← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 90

Sashe 32

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

be hana shi sake kicin kicin da fuskar sa ba, ba zaka ta6a gane menene a cikin zuciyar sa ba yadda kyakykyawar fuskar sa take babu annuri se ka d'auka haka ne a cikin ran sa ma, hannayen sa ya d'auka duka ya sak'ale su a k'irjin sa kafin ya d'an lumshe idanun sa kana ya bud'e su yace a hankali "Kuka bashi da amfani, ina ga gwara ki mik'e mu ida wannan aekin" ya d'an yi shiru bayan ya sauke ajiyar zuciya ya cigaba da fad'in "Wannan mutumin ya d'auko ki ne dan a d'aura muku aure dashi na dindindin, shiyasa ni kuma zan k'wace ki daga tarkon sa da kike k'ok'arin fad'awa..." da ya kae k'arshen maganar seya sake dakatawa yana cigaba da nazarin ta, sanda ta dena kukan se sheshshek'a da take yi kan ta har lokacin na kan gwuiwar ta, se a lokacin ta saka hannun ta ta share hawayen da suka k'i tsayawa da zuba a fuskar ta tace cikin raunanniyar murya "Idan da gaske taemako na zaka yi toh ka kira min Abba na, ko kuma ka maeda ni gidan mu saboda bana son ganin ka" tsayawa yayi ya cigaba da kallan ta yanda take maganar bilhak'k'i da gaskiyar ta, shi har yanzu idan tana wani abun mamaki take bashi, meyasa ta fishi d'aukar zafi haka? Meyasa duk da abinda Abban ta yayi wa Abbun sa besa ya guje ta ba se ita? Meyasa take abu kamar da mak'iyin ta take tare? Meyasa ta chanja lokaci d'aya? Lumshe idanun sa yayi yana hana yanda ran sa ke neman 6aci tasiri, sosae zuciyar sa ke masa zafi na maganganun ta amma ya daure ya sake runtse idanun sa na tsawon sakanni sannan ya bud'e su a kan ta sanda suka yi wani ja kamar wanda abu ya zubar wa cikin ido, seya maeda kallan sa kan ta sannan yace sanda bugun zuciyar sa ke cigaba da k'aruwa "Wannan shine abinda kike so na miki? Ki sani ba zaki ta6a barin garin nan babu aure akan ki ba, ko dae ki bari ki auri wancan mutumin ko kuma ki amince da aure na na Contract, The choice is yours.." yayi maganar yana lumshe idanun sa kafin ya d'ora da fad'in "Idan kuma kina tunanin abinda kike tunani shine mafita.. well.. se kije ki samu wad'anda suka sato ki dan a d'aura miki aure da d'aya daga cikin su kice su baki waya ki kira Abban ki..." ya k'are maganar da wani irin murmushin takaeci daya fice daga gefen bakin sa, daga haka ya juya yana shirin ficewa daga soron, bata san sanda ta mik'e da wani irin sauri ba se kawae tsintar hannun sa yayi cikin nata, ya dakata lokaci d'aya yana lumshe idanun sa lokaci d'aya kuma yana jin yanda jikin sa ya amsa, se kuma ta sake shi kafin kamar zata fashe da kuka ta furta "Na amince!!" ta fad'a dae_dae lokacin da wani kuka me sauti ya k'wace mata, seda ya sake runtse idanun sa kafin ya juyo inda take, ya sanya hannun sa cikin aljihu ya fiddo da wata takadda da biro sannan ya mik'a mata ba tare daya dubi kukan da take yi kamar ran ta ze fita ba "Ki saka hannu!" ya fad'a yana mik'a mata, kamar ba zata d'ago ba se kuma a hankali ta fara rage sautin kukan nata sannan ta sanya hannu ta kar6a, sosae bugun zuciyar ta ke k'aruwa ta kar6i takaddar daya mik'a mata, tsayawa tayi kawae tana kallan takaddar kamar me karatu ko me nazarin abinda ke cikin takaddar, hawayen da yak'i tsayawa a idanun ta se sauka yake akan takaddar, wajen minti 1 tayi a hakan da dae ta fahimci bata da wata mafita se kawae ta d'aga biron ta d'ora shi kan takaddar, duk da yadda hannun ta ke rawa hakan be sata dakatawa ba se da tayi signature sannan ta jefar da takaddar daga hannun ta tana runtse idanun ta, bata jira ta sake jin komae daga bakin sa ba ta mik'e ta fara takawa a hankali saboda jirin dake d'ibar ta, hakan ne ya sanya ta yin layi kamar wadda tayi maye, bin bayan ta yayi da kallo sanda ta 6acewa ganin sa daga inda yake yana jiyo sheshshek'ar kukan ta, ya kae minti d'aya a hakan kamar wanda aka sassak'a sannan ya lumshe idanun sa ya saka hannu ya d'auki takaddar kana ya fice daga soron. Kae tsaye cikin motar sa ya koma ya jinginar da kan sa akan kujerar daya kwantar da ita, idanun sa a lumshe zuciyar sa na harbawa da k'arfin gaske, hannun sa dake d'auke da takaddar ya rufe ta a cikin hannun nasa kamar wanda ze yaga takaddar, se kuma ya bud'e hannun yana sauke numfashi a hankali, wayar sa dake ajje kan kujera ce tayi ringing, se a lokacin ya bud'e lumsassun idanun sa ya d'ora akan wayar "Abbu" ya bayyana akan screen d'in, seya maeda idanun sa kawae ya rufe yana cigaba da sauke numfashi akae akae, be d'aga wayar ba har ta gaji dan kan ta ta dena ringing d'in sannan ya janyo ta ya kashe ta gaba d'aya, gaba d'aya zuciyar sa a dame take yanzu haka, ya rasa ma meya kamata yayi, baya tunanin koya d'aga wayar ma ze iya cewa wani abun, dan haka k'in d'agawar kawae shine mafita. ... B'angaren Ayrah kuwa a tsakar d'akin ta zube tana sakin wani gigitaccen kuka me tsuma zuciyar me sauraro, zuciyar ta gaba d'aya a cunkushe take, ta rasa abinda zatayi, ta rasa tunanin daya kamata tayi, abinda ta sani kawae shine yanda zuciyar ta ke bugawa kamar zata faso k'irjin ta ta fito, ta kae fiye da minti 30 tana kukan sannan ta fara sauke ajiyar zuciya lokaci d'aya kuma tana neman kan wani d'an madaedaecin gado dake cikin d'akin ta d'ora kan ta akae cikin rashin sanin abinyi. ... "Yalla6ae kayi hak'uri ka zauna mu samo mafita" Muttala ya fad'a yana kallan Alhaji Mato daya kasa zama, idanun nan nasa sun sake ja kamar garwashi, haka zalika bak'ar fuskar sa ta sake had'ewa cikin rashin walwala "Waye shi? Wanene uban shi? Me yake tak'ama dashi? Ya akayi yasan da plan d'in mu? Ya akayi ya biyo mu cikin garin nan?" shine abinda Alhaji Maton ya fad'a a zafafe "Ka kwantar da hankalin ka Yalla6ae, zuwa gobe zan bincika maka waye shi" wani banzan kallo Alhaji Mato ya watsawa Muttala kafin yace "Muna da wannan lokacin? Tambayar ka nake muna dashi?" ya k'are maganar yana kallan sa, shiru Muttala yayi yana sake tunanin wata mafitar, hakan ya sake bawa Alhaji Mato damar yin shiru shima yana nazarin abinda ya kamata yayi kafin goben "Ya shiga gona ta, bazan k'yale shi ba wallahi, yana so yayi wasa dani, ba zeji da dad'i ba, Muttala asan yadda za'ayi a gama mun dashi kafin goben, shi kad'ae ne matsala ta a yanzun.." Alhaji Mato ya k'are maganar yana kallan Muttala "An gama ranka ya dad'e" .... Washe_gari da safe wajen k'arfe 8 tana zaune kan dadduma kamar maraeniyar data rasa uwa da uba, manyan idanun nan nata sun sake yin zuru zuru, ga yunwar da take ji amma saboda tashin hankalin da take ji ta kasa kae koda ruwa ne cikin bakin ta, haka nan kawae take zaune, ita ba Azumi ba ita ba cin abinci ba, idan ka gan ta seta baka tausayi musamman yadda har lokacin hawaye be bar zuba akan kuncin ta ba duk da yadda ta dena kukan amma hakan be hana hawayen zuba ba, ita kad'ae tasan yadda take ji a cikin zuciya, k'wak'walwa da gangar jikin ta, tana nan zaune gaba d'aya bata a hayyacin ta kamar wadda ta zare, ta tsaya ta k'urawa waje d'aya idanu se kuma hawayen dake sauka akan fuskar ta. Babu dad'ewa aka turo k'ofar d'akin, bata damu dame shigowar ba dan ita wannan sam ba damuwar ta bace, wadda ta shigo ta k'arasa ta ajiye abincin data shigo dashi, duk da ganin abincin data kawo jiya duk suna ajiye bata ce komae ba ta fice daga d'akin tunda dae ta gama aekin ta. .... Wajen k'arfe 1pm aka sake shigowa d'akin, har lokacin dae tana zaune a wajen yanzu kam ko hawayen ma sun gaji da zuba, tayi shiru kawae tana jiran taga yadda Allah zeyi da ita, yanzu wata matar ce ta shigo daban ta kalle ta sannan tace "Baba na kira!" sam bata ji ta ba dan kuwa bata tare da ita, hankalin ta da tunanin ta gaba d'aya suna ta wani wajen ne, ganin da matar tayi kamar bata tare da ita ne ya sanya ta k'arasawa gaban Ayrah ta tsuguna sannan tace "Baba na kiran ki" firgigit ta lumshe idanun ta sannan ta bud'e da sauri lokaci d'aya kuma k'irjin ta na bugawa, seta kalli matar dan har lokacin bata san aenahin abinda ta fad'a d'in ba, seda ta sake maemaetawa sannan kawae ta mik'e tana gyara zaman hijab d'in ta kan doguwar rigar da aka bata ta saka wadda take over size dan kuwa yawo take a cikin ta, lumshe idanun ta tayi bayan ta mik'e d'in sanda taji wani irin jiri na neman kada ta, a hankali ta kama kan ta tana sake rufe idanun ta, a haka dae suka cigaba da tafiya ba dan tana gane inda suke zuwa d'in ba. Cikin wani d'aki me madaedaecin kyau, ehh zamu iya kiran sa madaedaeci musamman idan muka yi duba da gidajen cikin k'auyen, dan kuwa wannan d'in shimfid'e yake da manyan tabarmi masu kyau, da kuma wata k'aramar kujera wadda Me gari ke zaune a kae, sam bata san wad'anda ke cikin d'akin ba dan idanun ta da kan su suke lumshewa ga kan ta daya cigaba da sarawa, Me gari yayi gyaran murya sannan ya fara magana a nutse "Kin yanke hukuncin wanda kika za6a a matsayin mijin ki?" ya jefawa Ayrah tambayar, seda matar nan ta d'an ta6a ta dae_dae lokacin da kan ta ya sake sarawa, a hankali ta sanya k'aramin red lips d'in ta na k'asa cikin bakin ta ta cija tana jin yadda ya bushe musamman saboda ruwan daya dad'e be shiga cikin bakin ba, d'aga ido Alhaji Mato
Chapter 32 · 0% Book details