← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 90

Sashe 60

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya kamata nayi ba bayan na tabbatar da Raj ya kamawa wata matar gida tana zaune a ciki gefe guda kuma suna rayuwa kamar mata da miji bayan yana da wata matar da aka aura masa.." Ummee ta k'arasa maganar cike da dakiya dan har yanzun zuciyar ta a karye take, d'aga idanun sa Abbu yayi da sauri yana jin yadda maganar ta tsorata shi cikin lokaci k'ank'ani, ya kalli inda Rk yake a zaune ya kasa kallan kowa, se kuma ya maeda kan Ummeen yace "Kin san me kike fad'a kuwa?" jinjina kae Ummee tayi kana tace "Na san abinda na fad'a ae gashi nan ka tambaye shi, ga kuma yarinyar da suke zaune tare" Ummee ta k'arasa maganar tana nuna Ayrah da izuwa lokacin hawayen da take ta rik'ewa sun k'i ruk'uwa sun zubo dan kan su, ta gaji da jin wad'annan kalaman, sun ginshe ta, se dae kuma bata ga alamar zasu dena fad'a ba har se lokacin da Rk ya tsaya ya musu bayani. Kallan Ayrah Abbu yayi na tsawon sakanni kafin ya d'auke idanun nasa ya maeda kan Rk "Suraj!!" Abbu ya fad'i cikakken sunan sa wanda ba kasafae ya fiya fad'a ba musamman daya kasance a ko'ina da Raj d'in yake amfani, se a lokacin ya d'aga idanun sa ya kalli Abbun, haka kawae ya ji wata kunyar Abbun yake ji musamman idan ya tuna abinda ze fad'a musu yanzun na cewar yayi aure ba tare da sanin su ba, se da Abbun ya dakata sannan ya d'ora da "Me mahaefiyar ka ke fad'a?" "Abbu.." ya fad'a bayan ya d'an lumshe idanun sa da suka d'an risina, d'aga masa hannu Abbu yayi cike da fatan ba hakan bane "Hakane ko ba haka bane?" ya tambaya cikin tsare gida "Abbu haka ne abinda Ummee ke zargi kenan amma ba shine aenahin maganar ba Abbu akwae abinda na 6oye muku baku sani ba.." "Inna lillahi wa inna ilaehi rajiun, Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" shine abinda Abbu ya dinga maemaetawa a fili ko ze samu rangwamin yadda zuciyar sa tayi wani irin nauyi, abinda ya dakatar da Rk kenan daga maganar da yake yi, Abbu ya kae wajen minti 1 a hakan kafin ya d'aga kae ya kalli Rk "Meyasa zaka mana haka Suraj? Meyasa? Yanzu kana da wata matar a gida shine zaka je kana bin wata a waje? Idan son ta kake yi meyasa baka fad'a min na aura maka ita ba da dae ka jawo mana abin kunya a idon duniya? Yanzu me kenan ka jawowa kan ka, da kuma ni da mahaefiyar ka har ma da matar ka?" ya k'are maganar yana nuna Muneerah da har lokacin ta kasa furta ko uffan, yanzu kam shirun da Abbu yayi ne ya bashi damar soma magana a nutse "Abbu har abada bazan ta6a ja muku abun kunya ba In Sha Allah, wannan d'in mata ta ce ta Sunnah wadda aka aura min ita ba tare da sanin ku ba, kayi hak'uri Abbu, Ummee kiyi hak'uri" yayi maganar kan sa a k'asa jikin sa kuma gaba d'aya a matuk'ar sanyaye. Abbu, Ummee, Muneerah gaba d'aya tsayawa suka yi suna kallan Rk dake magana, maganar da tayi kama da ta zararru, ko kuma wad'anda ke ba'a cikin hayyacin su ba, ita dae Muneerah har wani abu ta ga ya gifta mata ta gefen idanun ta da yayi silar rufe abinda take gani wanda hakan ya tilasta mata runtse idanun ta dan tabbatarwa da kan ta ba makancewa tayi ba, ta kae wajen minti 1 idanun na ta a rufe sannan ta bud'e cikin sa'a kuma se taga tana gani amma ba kamar yadda take gani ada normal ba, cike da k'arfin hali Ummee tace "Ae gaba d'aya bamu wani fahimci wannan kwana kwanar da kake yi ba" ta fad'a tana kafe shi da idanun ta yayin da shi kuma har lokacin yak'i bari su had'a ido "Ummee kuyi hak'uri na aure ta ne ba tare da sanin ku ba, ba dan na bijirewa umarnin ku ba ko wani abun makamancin wannan ba, a'ah Ummee akwae manyan dalilan da yasa na aure ta.." Ihu Muneerah ta saki tana kurma ihu hannun ta d'ore a kan ta ta zube a wajen kamar mahaukaciya sabon kamu "Wallahi baze yiwu ba, wallahi baka isa ba, bazan ta6a zama da kishiya ba kome za'a yi kuwa, ba zan ta6a ba, ni kad'ae ce taka har abada, wata tsinanniya bata isa ta shiga tsakani na da kae ba, kae d'in nawa ne ni kad'ae, dan ni kad'ae aka halicce ka" Muneerahn ta fad'a cikin ficewar hayyaci, Ummee da Abbu da suka tafi hutun rabin lokaci duk seda k'arar da ta saki ta shiga cikin kunnuwan su, se dae yadda suka shiga rud'ani da maganar ya saka babu wanda ya tashi ko dan isa inda take. K'arasawa inda Ayrah take tayi a durk'ushe saboda yanda ta kasa mik'ewa akan k'afafun ta, tana shirin kae hannun ta wuyan Ayrahn da kan ta ke duk'e Rk yayi maza ya rik'o hannun Muneerah sannan ya watsa mata idanun sa, fizge hannun ta tayi da k'arfin gaske tana kallan sa itama da na ta jajayen idanun, tuna a gaban wa suke ya sanya shi sakar mata hannun, kamar bata dama yayi se kuwa ta fashe da wani sabon kukan wanda ya dawo da Ummee hayyacin ta, ta d'aga kae ta kalle ta sanda ta soma fad'in "Ka sanar da ni wasa kake yi ba matar ka bace, ka sanar da ni wannan d'in karuwar ce ba matar ka ba, dan in dae matar ka ce zan iya mutuwa wlh" daga irin maganganun da ke fitowa daga bakin ta kad'ae ya nunawa Ummeen ba'a cikin hayyacin ta take ba, hakan ne ya sanya ta mik'ewa itama cike da k'arfin halin dae ta k'arasa inda Muneerahn take ta rik'o ta sannan ta d'aga ta, cigaba da kukan ta Muneerah tayi a ran ta tana ji kamar ta bud'e idanun ta ta ga mafarki take yi ba gaskiya ba, idan kuma gaskiya ne to a bar ta kawae ta kashe Ayrahn ta huta ko taji sanyi. Ummee ba tabi takan kowa ba ta fice da Muneerah dake cigaba da kuka kamar wadda akace uwa da uban ta sun mutu, har d'akin ta Ummee ta kae ta ta k'arasa da ita cikin spare bedroom na cikin parlourn ta sannan tace a hankali kuma cikin k'arfin hali dan kada ta sake karya zuciyar Muneerahn "Kiyi shiru ki kwanta ki samu kiyi bacci, zan je na dawo" ta fad'a tana shirin ficewa daga d'akin, rik'o hannun ta Muneerah tayi da sauri tana girgiza kae hawaye na cigaba da sauka akan fuskar ta tace "Ummee ni babu abinda nake so illa yace min wasa yake min, ba matar sa bace Ummee, Ummee yace min ba matar sa bace idan ba haka ba zan kashe kae na" kallan ta Ummee ta cigaba da yi cikin rashin sanin abin yi, dan kuwa zuwa lokacin ko tace zata tsaya ta bata baki tayi k'arya, ita kan ta bata da wannan k'warin gwuiwar, hakan ne ya sanya ta fad'in "Ke dae ki kwanta nace koh?" ta fad'a cikin rarrashi kuma tana kallan Muneerahn, ba dan ta amince ba kawae ta koma ja6ar ta kwanta kan gadon ba tare da tace komae ba. Ajiyar zuciya Ummee ta sauke sannan ta fito daga cikin d'akin kae tsaye ta koma parlourn Abbu, har lokacin kowa na zaune inda ta barshi, babu alamar wani ya motsa ko kuma wani yayi magana da wani, hakan ne ya sanya ta k'arasawa ta zauna tana kallan Abbu dake kallan Rk kamar me son gano wani abun, kamar wanda shigowar Ummeen ya sakawa k'arfin gwuiwa se cewa yayi "Aure kayi Raj ba tare da izinin mu ba? Wacece wannan d'in? Meyasa ka aekata hakan? Bata da iyaye ne ko kuwa menene?" Abbu yayi tambayar duka a lokaci guda. I zuwa lokacin Ayrah gaba d'aya kukan na ta ya tsaya cakk, ta rasa meke mata dad'i, ta rasa abinda ya kamata tayi, hakan ne ya sanya ta yin shiru d'in kawae tana saurarar abinda ke wakana cikin d'akin. Nannauyar ajiyar zuciya Rk ya saki kana a hankali ya d'aga kae ya kalli Ummee da Abbu sannan ya mayar k'asa ya soma bada labari tiryan_tiryan tun daga lokacin da Abbun yace masa baze auri Ayrah ba, har zuwa inda ya kamata su Abbun su sani, shiru ne ya ratsa kafatanin d'akin, kowa da abinda ke sak'awa, ta 6angaren Ummee sosae take kallan Rk d'in tana jira ya k'aryata abinda kunnuwan ta ke ji, "aure yayi? Auren ma da wadda Abbun na sa ya hana shi? Er gidan Alhaji Khaleel Abban Sadeeq?" ire_iren tambayoyin da suke ta lugude kenan a cikin kwanyar Ummee se dae ta kasa bud'e baki ballantana ta fad'a. Abbu kuwa wani zazzafan gumi ne ya shiga tsatstsafo masa wanda yak'i tsayawa, duk da sanyin A.C da kuma fankar dake kunne cikin d'akin hakan be hana shi fidda hular sa daga kan sa ba ya soma fifita saboda wani zafi da ya rufe shi, shi yama kasa tunanin komae, ya kuma rasa abinda zece, se kuma can ya bud'e bakin sa da k'yar ya furta "Ku je d'akin Ummee ku jira mu.." shine abinda Abbun ya fad'a har lokacin be kalli Ayrah ba, mik'ewa Rk yayi cikin mutuwar jiki duk da yanda yaji dad'i, ko ba komae yau d'in ya sauke wani nauyi ne da ya kamata ace ya dad'e da saukewa, se dae kuma hukuncin daze biyo baya shine be sani ba. Ganin da tayi ya mik'e ne ya sanya ta itama mik'ewar sannan suka soma takawa "Kada ta fita daga cikin d'akin nan ba tare da ka sake ta ba" Ummee ta fad'a ran ta a matuk'ar 6ace musamman da taji kalaman Abbu, cakk dukkan su suka dakata kuma kusan lokaci d'aya k'irjin kowannen su ya buga, ganin da Ummee tayi har wajen rabin second ya shud'e Rk be juyo ba kuma bece komae ba ya sanya ta sake fad'in "Ba zaka sake ta bane se na...." d'aga mata hannu da Abbu yayi shine ya dakatar da ita daga fad'in abinda tayi niyyar fad'a, be jira ta sake cewa komae ba yace "Ku je.." suma
Chapter 60 · 0% Book details