← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 90

Sashe 77

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nemi taemakon kowa ba shi kad'ae ya soma aekin sa a kan ta cike da k'warewa se dae kuma cike da tsoro. Zuwa lokacin da suka iso asibitin ta dena zubar da jini, amma duk da haka se ya duk'ufa wajen ganin ta farfad'o da kuma musabbabin abin da ya kawo zubar jinin. Ya dad'e akan ta sosae yana k'ok'ari wajen ganin ya shawo kan ta se dae abin yana nema ya gagari kundila, hakan ya sa ya sake mik'ewa tsaye cikin k'warewa ya cigaba da yin aekin sa a matsayin sa na k'wararren likita. Daga k'arshe dae se da ya nemi taemakon wata Doctor sannan suka had'u a kan ta, duk kuma abin da yake yi yana yi yana addu'a cike da fatan samun lafiyar abar k'aunar ta sa. Alhamdulillah, cikin sa'a se ga Ayrah ta soma numfashi amma shi ma da k'yar, hakan ne ya sanya suka yi amfani da oxygen wajen sanya mata shi dan ya taemaka mata. Babban abin da ya bawa Rk mamaki shi ne ganowar da yayi Ayrahn na d'auke da ciki ne, wanda da ta cigaba da bleeding d'in akan iya rasa cikin gaba d'ayan sa, se dae cikin yaddar Allah komae ya zo da sauk'i dan kuwa hatta cikin be fice ba, se dae wahalar da ita Ayrahn ta sha ba zata fad'u ba, dan kuwa ko da kallan yanda take sauke numfashi kayi se ka tausaya mata. Se kuma a lokacin ne ya gane ita zubar da jinin da tayi ba na 6ari ba ne, jinin yazo mata ne kamar yadda yake yiwa wasu masu cikin a watannin su na farko farko. Wata gauruwar ajiyar zuciya Rk ya sauke sanda komae ya kammala yana zaune a gefen ta hannun sa d'aya a cikin nata yana kallan ta cike da tausayawa, soyayya gami matsananciyar k'auna, se dae a yau d'in kaso 80 yafi ta'allak'a ne ga tausayin ta, musamman idan ya tuna wahalar da ta sha koma take kan sha. A hankali ya lumshe idanun sa wani murmushi na su6uce masa tunawa da yayi Ayrahn na d'auke da juna biyu, wannan wane irin abin farin ciki ne? Ya akayi be sani ba se yau d'in? Amma kuma abin da be sani ba ita kan ta me gayya me aekin ta san da zaman sa ko kuwa bata sani ba? A fili ya furta "Alhamdulillahil lazi bi ni'imatihi ta timmus salihat" ya fad'a yana ji kamar ya rungume ta, se dae a yanayin da take ciki ba wannan tafi buk'ata ba addu'a tafi buk'ata, yau d'in rana ce me cike da abubuwa da dama, se dae yanayin da Ayrahn ke ciki ya rage kaso me auki daga cikin farin cikin da ya kamata ya tsinci kan sa a ciki, wato ranar da ya gane Ayrah na d'auke da cikin sa, ya san da hankalin sa a kwance yake farin cikin daze tsinci kan sa a ciki se yafi haka amma duk da haka shi kad'ae ya san wani irin sanyi dake ratsa shi tun daga saman kan sa har k'asan k'afar sa. A hankali ya maeda duban sa kan Ayrah kafin ya mik'e a nutse ya k'arasa dab da ita yana cigaba da kallan ta da idanun sa da suka d'an janye a yau d'in, har yanzu dae numfashin take saukewa a hankali, idan ba dan Oxygen d'in dake hancin ta ba se ka d'auka tana bacci ne cikin kwanciyar hankali. A nutse ya kae hannun sa kan marar ta ya d'an shafa cike da tausayin ta da abin da ke cikin ta na wahalar da suka sha yau d'in, dan kuwa bama ita kad'ae da ke duniya ba hatta abin da ke cikin ta wanda ko halittar sa ba'a dad'e da farawa ba ya sha wahala. yace a hankali, "Sorry my luvs, Allah ya qara muku lafiya.." yayi maganar idanun sa akan Ayrah. .. Cikin tashin hankali Umma ta fito daga d'akin ta, Abba da Yah Sadeeq suka kalle ta cike da mamakin yanda ta fito a hargitse, cikin k'arfin hali Abba yace "Me ya faru?" "Abban su, Ayrah babu lafiya, an kwantar da ita a asibiti, wae cikin ruwa ta fad'a!" Umma ta fad'a muryar ta a raunane. Kusan a tare Abba da Yah Sadeeq suka mik'e kowa tashin hankali na bayyana akan fuskar sa. "Yah Salaam garin yaya?" Yah Sadeeq ya fad'a cikin k'arfin hali. "Ban sani ba, zuwa zan yi na gano lafiyar d'iya ta Abban su" tayi maganar tana zura takalmi a k'afar ta. Kallan Yah Sadeeq Abba yayi yace "D'auko mukulli ka kulle gidan, ku wuce muje dukan mu" Tun kafin Abba ya k'arasa maganar tuni Umma tayi gaba, dan kuwa gaba d'aya ta k'agu ta ga Ayrah ta ga a wane hali take ciki, se dae ita fatan ta d'aya ace yanzun tana cikin k'oshin lafiya kamar yadda Rk d'in ya fad'a mata duk da ta san ya fad'a d'in ne kawae dan ya kwantar mata da hankali. .. Kiran wayar Yah Sadeeq da ya shigo wayar sa shi ne abin da ya tashe shi daga wajen, ya juya ya kalli Ayrah sannan a hankali ya taka ya fice daga d'akin, se a lokacin ya d'aga wayar ya kara a kunnen sa. Daga can 6angaren Yah Sadeeq yace "Mu na cikin Asibitin" "Ohk" kawae ya iya furtawa yana katse wayar, kana ya k'arasa fitowa zuwa harabar Asibitin. Duk inda ya gifta kuwa magana kusan d'aya ce ake bin sa da ita. "Doctor ya mae jiki?" "Alhamdulillah" shi kuma yake bin su da ita kafin ya wuce, har zuwa sanda ya isa inda su Umman suke. Se da ya gaesa da su fuskar sa babu yabo babu fallasa sannan suka rankaya zuwa d'akin da Ayrahn take, kowannen su cike da zumud'in ganin lafiyar Ayrahn. Kusan a tare dukan su suka sauke idanun su akan Ayrahn dake kwance kamar matacciya, ban da numfashin da take ajewa a hankali ba zaka gane rayayyiya bace ba. Dukan su k'arasawa suka yi bakin gadon kowanne na kallan ta cike da tausayawa da kuma tsoron yadda suka gan ta. "Ya Ilahil alameen" Suka kusa had'a baki wajen fad'in hakan dukan su suna cigaba da kallan ta. Kamo hannun ta Umma tayi zuwa cikin nata, zuciyar ta fall rauni ga wani irin tausayin d'iyar ta ta da ya kamata, lamarin ya bata tsoro aenun, musamman da abin yazo a bazata, wanda har hakan seda yasa k'walla ta kawo a cikin idanun Umman, kallan ta take yi sosae kamar ba Ayrahn ba, a zuciyar ta tana dad'a tsarkake Ubangiji yadda a yanzun kana da lafiya anjima kuma babu ita, yanzu dae ga Ayrahn a kwance kamar bata ta6a lafiya ba. "Allah ya baki lafiya Ayrah" Abba ya fad'a jikin sa a matuk'ar sanyaye da yanayin da yaga Ayrahn a ciki, Yah Sadeeq da tun shigowar su ya kasa furta komae se a lokacin ya bud'e bakin sa da ya masa nauyi yace "Ameen" itama k'asa k'asa. Ita kuwa Umma har zuwa lokacin ba tace komae ba dan sosae ta tsorata da yadda ta ga Ayrahn, ga kuma yanda jikin ta ke rawa kamar mara gaskiya. A hankali ta kae hannun ta ta share k'wallar da ta tarar mata a cikin idanu na tausayin d'iyar ta ta sannan karo na farko ta furta, "Ya ilaehi ka bawa wannan baewa ta ka lafiya" tayi maganar muryar ta na rawa. .. Fitowa suka yi daga d'akin, yayin da aka bar Umma a ciki dan ta kasa matsawa ko nan da can ne daga kusa da d'iyar ta ta, se dae kuma hakan ba k'aramin sake karyar mata da zuciya yake ba musamman idan ta ga yanda take numfashi da k'yar se ta ga kamar ba Ayrahn ta ba. Haka dae ta cigaba da zama tana cigaba da addu'o'i a cikin zuciyar ta. Abbu ne yayi sallama a wajen da su Yah Sadeeq suka zauna, dukan su suka amsa masa sallamar, se a lokacin ya lura da wad'anda ke zaune a wajen, take jikin sa yayi sanyi, ban da wannan abin ya faru yau d'in ya so yaje wajen Abba ya masa bayanin komae ya dank'a masa dukiyar da suka ware suke kuma da tabbacin ta sa ce, amma duk da haka hakan be hana shi k'arasawa ya nemi waje ya zauna ba kana yace, "Abban Sadeeq barka da wannan lokaci, ya me jiki?" kallan sa Abba yayi dan be san da zuwan sa ba se yanzun, dan kuwa da yayi sallama be d'auki murya ba. "Jiki Alhamdulillah.." "Allah ya k'ara afuwa" Abbu ya fad'a yana maeda duban sa kan Rk ya tambaye shi ya me jiki, shi ma dae kamar Abban ya amsa masa da "Alhamdulillah" bayan ya gaeda shi. "Amma meye silar fad'awar ta ta ne?" Yah Sadeeq yayi k'arfin halin fad'in abin da ke ta ci masa tuwo a k'warya. Ajiyar zuciya Rk ya sauke kana ya d'an furzar da iska daga bakin sa sannan yace "Bana ce ga dalili ba, amma a iya sani na Ayrah bata da fitina, bare kuma fitinar da ze sa ta shiga cikin ruwa bayan tana da tabbacin bata iya ba, yanda nafi tunani dae wani abin ne ya kae ta wajen may be tsautsayi yasa taje wajen kuma ta fad'a" Rk yayi maganar a sanyaye.. Kuyi manage da wannan. Mhiz Innocent... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* Page 056 ___"Toh Allah ya tashi kafad'un ta" shine abin da kusan dukan su suka had'a baki wajen fad'ar hakan, kafin Rk da Umma dake gefe suka amsa da "Ameen" ... Se wajen maghrib sannan Abbu, Abba da Yah Sadeeq suka bar bakin d'akin da Ayrah ke ciki zuwa masallaci. Sam Ab ba be nuna akwae wani abu da ya ta6a faruwa tsakanin su ba, dan tun da ya riga yace ya yafe komae shikenan a wajen sa komae ya wuce d'in. Se dae shi Abbun da har lokacin ya kasa sakin jiki. Se bayan Isha'i sannan suka fara shirye_shiryen tafiya bayan sun je sun sake duba jikin Ayrah da har zuwa lokacin bata farfad'o ba. Kallan Abba dake shirin wuce motar sa yayi yace, "Amma da kun shigo na kae ku gidan koh?" Abbu ya fad'a yana kallan sa. Girgiza kae Abba yayi kana yayi murmushi yace "A'ah, zamu
Chapter 77 · 0% Book details