin sumar kan sa, meya kamata ya aekata yanzun? Tabbas ba dan dare yayi sosae ba babu abinda ze hana shi tashi ya tafi gidan su Ayrahn dan yasan tabbas Abban ta ne ya k'wace mata wayar dan kada tayi magana dashi, gaba d'aya zuciyar sa ta kasa sukuni ta kasa hutawa ko dae_dae da second d'aya ne a cikin daren nan, bacci kuwa beyi ko da gangancin d'aukar sa ba balle kuma ya d'auke san. ... Tun d'azu yake sintiri cikin d'akin ya kasa zama, ran sa a matuk'ar 6ace yake so yake kawae ya tuna mafita akan wannan al'amari, be ta6a tunanin yarinyar nan da yake so er gidan Ibraheem bace, Muttala dake gefen sa shi kan sa ya kasa cewa komae, kawae yayi shiru ne yana kallan Alhaji Mato, ya kae wajen minti 5 a haka sannan ya d'aga kae yana kallan Muttala fuskar sa d'auke da wani shu'umin murmushi yace "Muttala!" "Na'am yalla6ae" Muttala ya fad'a yana d'aga kae ya kalle shi, Alhaji Mato ya nemi waje ya zauna kan kujera sannan ya fara magana "Ayi yadda za'ayi a d'akko min yarinyar nan daga daren yau zuwa safiyar gobe bana son 6ata lokaci.." kallan sa Muttala yayi sannan yace "Ranka ya dad'e satowa kuma?" shima kallan sa Alhaji Maton yayi kana yace "K'warae kuwa, zan tafi da ita wani k'auye dana ta6a zuwa aeki, acan zan samu wanda ze d'aura mana aure" jinjina kae Muttala yayi kana yace "An gama ranka ya dad'e, In Sha Allah zaka ji ni daga yau d'in zuwa gobe" jinjina kae Alhaji Mato yayi yana murmushi a ran sa yana ayyana yadda Ayrahn zata zama mallakin sa. ... Washe gari da safe wajen k'arfe 7 yana sanye cikin k'ananan kaya da suka matuk'ar amshe shi, se dae fuskar sa a cunkushe take kamar wanda akama mutuwa, haka zalika idan ka lura ma da kyau zaka ga har wani 6urmawa idanun sa suka yi, se dae da yake shi d'in na musamman ne hakan ma k'ara masa kyau yayi, wayar sa ya sake d'auka ya sake danna kiran ta a karo na barkatae, daga wannan kiran baya tunanin ze sake kira se dae kawae a tsince shi a k'ofar gidan nasu, cikin sa'a se yaji wayar na ringing, babu shiri ya mik'e tsaye zuciyar sa na cigaba da bugawa tare da sautin yadda ringing d'in ke fita. A 6angaren ta kuwa ita kan ta bata samu ta rintsa ba tun jiyan, data gama kukan ta kawae seta kwanta tayi shiru abin ta tana tunanin halin d'an adam, koda Asuba ma kafin kowa ya fito ita ta riga kowa fitowa tayi alwala tayi Sallah ta koma ta kwanta har lokacin idanun ta suna nan a yadda suke sun yi jawur haka zalika sun kumbura. Tana nan zaunen ta janyo wayar ta ta kunna ta sannan ta shiga contact a hankali ta lalubo number sa zuciyar ta na cigaba da harbawa da k'arfin gaske, tana so tayi fatali da duk wani abu daya ke so ya kawo mata cikas dan haka ta d'an runtse idanun ta sannan ta bud'e ta sake d'ora idanun ta kan jerarriyar special number sa, tana shirin yin blocking number tasa sega kiran sa ya shigo, seta tsaya tana sake k'arewa number kallo kamar me son karanto wani abun, tabbas ya kamata ta isar da abinda ke ran ta, ta fad'a masa babu ita babu shi koda hakan zesa ya rabu da ita kada ya sake gigin koda kiran ta ne, dab da zata tsinke ta d'aga wayar, daga 6angaren sa ya sauke wata 6oyayyiyar ajiyar zuciya sannan yace a hankali kuma a tausashe yana son kawar da duk wani 6acin ran dake d'awaeniya dashi "Ayrah!" da sauri ta runtse idanun ta tana jin yadda zuciyar ta ke bugawa ta kae wajen second 30 a haka sannan ta bud'e, dan shi har ya fara tunanin ko Abban ne ya d'aga da kan sa seya ji ta tana fad'in "Kada ka sake kira na, ka manta ka ta6a sanin wata me suna na ko me kama ta ballantana ni, kayi k'ok'ari ka goge duk wani lokaci da muka ta6a kasancewa tare, ka manta da babin rayuwa ta, kada ka sake kira na a waya dan kuwa har abada bazan ta6a auran mutum irin ka ba" daga haka ta katse wayar bata jira yace komae ba ta jefar da wayar a gefen ta tana fashewa da kuka lokaci guda kuma tana tuna yadda ta kawowa Abba Rk a farko amma daga k'arshe su suka koma cikin arzik'in yayin da suka tura su su kuma suka koma cikin k'uncin rayuwa. Tsayawa yayi kamar wani sak'ago, ya sauke wayar daga kunnen sa yana sake k'arewa wayar kallo, anya kuwa ita d'in ce? Anya kuwa Ayrahn sa ce? Menene haka ya faru wanda ya chanja mata ra'ayi haka daga daren jiya zuwa yau d'in? Me akace mata yayi da zata jefe shi da wad'annan kalmomin? Tabbas da tasan yadda kalmomin nata suka jefa shi cikin wani irin yanayi da bata fad'a masa ba, meya same ta haka? Shin ba shine ya kamata ya fad'i hakan ba tunda iyayen tane suka yiwa nasa iyayen laefi ba? Amma beyi hakan ba se ita? Kodae dama bata son sa ne tuntuni? Ko kuwa dae akwae wani 6oyayyen al'amari wanda dukan su basu sani ba? Lallae ya zama dole yasan gaskiyar al'amarin nan, yasan dalilin Ayrahn na jifan sa da wad'annan muggan kalaman, zuciyar sa dake masa wani irin zafi tana kuma harbawa da k'arfi ya danne da hannayen sa yana runtse idanun sa, ya kae wajen minti d'aya a hakan sannan ya bud'e idanun sa yana fesar da iska me zafi daga cikin bakin sa sannan kae tsaye ya fice daga d'akin bayan ya d'auki mukullin motar sa. Da sassarfa ya k'arasa inda motar tasa take ya shiga ya tashe ta da sauri duk da shi d'in ba ma'abocin gudu bane, Abbu da fitowar sa kenan daga parlourn sa yaga tashin motar Rk d'in, mamaki ne ya kama shi sosae dan shi kam yayi tunanin tun yau Rk d'in ze koma asibiti bakin aeki, dan shi indae ta 6angaren sa ne babu lokacin 6atawa, kowanne lokaci baya barin sa ya tafi a banza seya nemo abinda zeyi a cikin lokacin wanda ze saka ya samu kud'i, shiyasa ko lokacin da Rk d'in yaje Zaria yaga baze iya barin sa haka nan babu wani abun daze samu kud'i ba, dan haka shi in dae ta shine tunda jiya ya dawo toh yau ma ya d'ora kan aekin babu wani 6ata lokaci "Toh ina ze je haka?" Abbu ya tambayi kan sa, ganin dae babu wanda ze amsa masa tambayar ne ya sanya shi cigaba da tafiya a ran sa yana cigaba da tunanin inda Rk d'in zeje. ... Driving yake yi amma har lokacin tunani yak'i barin ruhi da k'wak'walwar sa, shi likita ne yasan illar da tunani kan iya haefarwa dan ya kan sha bawa mutane shawara akan hakan, amma a wannan karon shi kan sa ya kasa hana kan sa, se yanzu ya fahimci ashe idan k'wak'walwa na son yin tunani ba mutum ke tsarawa kan sa yin tunanin ba ita da kan ta take yin tunanin kuma babu yadda ka isa kayi da ita. A haka dae har ya k'arasa unguwar ta su yana tuna kwatancen data masa, a d'an nesa kad'an ya tsaya da gidan yana kallan cikin layin da babu kowa kasancewar safiya ce dan kuwa har lokacin ko 8 ba tayi ba, seya d'aga lumsassun idanun sa dake d'auke da bacci ya dubi gidan a ran sa yana sak'a tabbas nan d'in ne in dae yabi kwatancen data masa dae_dae, wayar sa ya janyo da take ajje kan kujerar kusa dashi ya danno number ta cike da fatan ta d'aga wayar, se dae addu'ar sa bata kar6u ba dan kuwa har ta gama ringing d'in bata d'auka ba tana kuma jin wayar na ringing ta san me kiran shiyasa tak'i kula wayar, wani kiran ne ya sake shigowa seta mik'e daga kwanciyar da take tana ganin blocking d'in da tayi niyyar yi tun d'azun shine kawae mafitar da tasan idan tayi ze dena kiran ta, kafin takae ga aekata abinda tayi niyya Umma ta d'aga labulen d'akin ta lek'o "Ayrah ki fito ki samu wani abun ki ci" se ta d'aga kae da sauri sannan ta furta "Toh.." kawae, itama Umman bata takura ba dan tana so ne ta bari ta gama kukan ta sannan ta rarrashe ta, idan ba haka ba tasan yanzu tunzura ta kawae zata yi, Umman na fita Ayrah ta maeda kallan ta kan wayar dae_dae lokacin da wani sak'o ya shigo cikin wayar, seta dakata ta shiga cikin sak'on, gajeren sak'o ne daga number Rk a hankali ta shiga karantawa "Don Allah ki fito ina k'ofar gidan ku, inaso naji tabbacin maganar dake fitowa daga cikin bakin ki, ina so na tabbatar da abinda kunnuwa na suke ji" fuskar ta a matuk'ar tamke haka zalika ran ta ya sake 6aci, tana ga lokaci yayi da zata kira shi da sunan dake ta yawo a cikin k'wak'walwar ta koda hakan zesa ya fahimci ta gane wanene shi da mahaefin sa, ko kuwa ya d'auka saboda son da take masa zata iya fatali da umarnin iyayen ta? Ko kuwa me yake nufi da ita? "Butulu" shine sunan dake ta yawo a k'wak'walwar ta, wayar ta ta ta d'auka ta danna number sa a blocking sannan ta jefar da ita gefe ta mik'e tana sanye cikin doguwar rigar atamfa ta zari hijab ta saka sannan ta lek'o