← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 90

Sashe 41

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

maganar, a haka har ya k'arasa gida. A compound d'in gidan yayi parking motar ta sa, ya sauka ya soma takawa zuwa part d'in sa, dae_dae lokacin da yake k'ok'arin sanya mukulli dan bud'ewa ya jiyo muryar Ummee na fad'in "Yanzu kake dawowa ne?" seya d'an dakata kad'an sannan ya d'aga idanun sa ya kalli Ummeen kana yace "Ehh.." kawae dan a yadda yake jin sa baya jin ze iya doguwar magana haka nan, kallan sa Ummee ta cigaba da yi tana nazarin yanayin sa "Kana lafiya kuwa?" Ummeen ta tambaya, nan ma da "Ehh" kawae ya amsa yana k'arasa saka key d'in ya bud'e ya tura kan sa cikin d'akin, bin sa da kallo Ummee tayi, se kuma ta juya itama da nufin shiga cikin d'akin nasa se kuma ta dakata ta girgiza kae kamin ta wuce part d'in ta. .. A hankali ya kwanta kan kujerar d'akin, sannan ya d'auki hannun sa d'aya ya d'ora a kan sa dake cigaba da masa ciwo, idanun sa a lumshe suke yana sake tuna maganganun Yah Sadeeq, be san dalilin da yasa ya kasa k'arya ta Yah Sadeeq d'in ba a lokacin da yake fad'a masa ga abinda mahaefin sa yayi, ya rasa dalilin hakan, haka kawae yake ganin babu abinda ze sa Yah Sadeeq d'in ya zauna ya d'irka k'arya akan mahaefin sa kuma yazo yana fad'a masa, abu ne me kamar wuya hakan ya faru, amma kuma ta yaya zeyi gaggawar amincewa ba tare da wata hujja ba? Duk da yana buk'atar bincike ko da akan takaddun Abba ne da Yah Sadeeq d'in yace Abbu ya tafi har dasu, amma kuma akwae abubuwa da dama da ke ta masa dirar mikiya cikin k'wak'walwar sa, tunda Abbu ya fita da niyyar raka Abba Kano, dawowar sa gida cikin gaggawa suka bar garin, tun daga lokacin be sake ganin Ayrah ko wani daga cikin dangin su ba, ko kuma wani abu daya shafe su ba, kenan me hakan ke nufi? Lokaci guda bugun numfashin sa ya k'aru, baya fatan ace haka d'in ne dan idan hakan ya tabbata gaskiya ne be san da wane ido ze kalli Ayrah da shi kan sa Abba ba, mutum me hallaci a gare shi, mutum me kirki da dattako, wanda tun a lokacin ba wani k'arfi gare shi ba amma saboda wadatar zuci da kuma tausayi irin na sa ya taemaka masa, be tsaya iya nan ba ya taemakawa Abbun sa amma ace abinda Abbun sa yayi kenan? Ya zama dole ya bincika. .. Babu wanda yace uffan a cikin su sanda Yah Sadeeq d'in ya gama bada labarin, Ayrah na taya shi har lokacin tana share k'walla a idanun ta, Abba gaba d'aya bashi da abin cewa shiyasa ma yayi shiru yayin da Umma kuma mamaki gami da takaeci sune suka taru suka mata yawa yasa ta kasa cewa komae, a hankali ta shiga goge hawayen dake ta saukowa daga kan fuskar ta tana girgiza kae, se yanzu ta sake gane kuskuren da suka aekata na yankewa Ayrahn hukunci ba tare da sun yi bincike ba, hannu Umma ta mik'awa Ayrah bayan ta d'aga fuskar ta ta kalle ta, sannan ta mata alama da ta taho da kan ta, babu 6ata lokaci Ayrah ta k'arasa da sauri ta fad'a jikin Umman tana sakin wani irin kuka, itama Umma bata hana kan ta kukan ba ta rungume d'iyar ta ta sosae tana jin yadda ilahirin jikin Ayrahn ke rawa "Kiyi hak'uri Ayrah, don Allah ki yafe min, nice na fara d'arsawa Abban ku zargin guduwa kikayi daga gidan nan bayan tabbatar da ba zamu aura miki Raj ba, kiyi min afuwa Ayrah!" ta k'arasa fad'a tana sake jin wani irin takaeci, se da Ayrah ta sauke sheshshek'a sannan tace "Umma ni ba abinda kuka min, wannan dalilin ne ma yasa nake ta sauri in dawo gida dan nasan za'a iya tunanin hakan, Umma ba kuyi laefi ba dan kun yi tunanin hakan musamman daya kasance a washe garin ranar da kuka hanani auren sa ne kuka neme ni kuka rasa.. Umma ni baku min komae ba, nice ma zan baku hak'uri.." "Kuull..ki bar fad'in mu miki hak'uri Auta, babu abinda kika mana mu ma" Umma ta fad'a tana sakin Ayrahn, bata sake cewa komae ba se k'arasawa da tayi inda Abba ke zaune har lokacin, tsugunawa tayi tana kallan sa, dae_dae lokacin daya d'auke kae yana jin zuciyar sa na karyewa "Abba..!" ta fad'a har lokacin tana kallan sa "Ayrah je ki huta bazan iya cewa komae ba, kiyi hak'uri kawae.." Abban ya fad'a, wani irin sanyi taji yana ratsa kafatanin jikin ta, ko ba komae yau d'in gata ga iyayen ta kuma da alama sun yafe mata, gashi ma har neman yafiyar ta suke yi "Abba ni zan nemi yafiyar ku don Allah.." Abba be iya cewa komae ba se girgiza kae kawae da yake yana ajje numfashi a hankali, Yah Sadeeq kuwa da yake gefe murmushi ne kawae ke fita daga kan fuskar sa, tana shirin mik'ewa dan komawa d'aki Abba ya juyo kamar wanda ya tuna wani abu "Ayrah!" seta juyo a hankali tace "Na'am Abba.." "Kin san mutumin daya saka aka d'auke ki?" tsayawa tayi tayi shiru tana hasaso fuskar Alhaji Mato, kwata kwata ba zata iya cewa ga fuskar sa ba dan haka ta girgiza kae kamin tace "A'ah Abba bansan shi ba.." "Idan kika gan shi zaki gane shi?" shiru tayi tana nazari, ko da ta san shi ma bata tunanin zata iya gane shi ballantana bata san shi ba dan haka a nutse ta furta "A'ah Abba.." "Tashi kije Allah yayi miki albarka" lumshe idanu tayi kamin ta mik'e tare suka wuce cikin d'akin ta ita da Umma, shiru Abba yayi bayan barin su wajen yana nazari, ya zama dole ya gano mutumin daya d'auke masa yarinya ya kae ta wani waje dan a d'aura musu aure, idan kuma ya tuna da maganar auren Raj dake kan er tasa se ya sake jin jikin sa yayi sanyi, a yanzu be san wanene Raj d'in ba be san ko halin su d'aya da mahaefin sa ba, be san yadda za'ayi su kasance sirikae tsakanin sa da Kabeeru ba, abinda be ta6a tunanin ze kasance a rayuwar su ba, abinda ya guda tun farko, se dae gashi Allah yayi ikon sa akan su ta hanyar da basu ta6a zata ba, seya koma ya jingina bayan sa da jikin bango yana cigaba da sak'a da warwara. ... Da sallama ya shigo cikin d'akin hannun sa d'auke da envelope, Mummy dake zaune kan kujera ta mik'e tana fad'in "Alhaji sannu da zuwa" "Yawwah sannu kadae, ina Muneerahn? Na gan ki ke d'aya?" murmushi Umma tayi sannan tace "Toh Alhaji ae dole ka ganni ni d'aya a kwanakin nan, kasan sha'anin amarya fa yanzu haka tana wajen gyaran jiki" "Toh madallah, ga kati dae ya iso" ya fad'a yana mik'a mata envelope d'in hannun sa, da sauri ta sanya hannu ta kar6a da murmushi kan fuskar ta take fad'in "Kae toh Masha Allah.." ta fad'a tana k'arasawa ta zauna kan kujera ta fara fito da katinan masu kyau da k'ayatarwa, girgiza kae Daddy yayi yana murmushi ganin yadda Mummyn ta shagala da kallan kati, ko bi ta kansa ba tayi ba hakan ne ya sanya shi jan k'afafun sa ya bar d'akin. Be dad'e da fita ba Muneerah ta shigo cikin d'akin cikin hijab har k'asa hannun ta d'auke da jaka da had'ad'd'iyar wayar ta, k'arasawa tayi da sauri kan kujerar tana kallan Mummy kamin ta saka hannu ta tu6e hijab d'in jikin ta, nan take shigar dake jikin ta ta bayyana, gajeran wando tiet ne a jikin ta da vest irin me bin jikin nan hakan ne ya bayyana yanda ta cika daga sama ba kamar da ba wanda ke nuni da siyo shi ba natural bane, haka zalika hips d'in ta ma sun k'aru ba kamar da ba dake kamar 1, kan ta babu d'an kwali se dae kamar ko yaushe a kitse yake da kitson attachment daya zuba a gadon bayan ta, ta k'ara wani irin mahaukacin fari bauu, fatar nan ta sake d'ashewa, da alama ba mae ta shafa ba se dae ko k'waya ko kuma allura "Kin dawo?" "Ehh Mummy, na gaji wallahi" "Toh sannun ki, gashi nan kati ya iso" farr tayi da idanun ta kafin ta kalli katinan, seta saka hannu ta d'auki guda d'aya ta kalla ta shiga karantawa, sunan ta ne gashi nan ya fito 6aro 6aro dana Rk, wani murmushi ya k'wace mata tana jin ita kam burin ta ya gama cika daga lokacin data auri Rk d'in, ajiye katin tayi seta d'auki wayar data ajje a gefen ta kamar koda yaushe ta danno number sa, amsar d'aya ce dae kamar kullum baya kusa, bata gaji ba ta sake kira amma har ta katse be d'aga ba, a karo na 3 ta sake gwada kiran na sa cikin sa'a kuwa ya d'aga wayar se dae bece komae ba, daga inda take ta maraeraece fuska kamar za tayi kuka "Haba Baby, ina ta kiran ka amma kak'i d'agawa, na maka magana ta whatsApp kak'i kula ni, ya kake so nayi? Auren mu saura kwanaki amma kak'i tsayawa muyi magana ko da akan shirye_shiryen bikin ne" tsaki ya saki akan la66an sa, ya kasa gane wannan dalilin na had'a auren sa da Muneerah, idan so suke zumuncin su ya d'ore ae ba dole seta hakan zasu biyo ba, shi abinda ma yake tsoro kada ace zumuncin su ya rabu saboda auren nan, dan a yadda yake ji har abada baze iya zama da wata a matsayin matar sa ba in dae ba Ayrah ba, toh ina ze kae ta? "Yaya na!" ta katse masa tunani da fad'in hakan "Wannan ne dama dalilin kiran?" ba tare data kawo komae ba tace tana murmushi "Ehh shine kawae.." "Ohk" ya fad'a yana katse wayar sannan ya jefar da ita gefe "Hello" ta furta bayan jin kamar kiran ya katse, seta sauke wayar daga kunnen ta tana kalla cike da takaecin katse wayar ba tare da sun k'are maganar ba, seta cigaba da kallan wayar kamar me nazari ko kuma me kallan wani abun a cikin wayar "Ke lafiya?"
Chapter 41 · 0% Book details